Showing 195001 words to 198000 words out of 359620 words
ɗakin, a hankali ya lumshe dara daran blue eyes nasa, ba jimawa barci ya yi awon gaba da shi, asuba ta gari.
After some days, (bayan wasu ƴan kwanaki)
A cikin ƴan kwanakin nan da suka wuce abubuwa da dama sun faru, an miƙa case ɗin Jehan court, suna ta ƙoƙarin su ga sun yanke mata hukunci a kan lokaci, shi kuma Areef yana bincike sosai dan ya gane gaskiya, ya je har gidan mutumin in da abin ya faru, ya yi bincikensa, yana ƙoƙarin haɗa hujjoji da kyau da kyau. Tsakanin Akila da Aseef kuwa, abubuwa sai kara taɓarɓare musu yake yi, komai ya lalace musu, yau saura kwana uku aurenta da Irfan, a ɓangaren Lion da Rimsha kuwa, yanzu suna zaman lafiya, ta dai'na yi mishi rashin ji, tana bin duk abin da yake so, tana ƙoƙarin ganin bata ɓata mishi rai ba, so yana gudanar da aikinsa yadda ya dace, wani lokaci ya kirata kusan tare zasu yi aiki, baya tambayarta, sai dai ya zaunar da ita kusa da shi yana aiki tana kallon shi, daga nan yake fahimtar abubuwan da yake son samu amsoshi a kansu, wasa wasa shaƙuwa tana shiga tsakaninsu saboda yawan zama tare da suke yi, yanzu har ta kai kusan koda yaushe suna tare saboda aikin nan nasa, sai dai fa duk da haka yaki yardanwa zuciyarsa tana burgesa, kullum ƙoƙarin ƙaryata zuciyar tasa yake yi, dan a cewarsa bai ga wata halitta da zata burge shi ba bayan TRIPLETS nasa, su kaɗai suke burge shi, a ɓangaren school nata kuwa, kullum Mark ne yake kaita ya kuma kula da ita sai sun tashi ya dawo da ita, da yake yanzu suna Exam ne, karfe 12 suke dawowa, kullum sai Anaya ta yi wa Mark magana, tun baya amsawa har ya dawo amsa mata, idan ta ce good morning sai ya ce how are you, ba ƙaramin daɗi take ji ba da ya fara amsa mata ɗin.
GIDAN LION💋
Sanye take da uniform nata ta sauko zuwa palon kasa, kitchen ta nufa, Mark ta samu a cikin kitchen ɗin yana zubawa Lion abinci, wajen ajiye kwanikansu ta nufa, kula ta ɗauki mai kyan gaske, kusa da shi ta zo ta tsaya, cikin natsuwa ta ce ya zuba mata abinci a ciki, ba musu ya karɓa ya zuba mata, dan shi aikinsa ya girka, duk mai so ya zuba mishi, ɗauka ta yi tare da ɗauko ruwa mai sanyi da drinks guda biyu a cikin fridge, ta haɗo da fruits da ba'a yanka ba, sai kuma spoon guda ɗaya, duk ta zuba su cikin kwandon ɗaukar abinci ta ɗauka ta fito zuwa palo.
Babu kowa a palon dan haka sai ta nufi bedroom ɗin Aseef kai tsaye, yana kwance tamkar mara lafiya, yau saura kwana uku auren AKila, su Abbi duk su dawo gidan Abba, shirye shirye ake yi babu kama hannun yaro, ya shiga tashin hankali na wuce misali, ya kira daddyn Rimsha, shi ma ya yi magana da Abba amma a matsayin yaya ga Aseef ba Hosain ba, Abba ya bashi hakuri a kan ya rigada ya bawa Irfan aurenta, hakan yasa kullum Aseef ɗin yana cikin ciwon kai, ita kuma Akila zazzaɓi, shi kuma Lion baya zama kwana biyun nan, Areef yana fama da case ɗin Jehan, dukkansu basu da kwancinyar hankalin da zasu iya fahimtar ɗan uwan nasu yana cikin wani hali, suna jin ba daɗi a jikunsu sakamakon damuwar da Aseef ɗin yake ciki, amma sun bar abin a matsayin busyn da suke fama da shi kwana biyu ne, basu kawo a ransu cewa wani abin ne yake faruwa da Aseef ɗin ba.
