Showing 165001 words to 168000 words out of 359620 words
da sahibinta dan tun ɗazun yake ta tura mata saƙonnin soyayya da su flowers ta WhatsApp.
"Abban Imran bari mu haura sama da matar Imran ina zuwa". Cewar Ammie, ta kai karshen maganar tare da miƙewa ta riko hannun jelly'n dan ta mikar da ita, bayan ta miƙe ta ɗan rungumota suka nufi sama, dan ta san matsalar, Jellyn bata shiga ruwan zafi mai kyau bane, daga ita har Imran ɗin ba wanda ya yi tunanin idan ta shiga ruwan zafi tana gasa gaban nata da kyau zata sami sauƙi. Suna haurawa sama su kuma su Imran suka fara gaishe da Abban.
Bedroom nata ta wuce da ita, saman bakin gado ta zaunar da ita kafin ta nufi toilet, sai sannu take ce mata, ruwa mai zafi daidai ta haɗa mata tare da zuba mata wasu sinadarai nata da take amfani da su, ciki har da man zogale, da man zaitun, na tane wadda ta jima take amfani da su tun kafin ta sami wannan matsalar, bayan ta samu matsala bata amfani dasu, jiya Abba ya sake sayo mata su tun da ta dawo cikin hayyacinta, sai ta cigaba da amfani da su kamar da, suna gyara mace sosai, bayan ta kammala, daga karshe ta zuba mata ruwan jikakken sassaken mangoro da take jiƙawa, dan yana matikar kashe sanyin gabar mace ba kaɗan ba, bare ma ita jelly da take yanzu aka buɗeta, tana buƙatar ire iren su dan kada a sami wata matsala.
Dawowa cikin ɗakin ta yi, da kanta ta cire mata kayan jikinta, Jellyn bata yi mata kaddama ba, dan idan baku manta ba, ita jelly rainon namiji ne, duk da daddyn ya tsawatar mata a kan wada ta yarda wani ya taɓata ma bare ya cire mata kaya, amma ta san wannan maman Imran ne babu damuwa, kuma ita jelly bata da kunya ko kaɗan, shi ne yasa bata yi wani gardama ba, ta tsaya ta cire mata komai tas, ya rage daga ita sai pant ta kama hannunta zuwa cikin toilet ɗin, Allah sarki duniya kenan, yau ta sami sabuwar uwa, Allahu Akbar Allah mai yin yadda ya so da bawansa, ya bashi a lokacin da yake so, ya kuma karɓa a lokacin da yake so, ya karɓi mahaifiyarta tun ranar da ta zo duniya, yau kuma cikin ni'imarsa ya sake bata wata uwar, ba abin da zamu ce sai dai Alhadulillah.
Sai da suka isa bakin baf ɗin ne ta tsaya ta cire mata pant ɗin nata kafin ta ce to ta shiga, da yake jikin nata dai ba kwari, bata musawa Ammie ba, sai okey kawai take binta da shi, da yake da turanci Ammien take yi mata magana.
Da kyar ta iya zama a cikin ruwan saboda zafin shi, sai Weldon Ammien take ta ce mata, ganin ta ɗan jima ruwan yana ratsata sosai ne yasa Ammien ta fita zuwa palon kasa, hira ta samesu suna ta zubawa.
"Akila ta shi ki kawo mini kayanki ɗakina yanzu". "Okey my Ammie" . Ta amsa tare da miƙewa ta nufi saman. Dawo da kallonta a kan Akil Ammien ta yi tana faɗin "Son kar dai ka gaya mini abin da nake hasashe gaskiya ce?". Da sauri ya ɗago yana kallonta da mamaki "Ammie me kike hasashe kuma?" "Matarka ciki gareta mana". Ɗan kasa ya yi da kansa yana faɗin "E Ammie gaskiya ce, zai kai wata wajen biyu ma yanzu". Zaro idanu ta yi tare da nufar in da Umaisha ɗin take zaune tana faɗin "Wayyo shi ne a rasa wanda zai yi mini albishir a cikin ku? Ni yau ina zan saka kai'na saboda tsantsar farinciki, Allah nagode maka, ya Allah Alhadulillah". Tana magana ta rungume Umaisha ɗin sosai tana mai jin tsantsar farinciki, ita kuma Umaishar ta kasa sakin jiki da ita, sai ɗan murmushi da take yi, a zahirin gaskiya tsoron Ammie take yi kamar ta mutu, dan ma tafiyar Ammie sama da ta yi da jelly Abba ya ɗan yi musu bayani a kan abubuwan da suka faru a baya Ammien bata cikin hayyacinta ne, amma duk da haka ita ta kasa sakin jiki da Ita.
