Showing 189001 words to 192000 words out of 359620 words

Chapter 64 - Triplets Book 3 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2032

girman Allah ku daina, ku daina lalata ƴaƴan mutane, kuna cutar rayuwarsu, kuna ruguza musu duk wani farinciki, kuna rusa musu jin daɗi kamar sauran mata, kusa su fiskancin tsangwama wajen mijinsu da sauran ƴan uwa, ku ji tsoron Allah ku dai'na, akwai kiyama, akwai lahira ranar da zaku biya duk abin da kuka ci, akwai mutuwa, sannan ko baku mutuba akwai tsufa, bugu da kari kuma zaku haifi ƴaƴan nan ko ba jima ko ba daɗe, kuma maza kuji tsoron Allah ku rinƙa jin kan ƴaƴan da aka zalunta aka yi wa fyaɗe idan kun auresu, ku sani ba laifinsu bane, ku tausaya musu Allah zai biya ku, Allah ka bamu dacewa.

Sai misalin karfe 9 ya shigo gida abin da bai taɓa yi ba, a ko da yaushe idan ya je masallaci burinsa kawai ya yi sallah ya dawo wajen matarsa da mahaifiyarsa, sai ga shi yau kuma ko da ya yi sallah ya yi zamansa a masallaci har karfe tara sannan ya dawo, ta shiga damuwa sosai na ganin bai dawo ba, har kamar zata kira shi a waya, sai kuma ta fasa ta danne ta cigaba da kwanciya kawai tana jiransa.

A palo ya isko Ummi tana ƙoƙarin shiga bedroom nata dan lokacin barcinta ya yi, da mamaki take kallonsa na fitowa daga waje da ya yi, sannu tare da barka da dare ya yi mata kafin ya nufi bedroom nasu, da mamaki ta bishi da kallo. "Nawid lafiya kuwa? Ya A'afia bata fito ba yau, na yi tunanin bari naje na dubata sai kuma na tuna kila kana ciki ne, amma ya ka fito daga waje kuma? Ga dukkan alamu kuma kana cikin damuwa, lafiya me yake faruwa? Ko dai A'afia ɗin ce bata da lafiya?". A rikice take jera mishi tambayoyin nata.

Ƙaƙalo murmushi dole ya yi yana faɗin "Ummi ki kwantar da hankalinki babu komai, A'afia ce take ɗan jin zazzaɓi kuma nayi mata allura tana barci, dan haka babu komai, ki je ki yi barci". Murmushi ita ma ta yi a cikin zuciyarta tana faɗin Allah yasa cikine da surukuwar tata, kullum tana yi musu addu'ar Allah ya basu ciki mai albarka, Nawid shi kaɗai Allah ya bata, tana yi mishi addu'a shi kuma ya haifo mata ko dozen ne haka, zata riƙe su baki ɗaya, sai hamdala take ga Allah ta wuce bedroom nata bayan ta yi wa Aafia ɗin addu'ar samun sauki cikin gaggawa.

Shi ma wucewa ya yi nasu bedroom ɗin yana amsawa da Amin ya Allah, kwance ya iskota saman bed, sam bai bi ta kanta ba ya wuce saman sofa ya zauna tare da jawo takardunsa da laptop nasa ya fara aiki, cike da tsoro ta ce mishi ta zuba mishi abinci, ko kallon in da take bai yi ba bare ta sa ran zai amsa mata, cigaba da abin da yake yi kawai ya yi har zuwa karfe 11, bata yi barci ba, shi kuma bai ci abincin ba, ita ma bata ci ba saboda tare suka saba ci, sai 11:30 ya tattare komai ya wuce toilet, wanka ya yi tare da shirin kwanciya ya zo saman bed ɗin ya ɗauki pillow da bargo ya koma saman sofa ya yi kwanciyarsa, yana jin yunwa sosai haka ya kwanta, ita ma tana jin yunwa sosai haka ta kwanta, sai misalin karfe 2 na dare ta samu barci ɓarawo ya yi awon gaba da ita, shi kuma sai karfe 4 ya iya yin barci, nan ma da kyar, sai tunani yake yi a kan waye A'afia ta baiwa mutuncinta, kishi ya hana shi barci, abin ya tsaya mishi a ransa sosai, rashin sani ya fi dare duhu.

