Showing 258001 words to 261000 words out of 359620 words

Chapter 87 - Triplets Book 3 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2040

yau.

Wanka ya yi tare da fitowa ya shiga dressing room, tana zauna a wajen har ya fito cikin shirin kayan barci, saman bed nasa ya haye ba tare da ya bi ta kanta ba, cike da tsoro ta ce mishi "Yaya Saif in zuba maka abincin". Har cikin ransa ya ji dama dama najin sautin voice nata da ya yi, ga shi ta yi maganar cikin natsuwa, voice ɗin nata kuma da akwai shagwaɓa a cikinta.

Shiru ya yi bai tanka ba, mikewa ta yi cike da tsoro ta dawo saman bedside drawer, jikinta har kerma yake yi saboda tsoro, amma sai ta daure ta ɗan shagwaɓe murya kasa kasa a nitse ta ce "Ayya Yaya Saif in saka maka abincin ne?". Waro dara daran blue eyes da suke jawur ya yi a saman face nata, ta tsorata da ganin idanunsa ba kaɗan ba, shi kuma ya ji duk wani ɓacin ransa ya gudu da ya ga kyakyawan face nata, sai ya ji wani sanyi a cikin ransa.

A hankali ya lumshe idanun nasa tare da sake buɗesu akanta, still dai ita ɗin ce, Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke tare da mikewa zaune ya yi shiru kamar mai tunanin wani abin. Zuba mishi idanu ta yi ya ɗan ɗauki lokaci a haka kafin nan ya jinjina mata kai alamar ta zuba mishi abincin, ganin kyakkyawar fuskarta yasa ya ji zai iya cin abincin, saɓanin yanda ya shigo cikin ɓacin rai, sam bashi da niyar sanya wani abin a bakinsa, ya yi niyar ya yi barci ne kawai.

Amma sai ga shi a dalilinta ya ci abincin mai yawa ma, dan yana jin yunwa sosai, tun fitarsa da safe bai ci komai ba sai Maltina, dole dama ya ji yunwa over, ba ƙaramin daɗi ta ji ba ganin ya ci abinci, mikewa ya yi ya nufi toilet ya yi brush ya fito, zama ita kuma ta yi ta ci abincin kaɗan kafin ta kwashi kayan abincin da nufin ta mayar kitchen, ba tare da ya kalli in da take ba ya ce ta bar kayan abincin a wajen ai ya hanata fita ko nan da palo, so ta yi kwanciyarta duk time da Areef ya shigo zai fita da kayan abincin.

Ba dan ta so ba hakan ba ta ajiye kayan tare da kwanciya a saman sofa, kayan barci ne a jikinta sai ta ɗaura hijabi a sama, shi kuma saman bed nasa ya haye ya kwanta ba jimawa barci ta yi awon gaba da shi dan a gajiye ya dawo, ita kam mamaki da al'ajabin wannan al'amari ya hana yin barci Baiwar Allah, bare ma yanda daddynta ya bada goyon baya ta kwana a ɗakin mutumin da ba muharraminta ba, ba mijinta ba, abin ya ɗaure mata kai sai take ganin kamar ba daddyn nata bane, kamar an canza mata shi, ko kuma ciwon dake damun Lion da Mark ne yake damun daddyn nata shi ma. Tunani dai kala kala cike fal ranta har karfe 1, da kyar ta samu barci ya yi awon gaba da ita.

Karfe biyu daidai Lion ya tashi ya fara sallolinsa kamar yanda ya saba, bai mayar da barci na sai da ya yi sallar asuba, ita kuma da ta yi sallar asuba ta hau shirin zuwa school saboda partynsu.

Yana barci amma yana jin duk wani motsinta, tsab ta shirya ta yi wani irin azababben kyau tamkar ba Indiya, sai ta saki gashin kan nan nata har gadon baya bata ɗaure ba, sam bata san ita matar aure bace, ta yi dressing nata son ranta, ba karya ta fito ɗas.

Fitowa ta yi zuwa kitchen ta karɓi abinci, yau Mark duk rashin kallonta da baya so yi sai da ya kalle ta ya sake waigawa, dan fa ta fita, duk wanda ya kalleta a gidan sai ya sake waigawa ya kalleta, ga sarin nata launin pink color abin ba'a magana.

