Showing 30001 words to 33000 words out of 359620 words

Chapter 11 - Triplets Book 3 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

1960

ɗan bakin nan nata ta yi. "Ni yaya Irfan ka dai'na magana ka yi shiru na ƴan mintoci tukun nan". Shirun ya yi ya biye mata, dama haka take yi wa masoyin ɓoye wani lokaci, sai ta ce mashi ya yi shiru na minti goma, haka zai yi ta zama shiru yana sauraron sauƙar numfashinta, ta koyo hakan ne kuma daga wajen jelly, jelly ce mai wannan sabon iskancin tun tana yarinya, lokacin da suka je Kano, haka jelly take sanya daddy ya rufe bakinsa, ba yadda ya iya haka yake yin shiru har sai ta ce to lokacin magana ya yi, sai ya fara magana, to shi ne ita ma Akila ta koya, sai ta rinƙa cewa Heartbeat nata ya yi shiru kaɗan, yanzu kuma ga shi ta yi wa Irfan, shima ya ɗana.

Shiru ya yi ta zama har tsawon lokacin da ta ɗeba mashi, kafin ya yi magana, a lokacin kuma ta gama tikar kukanta ta share hawaye. Cigaba da hira suka yi, sun biya bashin tsawon kwanaki da suka ɗauka basa waya, sai misalin karfe 10 ta ce mashi tana jin barci, ba dan yaso ba suka yi sallama bayan ya yi kissing na wayar yana faɗin zai yi kewarta, ita ma kissing na wayar ta yi tana mai kara tabbatar mashi a yanzu ma har ta fara kewarsa, da haka suka yi sallama ba dan sun so ba.

Saman bedside drawer ta ɗaura wayar, sai kuma me? Sabon kuka ta rushe da shi, ita kanta ta bata san dalilin yin kukan nata ba, tamkar wata karamar yarinya haka take tiƙa wannan kuka, while ita kuma Ammie tana can tana cika tana batsewa, ta tasa Abba a gaba a kan lallai sai ya nemo mata Imran a daren nan, duk in da ya shiga, maza Abba ya nemo shi, a cikin daren nan zai rabu da jelly dan uwarsa, mamaki Abba yake yi, kullun idan zata zagesu sai dai ta ce Uwarsu ba dan ubansu ba, Ammie duniya mai zaman kanta.

Har karfe shaɗaya ta buga Akila na kuka, kuka kuma da bashi da dalili. Sai misalin karfe shaɗaya da rabi sannan wadda nake da tabbacin saboda shi take yin wannan kukan ya kirata.

Ƙin ɗaukar kiran ta yi, tamkar ya yi mata wani laifin, ashe dai yasan me ya aikata, dan haka sai shi da kansa ya yi received call ɗin, da kansa kuma ya sarrafa wayar tata, ya kara Volume yadda zata ji shi sosai.

"Am so so sorryyyyyyyyyy my heartbeat, ba zan sake ba, dan Allah ki yi shiru Kinji?" Cigaba da kukanta ta yi tamkar bata ji me ya ce ba.

"Wayyo matata, please amin afuwa, dan Allah ki yi shiru, wlh ba zan sake ba, zan iya jurar komai amma ban da hawayenki".

"Meyasa tun ɗazun baka kirani ba?" Ta faɗa can kasa kasa cikin muryar kuka.

"Kiyi hakuri zafin kishi ne yasa ban kiraki ba, na barine sai zuciyata ta ɗan sauƙa, amma na tuba ba zan sake ba, kuma fa heartbeat harda kissing na wayar ke ma kika yi ko? Amma ba komai yanzu dai daina kukan, shi ne babban abin da ya fi damuna". Turo baki ta yi kamar biro, kasa kasa take kunkuni ta yadda ba zai ji ba, tamkar wata ƴar baby, irin idan aka daki yarinya ta gama kukan nan, irin wannan kunkuni da suke kasa kasa da ƴan surutai, shi ita ma take yi.

Hakan yasa ya saki cool murmushi. "My Heartbeat sarkin rigima, to ko dai sai nazo na goyaki ne?". Lumshe idanu ta yi tana murmushi tare da rufe fuskarta ga hawaye a fuska.

