Showing 18001 words to 21000 words out of 359620 words

Chapter 7 - Triplets Book 3 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

1956

ashe akwai wani abin da zaka iya hidden mana ka da musani? Ashe akwai abin da bai kamata mu sani ba a dangane da kai?".

Cikin sauri ya ɗago kai jin yadda Areef ya yi maganar, hakan ta nuna In a serious matter Areef yake. "No Areef i can't hidden anything for you, trust me ba wani abin da yake damu na, just kawai dai..... " Sai kuma ya yi shiru.

"Anywhere just kawai ka riƙe maganarka no need ma ka gaya Mani, yanzu dai ya school?". "Kai Areef sarkin fushi, to ni nace ba zan gaya maka bane?" Ya yi maganar a shagwaɓe. Da mamaki Areef yake kallonsa, wato idan ya tashi tsiyarsa har yanzu bai manta yadda ake shagwaɓa ba kenan.

"Areef ba fa wani abu bane yake damuna, just kawai kullun idan na kwanta barci ne, sai na yi mafarkin wata ta yi kissed nawa, kuma ba iya kiss kawai ba, just like husband and wife dai".

Wani irin ɗan iskan dariya Areef ya kwashe da shi, wato just like husband and wife, eyye su Aseef husband, bawan Allah shi ne abin dake damunsa, kuma ya kasa gaya masu, Allah Mai iko a gabaɗaya family'n William jacop shi ne kaɗai ya samu albarkar kunya, ya rasa ta ya zai yi ya rabu da wannan ɗan iskar mafarkin.

Areef kuwa tsabar mugunta dariya har da riƙe ciki, zuba mashi ido Aseef ya yi yana kallonsa, suma su Rimsha, da mamaki suke bin shi da kallo, dan a gaskiya ba su ji me Aseef ya ce ba, da yake kasa kasa ya yi maganar, kuma na gaya maku kunya yake ji, hakan tasa ma ya yi maganar kasa kasa dan kar wani ya ji.

Saboda tsabar iskanci irin na Areef sai ya ce "No Aseef explain it dallah dallah for me, like how husband and wife?". Yana magana yana guntse dariya.

Ɗan turo baki ya yi "Kai my blood, Like husband and wife mana, i knew you knew yadda husband and wife suke yi, tun da ka wuceni a karatu, ni fa yanzu nake karanta"

"No ni dai I didn't know anything, kawai just explain it for me". Shiru ya ɗan yi kafin ya sunkuyar da kansa kasa, wani irin kunya ce take kara rufe shi, bawan Allah ya ciri tuta, ko ba komai ya zama zakara a cikinsu, tun da har ya yi nasarar samu al'kunya.

"She is sleeping on my chest, and she is socking my penis sometimes, and also she is kissing my lips, yesternight she wanted to sock my nipples, amma Allah yasa na hanata, ni bana son this kind of dreams, suna bani haushi, please my blood help me".

(Jama'a an sanu wata tana son lalata mana Aseef ɗin mu a cikin mafarki🤔 kunji shegiya,🤣🤣 to ya kamata mu tashi tsaye🤣)

Shi kam Areef kamar zai mutu saboda dariya, duk waƴan nan abubuwa sai yanzu Aseef yake saninsu, bai ma san menene aure ba sai da Musharraf ya fara koya mashi irinsu FIQHU da sauran littatafan addini, shi ne ya san ma'anar husband and wife, a gaskiya ciwon Aseef dai bata yi mashi adalci ba wlh, yana da 30 years a duniya amma babu abin da ya sani, sai yanzu da Allah ya ƙaddara yana da rabon jin daɗin rayuwa, shi ne ya sami lafiya har ya fara sanin abubuwa, kai amma abin sam bata yi daɗi ba, sai dai kuma ya yi nasarar samun kunya a lamuransa, duk mutumin da bashi da kunya, wlh da sauransa a addinance, addini bata tafiya sai da al'kunya, sai dai fatanmu Allah yasa su ma Areef da Saif su sami wannan kunya ko da kaɗan ce.