Saman table ta zauna ta ci abincin nata, tsabar murnar zuwa partyn nan ko neman su daddynta bata yi ba, haka ta tafi school basu haɗu da Lion ba, kuma bata nemi su daddy ba, ita kam kawai ta yi tafiyarta, ta kuma tafi da wayar da Lion ɗin ya bata dan su yi hotuna da classmate nata da Anayarta, dama sun yi da Anaya shigar India zasu yi, ita Anayar ce ma ta tsayar musu da kalar da zasu saka.

Haka Mark ya buɗe baki yana ganin kyau ɗin da Anaya ta yi, kamar wasu tagwaye, tamkar ka sace su ka gudu da su, kyau iya kyau ba'a magana.

Mark yana zaune a wajen har motarsu Areef ta iso, dama sun ce mata zasu zo, Aseef, Areef, daddynta, Akila, da kuma Jehan, ta sha faɗa wajen daddy ba kaɗan ba da bata sanya ɗankwali ba, sam bai ga fitowarta daga gida ba da ba zai bari ta fito babu ɗankwali ba, shi kam Aseef ko a jikinsa yana tare da rigimatinsa suna aikin da suka saba, wato zubawa juna shagwaɓa, Areef kuwa ba abin da ya ayyana a ransa irin a samu ɓacin lokacin Lion ya ce zai zo wajen nan, wlh Rimsha ta shiga uku, mai kwatarta sai Allah, dan wlh idan bata yi sa'a ba karshen gashin nan nata ne ya zo, shi kansa ya yi kishin ganin yanda idanun dubbanin jama'a har da iyayen yara manyan mutane suke kanta, suna kallonta, duk in da ta juya kowa ita yake kallo, lallai Allah dai yasa kada wata kaddarar ta kawo Lion nan, dan idan bai tashi jama'a da boom ba abu kaɗan ne zai hana, amma tabbas zai tashi kwakwalwar Rimsha da tunaninta, sai ta yabawa aya zakinta ba kaɗan ba, ga shi dan iskanci har da wani saka wasu siraran jigida masu bala'in kyalli da kyau suna ɗaukar hankali mutane a kugunta ta saman kayan, kun san dama suna ɗaura sarka a saman sarin, to ita ba ɗaya bama ta ɗaura almost guda biyar sirara ta zuba a wajen.

Areef dai yana taya ɗan uwansa kishi, ya kasa jurewa sai ya mike ya bar wajen dan ya kira numberta ta fito daga wajen cikin rufin asiri su koma gida, kash babu network, wayar ta ki shiga, hotuna take ta ɗauka da Anaya da classmate nata, anata gabatar da abubuwa.

After some minutes ta nemi Anaya a wajen ta rasa, ɗan waige waige ta fara yi bata ganta ba, wata classmate nasu dake kusa da ita mai suna Aisha ta tambaya ina Anaya? Cikin nuna kulawa ta bata amsa da Mr Emmanuel ya aiko an kirata, ɗan zaro idanu ta yi tana mamakin yanda akayi Anaya ta bar wajen ba tare da ta gaya mata ba, ko da yake jama'a sun yi yawa, to amma me Mr Emmanuel zai yi mata kowa yana tsaka da shagali?.

Tuna banzan hali irin nasa ne yasa ta sauko daga saman step ɗin da sauri ta fito daga cikin hall ɗin, kai tsaye office nasa ta nufa, shi kuma Areef yana ta baya wajen motocinsu yana gwada kiran numberta, Aseef da daddy tare da su Jehan suna zauna a saman kujerun da aka tanadawa iyaye, sam a cikinsu babu wanda ya lura da ta bar hall ɗin, da yake sai zuba hira Aseef da daddy suke yi kwana biyu basu haɗu ba.

