Showing 105001 words to 108000 words out of 359620 words

Chapter 36 - Triplets Book 3 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2039

hannayenta dukka biyu tayi, da kyar take numfashi ta nufi bedroom nata.

Aseef ne ya matso kusa da Areef ɗin yana faɗin "Me yake damun Lion ne? Ko dai yana son sister ne". Nisawa Areef ya yi "Ko kusa ko alama, a yanzu dai babu sonta ko ɗigo a ransa, ina ganin dai akwai abin da yake nema a tattare da ita, idan hasashena ya zama gaskiya a matsayina na jami'i, ko dai tana yi mishi kama da wata da ta tsaya mishi a rai, ko kuma akwai abin da yake bincika a kanta, akwai dai wani abin a kasa, amma ba soyayya bace, sai dai ina fatan hakan ya zama soyayya a tsakaninsu, tabbas zai bukace ta dan bincike, ina fatan hakan ya zama sanadiyar faɗawar shi soyayya da ita, ina son ganin ta cikin farinciki, ina son ganin ta sami abin da take so, ya Allah ya tabbatar mana nan ba da jimawa ba". Shiru Aseef ya yi, ya shiga duniyar tunani, ko Amin ɗin ma bai iya amsawa da shi ba, to wace ce Lion zai rinƙa gani tana yi mishi kama da sister? Aseef ne ya yi wa kansa wannan tambayar a cikin zuciyarsa.

Sun jima tsaye a wajen suna tattaunawa, daga bisani Areef ya ɗaukawa Rimsha abincinta ya bi bayanta da shi, dan yasan yunwa take ji, shi kuma Aseef ɗakin Lion ɗin ya nufa bayan ya ɗauka mishi laptop nasa da wayarsa da ya bari a garden ɗin.

Kwance ya iskota a saman bed nata, ta yi shiru tana tunanin yadda ta ga fuskarsa kusa da kusa yau, sai taga ya yi mata kama da wani wadda ta sani, sai dai ta rasa wanene, yau kewar ƴan uwanta ya dawo mata sabo, tunani take yi ko a wace duniya suke yanzu Oho. Gefen bed ɗin ya zauna tare da ɗaura mata abincinta a saman bedside drawer, rarrashinta ya fara yi yana bata hakuri tare da yi mata alkawarin akan Lion ba zai sake yi mata hakan ba, dan kuwa, idan ya canka daidai, mai irin wannan fuska tata tabbas ta tsayawa Lion a rai, kuma da alama a yinwa ce yake da ya san wace ce, so zai rinƙa binta a hankali.

Da kyar ta ƙaƙalo murmushi dole ta yi mishi tare da miƙewa zaune, abincin ya ɗauko ya miƙa mata, kusan a tare suka ci, dan sai da ya taya ta ci, saboda ita yau har daɗin abincin ya ji, sai da ya tabbatar da ta ƙoshi tap, ya miƙe ya nufi waje yana yi mata sai da safe.

Yana fitowa palon sama suka ci karo da Imran da jelly, cike da kulawa ya ce "Prof ina kuma zaku je a daren nan?". Ganin shi yasa jelly ta ɓuya a bayan Imran, dan mutuwar tsoron shi take yi, har wani duhu duhu ta fara gani. Ƴar murmushi ya yi yana faɗin "Jelly ta ce mini ba zata zauna a ɗakin sama ba, wai kuna nan sama, tsoronku take ji, dan haka mu koma ɗakin kasa". Jinjina mishi kai ya yi tare da wucewa ya shiga ɗakin Lion ba tare da ya sake yin magana ba.

Zaune suka isko Lion a saman gado, duk wasu kaya na mummynsa da ta bar mishi ya watsasu yana dubawa, da mamaki Areef yake bin kayan da kallo, kwata kwata ma shi bai san da waƴan nan kaya nata ba, ga shi babu hoto a ciki ko gwara ɗaya da zai gani ko dai a cikin kawayenta ne mai irin wannan fuska take, wani zuciya ce ta ce mishi to ya ɗauki Rimsha a hoto mana ya turawa Josephine ɗin, ya tambayeta wace ce mai irin wannan face ɗin, nan take ya ɗaure fuska yana faɗin no, shi baya neman taimakon kowa, komai da kansa yake yi, ɗauko hotunan Josephine ɗin ya yi daga cikin wannan ɗan akwatin, lokacin tun tana budurwa, duk hotunan ita kaɗai ce, babu ita da kawa ko ƴar uwa, a lokacin face nata sak na Aseef, ba karya Josephine kyakkyawar gaske ce, hancin nan nata kamar ita ta yi wa kanta, ga ɗan karamin red mouth nata irin na Lion ɗin sak.

Hotunan daddynsa ya kuma kwasowa, lokacin daddy na saurayi, yadda kasan Lion photo copynsa ne, da yana saurayi sak Lion ɗin, dama ga kalar idanunsu ɗaya, su dai su Areef zama suka yi suka zuba mishi idanu suna ganin ikon Allah ikon gaske, duk ya watsa komai da komai, sai dai babu komai a ciki da ya danganci abi da yake son sani, kwashe su ya yi ya mayar, da nufin idan ya gama bincike a kan daddyn Rimsha zai waiwayesu, koma wace ce kuma kome alaƙarsu sai ya gano, dan ba ta yadda za'ayi yana kallon Rimsha tsikar jikinsa na tashi kamar ba lafiya ba ace kuma babu wani abu a tsakaninsu, ina ba zai yiwu ba.