A ɓangaren gidan Lion kuwa, yau gabaɗaya Network sai rawa yake yi, shi kuma Lion yana son ya yi magana da Tyrone dan ya ɗauko mishi daddyn Rimsha su taho tare, jikin TGA har yanzu akwai sauran ciwo jikinsa da tafiya zai yi mishi wahala, shi kuma Lion yana bukatar daddyn Rimsha da wuri dan yana tantanma a kan wanda ya kama, ƴan biyu ne masu kama ɗaya, daddyn Rimsha ne kawai zai iya rabe wanene daga cikinsu abokin faɗan nasa, bayan haka akwai wasu abubuwa da yake son tasa daddyn Rimsha a gaba ya yi mishi bayani a kai, magana ce da ta shafi Na'urat mahaifiyarsu, yana son kammala case ɗin da wuri ya koma kasarsu dan ya ɗauki lokaci a nan, hakan kuma sam bai yi mishi ba, so yana son kashe komai ya shafe rikicin dan daddyn Rimsha ya dawo cikin family'nsa su yi zaman farinciki.

Bayan ya yi sallar mangariba da issha ya dawo, ya yi ƙoƙarin samun Tyrone a waya amma abin ya ci tura, rai a matukar ɓace ya nufi wajen gate baki ɗaya dan ya nemi wajen da akwai Network, dan shi dai dole sai ya yi wannan call ɗin tana da mahimmanci, baya son daddyn Rimsha ya wuce kwana biyu bai shigo Naija ba.

Haushi Brady ya fara yi mishi a kan lallai sai ya bishi, ɗaure fuska sosai ya yi tare da cewa Mark ya kwance mishi karen sa, waye zai wani ɗaure mishi sweetheart ɗinsa dan iskanci, bai san cewa Areef yasa Aseef ya ɗaure shi ba dan kada ya takurawa Rimsha, shi ne suka ɗaure shi.

Kwance shi Mark ya yi, da gudu ya taho ya rungume Lion ɗin yana wani kuka kasa kasa, shafa jikinsa ya fara yi alamar rarrashi tun da an yi mishi ba dai'dai ba, an kama an wani ɗaure shi an hana shi jin daɗin duniyarsa, ya sha alwashin Allah duk wanda ya sake ɗaure mishi sweetheart ɗinsa dai ya hukunta shi, ko da kuwa Aseef ne, akan me su suna jin daɗin rayuwarsu suna sake wa shi kuma zasu takura mishi? To wlh ba zai yiwu ba, dole ya taka musu birki.

Lion da Brady mutuka raba, akwai kauna da amana ba kaɗan ba, wanda yake son mutuwa cikin sauki to ya yi ƙoƙarin cutar da wannan sweetheart Bradyn ya ga ikon god, cikin sauki kuma cikin sauri zai wuce lahira.

Waje ya nufa da shi yana cigaba da shafa jikinsa, lafewa ya yi a jikin Lion ɗin alamar ya hakura kenan, kai Brady duniya, ya samu horo iya horo, wani lokaci idan yana abu kamar mutun.

Sun ɗan yi tafiya mai nisa tsakaninsu da gidan nasu kafin ya tsaya kusa da wani restaurant yana duba Network ko ya zo, Brady na manne a kirjinsa kamar wani yaronsa, ya kuwa yi Sa'a wajen akwai Network, number Tyrone ya kira, bugu ɗaya ya ɗaga, ba tare da ɓata lokaci ba ya sanar da shi on Monday ya taho mishi da daddyn Rimsha Nigeria, okey ya amsa cikin girmamawa, yana katse kiran nasa Brady ya diro kasa daga jikinsa ya nufi wasu guys dake tsaye su biyu ta gefensu ta ɗan baya kaɗan, da yake Lion ya rungume shi a kirjinsa ne shi yana iya kallon abin da yake bayan Lion ɗin, shi kuma Lion yana kallon gaba ne, shiyasa ya kallin guys ɗin.