Ammie kuwa yau murna a wajenta ba'a magana, Imran ya angwance, ya kawo mata jinyar amayar tasa, shi kuma Akil ya kawo mata tsarabar yaron ciki, kai abin sai godiya, yau murmushi bakinta yaki rufuwa, sai godiya take zubawa Allah tare da kirari mara adadi, haka ta tasa Umaisha a gaba a kan me zata ci? Me take jin ƙoɗayi? Me baby yake so? Ta faɗi koma me ne yanzu aiki da gamawa za'a kawo mata, to da yake na gaya muku Umaisha ta kasa sakin jikinta, sai ta rinƙa nokewa tana faɗin babu komai, babu abin da take so, kuma a zahirin gaskiya tun da suka shigo da ta ji kamshin girkin Ammien take haɗiyar yawu, cikinta har wani kulle mata yake yi saboda yadda daddaɗar kamshin yake dukan hancinta, burinta kawai ta ci wannan girki, sai dai kash ta kasa sanar da kowa abin da yake ranta, ta so su keɓe da mijinta ta gaya mishi, amma ba hali, yanzu kuma an tambayeta me take so ta kasa faɗa ta ce babu komai.
Sai da Ammie ta yi maya tambaya yafi baki goma, amma amsa ɗaya, shi ne babu komai, sai da Abba ya ce wai ta kyaleta mana ko dole sai ta cusa mata sha'awar abu ne, sannan ne ta kyaleta ta koma wajen jelly dan ta dubata. Kamar yadda ta barta haka ta dawo ta sameta, ruwan ya yi sanyi, riƙo hannunta ta yi tare da taimaka mata ta fito daga cikin baff ɗin ta tsaya a gefe guda, buɗe ruwan Ammien ta yi ya fita tare da haɗa wani mai ɗan ɗumi ta ce ta shiga bari ta yi mata wanka, ba musu ta shiga, Ammie da ƙoƙari tas ta kwanketa, dan ita gani take Akila ma bata wuce ta kamata ta yi mata wanka ba, kunga Akila kuma ai ta girmi jelly wajen da shekaru uku kenan.
Bayan ta kammala ta tsaneta da toilet tare da ɗaura mata mai ɗan girma a kirjinta ta ja hannunta zuwa cikin ɗakin, gaban mirror ta tsayar da ita a in da ta shafe ta da mayuka masu kyau da tsada, sannan ta zuba mata turaruka masu kyau da daɗin kamshi kafin ta ɗauko kayan da Akila ta ajiye mata a saman gado ta dawo gaban mirror, har da bra Akila ta kawo mata, dan haka sai ta shirya ƴar tata tsab tare da sanya mata bra ɗin, dama suna nan tula tulan ba a sanya bra bama, da aka sanya ba'a magana, sai suka kara cika waje, simple make up ta yi mata tare da kara fesa mata turare a saman doguwar rigar tata da ta sanya mata, ba karya ta haɗu iya haɗuwa, yafa mata gyalen rigar ta yi tare da riƙo hannunta suka nufi palo, Masha Allah yanzu kafan nata ya sake mata, gaba nata ma ya dai'na yi mata zafi, ya dawo dai'dai.
Tun daga suka sako kafarsu a saman benen Imran ya zubawa tauraruwar tasa idanu, ta yi kyau ba karya, ji yake yi tamkar ya tashi ya rungumo kayarsa, amma ina ba hali, dole ya danne dan saboda su Abba, kuma ya ga ma sai harararsa ta gefen ido take yi, da alama zasu sha dirama ba kaɗan ba, dan fushi take yi da shi.