"My Areef pls stop laughing at me mana, that's why fa naki gaya maka what's going on, shiyasa na yi hidden na abuna ni kaɗai, amma yanzu kazo kayi forcing ɗina na gaya maka, shi ne kake ta yi mani dariya ko?".

Tsagaita dariyar ya yi. "Do you know what Aseef?". Girgiza kai ya yi alamar a'a. "Good, duk abin da ta yi maka a cikin DREAM ɗin just kawai kaima ka yi mata reply, kayi accepting nata, idan ka tashi barci zaka ji you are normal". Ya kai karshen maganar tare da sake kwashewa da dariya.

Shiru Aseef ya yi yana kallon sanka sanka walaƙanci da Areef yake yi mashi. Ganin ya yi shiru ne yasa ya ce "Sorry my blood zan gaya maka solution, ka dage ka yi mata fyaɗe da karfi a mafarkin, idan ta ji wuya ba zata sake dawowa ba".

Nan ma shiru ya yi bai sake magana ba, dan shi maganar ma kunya take bashi sosai wlh. Shi kuwa Areef sake dariyarsa ya yi, domin kuwa yau Aseef ya kawo mashi sabuwar lamari.

After 2mins. "Am so sorry my Aseef" ya faɗa yana daidaita natsuwarsa. "Areef don't worry, ni ban damu ba, tun da kayi dariya, kayi farinciki to bani da wata damuwa, burina dama na ganku kuna farinciki!!".

Jinjina kai Areef ya yi, har cikin ransa yana mai jin tsantsan kaunar ɗan uwan nasa, shawara ya fara bashi akan ya rinƙa kwana da alwala, sannan ya rinƙa addu'ar barci sosai, In Sha Allah zai rabu da waƴan nan mafarkai mafarkan na banza, ba ƙaramin daɗi ya ji ba, daga nan Areef ɗin ya kara tambayarsa akan idan ya tashi barci yana yin wankar tsarki ne ko baya yi, wani irin kunya ce ta sake rufe shi, cike da kulawa ya ce yana yi domin Musharraf ya koya mashi, ya gaya mashi cewa idan mutum ya zubar da spam sai ya yi wankar tsarki, kuma ya mashi bayani sosai a kan yadda ita kanta spam ɗin take da sauransu, daga nan kuma ya koya mashi wankar tsarki, to ta hakan ne ma yasan aure da sauransu.

Sosai Areef ya ji daɗi, ya kuma kara jin Kaunar Musharraf sosai da sosai, domin ya bada gudun mawa ba kaɗan ba a rayuwar Aseef, wadda da ba dan shi ba, da abin zai yi masu yawa, domin komai daga farko a ka sake koyawa Aseef, amma cikin hukuncin Allah yanzu komai na tafiya daidai yadda ake so da taimakon Musharraf, kuma hakan ma yasa Lion yake Kaunar Musharraf ɗin, domin duk wani dirama da suke yi da Aseef yana ganinsu ta cikin laptop nasa, ta camerar dake gidan nasu, wadda ya haɗa da laptop ɗin nasa, yasan komai, kuma kunsan family'n William jacop suma basu manta Alkhari ko mai kankantarta.

Suna tsaka da hira Lion ya yi wa Imran massage akan Rimsha ta kawo mashi abincin rana, karfe 2:30 ta yi.

Wani irin faɗuwar gaba ta ji lokacin da ta ji saƙon Saif ɗin, jikinta har ya fara kerma, dama tana son ta tambayi Imran ɗin wai me Saif ya ci da safe ne, tun da ta zubar mashi da abinci, amma sai Areef ya zo ya shashantar da maganar.

Jiki ba kwari ta miƙe ta nufi cikin gida, tun da ta fito garden ɗin, sai binta da wani mayen kallo, da wasu mayun idanunsa gateman yake yi, tamkar zai cinyeta ɗanye.

A kitchen ta isko Mark, kamar dai kullun ya ji shigowarta, amma bai ɗago ya kalleta ba, kun dai san halinsa. Wucewa ta yi ta wanke hannayenta, bata ce mashi ko sannu ba, domin ko ta ce mashi ma, baya amsawa, shiyasa kawai ta daina yi mashi magana, sallama ma a cikin zuciya take yi abinta,

Cikin natsuwa ta zo ta ɗauki tray ɗin abincin, sai a lokacin ta fara jin wani azababben yunwa na nukurkusan cikinta, sai da ta nufi kaiwa Saif abinci, sannan ta tuna ashe ko abincin safe bata ci ba, kuma ba komai ne yasa ta tuna hakan ba fa ce bala'in tsoro.