Ko da ta shiga office ɗin babu kowa a ciki, har ta juya zata fita sai ta kalli takalmar Anayar guda ɗaya a dai'dai wajen table chairnsa, da sauri ta karisa wajen tana kallon takalmin, hakan na nufin kenan tabbas Anaya ta shigo office ɗin, to ina take? Ta tambaya tare da ɗagowa tana bin office ɗin da kallo, tuna cewa ya taɓa cewa Anayar ta shiga cikin toilet ne yasa ta yi saurin karisawa bakin kofar toilet ɗin tana knocking.

Kamar jira yake yi ayi knocking, cikin kankanin lokaci ya buɗe kofar daga ta ciki, yana buɗewa kuma ya fesa mata wani farar powder a fuska, nan take ta zube kasa sumammiya, dariya ya yi yana faɗin "Dama nasan dole zaki zo neman Anaya dan ɗaya bata tafiya sai da ɗaya, shiyasa na zauna zaman jiran zuwanki dan na haɗa ku lokaci guda nayi abin da nake so, nasan daga yau zamu tafi hutu ba zan sami cika burina a kanku ba, to dole nayi amfani da damata ta yau". Yana surutu yana ƙoƙarin ɗagota dan ya shigar da ita cikin toilet ɗin, daddaɗar kamshin perfume ɗin Lion da bai taɓa jin irinta ba ne ta daki kofofin hancinsa wanda ya sanya shi ɗago kai cikin sauri dan yaga daga ta ina wannan fitinannen daddaɗar kamshin ya fito.

Yana ɗago ido suka yi 4 eyes da blue eyes na Lion dake tsaye a bakin kofar shigowa, hannunsa na rike da wayarsa Mark yana tsaye a ta bayansa, shi Lion ya biyota ɗaukarta su wuce ne, idan baku manta ba suna da tafiya yau, shi kuma Mark dama aikinsa ne kula da ita, so ya kalli time da ta shiga office ɗin, shi ne da Lion ya zo ya ce ina take Mark ya kirata su tafi, sai ya ce tana office na uncle nasu, ba zai iya jira ba, shi ne ya fito da kansa dan ya ɗauketa su wuce, shi kuma Areef ganin Lion yasa ya shiga tashin hankali, dan kuwa yasan Rimsha ta shiga uku.........E KAM TA SHIGA UKU HAKA ZALIKA WAƳAN DA SUKA SHIGA UKUN ALLAH YA YI YAWA DA SU A SCHOOL ƊIN, CIKI HAR DA DADDYNTA DAN BASHI DA HANYAR WANKE KANSA, KO ZAI MUTU ZA'ACE AI YAGA DRESSING DA TA YI, TO JUSTICE FOR MUTANE DAYAWA.

E 65-66💋


Ganin idanun Lion ba karamin razana ya yi ba, dama abin da kuka sani ne, duk dakiyar mutun da kwarin zuciyarsa yana yin idanu biyu da Lion sai ya razana, dan blue eyes yanayin su ma tun ainahi idanu ne masu firgitarwa bare ace dara dara ga masu shi fuska a ɗaure, dole a hantar maza ta kaɗa sosai.

Sakinta ya yi tare da watsawa a guje ya koma cikin toilet ɗin ya rufo kofar tare da murza key. Wani irin huci Lion yake fitarwa tare da furzar da wani iska mai azababben zafi daga bakinsa, idan ya runtse idanunsa kawai ganin yanda Mr Emmanuel ya riko hannayenta zai ɗaga ta yake yi, jin zuciyarsa yake yi tamkar zata faso kirjinsa ta fito waje, har wani irin tsuma jikinsa yake yi tsabar tsananin ɓacin rai, gabaɗaya gashin jikinsa sun miƙe tsaye saboda halin da ya shiga, shi kansa Mark da already ya san halinsa, amma yau ya razana, dan gaskiya bai taɓa ganin ogan nasa ya yi irin wannan zuciya haka ba, yana zuciya a baya amma baya kai haka, dan ko bai zuciya bama hukuncinsa bata da kyan gani bare kuma ace ya zuciya, so bai cika bari yana zuciya yana hawa sosai bama, dan idan fa ya zuciya ya hau kifar da komai yake yi, babu wanda ya isa ya tinkaresa ma bare ya dakatar da shi.