"My heartbeat yau kuma ni ake jin kunya?". Gyaɗa mashi kai kawai ta yi alamar e.

"To shikenan ki cigaba da jin kunya ni bani da wata damu, abin da na sani dai shi ne, a ranar da muka yi aure, a ranar zan cire maki kunyar tas na watsar, yanzu dai duk ba ma wannan ba kin ci abinci?".

"E naci kai fa ka ci ne?" "A'a My Heartbeat, ni ban ci ba, kuma ba zan iya ciba har sai naji voice naki, yanzu zan ɗauko muci tare, kina bani a baki". Kayatatcen murmushi ne ya bayyana a kan fuskarta, ba komai ne kuma ya haifar mata da murmushin nan ba face yadda ya yi maganar, tamkar wani ɗan yaro, ya iya shagwaɓa sosai da sosai.

"My Heartbeat Murmushi yana yi maki bala'in kyau". "To dan Allah nima ina son ganin Murmushinka ka ji Heartbeat ɗina?". A shagwaɓe ta yi maganar.

"My heartbeat na yi maki alkawarin zaki ganni, yau ba alhamis ba?" E ta amsa mashi da shi. "To ranar Wednesday zan kawo maki kaina har gida domin ki ganni da kyau, ki kare mani kallo son ranki, ki ɗaukeni videos, ki yi mani hoto, ki ji murya, kiyi yadda kikeso dani gabaɗaya, amma kuma da sharaɗi!".

"Sharaɗin ne?" Ta faɗa cikin zumuɗi. "Idan nazo gida, ko a gaban waye zan gaya maki ina son ki, sharaɗin shi ne ba zaki gudu cikin gida ba, zaki tsaya mu kalli juna cikin ido, ki zuba mani shagwaɓa, ki yi alkawarin yin hakan, idan ki ka yi alkawarin yin haka, to nima zan yi alkawarin tabbas zanzo".

"Nayi, ba dai alkawari ba? To nayi maka, tabbas ba zan gudu ba, zan tsaya mu sha hira ". Ajiyar zuciya ya sauƙe kafin ya ce "Ina nan zuwa my Heartbeat, nima ai nafi son ganinki fuska da fuska, hakan zai fi, yanzu dai tsarabar me kike so na kawo maki?".

"To ai baka gaya mani kasar da kake ba bare na san me da me ne a kasarku har nace ka kawo Mani". "Heartbeat kasarmu ɗaya, a Nigeria nake ai". Shiru ta ɗan yi kafin ta ce "Tom tsarabar goriba zaka kawo Mani ". To ya amsa mata da shi.

Mamaki ne ya kamata, wai har da wani cewa to, shi kuma bai kawo komai a ransa ba, ita kuma ta dage shi ba ɗan Nigeria ba ne, shiyasa ta yi mashi wayo dan ya gaya mata kasarsa ta hanyar cewa da ta yi bata san kasarsa ba, bare ta san tsarabar me zai kawo mata, amma ya ce a Naija yake, ta ce goriba ya ce mata to, anya kuwa da gaske yake yi? Anya ya san wannan goriba kuwa? Amma dai zata gani ai, ba dai ranar laraba ya ce ba, to shikenan ai.

Ta nutsa duniyar tunanin can ta tsingayo zazzakar muryarsa kasa kasa yana faɗin "My heartbeat ki zo na baki abinci a baki kin ji ko?". "Ka bari sai ranar Wednesday idan kazo sai ka bani a baki ɗin". "Are you serious?" Tabbatar mashi da hakan ta yi, sosai ya ji daɗi kamar me, suna hira yana cin abinci a nutse, sai wuraren karfe 2 na dare suka yi sallama cike da kewa da kuma masifar kaunar juna, ba dan sun so rabuwa ba, dare ne kawai ya yi, daren ma dan ita yake tausayawa yasa ya hakura, baya son ta kasa tashi tayi sallar asuba.