Bakinta ɗauke da sallama ta shiga cikin ɗakin, yana kwance da idanu kawai ya bita, har ƴar rama ya yi, kusa da shi ta zauna, cikin sanyin murya ta ɗaga mishi gaisuwa, ƙaƙalo murmushi dole ya yi kafin ya amsa, kasa ta yi da kanta tana tunanin yadda zata yi ta aike shi.
"Rimsha lafiya kuwa?" Ya yi maganar yana miƙewa zaune, "Yaya Aseef dama ina son ne dan Allah ka kaiwa Jehan wannan abincin a prison". Shafa kanta ya yi yana faɗin "Tom shikenan, kina murna gobe daddy zai zo ko?" Kai ta gyaɗa mishi alamar e, karɓar abincin ya yi tare da miƙewa tsaye, cikin ɗari-ɗari ta ce "Yaya Aseef baka da lafiya ne?". Gyaɗa mata kai ya yi yana faɗin "Kaina ne yake yi mini ciwo, amma na ji sauki, kin yi breakfast ne?" Jinjina mishi kai ta yi alamar e ta yi.
"Okey tom ko zamu je na sauke ki a school ɗin kafin na wuce prison ɗin?". Girgiza mishi kai yi kafin ta ce "A'a yaya Aseef ka kaiwa Jehan ɗin dai, yaya Areef ya ce mini bata cin abincin da ake girkawa a prison ɗin, daren jiya ma da ya je bata da lafiya, kuma ta ki gaya mishi me yake damunta, sai da wata ƴar ɗakinsu ta gaya mishi ai bata cin abinci ne, yunwa ne ya kwantar da ita, shi ne ya ce kullum na rinƙa dafa mata irin abincinmu na nan zai rinƙa kai mata, yau nayi latti shi ne ban tsaya yi mata girkin ba na karɓa mata wajen Mark, na fito kuma sai naga yaya Areef ɗin baya nan, nasan kuma tana jin yunwa sosai, shi ne ka kai mata kawai Mark zai kai ni school ɗin". Jinjina mata kai ya yi yana mai yaba mata tare da gaya mata ai dama bai kamata Jehan ta ci abincin da ake dafawa a Prison ba, ta wuce hakan ai, amma dai yanzu bari ya kai mata da wuri ita kuma ta je ta samu Mark su wuce zuwa school lokaci na kara tafiya, okey ta amsa mishi da shi kafin ta miƙe ta nufi waje, shi kuma ya ɗauko makullin mota ya fito zuwa nashi motar.
Bedroom nata ta koma ta ɗauko school bag sabo da Areef ya saya mata, dan nata kam ta kaiwa Jehan kaya a ciki, palon kasa ta nufo, tana sanya kafarta a saman benen shi kuma yana haurowa rungume da Brady a kirjinsa, da alama daga wani wajen suka fito, yana ganinta ya diro kasa daga jikin Lion ɗin yana wani girgiza na iya shege.
Har ta fara ja da baya zata gudu sai ta tuna da huɗubar Akila, akan ta dai'na gudun karen, ta rinƙa nuna mishi bata tsoron shi, idan ya matsa mata sai ta rungumi Lion ɗin suga ta tsiya, tuna hakan yasa sai bata gudu ba ta tsaya, sai da Bradyn ya isota ya daka tsalle zai hau jikinta, cikin sauri ta kauce mishi tare da faɗawa saman faffaɗar kirjin Lion ɗin, dan ta ga karshen tsiyarsa, karen ya rainata da yawa.
Haushi ya fara daka mata a kan me zata taɓa mishi jikin Lion nasa, shi kuma Lion cak ya tsaya yana kallon wannan ikon Allah.
Kankame shi ta yi sosai tare da cusa kanta a cikin kirjin nasa, tsalle Bradyn ya yi ya haye kanta da nufin ya sakata ta sake mishi Lion ɗinsa, ai jikinsa ne shi kaɗai, shi kaɗai zai rinƙa kwanciya a kirjin Lion ɗin, dan haka ta sake shi ko ya cijeta.