Addu'a take yi sosai tana tafiya. Gabanta kara tsananta faɗuwa ya yi lokacin da ta kai bakin kofar ɗakinsa.

Tsayuwa ta yi tare da daidai ta natsuwarta sosai, ta yi sallama cikin sanyin murya, kamar dai kullum, a cikin zuciya ya amsa sallama, hakan ma saboda yasan mahimmancin sallamar ce yasa yake amsawa, duk wani cikakken musulmi mumini mai bin Allah da Annabi, to fa ya zama mashi dole ne wajibi amsa sallama domin cika addininsa.

Jin shiru ne yasa ta yi kamar yadda ta saba, wato ta kutsa kai cikin ɗakin.

Tana isa tsakiyar ɗakin karaf idanunta suka sauƙa akansa, wani irin mahaukaciyar razana ta yi wadda ta sanyata sakin tray ɗin abincin ya faɗi kasa.

A karo na biyu ta yi mashi kaca kaca da ɗaki, gabaɗaya komai ya watse, wasu kayan abincin har kan gado, ga shi babban abin haushin komai na ɗakin white color ne, harta bed sheet, kuma ta lalata komai, gabaɗaya bed sheet ɗin ya ɓaci. Ba komai bane kuma ya sanyata wannan irin Mahaukaciyar razana fa ce ganin ainahin surar jikinsa da ta yi, yana tsaye ne a gaban mirror, daga shi sai towel a kugunsa, da alama wanka ya fito, iya ta bayansa ta gani yasa ta razana haka, ina ga kuma sun yi ido huɗu ba riga a jikinsa? Ina ga ta gan shi ta gaba babu riga? Ko da yake dole ta razana, domin kuwa ya kai matakin da dole mai zuciya a kusa ya razana da ganin ainahin kyakkywar surar jikinsa, yana da wata sihirtaccen kyau ne na fitan Allah, ga shi ya yi gym sosai, damatsan hannun nan nasa ba'a magana, ga uban faɗin kirji, sannan ga bala'in kwarjini.

Turus ta tsaya ta kasa sake ɗaga ido ta kalle shi, haka zalika ta kasa gaba ta kasa baya, sai dukan uku uku zuciyarta ke yi mata, ji take yi ranta na barazanar fita daga gareta, wani irin wahalallen yawu ta haɗiye, wasu zufar wahale suka fara karyo mata a gefe da gefen kunnenta, tsoron kai kallonta a kan ɓarnar da ta yi ma take ji, a wannan karonfa ko kerma jikinta ya kasa yi, yadda zai tabbatar maka tashin hankalin dake sanya kerman jikima, ashe karamin tashin hankali ne, idan tashin hankali ya yi tashin hankali to jikinma kasa motsawa take yi, bare kuma ma har ta yi kerma.

Cikin natsuwa yake aikin dake gabansa, wato gyara dark black curly hair sa, tamkar bai san mutun ya shigo cikin ɗakin ba bare har ya yi mashi ɓari, tamkar babu shi a cikin ɗakin, haka ya kasance, amma kuma duk abin da take yi kunsan yana ji tun da shi ba kurma bane.

Tana tsaye a wajen tana kallon kasa ta kasa motsawa, har ya kammala gyaran gashinsa ya shafa Lotion nasa, sannan ya feshe jikinsa da perfume nasa. Bayan ya gama, cikin wannan natsuwa tasa mai ɗaukar hankali ya juyo...........

❤️❤️TRIPLETS❤️❤️


E5-6

Tana tsaye a wajen tana kallon kasa ta kasa motsawa, har ya kammala gyaran gashinsa, ya shafa Lotion nasa, sannan ya feshe jikinsa da perfume nasa. Bayan ya gama, cikin wannan natsuwa tasa mai ɗaukar hankali ya juyo, ko kallon in da take bai yi ba, dressing room nasa ya nufa, lokacin da ya juyo ita kuma tana kallon kasa, bata ɗago kai ba dan saboda tsantsar bala'in tsoro.

