Showing 141001 words to 144000 words out of 359620 words

Chapter 48 - Triplets Book 3 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2029

hannunta, lallai akwai case kenan, mu dai je zuwa.

A ɓangaren daddy jelly kuwa, suna barin gidan Abbi kai tsaye gidansu Anaya suka nufa, babu kowa sai mai aiki da Zaira da ta dawo daga school yanzu ba jimawa, bata da lafiya ne aka dawo da ita gida, school nasu daban daban da Anaya, su karfe 1 suke tashi, Anaya kuma karfe 2 , da farko school nasu ɗaya, daga baya daddynsu ya raba musu.

Sam daddyn Jelly bai ji daɗi ba, ya so su sami daddyn Anaya dan yana da magana da shi, amma baya nan yana Zaria, haka suka yi musu sallama suka nufi wajen shan ice cream, suna tafiya yana ta jan ta da hira, ta yi lamo a jikin kujera tana ganin hanya, a hankali yake tukin dan kula da lafiyarta, duk yadda ta ɗan motsa sai ya tambayeta ko lafiya, gyaɗa mishi kai kawai take yi alamar e tana lafiya, cigaba da tafiya yake yi yana satar kallonta.

Daidai bakin wani ɗan karamin kasuwa irin na bakin hanya wadda yake a unguwa haka, ba za'a kira shi da kasuwa ba, dan ba girma gare shi na, irin waje ne haka da masu sayar da kayan miya su tumatiri da sauransu ke kafawa a bakin hanya ta cikin unguwa haka, daidai zasu wuce wajen a tsananin razane ta miƙe zaune tana faɗin "Daddy ka tsaya ga mamata can!.". Ba shiri ya ja wata iriyar birki, tun bai gama tsayar da motar ba ta buɗe ta fito da gudu, saura kaɗan wata motar ta taketa, Allah ya takaita mai motar ya kama birki, ita kam bata bi ta kan motar ba, wajen maman nata kawai ta nufa a guje, burinta kawai ta isa gareta.

Zaune take a kusa da masu sayar da kayan miyar, tana ɗauke da kwanon bara a hannunta, ta yafo wani koɗaɗɗe kuma jemammen zaninta a kanta, ga wasu uban gudaje dake binta saboda dattin dake jinta, tamkar mahaukaciya haka take zaune a wajen, da alama ta murji bakar wahala na wuce misali, kuma da alama har yanzu bata da lafiya, ta rame sosai, fuskar nan tata duk ya mokaɗe saboda rama, wasu kasusuwar wahala ne suka bayyana a saman face ɗin nata, tamkar mai cutar kanjamau.

Tun bata karisa wajen ba take ambatar mama, mama, mama, a hanzarce ita ma matar ta ɗago kanta dan ko mutuwa ta yi ta dawo ba zata taɓa mantawa da muryar ƴar ta ɗaya tilo a duniya ba, a guje ta zo ta rungumeta tana sakin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro tare da ambatar sunan maman nata, ita ma maman rungumeta ta yi tuni hawaye suka wanke mata fuska baja baja. A wannan hali daddy ya iskosu bayan ya yi parking na motar da kyau, gabaɗaya jama'ar dake wajen hankalinsu ya dawo kansu, harta masu sayar da kayan miya a wajen dukkansu hankalinsu ya karkato izuwa kansu, sai kuka Ayla take yi tamkar ranta zai fita, ita ma maman kuka take yi ta kasa magana, an rasa mai rarrashin ɗan uwa.

Shi kansa daddy sai da idanunsa suka kawo kwallah, uwa ba wasa ba, almost shekara 4 kenan yanzu basu tare, ai dole su yi kuka, ko da ace ma rabuwar daɗi suka yi bare kuma rabuwar wahala, sace Ayla ɗin akayi idan baku manta ba, kun ga kuwa rabuwar wahala rabuwar da basu shirya ba suka yi shi.