Da farko zai kira Brady ɗin, sai kuma ya fasa dan ya san horon da ya bawa karen nasa, na farko baya kwaɗayi, na biyu baya bin mutane a hanya, shi baya yarda ma da kowa kamar ogan nasa, sannan baya yin abu babu dalili, ko Rimsha da yake takurawa ita ce take gudunsa, take yin abu kamar mara gaskiya, to a irin hoton da ya samu kuma idan ya kalli mara gaskiya dole zai bishi, shiyasa idan ta gudu yake binta.

Zuba mishi ido Lion ɗin ya yi yana kallon ikon Allah bayan ya ɗan juyo garesu kenan, yana zuwa ya yi tsalle ya sanya bakinsa ya kwace wayar dake hannun guy ɗin, yana kwacewa ya nufo Lion da gudu ya kawo mishi wayar tare da hayewa jikinsa, karɓa ya yi tare da juyo screen ɗin wayar dan ya gani menene Bradyn ɗin ya gani, yasan dai haka kawai ba zai kawo mishi wayar mutane ba.


Hoton Rimsha ne tana tsaye sanye da wani wandon jeans baki mai bala'in kyau sai ƴar t-shirt fara tas mai ratsin baki a jiki, ta saki dark black curly hair nan nata har gadon baya, ta yi kyau over kamar ka saceta ku gudu, ka je ka ajiyeta kayi ta kallo, ga shi ta ɗan ɗaga idanunta sama, sleeping eyes ɗin sun fito sosai a hoton, ta ɗan motsa laɓɓanta kaɗan dimple nata ya bayyana, da alama hoton bata jima da yin shi ba suka rabu da iyayenta, dan a gidansu na Abuja ta yi hoton tsaye wajen pool nasu.

Zubawa hoton idanu ya yi sai haushi a hankali hankali Brady yake yi mishi, Abin da ya faru shi ne, guys ɗin suna tsaye ta bayansu shi kuma Brady yana kallonsu, ya kalli lokacin da suka buɗe hoton, shi kuma kare baya mantuwa, musamman ma irin Brady da ya samu horo, so ya san Rimsha sosai, ya san a gidansu take, dole idan ya ga hotonta zai ganeta, dan su karnika akwai rike mutun, in dai sun san mutu wlh ko shekara zasu yi basu gan shi ba, to duk ranar da suka haɗu sai sun gane shi, haka zasu yi ta hawa jikinsa suna nuna murnar ganinsa da suka yi.

Ya ɗan ɗauki ƴan mintoci da zasu kai a kallah biyu yana kallon hoton kafin ya fita daga kan hoton, sai ya kallima ashe a WhatsApp na mutumin aka turo mishi hoton, ɗago kai ya yi dan ya kalli guys ɗin, sai ya kalli wayam sun gudu, dan su da kansu ba su ga wajen da zasu tinkara suce ya basu wayarsu ba, kuma sun san su masu laifi ne, dama duk wani mara gaskiya da ya ji ɗan motsi zai gudu.

Ganin basu nan yasa ya dawo da kallonsa kan wayar ya fara bin chatting na guy ɗin da wanda ya turo mishi hoton, dan ya ga me hoton Rimsha yake yi a wajensu? Me kuma za'ayi da ita?. Voice dake saman hoton, wadda aka fara turowa kafin hoton ya buɗe, cikin harshen Hausa mutumin ya yi magana, da wata muryarsa kamar na hamshakan bugaggu ƴan kwaya ya ce "Ni ban san in da take ba, kawai dai ku nemota, iya abin da na sani shi ne, ita Jehan ta turawa video na da ta ɗauka, dan haka ku nemota, ku tabbatar kun karɓa mini video na, idan taki ku kasheta, ni zan ji da Jehan tun da tana prison, dolema na san hukuncin kisa za'a yanke mata tun da Abubakar jaja ya mutu, zan turo muku hotonta wadda na sha bakar wahala kafin na samu, na wahala kafin na gane ƴaƴan Nawazudden ne, akwai wan da ya ce mini tabbas ya taɓa ganin ita Rimshar a Kaduna, na tura mishi hoton ta ne sai ya ce wlh tana Kaduna, shiyasa na nemo ku, dan haka ku nemota, idan kuka kuskura kuka bari video na ya fita wlh sai kun mutu". Shi ne abin da yake cikin voice ɗin, sai dai kafin ya gama jin voice ɗin wayar ta shiga key.