Saman sofar da Umaisha take Ammie ta zauna tare da zaunar da ita a gefenta, ya zama da Jellyn da Umaisha sun sakata a tsakiya, ita kuma Akila ta je ta tada kai da cinyar Abba tana aikin latsa waya, shi dai Imran ya san latsa wayar me take yi, dan shi ya haɗa komai, yana taya kanwar tasa murnar samun ɗaya daga cikin TRIPLETS da ta yi, yasan zata more ta ji daɗi, hankalinta zai kwanta sosai, zata sami soyayya mai tsabta wadda babu mix, dan duk TRIPLETS basu karya kuma basu yaudara, idan suna son abu, to zasu yi mushi mahaukacin so ne, za kuma su zage dantse sosai wajen kula da duk wani motsin wannan abin, ga dai misali a kan ita Akilar, duk wani motsinta Aseef yana sane da ita, kuma yana matuƙar kulawa da ita over, to haka suke idan suna son abu, idan kuma suka tsani abu, to fa wannan abin ya shiga uku, zai sha bakar wahala ba kaɗan ba, dan ko ganin mai kama da shi suka yi sai sun zage shi, haka suke, shiyasa Imran yake tayata murna na samin Aseef a matsayin masoyi da ta yi.
Kada ku manta duk in da Akila zata je tana rungume da wannan teddy ɗin nata na tsarabar masoyin nata, a ɓangaren Umaisha kuwa, ta ƙosa kuma ta matsu Ammie ta ce azo a ci abinci, rashin sani yafi dare duhu, ita kuma Ammie da yake bata sani ba, sai bata kawo zancen abincin bama kwata kwata a kanta, dan a nata ganin yaran nata ba baki bane, idan suna son cin abinci ai dole su nufi table su ce a zuba musu, to ita kam Umaisha ta gasu, tsoron ma magana take yi dan kada ya zama laifi, Ammien ta daketa, Allah sarki.
Haka suka rinƙa zuba hira cikin nishaɗi har sai da lokacin sallar issha ta yi, a tare Abba, Imran, AKil, suka nufi masallaci, su kuma matan suka haura sama, Akila, Umaisha, suka nufi bedroom ɗin Akilar, ita kuma jelly Ammie ta riƙo hannunta suka nufi nata ɗakin.
A ɓangaren gidan Abbi kuwa, bayan wasu ƴan kwanaki, gabaɗayansu zaune suke a palo, Ayla ta tada kai da cinyar mijinta tana lumshe idanu tamkar mai jin barci, Aunty ma hakan ne, ta tada kai da cinyar Abbi tana kallon Tv, maman Ayla tana zauna saman nata sofa daban suna kallon labaran safe a Tv, har wani haske ta kara ta yi kyau kwana biyu da ta yi a gidan, tana samun hutu ga cima mai kyau, nan take ta fara murmurewa tana kiba abinta, ashe ita Ayla ta biyo wajen yin ƴar ƙiba, Hanan tana zaune kusa da maman Aylar tana latsa wayarta, da alama dai chatting take yi, suna cikin matsananciyar nishaɗi ba kaɗan ba, Irfan yana zaune kusa da daddyn Jelly amma ba a kujera ɗaya ba, kowa da nasa kujerar, kowa da abin da yake yi, Ommu wato Hjy Hadiza tana cikin bedroom nata tana barcin asara da ta saba yi.
Gyaran murya Abbi ya yi tare da fara magana a nutse "Yanzu ya mata ki bamu labarinki, da kuma labarin Aliya tun da kin ɗan huta ai ko?". Shiru ta ɗan yi, sai dai ga dukkan alamu ta shiga damuwa jin tambayar Abbin, amma bata da zaɓi dole ta basu labari,. Ɗago kai ta yi tana ƙoƙarin fara yin magana sai suka ji sallama daga bakin kofar shigowa. Har suna haɗa baki wajen amsawa, A'A SALAHUDDEEN ne ya shigo, sai murmushi yake yi, jikinsa na sanye da wata danƙareriyar shadda mai bala'in kyau da tsada launin sky blue, ya sha bakar hula da bakar takalmi, ɗinkin half jampa ne, ba karya ya fito ya yi kyau sosai abinsa.
