Showing 279001 words to 282000 words out of 359620 words
"Ba zan iya tashin bane, jikina duk a mace yake". Zuba mata idanu ya yi yana kallon yanda take faman turo baki tana magana.
Yatsa ya ɗaura a saman lips ɗin nata yana ɗan murza su, kara turo bakin nata sosai ta yi tana wasa da hannunta a saman kirjinsa, tana yi mishi tamkar tana zana zane a wajen, ɗan gyara mata kwanciya ya yi a jikin nasa ta yanda zai sami damar buɗe tula tulanta, hannu ya kai ya ɗan yi kasa da wuyar rigar zuwa saman tudunsu, a hankali ya shafa zanen sunan nasa, can kasan maƙoshinsa ya furta "Waye ya zana miki wannan zane?".
Ɗan ɗago idanu ta yi dan ta saci kallonsa saboda yanda ta ji ya ya kuke maganar alamar baya cikin mood mai kyau. Tana ɗagowa karaf suka haɗa idanu, kasa ta yi da nata tana faɗin "Wata mata ce a garinsu Kausar". "Kuma sai kika buɗe mata jikinki ta yi zanen? Sannan a rasa ina za'a buɗe mata ta zana sai nan wajen?".
Ɗan saƙalo wuyarsa ta yi dan ta miƙe ta bar jikin nasa saboda ta ji yanayin maganarsa ya fara sauyawa, kada ya je ya zaneta ko ta sha mari, gara mata ta yi nesa da shi idan ya so ta amsa mishi tambayar a can, idan ta kama duka ne kafin ya miƙe ya capkota ta zunduma waje a guje abinta, sai dai ina tana ƙoƙarin miƙewa ya ɗaura hannu a saman bayanta tare da mayar da ita ta kwanta dan dole ba dan ta so ba.
"Ba yanzu kika ce ba zaki iya tashi ba? Amsa my question first ma dai". Har lokacin hannunta na a sakale a wuyarsa bata saki ba, ɗan shafa wuyar tasa ta fara yi tana tunano shawarar da gwaggo take gayawa mummy idan ran daddy ya ɓaci abin da zata yi mishi ya sauko cikin ƙanƙanin lokaci, yau karatun gwaggo take tunanowa, nan take zuciyarta ta amince mata da shi ma ta yi mishi hakan ko zai sauko yanda ya fara yi mata magana da zafan nan, kishinsa ya motsa.
Tuna hakan yasa ta cigaba da shafa wuyan nasa a hankali tana haurawa zuwa baki bakin gashin kansa ta sake sauko da hannunta zuwa saman bayansa. "Yaya Saif lokacin fa da aka yi mini zanen ina karama, ban kai haka ba, lokacin kamar ma ban cika 13 years ba". Ta yi maganar tana ɗago da dara daran sleeping eyes ɗin nan nata, ga su sun kara wani irin fari tas da su kamar audiga.
Tana ɗago idanu ya ɗago haɓarta shi kuma ta yanda zasu ji daɗin ganin juna da kyau, hannunsa dake saman bayanta ya zura cikin rigarta yana shafa lallausan bayan nata, kwanciya ya yi da ita a jikinsa har lokacin yana kallon cikin kwayar idanunta da ta saukesu kasa tana ɗan kallon gefe hannunta na saman wuyarsa, cikin ɗarɗar ta ɗaura hannu a saman ƙashin maƙoshinsa, wani irin zirr ya ji a jikinsa, bai san time da ya rungumeta sosai a jikin nasa kamar wani ya ce zai kwace mishi ita ba.
"Meesha" Ya ambaci sunanta a hankali, ɗago kai ta yi da nufin ta amsa, tana ɗagowa ya haɗe ɗan bakinsa da nata, wani irin guguwace ta ɗebeta zuwa wata duniya, dan kuwa a kiss da ya yi mata yau karo na uku, biyun dukka bata cikin hayyacinta, ba zata iya wani gane me ma ta ji ba, yanzu kuwa tana cikin natsuwarta, sai jinta ta yi tamkar wanda aka zarewa laka, sumar kwance ta yi tana jin lallausan lips nasa dake yawo a tsakanin laɓɓanta na sama da na kasa, jin abin take yi tamkar a mafarki ko a tunani.