Kashe hasken screen ɗin wayar ya yi tare da zubawa screen ɗin idanu yana karantar wajajen da aka fi yawan taɓawa a kan screen ɗin, sune zasu iya kasancewa password na wayar, dan in da ake yawan taɓawa dan buɗe password ɗin, dole zata yi daban da sauran jikin screen ɗin. Ganin babu haske sosai da zata ishe shi ya kalli abin da yake son kallah ne yasa ya nufi gida dan ya buɗe wayar ya yi bincike a cikinta.

A bakin gate ta waje ya isko Mark, da mamaki ya tambaye shi me yake yi a waje kuma? Bawan Allah ɗan amana sai ya ce kawai ya fito ne dan hankalinsa ya kasa kwanciya ogansa yana waje, shi ne ya fito dan ya jira shi a nan ya kuma duba lafiyarsa, har cikin ransa ya ji daɗi sosai, umarni ya yi mishi a kan to suje ciki, hannu yasa yana ƙoƙarin ɗaukar Brady da ya wani kanainaye wuyar Lion ɗin kamar wani ya ce zai kwace mishi shi, da yake Mark mutuminsa ne, sai ya saki Lion ɗin ya koma wajen Mark ɗin yana yi mishi kuka a hankali alamar yana bashi labarin yaga hoton Rimsha a wani waje, da yake Mark ɗin ma ya yi mishi farin sani sai ya ce da Lion me Brady ya gani, shiru Lion ɗin bai tanka mishi ba, hakan yasa ya gane abin bai shafi kowa ba kenan, case ɗin na ogan nasa ne shi kaɗai.

Palo suka nufa, tun da ya sako kai cikin palon daddaɗar kamshin kayan tea ɗin da Rimsha ta dafa mishi a Abuja ya daki hancinsu dukkansu biyu, harta Mark ya ji mugu mugun daɗin kamshin, shaka suka yi suka lumshe idanu, bai yi magana ba har sai da suka shiga tsakiyar palon.

Suna kaiwa tsakiyar palon ya juyo tare da sauƙe dara daran idanunsa a kan Mark ɗin, ya kuma dakata daga tafiyar da yake yi.

Ƙasa da kai Mark ɗin ya yi tare da fara ƴan kame kame, tun ba'ayi mishi magana ba ya yi saurin fara magana cikin girmamawa. "Sorry sir am not the one and I don't know how it happened, it might be prof sister". Shiru ya yi bai yi magana ba, bai kuma ɗauke idanunsa ba, bai kuma juya ya cigaba da tafiyar da yake yi ba, da alama tunani yake yi a kan hakan.

Almost 5 mins suna a haka, gently ya mayar da kallonsa izuwa hanyar kitchen na ƴan sakanni babu ko kyaftawa, daga bisani kuma ya juya ya cigaba da tafiya dan zuwa in da yake da niyar zuwa wato bedroom nasa. Sauke Brady Mark ya yi tare da nufar kitchen ɗin dan ya ga waye ne ya yi wannan aiki da ya canzawa gidan daga kamshin abincinsu zuwa na kayan tea, ba kowa bace ta yi aikin nan fa ce Rimsha, ganin Mark ɗin baya kitchen ɗin ne yasa ta zo ta tafasa tea ɗin ta abinta, shi ne kamshi ya bule daga kitchen ɗin har palon.

Lion kuwa yana shiga bedroom nasa ya iskota ta ajiye mishi abinci tana jiransa, ta wutsiyar idanu ya kalleta kafin ya wuce zuwa dressing room nasa, Jim kaɗan ya fito sanye da pajama launin white color, dama already kafin ya fita neman Network ya yi wanka ne ya zura jallabiya bai tsaya shiryawa ba, dan yana matuƙar son ya yi magana da Tyrone.