GIDAN LION💋

Dare misalin karfe 8, Rimsha, Imran, da kuma Areef, suna zaune a palon sama, Areef dai Alhamdulilah jiki ya yi kyau sosai da sosai, waƴan nan shaiɗanun matsafa sun sake shi da karfin ikon Allah, amma anci kwakwa fa, Lion ya sha baƙar wahala ba kaɗan ba, su TGA sun yi nasarar tarwatsa kunjiyar tsafinsu Josephine ɗin, sai dai sun rasa sojoji da dama, ciki kuma harda babban yaron TGA, shi ma TGA ɗin ya ji ciwo sosai a kefen cikinsa, yanzu haka yana gadon asibiti. To sai dai muche Alhadulillah, an gama da shegun matsafa, yanzu Josephine da Areef sun fita daga koma.

Sai hira suke yi cike da kula, da kuma girmama juna, massage Lion ya yi wa Imran akan RIMSHA ta kai mashi abinci, da alama yau ya ji yunwa sosai, bawan Allah yau yasha wahala sosai gaskiya, kawai mutun ba zai taɓa gane hakan a kan face nashi or a yanayinsa bane, domin kuwa kullum a siffa ɗaya yake idan baku mance ba, amma yau saboda waƴan nan ƴan iska matsafa na jikin Areef ya sha wahala over, dan sai da ya yi wa Areef ɗin dannar yankar rago kafin ya samu ya fara yi mashi addua'o'i da karatun Alqur'ani mai girma, ba ƙaramin dambe suka sha ba, Imran kam guduwa ya yi tun da Areef ya maka shi da kasa sau ɗaya, ita kuma Rimsha tana ɗaki tana sallah tana kuka tana riƙon Allah da ya bawa Areef ɗin lafiya.

Yanzu dan ance ta kai mashi abin bata damu ba, dan tana ganin ɗazun sun wanye lafiya, a shirmenta wai ta fara gane me Saif yake so, yarinya yarinya ce, har izu yau TRIPLETS nasa ma sun kasa iya tantance abu guda ɗaya da yake so bayan kaunarsu, sai ita ce wai ta gano me yake so, to fa mu dai je zuwa.

Miƙewa ta yi ta nufi kitchen, binta da kallo Imran ya yi, ciro wayarsa ya yi domin ya kira tailor da ya bawa ɗin kin kayansu, ya ga ji da kallonta da shigar riga da wando, yana tsoron abin da zai je ya dawo, baya son su yi aikin danasani.

Tabbatar mashi tailor ya yi akan tabbas rana ita yau azo a karɓi kayan, to ya amsa da shi kafin su yi sallama, ajiye waya ya yi suka cigaba da hira da Areef.

A cikin zuciyarta ta yi sallama a bakin kofar kitchen ɗin, annabi ya ce katabbatar da kana yin sallama ne a in da aka san darajar sallama, a in da ake amsata, kada ka yi sallama a in da za'a walakanta sallamar, to shi Mark ai bai san darajar Sallama ba, kuma ba amsata zai yi ba, shiyasa take yi a cikin zuciya, karisawa cikin kitchen ɗin ta yi, sannu ta yi mashi, tamkar babu shi a cikin kitchen, kamar dai yadda suka saba, bai ɗago kai daga abin da yake yi ya kalleta ba, haka zalika, bai amsa sannun da ta yi mashi ba, kamar wani mai aljanu, ɗazun ya yi mata magana da bai taɓa yi ba, yanzu kuma ta yi mashi yaki amsawa, to Allah ya shirye shi.

Wucewa ta yi ta wanke hannunta kafin ta ɗauki abin nasa, har lokacin tamkar babu Mark a cikin kitchen ɗin nan, ficewa ta yi abinta, sanye take da wandon jeans baki ya kamata da ga sama har kasa, jikin wandon akwai kyalli sosai farare a jiki, sai ta sama kuma, top mai dogon hannu ta sanya, launin maroon color, ba karamin kyau ta yi ba, kamar kullun hijabin ɗan karami mai taken please call me ne a jikinta, bakin hijabi ne kalar wandon, kafarta na sanye da takalma flat shoe Maroon color, sai tashin kamshi nata perfume ɗin take yi.

Sallama ta yi mashi a bakin kofar ɗakin, yana zaune saman sofa set yana latsa wayarsa, jin ya yi shiru ne yasa ta kutsa kai cikin, tana mai kara kwaɗa wani sallamar.