Gently ya sanya hannunsa ya rabata da jikinsa yana kallon face nata, ta datse idanu gam tamkar zata fasa su, ga kuma Brady a saman bayanta wajen school bag nata ya ki sauƙa, kiris ya rage ta saki fitsari a wando dan azaban tsoro, calmly ya ce da sweetheart ɗin nasa ya sauka daga jikinta, girgiza ya yi alamar shi gaskiya ba zai sauƙa ba, waye ya ce ta hau mishi kirjinsa in da yake kwanciya, dan haka sai ya bata azaba, yana ƙoƙarin sake yin magana sai ya ji tana ƙoƙarin zubawa kasa alamar ta suma dan bala'in tsoro.
Tallabota da kyau ya yi yana mai kara ɗaure fuska sosai ya ce da Brady ya sauka, ganin ya ɗaure fuska sosai ne yasa ba dan ya so ba ya diro kasa yana wani kuka mara sauti irin ya ji haushin nan, an ɓata mishi rai.
Hannunsa ɗaya ya kai ya riƙo lallausan kumatunta yana ɗan girgizawa, ina ta sume, kawar da kallonsa ya yi daga kanta zuwa kan sweetheart ɗin nasa, ruwa ya ce mishi ya je ya kawo mishi, ya yi maganar tare da saɓarta a kafaɗarsa suka karisa saman benen, bedroom nasa ya wuce da ita, saman sofa ya shimfiɗeta tare da zama kusa da ita.
Yana zama ba jimawa sai ga Bradyn da ruwa roba ɗaya mai sanyi a bakinsa ya riƙo, karɓa ya yi tare da buɗewa, kaɗan ya tarbo a hannunsa ya shafa mata a fuska, doguwar numfashi ta ja tare da saukewa a hankali, gently ta waro idanunta kai tsaye sai cikin nasa idanun dan kuwa ita yake kallo, zubawa juna idanu suka yi, da alama ita tana ɗauka a mafarki take kallonsa, dan da alama bata dawo normal ba, shi kuma Allah ne kaɗai yasan me yake tunani da ya tsareta da rikitattun dara daran idanun nan nasa.
Sun ɗauki a kallah minti ɗaya suna kallon juna babu ko kyaftawa, haushin Brady ne ya dawo da shi daga duniyar tunanin da ya faɗa, miƙewa ya yi tare da nufar toilet, ita kuma lumshe idanunta ta yi tare da sake buɗe su dan ta tabbatarwa da kanta ba mafarki take yi ba, ganin yes da gaske a cikin ɗakinsa take ne yasa ta miƙe jiki ba kwari, already Brady ya bi Lion ɗin cikin toilet.
Kyawawan kafafuwanta ta zuro kasa kafin ta miƙe ta nufi waje, a harabar gidan ta isko Mark yana jiranta, gidan baya na motar ta shiga, shi kuma mazaunin driver, kunna motar ya yi suka nufi school.
Suna yin parking a parking space na school ɗin Anaya ta taho da sauri, ita ta buɗewa Rimsha motar, fitowa ta yi suka rungumi juna, dukkansu fuskokinsu ɗauke da kayatatcen murmushi da zata tabbatar maka da suna tsantsan kaunar junansu sosai, farinciki a wajen su ba'a misiltawa. Leƙowa Anaya ta yi ta gaban motar ta ce mishi good morning, ba tare da ya kalli in da take ba ya amsa tare da tambayarta ya take, da fara'a ta amsa mishi da lafiya lou Alhadulillah, daga haka bai sake magana ba, kuma har lokacin bai ɗago ya kallesu ba, shi dama irin ogan sa ne, in da suka saka gaba nan kawai suke kalla, ba ruwansu da juye juye.