Sai da ta ji saukar hannunsa a saman mazaunanta ne ta dawo daga duniyar da ta afka, nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke cikin tsoro jikinta na kerma ta yi ƙoƙarin kissing na shi ita ma dan laushin lips nasa sun kiɗimata over, tana son ta ji, dama idan baku manta ba, ɗan bakin nan nasa yana ɗaya daga cikin abin da take bala'in kauna a face nasa.
Hannunta dukkan biyu tasa ta tallabo kumatunsa tare da capko lips ɗin nasa ta datse idanunta gam dan ma kada ta ga wani irin yanayi ne zai bayyana a saman face nasa. Tana fara kissing nasa bai san time da ya waro dara daran idanunsa waje sosai ba, ga idanun nasa sun yi jawur kamar wuta. Ganin da gaske ita ce take kissing nasa yasa ya lumshe idanunsa saboda wani azababben daɗi dake ratsa shi, ji yake yi tamkar ya mayar da ita cikin cikinsa, duk wannan abin da yake faruwa sam baya cikin hayyacinsa, ya jima da afkawa duniyar sama jannati, ga shi ta zo ta kara rikita masa ƙwaƙwalwarsa da kissing nasa da ta fara yi.
Ita ma kuma laushin laɓɓansa ya jata zuwa duniyar da ya faɗa wato duniyar sama jannati, sam bata ji bata gani ta fita a hayyacinta, kissing nashi take yi babu kama hannun yaro, hannunta ya kama ya ɗaura a kansa, watsa gashin nasa ta shiga yi tana kara lafewa a jikinsa, nan take sautin numfashinsa ya sauya, hannu ɗaya ya ɗaura a saman gashin kanta yana ɗan shafawa izuwa bayanta.
Call ɗin daddynsa ne ya dawo da su daga duniyar da suka faɗa, sakin lips ɗin nasa ta yi tana ƙoƙarin sauka daga jikin nasa, rikota ya yi idanunsa a lumshe ya mayar da ita saman kirjin nasa yana sauke numfashi a hankali hankali, call na farko ya katse na biyu ya sake shigowa, sam baya ji kamar zai iya ɗaukar kiran, cigaba da shafa bayanta ya yi yana wani sauke nauyayyar ajiyar zuciya.
"Yaya Saif ana kiran wayarka, in ɗauko maka ne?" Ta yi maganar cikin sanyin murya, shiru bai amsa mata ba, kira na uku ne ya sake shigowa da alama dai daddy yana bukatar yin magana da shi cikin gaggawa ne. "Yaya Saif kayi magana mana, sai mutun ya yi ta yi maka magana amma ka share shi". A wannan karon ta yi maganar a shagwaɓe sosai.
Waro idanunsa da suke jawur da su ya yi, can kasan maƙoshinsa ya furta "Ni ban san yaushe kika zama irin Aseef ba a wajen magana". Turo baki ta yi tana faɗin "Kai yaya Saif ni dama haka nake maganata". Tana magana idanu a rufe ruf, shiru ya yi bai sake yin magana ba ya zubawa face nata idanu yana jin wani iri a cikin zuciyarsa, tabbas face ɗin Rimsha da Jehan suna gefa shi cikin yanayi a duk lokacin da ya kallesu, musamman ita Rimsha ya rasa me dalilin da yasa yake jinsu a cikin zuciyarsa.
Call ɗin daddy na biyar ne ya sake shigowa, hannu ya miƙa saman bedside drawer ya ɗauko wayar, video call ne, dad ya kira ne dan ya ga ɗan nasa ya ji kuma ya tafiyar tasu ta kasance, ko a jikinsa ya ɗauki kiran tana kwance a saman kirjin nasa yana shafa kanta zuwa bayanta da hannunsa, ta lafe abinta idanu a rufe.