Zama ya zo ya yi a in da ya saba zama, calmly ya ce ta kawo mishi laptop nasa, da sauri ta ɗauko ta miƙa mishi, abincin ya ce ta zuba mishi kafin ya shiga ƙoƙarin buɗe wayar mutumin, tana tsaka da zuba mishi abincin ne zazzakar sexy voice nasa ya daki dodan kunnenta a in da yake ce mata "Daga yau ban yarda ki sake fita ko ina ba, school Mark zai kai ki ya kuma ɗauko ki, shi ma school ɗin idan kin je kada ki kuskura ki yarda da kowa, ko wani ya kira ki kije ko makamancin hakan, ko da su Areef ban yarda ki sake bi ki fita ba". Okey ta amsa mishi da shi, can kuma wani tunani ya faɗo mishi, to me zai hana ya haɗa ta da soja ɗaya kawai ya rinƙa tsaronta a school ɗin, tun da Jehan ta rigada ta jefa mata rayuwarta cikin haɗari, yanzu sai Allah kaɗai yasan adadin mutanen da wannan azzalumin ya turawa hotunanta a kan su kamota ta kawo video da Jehan ta zuba mishi karya akan ta turawa Rimshar, idan baku manta ba, lokacin da Jehan ta yi wa Alhajin can na gidan hajiyar daɗi video, ta ce mishi ta turawa ƴar uwarta Rimsha, to kuma dama kunsan manya mutane irin waƴan nan ba zasu bar abu makamancin haka ya fita ba, dan idan ya fita sun san shikenan rayuwarsu tana kwale kwale, shi ne to yasa aka nemo mishi hoton Rimsha yanzu kuma yasa a kamota a karɓa mishi videonsa, shi kuma zai ji da jehan.

Gaskiya Jehan ta tara makiya ta ko'ina, yanzu ga shi ta tsundumo Rimsha da bata san komai bama a ciki, shiyasa wani lokaci ake son kafin ka yi abu ka yi tunani, tunani ma mai zurfi a kan me zai je ya zo, Jehan ta yi babban kuskure a nan tun da ta san babban mutun ne, ba zai taɓa rabuwa da ita tana riƙe da videonsa tsiraicinsa ba, to ya kamata mu rinƙa tunani wani lokaci kafin mu yanke hukunci.

Abincin ta zuba mishi ya ci mai ɗan yawa kafin ya cigaba da abin da yake yi, ta miƙe zata kwashe kayan abincin ya ce mata idan ta kai ta dawo, okey ta amsa cike da mamaki ta nufi wajen. Tana shiga kitchen ɗin suka yi ido huɗu da Mark, ga shi yau bai sanya glass ba, Hazel eyes nasa dara daran nan yau dai a waje suna shan iska, mamakin idanun nasa ta yi, bata taɓa ganin irinsu ba, ajiye kayan abincin ta yi bata kula shi ba kamar dai kullum, zata fita ya ambaci sunanta, da mamaki ta juyo, wai dama Mark mai kama da robot ɗin nan dumkum ba magana nan ya san sunanta ne? Ta tambayi kanta da kanta.

Tambayarta ya yi a kan waye ya ce ta yi girki a kitchen ɗin nan? Turo baki ta yi kafin ta ce mishi Areef ne ya ce ta yi, daga haka ya yi shiru bai sake yin magana ba, sa kai ta yi ta wuce abinta, ɗakin Lion ɗin ta koma dan amsa kiran da yake yi mata.

A gefensa ta je ta zauna abinta, ya sha ruwan mamaki yadda ta wani zauna a gefensa ko a jikinta, can kuma ko me ta tuna ne ta miƙe da sauri ta fito zuwa bedroom nata, cup ɗin tea ɗinta ta ɗauka ta dawo bedroom ɗin nasa, in da ta tashi ta koma ta zauna.

A hankali ta fara shan tea ɗin tana jiran ta ji kiran me ya yi mata, shi kuma ya buɗe wayar mutumin sai bincike yake yi a ciki, a hankali hankali kamshin tea ɗin ta yake dakan masa hanci, har cikin zuciyarsa yake son kamshin, akwai


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login