Rungume da juna suka nufi class nasu, yau Exams biyu suke da shi, ɗaya na Mr Emmanuel ne, ɗayar kuma na Mss Deborah, na mss Deborah ne farko, Mr Emmanuel nasa ne na karshe. Dukkansu sun sha jinin jikinsu lokacin da suke rubuta Exam na Mr Emmanuel, ba dan komai ba sai dan sun san faɗuwa za su yi, sun san ba zai basu marking mai kyau ba, fuskokinsu ya rage yelwan farinciki sosai, sun shiga damuwa, amma haka suka daure suka rubuta tsakaninsu da Allah, suka sanya abin da suka sani na amsa, kujerar zamansu daban daban, amma abin mamaki amsa iri ɗaya suka rubuta, hakan ne zai nuna maka kwakwalwarsu ɗaya, akwai basira na wuce misali.
Exam nasa shi ne na karshe da suka rubuta, daga nan suka tashi zuwa gida, har wajen mota Anaya ta rakota dan ta sake ganin Mark, yana zaune ya buɗe kofar motar ta gefensa ya zuro kafafunsa waje yana latsa waya, a duk cikin sojojin Lion ba wanda Lion ɗin ya yarda da shi sai Mark, shi ma dai ba wani yarda 100 ya ba shi ba, sai dai kawai ya fi sauran sojojin samu waje a zuciyar Lion ɗin ne, suna shiri sosai saboda hali ya zo ɗaya.
Rungume juna suka yi kafin ta saketa ta shiga cikin motar suna yi wa juna bye bye, a hankali ya dawo da kafafunsa cikin motar dan su tafi, yana ɗago idanunsa ta cikin mirror motar karaf idanun nasa suka sauka a kan face nata, ta buga uban tagumi a kujerar baya, sai bye bye Anaya take yi mata bata amsa ba, kawar da kallonsa ya yi yana tunanin me ya sameta, dan kallo ɗaya ya yi mata yasan tana cikin ɓacin rai da damuwa, wani tunanine ya faɗo mishi na ya kalli Anaya mana ko ita ma tana cikin ɓacin rai ɗin, tuna hakan yasa ya ɗan ɗago kansa tare da juyowa ya kalleta, karaf suka haɗa idanu, dan kuwa shi take kallo, kawar da kansa ya yi yana tunanin to me ya samesu, kamar zai tambayesu sai kuma ya tuna hakan bata cikin aikinsa, amma har cikin ransa bai ji daɗin ganin damuwar da suke ciki ba, ko dan kaunar da su Aseef suke yi wa Rimsha dole ne ya tsaya tsayin daka ya bata kulawa dan yana bala'in kaunar TRIPLETS shi ma fiye da tunanin mai tunani, bugu da kari kuma ita ce mace ta farko da ya fara gani tare da ogansa, duk da bai san menene yake tsakaninsu ba, a yadda ya fahimta yake kuma tunani, dole tana da matsayi a wajen ogan nasa, sannan a ƴan kwanakin nan yana yawan ganinsu inuwa ɗaya, wani lokaci zai gansu a garden zaune, Lion na zaune tana zaune kusa da shi kamar wasu wa da kanwa, hakan ya kara tabbatar mishi lallai tana da mahimmanci a wajen Lion ɗin, amma a tunaninsa ne hakan, so dole ya kula da ita kamar yadda yake kula da ogan nasa.
Har ya tada motar sai ya ji kai ina gara dai ya tsaya tun suna tare su biyun ya ji menene matsalarsa ne wai, kashe motar ya yi duk da yana tsoron yin hakan tun da Lion bai bashi umarni ba, amma ya daure ya ce mata "Rashmee menene yake damunki? Me ya faru a cikin class ɗin naku? Dan da kuka fito waje dai ban ga wani abu ba!". Da yake baya kiran sunan Rimsha sai dai ya ce Rashmee, kada ku manta da English ya yi magana.
Daga ita har Anayar sai da suka zaro idanu waje kamar zasu faɗo kasa, mamaki Anaya take yi dama haka muryarsa take? Dama ya iya magana kenan? Lallai ma Mark. Kallon Anaya ta yi tana tunanin ta gaya mishi ne ko kada ta gaya mishi, cikin sauri Anayar ta gaya mishi cewa Mr Emmanuel ne yake kin basu Marking nasu dai'dai da abin da suka rubuta, sai ya basu zero kullum, kuma amsa dai'dai suke rubutawa dan suna kallon paper ƴan class da yake bawa marking duk amsar iri ɗaya ce.