Karisowa cikin palon ya yi, sai sannu da zuwa suke yi mishi, yauwa ya rinƙa amsawa da shi, kusa da Irfan ya zauna tare da miƙawa Irfan ɗin hannu dan su gaisa, miƙo mishi ya yi suka gaisa, daga nan ya ɗagawa su Abbi ma gaisuwa, da fara'a ɗauke a kan fuskar ko wannensu suka amsa mishi da lafiya, Hanan ta ɗaga mishi gaisuwa bayan sun gama gaisawa da su Abbi kenan, shi ma da fara'a ya amsa mata.
Shiru palon ya yi kowa da abin da yake tunani, can A'A ya katse musu shirun da tambayar daddyn Jelly ina ƴarsa take? Wato jelly, cool murmushi ya saki yana faɗin "Jelly tana can wajen mijinta ai". Ɗan zaro idanu ya yi, sai kuma ya yi kasa da kai yana faɗin "Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun yanzu rashin zumuncinmu har ya kai Jalila ta isa aure ban sani ba? Kenan yanzu zan iya haɗuwa da ita a hanya ban gane ita ɗin bace fa na wuce, kai amma abin bai yi mini daɗi ba, amma dai dole a wannan karon zan je na kalleta dan gaba, dan kuma mu gyara laifin da muka yi a baya, gaskiya ban yi wa Aunty Umaima adalci ba". Irfan ne ta caɓi zancen da cewa "E gaskiya kam baka kyauta ba". "Rufe mini baki, ba duk haka kuke ba". Cewar Abbi, shiru ya yi yana ɗan sosa kai, dan kuwa yasan haka suke, shi yanzu bai san ya kalar ƴaƴan Azharuddeen Bature wato su Anaya suke ba, zai iya haɗuwa da su a hanya ya wuce su wuce bai san su bane, gara A'A ma ace basu gari ɗaya, shi kuma da shi da su Anaya gari ɗaya unguwa ce ta raba, to ko yayan su Anaya ɗin Feroz da ya kasance babba ma, matashin saurayi kamarsu bai san shi ba bare mata yara dake cikin gida, haka zalika bai san ko ɗaya daga cikin ƴaƴan Hjy Batula ba, shi su Imran kawai ya sani, dama daddyn Rimsha kam ba'a sanya ƴa'ƴansa a lissafi, dan saboda babu wanda ya san shi ne ma Hossain... Matasa kuji tsoron Allah ku daina zubar da zumunci, wlh gaskiya ce zumunci tana hana bawa tsallake gadar siraɗi, to kada ku yarda ku zama ɗaya daga cikin waƴan da zumunci zai riƙe a ranar gobe kiyama, ku kasance masu ziyartar ƴan uwanku, dayawa daga cikin matasa da sun girma dai shikenan, sai su watsar da kowa, suna ganin kamar zubar da girma ne zuwa gidan kawune da bappanu, hakan ba dai'dai bane wlh, kuskure ne babban ku ke yi, yana da kyau ku gyara dan mu gudu tare mu tsira tare, Allah ya bamu dacewa, mu dai mata ko dan biki muna sada zumunci, mu an san mu da zumunci ba karya.
Sai wani sunkuyar da kai suke yi, A'A ne ya ce "Gaskiya dai Abbi dukkanmu mun yi babban kuskure, dan haka ya zama dole yanzu mu gyara da izinin Allah". Caɓe zancen Irfan ya yi da cewa "E gaskiya kam, ni yanzu ma weekend zan shirya na je Maiduguri wajen gwaggo Batula, idan na dawo zan yi yawo a gabaɗaya dangi har Bauchi zan je dan na gyara kuskurena". "Ba zaka je har kasar Russia bane sai iya Bauchi kawai? Ya kamata ka je ka gano mana ƴan uwan mummy ai". Cewar daddyn Jelly, ya yi maganar cikin zolaya.