Jin ya shiga dressing room ne yasa ta duƙa ta fara kwashe kayan abincin da sauran irin su fruits, sai kuma lokacin ne jikinta ya sami damar yin karma, ta kasa tattare kayan saboda ɓari da jikinta yake yi, sai zata ɗauki abu ta kasa, wani irin wahalallen kuka ta saka kasa kasa, ita ina zata sa ranta ne yau?.

Tana a haka har ya fito sanye da wando three quarter fari tas, da kuma riga polo shirt sky blue, ba karamin kyau ya yi wa kayan ba, domin idan baku manta ba, shi fa tsabar kyansa shi yake yi wa kaya kyau, ba wai su suke yi mashi kyau ba.

Da ya yi niyyar idan ya fito ya bata punishment mai matikar tsauri da wahala, domin ta shiga hankalinta da kyau, amma kuma ganin yadda jikinta ke kyarma, hannunta sai rawa yake yi, ta kasa ɗaukar kayan abinci, tana duƙe a kasa, hakan yasa ta wuce ya fita, domin idan ya yi wani yunkuri kaɗan yana da tabbacin kisan kai zai yi, saboda ya lura wannan yarinta tsoro ma ya sara mate ne, in dai fagen tsoron ne, kuma tana matukar cin albarkacin Imran da kuma farincikin da daddynta yake sanya Aseef, ba da ban hakan ba, da yanzu wani zance ake yi ba nata ba.

Ganin ya fita bai ce mata komai bane ya sanya ta ji jikinta ya ɗan yi kwari, ta tattara karfinta dukka ta miƙe ta hau gyara mashi ɗaki, tana roƙon Allah da ya bata ikon rinƙa faranta mashi, ita kullun suka haɗu cikin laifi take, kullun sai ta yi mashi laifi, dan ma Allah yasa Areef ya taimakonta, ai da ya jima da ɓallahta koma ya hallakata baki ɗaya.

Tas ta tattare mashi ko'ina, sannan ta miƙe ta fitar da kayan abincin, ta dawo ta goge ko'ina, sai da ta tabbatar wajen ya yi tsab, sannan ta fice daga ɗakin ta nufi wajen su Imran dan ta gaya masu abin da ta yi, ba zata iya komawa ɗakinta ba, domin tana matukar jin tausayin Saif ɗin, tasan tun da ya ce a kawo mashi abinci, to tabbas yunwa take ji ne, ga shi ta zubar da abincin, na safe ma ta zubar.

Kamar yadda ta bar su Imran, haka ta dawo ta samesu, kusa da Imran ta koma ta zauna, cikin harshen turanci ta gaya masu abin da ya faru, shiru Areef ya ɗan yi kafin ya ce ta kira mashi Mark.

Cikin sauri ta miƙe ta nufi cikin gida, da kallo suka bita da shi, kowa daga cikinsu da abin da take tunani a kanta.

Ta zo zata shiga cikin Palo, suka yi karo da shi yana fitowa, yana tafiya yana latsa wayarsa, yau ma dai sake buge mashi waya ta yi, sai dai wayar bai kai kasa ba ta tare, cike da tsoro ta miƙe mashi wayar, saura kaɗan ta furta karlamar sorry, sai kuma ta tuna Areef ya gaya mata, babu kalmar da Saif ya tsana biyun Sorry, da ta yi gangancin furtawa kuwa, da sai dai a kwasheta sumammiya, dai sai ya ɗauketa da wani mahaukacin mari wadda zai sanyata barin duniyar mutane, amma kuma bata furta ba, cikin girmamawa dai ta miƙa mashi wayar.

Ba tare da ya kalleta ba, ya karɓi wayar kawai ya wuce, domin shi ma addu'a yake taya ta da shi akan kada Allah ya sanya taji sauƙar hannunsa a jikinta, domin duk ranar da ya mareta, ko ya daketa, to da wuya ta sake moruwa.