Cikin sanyin murya ya ce ta bashi paper test ɗin nata bari ya gani, a hanzarce ta sauke jakar bayanta tare da buɗewa ta fito da paper ta miƙa mishi, karɓa ya yi yana dubawa, tabbas dukka amsar da ta rubuta daidai ne, amma kuma zero ya bata, kara ɗaure fuskarsa sosai ya yi, dama ga fuskar ba'a magana a ɗaure take tamau, ɗago da kallonsa ya yi zuwa kan ta, cikin sanyin murya ya ce su kai shi office ɗin Mr Emmanuel ɗin bari ya ga ɗan uban waye ne shi ya kuma ji a kan me zai tauye musu marking nasu.
Okey suka amsa mishi da shi, fitowa ya yi Rimsha ta biyo bayansa, daga manyan student har yara sai kallon shi suke yi sun ga Bature fari kal kamar ka taɓa jini ya zuba, tuni ƴan matan suka fara santinsa, shi kuwa abin da kuka sani ne, in da yake takawa kawai yake kalla, bai ɗago idanu ba ma bare ya ga wata yarinya or wani uncle, gabansa kawai ya zubawa idanu, karin abin burgewa da shi, yana tafiya ne a bubbuɗe kamar ogan nasa wato Lion, irin tafiyarsu ɗaya, kuma tafiyar tana ɗaukar hankali ba kaɗan ba, yana da kyau da burge mutane, dan tafiya ce da take nuna cikakkun jarumai masu jini a jika ne, babu wasa a lamuransu ko kaɗan.
Suna gaba yana biye da su har office ɗin Mr Emmanuel, ba ko excuse ya shiga office ɗin fuskar nan tasa tamkar hadari, babu alamar wasa a tattare da shi. Ba ƙaramin razana Mr Emmanuel ya yi da kallon shi ba, ya tsorata ainun, jikinsa har kerma ya fara yi, a razane ya tambaye shi lafiya, yana magana yana zaro idanu wanda zai nuna maka tsantsar rashin gaskiya a tattare da shi, sannan yana magana murya na kerma da sarkewa, da kyar ma ya iya furta maganar.
Ko kallon arziki Mark ɗin bai yi mishi ba, dama can shi ba kallo mutane da arziki yake yi ba, cike da isa ya miƙa mishi paper ba tare da ya yi magana ba, hannu yasa ya karɓa ya buɗe dan ya gani.
Ganin wannan paper ta Anaya ɗin ce yasa ya ɗago ya dubi Mark ɗin, ina ai bai ga wajen wargi ba, yasan idan ya yi wani abin da ba dai'dai ba yanzu zai ji shi a in da ba'a dawowa, dan haka cikin sanyin murya ya ce "Am sorry sir it's a mistake, amma yanzu zan gyara". Ko sannu dai bai ce mishi ba, shiru ma magana ce, dan a cewarsa bai ga abin da zai buɗe baki ya ɓata wajen magana da wannan banza kazami da bai wuce ya yi ball da shi ba.
(Wannan ma Mr Emmanuel baka haɗu da zakunan William jacop ba, ashe da fitsari zaka yi a wando, to ka yi fatar kada ka haɗu da su kuwa, Mark ma kawai ya razana ka, ina ga kuma manyan shegun? Wato Lion and Areef 🤔)
Cikin sauri ya gyara mata marking nata, da mutunci ya miƙa mata paper, karɓa ta yi tare da daka tsalle ta rungumi Rimsha suna dariya kamar wasu zautattu, Allah sarki bayin Allah sun yi murna ba kaɗan ba.
Ganin Mark yana tsaye bai motsa bane yasa Rimsha ta ɗago tana kallon shi, to me ya tsayar da shi kuma ba zai zo su tafi ba? Ta tambayi kanta.
Shi kuwa Mr Emmanuel ganin hakan yasa ya gane abin da Mark ɗin yake nufi, wato ya shigar da marking na Anayar cikin list da zai sanya a result nata yanzu a gabansu yana ganinsa, hakan yasa cikin sauri ya fito da list na marking ɗin ya dubo sunanta, mugu har ya sanya mata zero a wajen, a gabansu ya canza zuwa