Zaro idanun nan nasa na gado ya yi yana faɗin "Russia kuma? Ai sai dai a mafarki, yadda kuka bani labarin ƴan uwan Barrister Naurat ɗin nan balaƴaƴƴu ne, ina ni ina tinkararsu, salon su sauke haushin musuluntar da ita da Dr Salman ya yi a kai'na, su kamani su peɗeni da raina, bappa Maik kasan fa har ƴanzu nasan mugu mugun haushin gabaɗaya family'n Dr suke ji, tsoho ya rasu ya barmu da gaba mara iya ka, ai tsakanina da Barrister sai dai nayi mata addu'a wlh, Allah ya jiƙanta a koma ina take, amma ƴan uwanta, ni ban ma sansu ba, kai kaddara ma bamu da wata alaƙa". Dariya gabaɗaya palon suka saka A'A yana faɗin "Wlh da gaskiyarka, kasar Russia ba wasa ba, yanzu idan ka kawo musu wargi za'a ɗauki gawarka, bare ma Dr da ya yi babbar laifi ya shiga ya ɗauko ƴar cikin kasar ya musultar da ita ya kuma kawota Nigeria, tab ai akwai kura ba kaɗan ba, ku da shiga Russia sai dai a Tv wlh".
Shi da Abbi da daddyn Jelly sai murmushi suke yi, dan sun san fin haka ne ma zata faru idan jininsu ya tinkari ƴan uwan Barrister, domin sun san ƴan uwan nata a manya manyan abokan gaba suke ɗaukarsu, babu yafiya, ko yanzu suka je suna iya kashesu har lahira, kuma sun kashesu sun kashe banza, babu mai tankawa dan su ƴan Nigeria ne bakaken fata a cewar ƴan uwan.
"Abbi ni fa magana nazo nayi da kai". Cewar A'A, yana magana yana wani sunkuyar da kai kasa, "To Ahmad in zo kenan ne?" Girgiza kai ya yi yana faɗin "A'a Abbi a nan ma ya yi, zan iya maganar ai, zan fi jin daɗi nayi a gaban kowa, sannan ga yaya Maik a kusa". "Okey tom ina jinka".
Shiru ya ɗan yi kamar mai wani tunani, can kuma ya ce "Dama Abbi auren ƴarka nazo nema, a gaskiya ba zan ɓoye maka ba ina sonta, tun last zuwana da nayi, na kasa faɗa maka ne kawai, amma yanzu naji ba zan iya cigaba da ɓoyewa ba, gara nazo na nemi izini kawai". Yana magana yana kallon Hanan dake ta faman buga game a waya, miƙewa zaune Aunty ta yi tana faɗin "A'a gaskiya, ai auren Hanan a wajena za'a nema ba wajen Abbi ba, ni zan bada ita". Jin an ambaci sunanta yasa ta ɗago kanta, karaf sai cikin idon A'A, kawar da kallon nata ta yi zuwa kan Aunty, dan ita bata ɗauka ma zancen a kanta ake yi ba idan ba da ta ji Aunty ɗin ta yi ambaci sunanta ba.
Daddyn jelly ne ya katse su da cewa "Kai duk ku lafa haka nan, Hanan dai ƴata ce, kuma idan har tana son kanina Ahmad to na bata, Ahmad ga Hanan ka tambayeta idan tana sonka to shikenan, ka kawo mini sadakinta ni zan isar da shi Katsina da kai'na". "Wannan gaskiya ne, Ahmad ga Hanan idan tana sonka, to zamu shige maka gaba zuwa Katsina, nasan ba za'a hanamu aurenta ba". Cewar Abbi. Shiru palon ya yi kowa ya zubawa Hanan da A'A idanu, sai wani kasa da kai take yi, shi kuma ya tsareta da ido babu ko kyaftawa.
Hanan, ya ambaci sunanta, kin ɗago kai ta yi, sai ma kara kasa da kai da ta yi, abin ku da jinin Turawa, su Abbi dukkansu babu kunya a lamarinsu, duk Naurat suka biyo, idan baku manta ba su Turawa dama haka suke, a gaban iyaye ake shan soyayya, suma iyayen a gaban ƴaƴa suke shan love nasu son ransu, to shi ne yasa abin sam babu kunya a cikinsa, su