Lokacin da ya ɗauki kira suka yi 4 eyes da dad ɗin, wani irin murje idanunsa daddyn ya yi dan ya sake ganin wai shin abin da yake ganin nan gaskiya ce ko mafarki ne, mace a kwance a saman kirjin Lion, bayan haka kuma yana shafa lallausan gashin kanta? Anya ba mafarki yake yi ko kuma gizo idanunsa suke yi mishi ba kuwa? Ya tambayi kansa da kansa. Shi kuwa Lion ko a jikinsa, ita ma bata san cewa ya ɗauki kiran ba, bata san cewa Video call bane, haka zalika bata san cewa daddynsa ba ne, idan baku manta ba idanunta a rufe ruf.
"Why are you looking at me like that daddy?". Ya tambaya yana dawo da kallonsa a saman face ɗin uncle Herry dake kusa da daddyn.
"Romeo what do I see? tell me that it's not what am thinking, tell me it's a dream not reality". Cikin tsananin tashin hankali ya yi maganar
Jin voice ɗin daddyn yasa ta waro idanunta waje da sauri, karaf sai cikin idanun daddy, domin kuwa wayar tana saitin face nata da yake ya ɗan yi baya da wayar ta yanda zai kalli daddyn nasa da kyau.
Ganin shi yasa ta yunkura da gudu zata sauka daga jikin mijin nata, riketa ya yi tare da mayar da ita yana faɗin "Ina zaki je kuma?". Kallon wayar ta yi ta kasa magana, mayar da kallonsa a kan daddyn ya yi yana faɗin "This is the reason why you called me dad? You called me to ask me if you are dreaming or not, Why didn't you ask Aseef or Areef?". Tashin sense, wato ma shi Lion ya nuna sam bai san me daddy yake yi wa mamaki ba.
"Romeo why do you always want to see me sad?". Shiru ya yi bai tanka ba, dan bai san me zai ce ba, ita kuma ta datse idanunta gam tare da juyar da fuskarta gefe guda dan ma kada daddyn ya yi ta kallonta.
Jin ya yi shiru ne yasa daddyn ya tausasa muryarsa dan yasan wannan shiru na Lion ba alkhairi bane a gareshi, zata iya kwaɓe musu ne kaca kasa, so sai ya tausasa muryarsa tare da canza maganar yana faɗin "How is your journey?" Jinjina mishi kai ya yi alamar komai normal ba tare da ya yi magana ba. "Okey good where is Brady?".
Shiru ya yi na almost 2 mins tamkar ba zai yi magana ba, sai can kuma ya ce "Daddy how are and how was your body?" Idan da sabo sun saba da halinsa, kullum ba wani canji a tattare da shi, tun da ya taso har izuwa yau hakance, idan ka yi mishi tambaya bata yi mishi ba baya amsawa sai dai ya yi maka magana akan abin da yake gabansa kawai, Rimsha ce kawai a duniya taga canji a tattare da shi, bayan ita ko TRIPLETS nasa babu wani canji da suka gani, yanda yake a baya hakan yake yanzu ma, babu wata annuri ko tausayi bare girmama ɗan adam a lamuransa, so har yanzu kamar baya yake amsawa daddyn nasu ma, idan ka yi mishi magana sai ya ɗauki mintuna yake amsawa, a hakan ma idan ya ga damar amsawar kenan, idan bai ga dama ba sai dai ka jira amsa har ka gaji ka hakura, Rimsha ita ce mutun ta farko da yake amsawa magana idan ta yi mishi a tsakanin ƴan sakanni, ko su Aseef sai ya ɗauki lokaci, wani lokacin ma baya amsa musu sai dai ya jinjina musu kai kawai alamar ya ji, shi ma jinjina kai ɗin ba kowa yake samu ba.