Sai da daddy ya ga kukan da take yi ɗin ya yi yawa, zai iya illatata, sai ya matso kusa da su tare da tsugunnawa a gaban nasu ya sanya hannunsa ya jawo Ayla ɗin zuwa jikinsa, juyowa ta yi ta kankame shi tana kuka tana faɗin "Daddy mamata ce, wlh ita ce, ita ce daddy!". Hannu yasa yana goge mata hawaye yana faɗin "Ya isa haka babyn daddy, ya isa kukan, ba shi ya kamata ki yi yanzu ba, murna zaki yi tun da mama ta bayyana, ki godewa Allah da ya bayyyana mana ita, dan Allah ki yi shiru kin ji ko?". Da yake bata yi mishi musu, bata saba ba kuma bata taɓa yi ba, sai ta yi ƙoƙarin haɗiye kukan nata, amma hawayen sunki tsayawa, ganin hakan ga kuma jama'a sun rufesu wasu ma har sun fara ɗaukarsu a video, sai ya miƙe tare da ita a jikinsa yana faɗin "Mama dan Allah ki tashi muje ko?". Bata musa mishi ba, ta miƙe ta bi shi, dan tun da ta kalle shi tare da ƴarta, tasan shi ne ya taimaki ƴar tata kenan, dan haka ba macuci bane, shiyasa ta yarda ta bishi zuwa cikin mota, jama'a da gulma sai video suke yi musu dan a sami na yin posting a media, yanzu da abu ya fara faruwa a waje, a maimakon jama'a su jajanta, sai su ɗauko waya su fara ɗauka, ko da kuwa accident aka yi a waje, Allah dai ya kyau.

Gidan baya maman ta shiga, ita kuma Ayla ya sanya ta a gidan gaba, dan baya son barinta ta je wajen mama ta cigaba da yin kukan nan nata, tana ɗaga mishi hankalin, shiyasa ya rabasu, kunna motar ya yi ya nufi gida, an fasa zuwa yawon, har lokacin sai kuka Ayla take yi, ita ma maman nata sai hawaye take yi, da yake yanzu ba hira suke ba, sai ya zuba gudu sosai da motar, cikin ɗan ƙanƙacin lokaci suka isa gida, kai tsaye part ɗin Abbi suka nufa, yaki yarda ya bar Ayla ta je jikin mamanta, dan baya son kukan da take yin nan ko kaɗan, dan haka sai ya rungume kayansa suka shiga cikin palon.

Aunty ce kawai a ciki tana zaune saman sofa bayan sun kammala cin abinci kenan, tana ganinsu ta miƙe tana yi musu sannu da dawowa, ganin wata a tattare da su yasa ta kara faɗaɗa fara'arta tana yi musu sannu da zuwa, saman sofa daddy ya zauna da Ayla a jikinsa sai aikin rarrashinta yake yi, ita kuma maman nata zata zauna a kasa ya ce mata a'a ta zauna a saman sofa, ganin Ayla na cin uban kuka haka yasa Aunty ta kariso wajensu da sauri tana tambayar ko lafiya, cike da kulawa daddy ya gaya mata abin da ya faru, sannan ya ɗaura mata da cewa ta kai maman Aylar ɗaki ta yi wanka ta ci abinci, ta huta zuwa anjima zasu yi magana, daga karshe ya tambayeta ina Abbi? Ya fita ta bashi amsa Kafin ta nufi maman Aylar tana faɗin "Muje ko? Ki dai'na kukan haka ya isa". Allah sarki Aunty baiwar Allah, ita dai ba ruwanta, koma waye aka kawo, in dai mijijta da ƴan uwansa ne, hannu bibbiyu take karɓarsu, bata da wata matsala a rayuwarta, ba kyashi bare hassada, haka ta riƙo hannun maman Aylar, bata damu da dattin da yake jikinta ba, ta wuce da ita zuwa ɗakin Hanan.

Shi kuma daddy rarrashin babyn nasa ya cigaba da yi yana gaya mata ai murna zata yi, wannan abin faranciki ne ya same su, dan haka ta kwantar da hankalinta, shi ya fi kowa ma murna, dan ko ba komai yanzu zai san su waye familyn babyn nasa da har take masa kama da tsohuwar matarsa wato mummyn Jelly. Da kyar ya lallaɓata suka wuce bedroom nasu dan ya je ya sakata tayi barci kada kanta ya yi ciwo, yasan yanzu tana lokacin barci ne saboda cikin nata, da ta kwanta kaɗan sai barci, abin ba sauki sam.

