Showing 312001 words to 315000 words out of 359620 words

Chapter 105 - Triplets Book 3 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

1953

na ne da aure, da yake ni ban san cewa shi ne Anwar yake yi wa aiki ba, sai na karɓi soyayyarsa, mun yi soyayya sosai amma kusan zan ce muku soyayyar ta sirri ce, dan har mamaki nake yi watarana a kan baya taɓa zuwa wajena da rana sai da daddare, yana yin abu tamkar mara gaskiya, kuma a lokacin sam bai shiga siyasa ba.

A hankali yana jana da kalamai na yaudara irin na mazan banza da idan suna son abu a wajen mace ba irin kwatar da murya da marairaicewa da basu yi, tun ina ɗari ɗari da shi har na saki jiki muna hira tare da zuba soyayya, karatuna ya ja baya sosai saboda kayan mayen da nake sha, sam kwakwalwata bata ɗaukar karatu, da anyi karatu after 10 mins na mance komai, na zama wata iri da ni, haka zalika ita ma Maryam ta zama sai a hankali, ita kam Abida dama ai ta saba, so bata jin komai, su mamana kuwa, sai na fi sati ban nemesu a waya ba, sai idan su suka gaji da kansu suka kirani, idan na ɗauka sai nayi musu karya na ce musu wlh lectures ne suka ɗauki zafi yanzu, abubuwa ne sun sha kai'na, suna yi mini uzuri, haka mama zata yi ta yi mini nasiha duk a banza, dan a wannan lokacin nasihar ma sam bata shiga kai'na, a yanda nake ma ji nake yi mama fa tana takura mini, idan kuma ta cigaba to watara zan buɗe mata aiki ko da tawayar ne.

Haka muka cigaba da rayuwa har Abubakar ya fara cewa na raka shi shopping da sauransu idan ya zo Zaria, ba a Zaria yake ba zuwa yake yi, ni ban san garin shi ba daga farko, sai daga bayana na san cewa shi ɗan Kano ne, da tafiya ta yi nisa ne ya gabatar mini da kaninsa Farooq duk dan na kara yarda da shi sosai, ya kuma yi sa'a dan na kara yarda da shi over, na saki jiki aurena zai yi da gaske kamar yanda yake faɗa, haka zan raka shi shopping muje mu dawo lafiya lou, wani lokaci ma tare da Farooq ɗin muke zuwa, so yana da gidan hutawa a Zaria, a lokacin sau ɗaya da muna dawowa daga shopping ya ce mu biya ta gidan dan mu ɗan huta, to a nan ne nasan da gidan.

In takaice muku labari Abubakar da Farooq sai da suka yaudareni suka zuba mini kwaya a cikin abin sha a cikin school namu da ya zo muna hira da shi, tare da Farooq suka zo ranar, sun saka mini kwayar barcin bayan na sha na yi barci a cikin motar ne suka ɗauke ni muka fita zuwa gidansa, ban taɓa kawowa zai sanya mini kwaya a abin sha ba, na yarda da shi sosai da sosai, hakan yasa nake karɓar abin hannunsa na sha.

Ban sake sanin in da kaina yake ba tun da na sha lemun da ya bani sai farkawa na yi na ganni a cikin ɗakinsa na gidan hutawarsa, shi kuma yana kwance kusa da ni yana barci abinsa, ya bani kwaya na sha na yi barci ya lalata mini rayuwa, ya yi mini fyaɗe, na yi kuka sosai, ban da mamana babu wanda nake tunani, na san idan ta san da haka zata iya mutuwa, ta bamu tarbiya iya karfin iyawarta. Ko da na tashe shi daga barci sai ya nuna mini ai ba wata matsala ni matarsa ce In Sha Allah, yaudara ta ɗan bariki, da naki yarda ina ta kuka sai ya kira Farooq ya zo suka haɗu suka yi mini daɗin baki har na sake yarda da shi.