A wannan karon ma saura kaɗan ta saki tray ɗin abincin saboda razana da kallonsa da ta yi, sai dai Allah yasa ta riƙe abincin da kyau sosai, hakan yasa bai ɓare ba. Sanye yake da kayan barci, wando dogo har kasa, sai riga mai guntun hannu, damatsan hannunsa suka firgitata, domin gajartar hannun rigar ta bayyanar da su a waje, kamar dai kullun kunsan yana tashin wannan fitinannen kamshin nasa, da alama yau barci yake ji da wuri, Shiyasa ya buƙaci abicnin da wuri haka, ga alamar hakan ka a face nasa, sai lumshe idanu yake yi, gashin kansa a kwance, ta zubo mashi a fuska kasancewar ya sunkuyar da kai a kan wayarsa.

A in da ta saba ajiye mashi abin cin, a nan ta ajiye mashi, saboda neman magana irin nata har da wani ce mashi good evening, ai ko tamkar babu shi a cikin ɗakin bai amsa ba.

Ganin hakan yasa kawai ta fara zuba mashi abinci, sai da ta zuba rabi ya sauƙo daga saman sofar ya dawo wajen da yake zama dan cin abincin, ya zauna, abin da ya bata mamaki shi ne kafin ya zauna sai da ya yi bismillahi, tana jiyoshi ya yi kasa kasa, kenan hakan ya nuna duk wasu dokoki da wasu abubuwa da suka danganci addin dan korar shaiɗan a kusa da mutun kenan yana yi, kuma yasan su fa, amma meyasa baya amsa sallama na? Ta tambayi kanta, abin da bata sani ba shi ne, kamar yadda ya yi wannan bismillahi yanzu, to fa haka yake amsa mata sallamarta, sai dai maganar tasa ce idan ba'a kusa da shi sosai kake ba, ba ji zaka yi ba.

Bayan ta gama zuba mashi ta tura mashi abincin a gabansa, ba ɓata lokaci ya ɗauki spoon ya fara cin abincin nasu, wani irin kalar green ne abinci, ita ko kallon abincin ma bata son yi, sai mamaki take yi, abin cin wani gubar wani, su kuma nata abincin ne suke jin ko da me sun yafe cin shi.

Spoon ɗaya ya kai bakinsa, da kyar ya haɗiye abinci, kawai ma dan baya son dawo da ita ne yasa ya haɗiye da kyar ɗin, ta lura da hakan, da mamaki take satar kallon shi, ko me ya faru da abincin Oho.

Ajiye spoon ɗin ya yi tare da ɗaukar wayarsa, kasa ya yi da kansa yana latsawa, zuba mashi idanu kawai ta yi tana kallon yadda ya kara ɗaure fuska sosai, dama yaya lafiyar kura bare kuma ta yi zawo, tabbas akwai abin da ya faru da abincin, wannan irin uban ɗaure fuska da ya yi haka ba'a banza ba.

Nan take wani irin tsoron shi ya dira mata a ranta, ji take yi tamkar ta tashi ta gudu, dan ganin ya kara ɗaure fuskar, suna a haka Mark ya shigo ɗakin ya same su, hannunsa rike da bowl mai ɗan girma, gabansa ya zo ya ajiye bowl, ba tare da ya yi magana ba ya juya ya koma wajen hukuncin da aka yanke mashi yanzu, shi mai girkin ma first.

Da mamaki take kallon pepper dake cikin bowl ɗin, an wankesu da kyau, ga su fresh, ta rasa me hakan yake nufi, me kuma za'ayi da su.