A ɓangaren matafiya kuwa.

Rimsha tun tana iya ganin mutane har ta dai'na, gabaɗaya sun fita garin Kaduna sun ɗauki hanyar Abuja, tsoro ne ya kamata, amma tuna cewa duk wuya ba zai taɓa cutar da ita ba, yasa ta hakura ta lafe a jikin kujerar motar, shi kuwa sharara uban gudu yake yi tamkar ba gobe, ban da hanya babu abin da yake kallah. Dai'dai wajen checkpoint na sojiji bayan ka fita Kaduna ta wajajen jare, a nan suka tsayar da su, a lokacin ma ta yi barci abinta.

Tun da ɗaya daga cikin sojojin nan ya dallah wutar torch light ɗinsa ya kalli motarsu, yasa a ransa sun yi kamu zasu samu kuɗi, dan kuwa ba ƙaramin mota bane wannan, nufarsu ya yi kai tsaye, da yake glass ɗin motar a sauke take kasa, sai ya danna musu torch light a cikin motar kai tsaye, har sai da Lion ya ɗan rintse idanunsa saboda bala'in hasken light ɗin.

Da sauri sojan ya haska Rimsha bayan ya haska Lion ɗin kenan, da mamakinsa sai ya ga ita chocolate color ce, shi kuma Lion Bature kamar ka taɓa jini ya zuba saboda haske, ga shi ita karamar yarinya, bugu da kari tana barci, fusataccen face ɗin Lion kuma idan ka kallah wani lokaci zaka rantse irin bakaken mugayen nan ne masu kashe mutane ba gaira ba dalili, dan haka sai sojan ya tuhume shi da satar yara, wato ya sato Rimsha kenan, kuma a yanayin da suke ɗin nan dole za'ayi mishi irin wannan tuhuma, cikin wannan dare ya ɗauko ƴa mace sun nufi Abuja, kuma kunsan dole wanda bai san su ba ya yi tunanin hakan, to da yake shi ma soja ne, yasan a kan aikinsu suke, sai bai wani nuna musu karfi ko ya dake su ba, hakan da suka yi dama shi ne dai'dai, gently ya ce musu wannan sister sane cikin Abuja zasu je, kwata kwata baya son a gane waye shi, dan shi bai zo Nigeria dan a gane ne yana ƙasar ba, yasan idan ya cire face mask na face nasa to tabbas ko basu san face nasa ba zasu san shi ne.

Kin yarda sojojin suka yi, suka ce sam sai ya tashi Rimsha su ji daga bakinta, ya tasheta a gabansu, ta ya za'ayi yana Bature ɗan haure zai ce musu bakar fata kanwarsa ce,? Ai wannan hankali ba zai ɗauka ba, babu wata kama da take nuna wannan kanwarsa ce, ko suna da alaƙa da ita, dan haka ko ya tashe ta, ko kuma ya miƙa musu ita ya kawo wani abu na cin hanci kenan, sai su yafe mishi ya tafi ya barta a wajensu, da farko ya ɗauka faɗa suke yi a kan gaskiya, sai yanzu ya fahimci in da zancen ya dosa, ashe marasa gaskiya ne ma, ba suna faɗa dan kare kasarsu daga miyagu bane ma, dan aljihunsu suke yi ashe.

Cike da izza ya ce bai ga uban da ya isa ya tashi Rimsha a nan ba, kuma wlh su basu hanya su wuce ko kuma ya yi musu abin da sai sun yi danasanin zuwarsu duniya, cike da izza shi ma ɗayan sojan ya sanya gindin bindigarsa zai taɓa kumatun ta da shi ya tashe ta, ɗayan kuma ya ja kofar motar zai buɗe, sai surfa masifa suke yi, wai ai ɗan haure ne, ya hauro musu kasa ba ta hanyar da ta dace ba, dan haka sai ya ɗanɗani kuɗarsa yau.