Haka muka cigaba da rayuwa, mun cigaba da zuba soyayya tamkar ba gobe, bayan shi ni bana kula kowa, bai canza mini ba bai kuma gujeni ba har sai da ciki ya bayyana a jikina, nan fa rikici ya ɓarke a tsakaninmu, ya ce shi wlh ba cikinsa ba ne, ni kuma nasan shi kaɗai ne na taɓa kwanciya da shi, nan fa ya ce shi wlh ba cikinsa ba ne na nemi uban cikina kuma shi ya fasa aure na dan ba zai auri ragowar wasu ba, amma taimako ɗaya zai yi mini shi ne ya bani makudan kuɗaɗe na kuma zubar da cikin ko zan sami mijin aure, dan babu wanda zai aure ni idan ya ganni da ciki ko kuma ya ji labarin na taɓa yin ciki, to rufin asirina shi ne na zubar, ni kuma na kafe na ce wlh ba zan zubar ba, nan ne fa ya yi yunkurin kashe ni, ya aiko wasu maza biyu dan su kashe ni, Allah ya tseratar da ni, na sha da kyar.

Sanin cewa shi ya aiko a kashe ni yasa na tura mishi da sakon Video da na ɗauke mu ni da shi a gidan hutawar tasa muna shan soyayyarmu, ina da ire iren videos ɗin da yawa dana ɗauka ba tare da saninsa ba, ganin video yasa hankalinsa ya yi mummunar tashi, a karo na biyu ya sake aikowa da a rufe babin rayuwata, da Allah yasa nan ma ina da rabon rayuwa a gaba, na tsira sanadiyyar ƴan'sanda da suka fito patrol, hakan tasa na haɗa kayana na koma Bauchi dan na je na reni cikina, na yi alkawarin wlh ba zan zubar da cikin ba sai na haifa, ina komawa Bauchi nan kuma babana ya ce wlh wane ubana, sai dai na koma in da na fito, ba zan zauna mishi da cikin shege a gida ba, ace yana matsayin babban malami a unguwa kowa yana girmama shi kawai sai ƴar cikinsa na ɗauke da cikin shege!, Na zubar mishi da mutunci, to wlh ba zai yi wu ba, na yi maza na je na nemi wani uban shi ya sallamani wa duniya, haka yayanmu babba ma ya rinƙa zagina, mamana ce kawai take ta kuka tana bawa babana hakura a kan ya hakura idan na tafi yanzu ina zan je? Fir babanmu ya murje idanu ya ce duk in da nake so na je amma ba'a gidansa ba.

Haka na kwashi jiki na koma cikin Kaduna, da kuɗin da Abubukar ɗin ya bani na kama gida na zauna a in da na cigaba da renon cikina, muna zaman mutunci da ƴan unguwa, dan a tunaninsu ni bazawara ce da mijina ya rasu ko muka rabu, a yanda suke ganina da mutunci babu wanda yake yi mini kallon mai cikin shege. Bani da kowa haka na zauna cikin kunci tare da kewar kanwata da mamana, Allah sarki kanwata ko kallon karshe ba mu yi wa juna ba, lokacin da na je gida tana makaranta bata sani ba, shi ne yasa dana haifi ƴa mace na yi mata takwara Aliya ina kiranta Ayla, ko kaɗan banga laifin babana ba, domin kuwa da farko baya son naje makarantar, ni ne nan na kafe zan je, sai da muka yi yarjejeniya da shi a kan zan tsare mutunci na, sannan ne ya barni na je, amma na rusa komai.