"Am fine my son what of u?". Nan ma jinjina mishi kai ya yi alamar yana normal. "Romeo wai me zaka je yi a kasar Russia ne? Baka faɗa mini abin da zai kai ka ba". "Daddy do you have any relationship with Russia ne da ka damu haka?". Cikin sauri ya girgiza mishi kai alamar a'a, yanayin yanda ya amsa mishi da sauri ma sai da yasa Lion ɗin zargin wani abin, amma sai ya basar da cewa "To dad you don't have any relationship with then amma kake takura wa kanka har haka?". Shiru ya yi dan yasan waye ɗan nasa, idan suka cigaba da jan magana zai iya sanya shi ma ya faɗi abin da bai yi niyya ba.
Tun da suka fara magana daddyn yake son tambayarsa meyasa idanunsa suka yi jawur har haka, amma gudun amsar da ɗan nasa zai ba shi ne yasa ya danne, dan kuwa idan ya ji cewa ɗansa ya haɗa jini da bakar fata, ma'ana ya kwanta da Rimsha ne to fa gaskiya zuciyarsa zata iya bugawa ya mutu, dan ya yi wa bakaƙen fata mummunar tsana, a hakan ma bai san cewa su musulmai bane, da ya san su Rimsha musulmai ne ai da bala'in ta fi hakan, tsanar sai ta ninka hakan, kuma yasan halin Lion baya karya, duk abin da ya tambaye shi amsa kai tsaye zai bashi, babu shayi ko wani ɗar, so yana iya gaya mishi kaza ne ya faru, dan su ba kunya ce ke garesu ba, rufin asirinsa kada ya jiyowa kansa bala'i ne yasa ya danne ya yi shiru tsit bai tambayi dalilin jan idanun nasa ba, yanzu ma da yake ganinta a saman kirjin ɗan nasa tamkar zai mutu da bakin ciki haka yake ji, har wani harbawa zuciyarsa take yi, bare ya ji wani labari daban, ai abin ba'a cewa komai, sai dai fa zuciyarsa sai zargin hakan take yi mishi, duk da yasan canzawan launin idanu ga namiji ba lallai sai idan sha'awarsa ta motsa ba, akwai dalilan da suke kawo hakan, ciki kuma har da ɓacin rai, wahala da kuma gajiya, barci, rana da sauransu.
Jin saukar hawayenta a saman kirjin nasa ne yasa ya dawo da kallonsa kanta, kuka take yi hawaye wani na bin wani, ita kanta bata san dalilin yin kukan nata ba.
Meesha ya ambaci sunanta, can kasa kasa ta amsa mishi na'am. "Why are you crying?". Shi dai daddy ya saki baki yana ganin ikon Allah, tunani ma yake yi wai ko dai ba da ɗansa yake magana bane? Ko dai an canza mishi Lion nasa ne?.
Shiru bata yi magana ba dan bata san me zata ce ba, bakin ciki take ji yanda daddynsa yake nuna musu kiyayya karara, ita dai tasan babu wanda ya isa ya halicci koda ɗan yatsa a duniyar nan, da fari da baki dukka Allah ne ya yi su, kuma da ya yi su bai ce baya son baki ko kuma yafi son fari ba, ba wanda ya fi so face wanda ya fi tsoronsa ya kuma fi bauta mishi tare da aikin alkhairai, amma ta rasa meyasa wasu suke cewa basu son bakake fata sai farare, su sanya wasu suna kauce hanyar Allah ta hanyar yin bleaching na fatarsu dan su burge mutane, yin hakan babban kuskure tare da gefa kai ga hala, duk wanda ya canza halitta daga yanda Ubangiji ya halicci shi to ya jira sakamako mai girma na azaba da Ubangiji ya tanada mishi, ba sai kin canza wani abin daga cikin halittarki ba zaki sami abin da kike so, Allah baya sanyawa bawa abin da bata dace da shi ba, kowa abin da ya dace da shi ake ba shi, ku ɗauki darasi a kan Rimsha, ita dai gata chocolate color, bata taɓa raina