Miƙewa ya yi, ya koma saman sofa ya zauna, gently ya ce ta cinye attarugun nan dukka, zaro idanu waje ta yi, yau ta shiga uku laifin me tayi? Ta tambayi kanta da kanta, abin da bata sani ba shi ne, abinci da ta kawo mashi, yau Mark ya yi kuskuren da bai taɓa yi ba, yaji ta kubce a cikin abinci, shi kuma Lion kwata kwata baya cin yaji, komai kankantar ta saboda gym da yake yi, idan har ya ci yaji takan iya yi mashi mummunar illar a jiki, kuma tun kafin ya fara gym ma, shi baya haɗa hanya da yaji, ba'a taɓa yi mashi girki da ya ji ba sai yau, Mark ya yi kuskure, kuma yau kamar ba lafiya ba, sai bai ɗan ɗana abincin ba, haka ya shiryawa ogan nasa, to ita laifin kawowa kawai ta yi shi ne a kace ta ci attarugun, shi kuma Mark na shi hukuncin wa iya zubillah kwakwalwa ba zata ɗauka ba, kuma babban abin haushin shi ne ma zai hukunta kansa, idan kuma ya yi ɗaya ba daidai ba yasan halin ogan nasa, bai ma isa ya tsallake ba. BABBAR MAGANA MAI GIRKA ABINCI DABAN WAƳAN DA HUKUNCI KE SHAFA SU MA DABAN, KENAN KO MAI KANKANTAR SA HANNUN DA MUTUN YAKE DA SHI A WAJEN YI WA LION KUSKURE YA SHIGA UKU TAB ƊI JAM!!!.

Hawaye ta fara yi tare da fara ɗaukar attarugun tana kai wa bakinta, har ga Allah ita ma ba ma abociya cin yaji bane, bata ci ko kaɗan a baya, ɗan zamanta a gidansu Kausar ne ma ta ɗan koyi cin yajin, kunsan Yarabawa da shegen son yaji kamar me, to a nan ta ɗan koya, amma a gida wajen mummynta, bata ci, mummy ma bata ci ne yasa bata sanya masu a cikin abincin, yau ta ga tashin hankali iya ganin idon ta.

Kwara ɗaya ta ci harshenta ya ɗaye ya yi jawur kamar wuta, kai gaskiya punishment ɗin soja Bala'i ne, shi saboda sun wahala wajen horo, sai ya rinƙa ganin kamar kowa ma irin sane, sai ya rinƙa ganin kamar komai ya yi wa fararen kaya daidai ne, saboda shi already ya hororu, abin da bata sani ba, duk abin da kake yi, zakaga kowa ma tamkar haka take yi, walau mai kyau walau mara kyau, shiyasa idan sojoji suna hukunta mutun, zaka samu hukuncin na da bala'in tsauri fiye da tunanin mai tunani, su kuma normal ne a wajensu.

Tana hawaye ta ɗauko na biyu, ga shi har guda goma ne a cikin bowl ɗin, alama ya yi mata da hannunsa ba tare da ya kalleta ba, akan ta ɗebo ruwan tea nasu mai jafi ta rinƙa korawa da shi, TASHIN SENSE bala'i kan bala'i kenan, zafi kan zafi, ruwan zafi haɗe da attarugu, eyya i pity you RIMSHA, Lion ya kware wajen horarwar mugunta, ba kalar da bai iya ba, attarugun ita kaɗan ta ma yaya bare kuma da ruwan zafi, ya ilahi ya lillahi.........😭

Haka ta ɗebo ruwan tea ɗin, ga shi ya haɗu mata da bata son green tea ɗin nan nasu, wlh yarinyar nan ta yi kuka ne har idanunta suka kumbura, shi kuwa tamkar babu shi a cikin ɗakin, Areef Imran suna Palo, kuma shi Areef ya san me yake faru, abin da yasa bai tinkari Lion ɗin ba, yasan idan ya je ba ƙaramin faɗa za su yi ba, saboda Lion ɗin yana jin yunwa sosai, yana son cin abinci ya yi barci saboda ya gaji, sun ɓata mashi rai sosai, a yadda yake nan babu uban da ya isa ya kwaci Rimsha da Mark a hannunsa har sai sun lashe hukuncin nan tas, to yasan idan ya je fa ba ƙaramin faɗa za su yi ba yau, to wai ita Rimsha me laifinta ne? Dan kawai ta kai mashi abin? Ita ta girka ne? Ita da kitchen ɗin ma bata shiga har sai idan zata je ɗaukar abinci, amma saboda bakar zuciya na fitar hankali shi ne har da haɗawa da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login