Wani irin daɗi ta ji da bai daketa ko ya ɗago ya kalleta ba, yau sau uku kenan ta yi mashi laifi, da safe ta zubar da abinci, haka na rana, sannan ga buge mashi waya yanzu, amma duk ya danne saboda baya son ya yi kisan kai, bala'in tsoron ta yake cetanta a wannan fagen.

Kitchen ta koma kira Mark, ta dawo garden ɗin, nan ta same shi a wajen, kuma a in da ta tashi ya zauna, kusa da Imran kenan, turus ta tsaya, ta kasa karisawa.

Zuba mata ido Imran ya yi, shi kuma Areef da ya ga hakan sai ya ce ta zo ta zauna kusa da shi, ba musu ta karisa wajen ta zauna kusa da shi ɗin tana satar kallon abun kaunar nata.

Sai wani nuku nuku take yi, shi kuwa Saif daga su Imran ɗin har ita tamkar bai san da zamansu a wajen ba, kallonsa na akan wayarsa.

Shiru suka kasance a wajen har Mark ya zo, umarnin Areef ya yi mashi a kan ya sake ɗaura wani abincin, domin abincin Lion ta tashi aiki, to ya amsa da shi, daidai lokacin kuma wayar Rimsha dake kusa da Imran ya fara ringing, wayar tana daidai tsakanin Saif da kuma Imran ɗin, saboda a nan ta zauna ɗazun.

Jin karar wayar ba karamin haushi ta bashi ba, gashi ta fi kusa da shi, kuma waka ce ringington na wayar, ai kuwa Imran na ƙoƙarin ɗaukar wayar ya riga shi, ɗauka ya yi ya yi wurgi da ita, shi da kansa bai san a ina ya yi wurgi da ita ɗin ba, domin kuwa kallonsa a kan wayarsa ne har lokacin.

An yi sa'a kusa da Areef ya wurga wayar, hannu Areef yasa ya yi maza ya capke wayar tare da miƙe mata kayanta, zata miƙe Areef ɗin ya zaunar da ita, ba dan komai ba sai dan yana son Saif ya rinƙa sauraron daddaɗar muryarta.

Ɗago kai ta yi tana kallon Areef ɗin da mamakin, me yasa zai hana ta tafiya ta je ta yi wayarta, tsoro take yi kada ta fara waya a nan Saif ya daka mata Tsawa, yanzu ga shi iya ringing na wayar ma kawai ya ji, ya kama ya yi wurgi da ita, to ina ga kuma ya ji tana zuba hira, idan baku manta ba, baya son yawan magana, shima Areef da gangan ya dakatar da ita, yana son ja mata ne kawai.

Dubawa da zata yi waye mai kiran nata, sai taga new number ne, sake kira aka yi domin ta baya ta katse, cikin sauri ta ɗauka dan kada Lion ya sake jin ringing na wayar tata, tana kuma tsorace saboda new number ce a ka kirata da shi.

"Hello My Rimsha iyayen kauna, wato kin mance dani ko? Kin koma gidan masoyi kin manta da Ni". Cewar AKILA, domin ita ce ta kirata a wayar da sabuwar number, Allah yasa su Areef basu jin Hausa, ba su ji me Akila ta ce ba, shi kam oga dama ko ya ji ba shiga harkar zai yi ba, ita ce ƴar wahala da wahala bai isheta ba, take dakon wahala wai son shi tab hmmm,

Wani irin kayatatcen murmushi ta saki har sai da dimple da kuma wushiryarta suka bayyana. "Aunty Akila na yi kewarki, nayi kewarki sosai wlh, yaushe zaki zo mu haɗu?". Ta yi maganar cikin sanyin murya da natsuwa.

"Ke dai zan cewa yaushe zaki zo Rimsha, ni kam Heartbeat nawa ya hanani fita, daga school sai gida, bayan haka ya ce ko leƙa waje bai yarda nayi ba".

Kara faɗaɗa murmushin kan fuskarta ta yi. "Aunty Akila to ni dai ban san yashe zan zo ba, amma....." Bata kai karshen maganar ba zazzaƙar muryarsa ya katse ta, gently ya furta "Get out!" Ya yi maganar


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login