Kofar toilet ɗin ya nufa da wani irin taku na nuna isa da jarunta, da sauri Mark ya bi bayansa, cikin fushi ya yi wa kofar wata mahaukaciyar taku, sai ga kofar ta ruguje ta faɗi kasa ta cikin toilet ɗin, sam bai shiga cikin toilet ɗin ba, dan kyama gabaɗaya office ɗin ya bashi, ba dan Rimsha ba wlh yafi karfin shiga irin wannan dattin wajen a cewarsa, kuma kunsani already baya son datti komai kankantar shi, baya shiri da datti sam, shiyasa yaki shiga cikin toilet ɗin dan yasan zai yi amai, haka gabaɗaya TRIPLETS suke da wannan azababben kyamar, idan suka ga abin da bai yi musu ba, to sai sun yi amai ko a ina ne.

Ta gefen idnaunsa ya kalli Mark, Mark ya gane karatun ma'ana shi ya shiga ya fito da Mr Emmanuel kenan, da sauri ya shiga, ba shiri ya ja birki ganin Anaya kwance cikin baf ɗin wanka babu kaya a jikinta, wani irin azababben harbawa zuciyarsa ta yi lokaci guda, dafe kansa dake barazanar tarwatsewa lokaci guda ya yi, nan take idanunsa suka yi jajir tamkar wuta, kawar da kallonsa daga kanta ya yi zuwa kan Mr Emmanuel dake manne da jikin bango yana zare idanu kamar ɓera a tarko.

Kayanta ya ɗauka ya rufa mata a jikinta kafin ya damko wuyar rigar Mr Emmanuel ɗin ya ja shi zuwa wajen, har wani ruwa mai kama da hawaye ne suka kwanto mishi a cikin idanunsa, tun bayan mutuwar budurwarsa bai sake shiga tashin hankali irin na yau ba, bai taɓa shiga ɓacin rai irin na yau ba, har wani irin numfashi yake yi mai kama da shasshekar kuka, zuciyarsa na harbawa da sauri sauri ji yake yi tamkar zai zube kasa, kafafunsa suna ƙoƙarin kasa ɗaukarsa saboda abin da ya gani.

Mikawa Lion shi ya yi tare da ɗan yin gaba kaɗan dan zuciyarsa gab take da tarwatsewa, da kallo daya Lion ya yi wa Mark ɗin ya fahimci yau ran Mark ya kai kololuwa wajen ɓaci, yau tsawon shekaru 5 suna tare bai taɓa ganinsa a cikin irin wannan hali ba sai yau, hakan yasa ya fahimci dole akwai abin da ya gani a cikin toilet ɗin ne da ta jefa shi cikin wannan yanayi haka.

Amma sai ya basar tare da damko wutar Mr Emmanuel ya ɗaga shi sama tare da shakesa sosai, wurgi da shi ya yi a can gefe guda, yana mai jin kuna a cikin zuciyarsa. Wani irin karfi Mark ya ji ya zo mishi lokaci guda, har haɗa zufa yake yi, watsi ya fara yi da computers da kuma gabaɗaya takardun dake cikin office ɗin dan tsabar ɓacin rai, Lion kuma yana aikin jibgar Mr Emmanuel, sake ɗaga shi ya yi, ya yi wurgi da shi ta gefe guda.