Bai kai ga taɓata da bindigar ba ta farka saboda surutansu da ya yi yawa, shi kuma Lion sai ƙoƙarin dannar zuciyarsa yake yi dan abin da yake gabansa ya fi masa sauraran waƴan nan banzaye muhimmanci a cewarsa, miƙewa ta yi zaune tana murje idanunta. Tsawa sojan ya daka mata wadda ya sanyata firgita, shi kuma Lion wayarsa ya ɗauko ya fara latsawa, dan shi bashi da lokacin sauraran waƴan nan marasa hankali da basu san aikinsu ba a cewarsa,.

"Ke waye wannan kuma ina zai kai ki?" Ɗaya daga cikin soldiers ɗin ne suka mata magana cikin tsawa, a firgice cikin magagin barci murya na rawa ta basu amsa da cewa "Yayana nane ya ce zan raka shi wani waje ne, amma ni ban san wajen ba". Dawo da kallonsu kan shi suka yi, sai latsa waya yake yi, zasu yi magana wani daga cikin sojojin da alama babbansu ne ya kariso wajen, cikin girmamawa ya ce da Lion su tafi, ya samu kira daga sama, su kuma sojojin su bashi hakuri, bai jira wani hakurinsu ba, dan idan baku manta ba, ya tsani kalmar sorry a rayuwarsa, da gudun gaske ya ja motarsa ya bar wajen, yana barin wajen kuma suka sake samin kiran waya an soke aikinsu baki ɗaya, an koresu daga aiki kenan, gabaɗayansu da suke wajen, a nan dai ya yi musu amfani da karfin ikonsa ne ba karfin damtse ba, ya fahimci sojojin irinsu masu karɓar cin hanci, sam basu da wata amfani a hukuma, domin kuwa, ba kasa da al'umma suke yi wa aiki ba, aljihunsu da cikinsu suke yi wa aiki, to yana da kyau su bar aikin al'umma su je su nemi aikin cikin nasu, dan aikin soja aikin kasa da al'umma ne, da mutane masu kishin kasa kishin kansu da al'ummarsu ya dace ba banzaye irin waƴan can ba.

Cigaba da sharara gudunsa yake yi, sun yi nisa sosai har ma sun kusa shiga Abuja, sautin garuwar hakwaranta ne ya saka shi waigowa ya kalleta, tun da ya bar wajen sojojin nan ya ɗage glass ɗin motar saboda sanyi da ya fara sauƙa, amma a haka wai rawan sanyi take yi, da farko kamar ba zai kula ta ba, sai ya tuna idan wani abin ya sameta shikenan shirin shi ya ruguje, dan ba zata iya fita ba, tuna hakan yasa ya yi parking na motar a gefen titi ya cire jacket ɗin jikinsa ya rufa mata a jikinta, sai zuba barci take yi, kunna motar ya yi ya cigaba da tafiya dan sun kusa shiga, kamar a mafarki ta ji kamshin perfume nasa sosai yana ratsata, ga kuma ɗumi da ta ji, karayin lamo ta yi a jikin kujerar tana sauke numfashi a hankali hankali cikin kwanciyar hankali.

Misalin karfe 11 dai'dai suka shiga cikin garin Abuja, kai tsaye gidansu ya nufa, tamkar already ya san hanya, amma kuma bincike ya yi ya gane location na gida, sai ya yi amfani da google map, sai zuba barci take yi bata san ma sun iso ba, da yazo shiga babban gate na duplex apartment ɗin sai da aka charje motarsa tsab, bai hanasu ba, dan ma baya son wasu su san ya shiga gidansu Rimsha ɗin, baya son kowa ya sani.

Bayan sun gama charjewa, kai tsaye kofar gidan ya nufa, rufe take gate ɗin, ga wani zabgegen kwaɗo da aka sanya a babban gate na shigar da mota, parking ya yi a bakin gate ɗin, gently ya fito ya nufi wajen gate ɗin, ga mamakinsa sai yaga babu kura ko wata alama da zata nuna an jima ba'a shiga gidan ba, alamu sun nuna akwai masu zuwa gidan, shiru ya ɗan zubawa kwaɗon idanu, gently ya kai hannunsa har kamar zai taɓa kwaɗon, sai kuma ya fasa ya juya zuwa wajen motar tasa dake kunne, juyawa da zai yi sai ya kalli mutun daga gidan kusa da su ya leƙo ya kuma koma, bai bi ta kansu ba ya koma cikin motarsa.