halitta ko kalar fata da Allah ya yi mata ba, kullum tana gode mishi da ni'imar da ya yi mata, ga shi ya yi mata sakayya ta hanyar bata jarumin miji fari tas tamkar daga kansa an gama haske da kyau, komai ya haɗa, kuɗi, mulki, isa, izza, kyau na wuce misali, hasken fata na wuce misali, hutu, mukami mai girma, gashin kansa bakinkirin mai bala'in kyau har tsakiyar bayansa idan da zai bari bai yanke ba, fuskarsa kawai ya isheta ta zauna ta yi ta kallo daga safe har yamma saboda kyau, kalar idanunsa mai tsada wanda kowa yake burin mallaka, idan ta zo kusa da shi bakakirin take zama, amma a haka Allah ya jarrabe shi da sonta, duk duniya ita kaɗai take jin wani irin muryarsa da ba wanda ya taɓa yi wa magana da shi, ita kaɗai take yi mishi magana ya amsa kai tsaye ba sai ya ja lokaci ba, ita kaɗai take zuba mishi shagwaɓa kuma ya burge shi, mutumin da a baya babu wani abin da yake burge shi sama da aikinsa, baya ɗaukar komai da daraja face TRIPLETS nasa da kuma aikinsa, sai daddynsu, amma yau an wayi gari ta shigo cikin rayuwarsa a in da ta zama ciwon TRIPLETS ɗin nasa, wato cikonsa kenan, dan ita ce shi, wasu abubuwa ma ya fi sake mata sama da TRIPLETS nasa, to bai kamata ku canza daga halittar da Allah ya yi muku dan burge wasu ba, idan wani bai so ki a haka ba, Allah zai kawo miki wanda ya ninninka shi, Allah dai ya bamu dacewa yasa ku gane gaskiya ku dai'na cutar kanku, ku canza halittarma sam baku kyau, sai ku zama kamar wasu dodanni, dan babu wanda ya isa ya haɗa na Allah da na kari na kanti, da kunsan munin da kuke yi idan kuka canza wani abin na daga halittarku, wlh da ko kusa ko alama ba zaku yi ba, Allah ya yi mana kyakkywan karshe.
Katse kiran ya yi tare da kashe wayarsa bakiɗaya dan kada su dame shi da kira, ɗago haɓarta ya yi yana tambayarta meya faru take kuka. "Yaya Saif menene laifin mu da daddy zai ce baya son bakaken fata? Mune muka yi kanmu?". Shiru ya yi yana tunani, tana da gaskiya, shi bai ga abin ki a bakin fata ba, shi dukka ma ɗaya yake ɗaukarsu, kafin ya musulunta ne lokacin da yake krista ne yake wannan kabilanci, amma da ya musulta yasan da fari da baki dukka Allah ne ya yi su, daga nan bai sake cewa baya son baki ba, kowa ma shi ba ruwansa, idan aiki ta haɗasu to za'a yi kawai, sannan a kan Rimsha ya kara jin yana son bakaken fata over, domin kuwa ita dai chocolate color ce, color mai tsada a duniya, amma ba wata macen da yake ji a ransa biyunta, tana bala'in yi mishi kyau kuma tana burgesa, Turawa ƴan uwansa sam basu burgesa ko kaɗan.
Goge mata hawayen nata ya yi ba tare da ya bata amsa ba ya ce "Jeki ci abinci bari na kira Mark ya kawo miki". Da mamaki ta ɗago tana kallonsa, ko yaushe yasan cewa tana jin yunwa kuma?. "Why kike yin mamaki? Ai ba iya aikin soja kawai na iya ba, harda karantar mutane, ki ci abinci ki zo ki gaya mini why are you watching my pic's like film?". Yana magana yana kunna wayarsa dan ya yi wa Mark massage ya kawo musu abinci.
"Kai yaya Saif, ashe kai ma ka iya sa ido ko? To ni ai bana kallon hotonka" Shiru bai sake yin magana ba, hannunsa ta riko cikin nata tana kallon ƴatsun hannun nasa, dama tana burin ta ga ta taɓa waƴan nan kyawawan latsun nasa,