Haka na cigaba da rayuwa komai yana kare mini, duk kuɗin da Abubakar ɗin ya bani suna ta karewa dan ba juyasu nake yi ba, sai dai na zara na kashe, har ta kai ta kawo bani da abincin da zanci, kuɗin haya ya kare, ga Ayla tana karama bata fi shekara ɗaya ba lokacin, bani da zaɓi dole na kwashe gabaɗaya videos ɗin da na yi wa Abubakar daga kan wayata na zuba a cikin memory card a in da na ɓoye memory a wani wajen da na san ko yanzu na je wajen memoryn na nan, shi kuma wayar na sayar, a kwana a tashi shi ma kuɗin wayar ta kare a sayan abinci, nan fa na fara shiga kangin bauta da wahala, kuɗin haka ya kare, haka na sayar da wasu daga cikin kayan amfanina su gas da sauransu a in da na tashi daga unguwar da nake ɗin dan a wannan lokaci ba zan iya biyan kuɗin hayar wannan gida har naira 70k ba, shi ne na bar gidan na bar unguwar mutanen kirki na je na kama wani ƴar kango naira dubu 10 a shekara, duk kayana na wancan gidan na kwasosu zuwa wannan kangon, a takaice dai mun rayu cikin kunci da wahala ni da Ayla har na fara ciwo, haka yarinyar nan ta taso cikin kunci da bakin ciki, ba makarantar boko, gara Arabic ma lokacin da nake da lafiya ina koya mata sosai, kuma tana ɗaukar, sai dai na fi koya mata addua'o'i da sauransu, unguwar da muka koma sai su rinƙa ce mata shegiya idan ta fito, bata sakewa ta yi wasa koda a tsakar gida ne, sai dai a ɗaki, dan gidan ba mu kaɗai bane, akwai wasu matan da nasu yaran, to yaran suna tsangwamanta, kuma iyayen basu ce musu komai, haka zan wuni ina kuka tare da danasani na zuwata duniya, baiwar Allah bata san komai ba ta rayu cikin kunci da wahala tare da bakim ciki, lokacin da na san mahaifinta ya shiga siyasa, kara ɓoye kai'na na yi daga gare shi, dan kada ya kashe mini Ayla, na san cewa duk in da ya ganta sai ya san ƴarsa ce, dan kuwa babu in da ta barshi a kamanni, harta murya, kullum idan na ganta, sai na yi kuka ba kaɗan ba, saboda fuskar Abubukar da nake gani a tattare da ita, ban sake komawa gidanmu ba har yau da nake yi muku magana, lokacin da Ayla ta ɓata, aka sace mini ita, haukace kawai ban yi ba, Allah ne kawai ya kaddara ina da sauran rayuwa a gaba, amma da na jima da mutuwa saboda bakin ciki, ga shi bana iya tafiya a lokacin bare na je na nemota, na azabtu ba kaɗan ba, a haka har Allah ya haɗani da wata mata ta taimakeni, irin matan nan ne masu taimako bayin Allah, ita ta kaini asibiti, ban san waye ya bata labarina ba, kawai ina kwance a cikin ɗaki rai a hannun Allah ta zo ta ce mini daga kunguyarsu na tallafawa marayu da gajiyayyu ta zo, haka suka ɗauke ni zuwa aisbiti, bayan na warke ina iya tafiya da kafata, na yi tsantsar farinciki a in da na fara neman Ayla ido rufe, ban ganta ba, ban san a ina zan sameta ba, amma kullum addu'a ta ɗaya shi ne Allah ya kare mini ita a duk in da take, ban taɓa cire tsammani zamu haɗu zan ganta ba, bani da sana'ar komai hakan tasa dole na koma bara, bani da gidan da zan zauna dan kuwa gidan da muke ciki bayan na warke daga ciwo, na baro asibiti kenan, da na koma sai naga babu gidan an rushe shi, hakan tasa na fara kwana a kasan gada kawai, a takaice wannan shi ne labarina dana Ayla, na san saura abubuwan da suka faru kunji daga bakin ita Aylar?". Ta kai karshen maganar tana sharar kwallah.

Daga Abbi har daddyn Jelly sai da suka yi kwallah, shi kam daddy dama kun san shi da saurin kuka, dan haka kukansa ya fi na kowa yawa, ya zubar da hawaye har da shessheka yana sauke ajiyar zuciya, sun tausaya mata sosai, shi kuma daddy ya kara jin tsantsar kaunar Ayla over fiye da a baya, ya tausayawa rayuwarta ba kaɗan ba, baiwar Allah ashe haka taci bakar ukubar rayuwa, kai gaskiya Ayla tana da tawakkali sosai yarinyarnan, da wata ce ai da yanzu wani labari ake yi ba wannan ba.

Jin sautin kukan Ayla ne yasa dukkansu suka ɗago kai da sauri tare da kai kallonsu kanta, kuka take yi na wuce misali, ta jima da farkawa daga barci, duk labarin da mamanta ta bayar ta ji komai, baiwar Allah hawaye tamkar ruwan famfo haka yake bin kuncinta, tana daga kwance sam bata motsa ba.