Yana yin wurgi da shi Mark ɗin ya tinkare shi gadan gadan tare da damƙo wuyarsa da rigar jikinsa bakiɗaya ya haɗe ya shaƙosa tare da yin sama da shi ya sake wurga shi kusa da Lion ɗin, tamkar kwallo haka suka mayar da Mr Emmanuel a cikin office ɗin nasa, gabaɗaya sai buga shi suke yi, suna haɗe shi da jikin bango ne chairs dake office ɗin da sauransu, duk wasu takardu, desktop computers ba abin da ya rage da ransa, komai ya tarwatse, ko kwallo suka samu ba zasu buga shi kamar yadda suka buga Mr Emmanuel a yau ba, shi kam Mark idan ya tuna yanayin daya ga Anaya a ciki sai ya ji kamar ya haɗiyi zuciya ya mutu, hakan tasa ya ji wlh ko gawar Mr Emmanuel ba zai iya bari ba, a haukace dai suka yi mishi duka har rai ya yi halinsa basu sani ba, dan kusa dukkansu sun shaki bakin ciki ne na wuce misali, sai da suka karya mishi kafafu da hannaye, shi Lion ma ya kasa hakura har sai da ya ɗaga shi sama ya ɓalla mishi baya da jikin wata table dake cikin office ɗin, sannan ne suka rabu da gawarsa, dukkansu biyu an rasa mai ɗaga idanu ya kalli su Rimsha, wani azababben kishi ne yake cin zuciyarsu, shi dai Lion idan ya lumshi idanu sai kawai yaga lokacin da Mr Emmanuel ya kama hannunta, wannan abin idan ya tuna ji yake tamkar ya haɗiyi zuciya kawai ya mutu sai ta fi mishi sauki, shi kuma Mark yanayin da ya sami Anaya yake tunawa, sai ya ji kamar yasa bindiga ya harbi kansa ko zai huce, duk idan suka tuna sai sun sake taka gawar Mr Emmanuel, da alama dai sun fita a hayyacinsu sosai, tsantsar kishi ne yake ɗawainiya da su.

Sun jima a haka kafin Lion ya nufi wajen da take kwance, ji ya yi kamar kawai ya yanke hannun nata da Mr Emmanuel ya taɓa dan haushi, dukawa ya yi ya saɓeta a kafaɗarsa ya nufi waje, sam bai san da Anaya a cikin toilet ɗin ba. Ganin ya fita ne yasa Mark ya nufi cikin toilet ɗin, da kansa ya mayar mata da kayanta kaf, wasu zafafan hawaye ne suka fara gangaro mishi a face nasa, tabbas ya san cewa Mr Emmanuel bai yi mata komai ba, dan da alama ya gama cire mata kayan ne Rimsha ta shigo ta yi musu knocking, amma duk da haka, zafin ya cire mata kayan ne yasa shi cikin wannan hali da yake ciki, dole ya yi hawaye, dan wani lokaci idan bakin ciki ta yi maka yawa, idan baka zubar da kwallah ba, to kana iya haɗiyar zuciya ka mutu, zubar da kwallah ne rufin asirinka, shi zai taimaka ya rage maka raɗaɗin da kake ji a cikin zuciyarka, shi ma dai Mark hakan ce ta kasance da shi........... Tab da ace Lion ne ya sami Rimsha kamar yanda Mark ya sami Anaya, da ina ga yau kashe kansa kawai zai yi dan kishi🤔😭😌

Kallon face nata ya yi, tunanin powder daya hura musu ɗin yake yi, powder ce mai haɗari da suke hana amfani da ita, goge hawayen face nasa ya yi tare da ɗaukarta a saman kafaɗarsa ha bi bayan Lion.

A cikin motarsa Lion ya shifiɗeta a gidan baya tare da bawa sojojinsa guda biyar da ya zo da su umarnin a kan su kama mishi gabaɗaya malaman da suke cikin school ɗin nan, su kuma students ɗin su rufe su a cikin hall ɗin, cikin girmamawa suka karɓi umarni tare da wucewa.

Su daddy suna tsaka da kallon party, anata abubuwa kawai basu ankara ba suka ga diran jibga jibgan Turawan sojojin Lion, gasu da tsawo da faɗin kirji kamar wasu zakuna, farare tas tamkar ka taɓa jini ya zuba, sai dai fa fuskokinsu babu alamar imani ko ɗigo a wajen, shi ma Areef a lokacin ya dawo yana cikin hall ɗin, ya kasa sukuni dan yana jiyewa Rimsha abin da zai biyo baya, ya kasa gayawa daddy Lion ya zo.

A ɓangaren Mark kuwa, shi ma a cikin mota ya kwantar da Anaya, sai lokacin Lion ya fahimci dalilin da ya sanya Mark cikin tashin hankali haka, shiru ya yi bai tanka musu ba.

Mu koma baya kaɗan, da daddyn Rimsha da daddyn Anaya duk sun zo taron, sai dai basu haɗu ba, shi dai daddyn Anaya yana ta kallon Rimsha, ya kuma kuduri


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login