After some minutes ya fito ya dawo gaban gate ɗin, wani ɗan ƙaramin kwalba da ya ɗauko ya buɗe ya zubawa kwaɗon ruwan dake cikin kwalbar, nan take kwaɗon ta ɓalle gida biyu gate ɗin ta buɗe, daddyn Rimsha ya cika mai sa'a da har Lion ya tsaya tsayin daka a kan case nasa har haka, dan ma dai idan ya ce zai yi abu, to wuya ko akasinta bata sanya shi ya juya baya, muddin ya fara abu, to sai ya kai in da yake buƙata, komai wuya komai daɗi baya sarewa kuma baya gajiyawa, akwai shi da taurin zuciya na bala'i, ga zafa a kan aikinsa da ya sa a gaba, rashin tsoro, tashin tausayi, karfin da kuma zafin zuciya, baya tankwaruwa kamar yadda baya juyuwa, in ya miƙe, ya miƙe kenan har sai in shi ya ga damar zama.

Da kansa ya buɗe gate ɗin sannan ya koma ya shigo da motar ciki, babu ko tsoro a ransa, yana sane sarai akwai masu shigowa gidan, da alama ma ƴan shaye shaye ne, ko kuma wasu criminals, sun mai da gidan gidan maɓoyansu idan suka aikata wani laifi.

A parking space na gidan ya yi parking na motarsa, a nitse ya fito yana bin ko'ina da kallo, tabbas hasashensa gaskiya ce, akwai masu zuwa gidan, dan ga tayan motoci nan alamu sun nuna ma kwana biyu da suka wuce waƴan nan motoci suka shiga, suka kuma fita, da yake akwai taɓo na ruwan sama a jikin tayun ne sai ya bada shati sosai, da hasken screen ɗin wayarsa ya haska yake gani, dan gidan babu wuta, da alama an yanke wutar gidan an cire baki ɗaya.

Ya ɗauki almost 10 mins yana ƴan dube dubensa kafin daga bisani ya dawo cikin motar, da hannu ɗaya ya saɓeta a kafaɗarsa dan yanzu kula da ita zai yi sosai kada wani abin ya sameta, dan ya cinma abin da yake son cin ma wa, trolleynsa ya zaro da ɗayar hannun nasa ya ja zuwa cikin palon, da yake suma kofar palon nasu mai amfani da fingerprint ne, sai ya saki trolleyn nasa ya sanya hannu a aljihunsa ya fito da wata kati, har lokacin tana kwance a saman kafaɗarsa tana zuba barci, ta wahala baiwar Allah tafiyar dare, Lion sai Allah bai tashi yin tafiyar ba sai dare.

Sanya card ɗin mai kama da ATM card ya yi a daidai saitin fingerprint na kofar, nan take kofar ta buɗe, gyara ɗaukarta da ya yi da kyau ya yi sannan ya ja trolleyn zuwa ciki, palon kawai duhu sosai, a haka ya shiga zuwa tsakiyar palon, kafin ya saki trolleyn ya ciro wayarsa ya haska, saman doguwar sofa ya kwantar da ita, sannan ya ja trolleynsa ya haura sama tamkar already ya san gidan, ɗakin daddynta kai tsaye ya nufa, komai yana nan yadda suka barshi, da alama masu shigowa gidan basu shiga cikin bedrooms sai iya tsakar gida or palo.

Ƴan dube dube ya yi a ɗakin kafin ya wuce zuwa toilet, wanka ya yi, Allah yasa akwai ruwa sosai, da ruwan sanyi ya yi wankar tasa, ya fito, shiryawa ya yi cikin kayan barci masu kyau da tsada farare tas, ya sanya perfume nasa sannan ya fito zuwa balcony dake tsakanin bedroom ɗin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login