Da sauri daddy ya dawo kusa da ita dan ya rarrasheta, Abbi da maman nata duk dawowa kusa da ita suka yi, zama daddy ya yi saman sofar tata tare da ɗagota ya rungume yana rarrashinta, shi dama tun farko bai so ma ya tsaya ya ji labarin ba, ya so a bar komai kawai ya wuce dan baya son tashin hankali, ga shi yanzu sun sa babynsa ta ji komai tana kuka, yasan yanzu abin zai tsaya mata a ranta ga kuma ƙaramin ciki, da wanne ɗaya zata ji? Duk irin ukuban da wahalar da ta sha a baya bai kamata yanzu su barta ta sake yin kukan bakin ciki ba a rayuwarta.

Dukkansu haɗuwa suka yi suna rarrashinta, da kyar suka samu ta yi shiru, ruwa mai sanyi Abbi ya ɗauko mata, karɓa daddy ya yi tare da buɗe mata ya bata a baki, sai faman sauke ajiyar zuciya take yi, duk wata zuciya mai imani sai ta tausayawa Ayla da mamanta, sun ga rayuwa ba karya.

Ɗaukarta daddy ya yi suka bar palon dan sam baya son abin da zai sa yaganta cikin damuwa, gara su koma Part nasu ya sanyata farinciki, Abbi kuma rarrashin maman Aylar ya yi a in da yake gaya mata ai ga shi nan Allah ya saka mata, ta yi hakuri komai ya wuce, kuma In Sha Allah shi da kansa zai mayar da ita gida wajen iyayenta, zai yi musu bayani tare da nasiha, da izinin Allah za su yafe mata, dan haka ta dai'na damuwa ta koma ɗaki ta kwanta ta huta, godiya ta yi mishi mai tarin yawa kafin ta miƙe ta haura sama, shi ma miƙewa ya yi ya haura sama wajen Aunty..........TO JAMA'A KUN JI LABARIN AYLA, KUMA KUN JI ALAƘARTA DA MUMMYN JELLY, MUMMYN JELLY DAI ƳA CE GA FAROOQ SALAHUDDEEN KANIN ABUBAKAR SALAHUDDEEN, SO DA AYLA DA MAMAN JELLY CAUSINS SISTERS NE, FATAN KUN GA NE? BA SAI NA TSAYA DOGON BAYANI BA, NASAN KUN GANE IN DA MUKA DOSA, SHAWARATA A NAN SHI NE MATA MU JI TSORON ALLAH A DAI'NA SHAYE SHAYE, WANNAN SHAYE SHAYE DUK SHI YA JEFA RAYUWAR MAMAN AYLA CIKIN GARARI, DOMIN DA BATA FARA SHAYE SHAYE BA, DA KWAKWALWARTA YANA NAN GARAU BA ZATA BIYEWA SAMARI BA, KADA KU MANTA KO MATA BATA BIYEWA DA FARKO, KARATU KAWAI TAKE YI, SANADIYAR SHAYE SHAYE NE HAR TA YI ABOKI NAMIJI WATO ANWAR, YA SHIGO CIKIN RAYUWARTA YA TARWATSA MATA DUK WATA FARINCIKI NATA WANDA HAR YAU BATA SAKE SAMUN FARINCIKI BA A RAYUWARTA, YA LALATA MATA KOMAI, SANNAN SHAWARATA GA ƳAN MATA, KU SANI SHI FA NAMIJI ƊAN YAUDARA BASHI DA KAMMANI, TAMKAR YANDA MUGU BASHI DA KAMANNI, TO SHI MA MAYAUDARI HAKA NE, ZAI IYA YAUDARARKI TA KO WACE SIGA, BAR GANIN KINA DA WAYO, WLH ƊAN BARIKI YA WUCI TUNANINKI, ABU MAFI SAUKI DA ZAKI YI KI GUJEWA FAƊAWA TARKONSA SHI NE ADDU'A, ALLAH NE KAWAI WLH ZAI IYA TSAREKI DAGA SHARRIN ƊAN BARIKI KUMA ƊAN DUNIYA, WLH DUK WAYONKI IDAN ƊAN DUNIYA YANA SON CINMA BURINSA A KAN KI TOFA SAI YA YI, DAN HAKA DA ALLAH KAWAI ZAKI HAƊASU, SHI ZAI TSAREKI DAGA SHARRINSU, BASU DA KAMANI BARE KI CE IDAN KIN GANSU ZAKI GUDU, A DUK LOKACIN DA KIKA KAFA GOSHINKI A KASA DA NUFIN SUJJADA TA SALLAH IN MA NAFILA KO FARILLAH, TO KADA KI YARDA KI ƊAGO DAGA SUJJADAR NAN BA TARE DA KIN ROKI ALLAH DAYA KAREKI DAGA SHARRIN MAZAN BANZA BA. ALLAH UBANGIJI DUK HALIN DA ZAMU SHIGA, YA ALLAH KA TAUSAYA MANA KA BARMU DA IMANINMU.

STORY💋

❤️LION and RIMSHA💋

Almost 2 mins yana tsaye yana ɗan tunani kafin ya wuce ya ɗauki wayarsa, kusa da ita ya dawo ya zauna tare da fara latsa wayar tasa, da amala sako yake turawa, lallaɓowa ta yi a in da ta ɗaura kanta a saman cikyarsa tana hawaye, ɗaura hannunsa a saman face nata ya yi ba tare da ya yi magana ba yana cigaba da latsa wayarsa da hannu ɗaya.

Sai da ya kammala abin da yake yi sannan ya ajiye wayar a gefe tare da dawo da kallonsa kanta, goge mata hawayen nata ya yi yana faɗin "Gaskiya Meesha ke raguwace". Turo baki ta yi tana cigaba da hawaye ta ce "Allah Noori ni ba raguwa ba ce, ka san yanda nake ji kuwa? Ciwo sosai marata take yi fa". Maimaita sunan Noorin ya yi a fili ba tare da ya sake ce mata komai ba.

Zame hannunsa daga saman face nata ya yi tare da mayar da shi zuwa saman marar tata yana mai cigaba da kallon face nata, runtse idanunta gam ta yi tana jan dogon numfashi, shiru ya yi yana karanto mata addu'ar da annbi ya bawa Nana Fateema a lokacin da take fama da rashin lafiya, duk wanda ya karanta wannan addu'a sau uku ya tofa a hannunsa ya shafa a wajen da yake yi mishi ciwon, to fa duk karfin ciwo in dai bana ajali bane sai ya yi diff ya ɗauke tamkar an ɗauke wutar nepa, wannan addu'a bata da wahala kuma bata tsawo amma akwai aiki sosai. *YA HAYYU YA KAYYUMU BI RAHMATIKA ASTAGISU ASLILI SHANIN KULLAHU WALATAKIL ILAH NAFSA ƊARFATA AIN*. Wannan ita ce addu'ar, Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce da Nana Fateema a duk lokacin da ta ji ciwo kai or ciki ko dai wani ɓangare daga jikinta, to ta karanta shi sau uku ta tofa a hannunta sai ta shafa a wajen da yake yi mata ciwon, da izinin Allah zata sami sauki nan take ba sai anjum.

Wannan addu'a ya fara kasanto mata yana shafa mata a marar tata, shiru ta lafe a saman cinyar tasa tana jinsa, Allah da ikonsa yana yi mata wannan addu'a ba'afi da minti ɗaya ba ta ji tamkar anyi ruwa an ɗauke, ciwon ya tafi gabaɗaya, lumshe idanunta ta yi tare mai riko yatsun hannunsa cikin nata.

"Are you okey?". Ya yi maganar dai tamkar kullum, wato cikin sanyin murya. Jinjina mishi kai ta yi tana faɗin "Allah Noori ciwon dukka ya tafi". "To sai a dai'na ruwan hawayen ko?". Cool murmushi ta saki tana ɗan murza ɗan ƙaramin yatsansa da ta riƙo.

"Tashi kici abinci". Girgiza mishi kai ta yi alamar ta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login