Bayan ya mayar da kayan kyakkyawar mazaunin da ya yi musu, toilet ya wuce dan ya yi wanka, ruwa mai sanyi ya sakarwa kansa dan ya samu zuciyarsa ta yi sanyi, yana shiga toilet Areef ya ɗauko laptop nasa ya fara bincike a cikinta dan ya gane menene ainahin matsalar ɗan uwan nasa, shi kuma Aseef abinci ya wuce ya je ya ɗauko musu dan su ci.

After some minutes, bayan ya kammala shiri cikin kayan barcinsa masu shegen kyau da tsada, sai tashin kamshi yake zubawa kamar me, wajen abincin ya nufa, suna zaune suna jiransa, Aseef shi ya yi serving nasu a plate guda, a nutse suka fara cin abincin, ba wanda ya ce da ɗan uwansa ko uppan, har suka kammala cin abincin suka miƙe, Lion ne ya fara tashi ya haye bed nasa, Aseef ya kwashe kayan abincin ya fitar, ya dawo ya gyara wajen.

Dukkansu gadon Lion ɗin suka haye dan su sanya shi nishaɗi, sun san yana cikin damuwa, sun ko yi nasara, sai da suka saka shi nishaɗi, suka sanya ya mance duk wani abin da yake damunsa, Allah sarki ƴan uwa rabin jiki, sai dai kuma har gobe yaki ya yi koda murmushi ne su gani, abin yana damun Aseef sosai, shi kam Areef normal ne, ko a jikinsa, ba dai ya tabbatar da ɗan uwan nasa ya yi murna ba? Hankalinsa ya kwanta, to ba sai ya yi murmushi ba.

Da kyar suka rabu da ɗan uwan nasu suka koma ɗakin Areef, Aseef ya ce ba zai kwana shi kaɗai ba, tare suka kwana da Areef, suna kwanciya ba jimawa Areef ya yi barci, shi kuma ya hau aikin waya da Heartbeat nasa, sai zuba mata shagwaɓa yake yi, tana zuba mishi nata ita ma, kamar dai yadda suka saba, haka suka raba dare, sai misalin karfe 3 na dare suka yi sallama ya yi mata sai da safe, kwata kwata bai so su rabu ba, dare ne ya yi sosai yasa ya hakura, yana ajiye wayar ya yi addu'ar barci, ba jimawa barcin ta yi awon gaba da shi. ASUBA TA GARI.

Washegari da safe, misalin karfe 8, ta tsara wankanta cikin pakistan na Indiyawa, ta yi kyau sosai, wandon farine tas mai ɗan faɗin, riga kuma launin blue, mayafin ma blue ne kalar rigar, ta yi kyau sosai ba kaɗan ba, sai tashin kamshi take yi abinta.

Palo ta fito, babu kowa, kai tsaye ta nufi garden dan tasan da wuya idan bata same su a can ba, da sallama ɗauke a bakinta ta shiga wajen, suna zaune su biyun, kowannensu yana latsa wayarsa, sun yi shiga iri ɗaya, ga shi dukkansu sun sanya black glass a face nasu, no respect, idan har ba irin Rimsha da ta yi musu farin sani ba, to da wuya mutun ya iya banbantasu, wandunan jean ne blue color a jikkunansu, sai kuma riguna polo t-shirt farare tas, ga gashin kan nasu ma iri ɗaya, dukka brown hair ne, sai dai na Aseef ya fi shiga brown sosai, na Areef ya ɗan yi haske, amma sai ka lura zaka gane hakan.

Ganinta yasa suka saki cool murmushi a tare, ita ma cool murmushi ta sakar musu tare da karisawa ciki, kamar abin haɗin baki suka wani matsa mata tsakiyarsu akan tazo ta zauna, zata wuce zuwa ɗayar kujerar Areef ya jawota ta zauna a tsakanin nasu.

"Good morning my lovely brothers". Cikin sanyin murya ta yi maganar, Areef ne ya iya amsa mata, shi kuwa Aseef yana can duniyar sahibar tasa, baya tare da su, "Muje sayan abinci ko?". Cewar Areef "Yaya Areef zaka ci abincin ne?" Gyaɗa mata kai ya yi alamar e zai ci. "Yaya Areef da gaske kana son abincin mu?" Ta yi maganar cikin zumuɗi, fuska ɗauke da mamaki. "Sosai our Queen, wlh abincinku is so sweet, jiya baki ga naci ba? Amma matsalar ni bana son abincin restaurant ne, idan zaki rinƙa girka mana, to zan rinƙa ci sosai, bamu taɓa cin abincin restaurant ba sai jiya, duk wuya duk daɗi a gida muke cin abinci, idan tafiya ta kamamu, muna tafiya da mai yi mana girki, duk in da muka je, shi zai yi mana girki". "Yaya Areef to ai wannan Mark ɗin ya hanani yin girki, ranar da nayi ya zubar" "Akan me zai zubar miki?!" Ya faɗa a ɗan zafafe, "Nima ban sani ba".

Shiru ya ɗan yi kafin ya ce "Okey yanzu dai zamu je mu sayo abincin, amma in the afternoon ke zaki girka mana, nima kuma zan taya ki yin girkin, jeki wajen Lion ki ce nace ya baki kuɗi zamu je sayan abu, daga nan sai mu je wajen gyaran gashi ko?". Cike da mamaki ta ce "Yaya Areef waye ya ce maka ina son a gyara mini gashi na?" Kashe mata ido ɗaya ya yi yana faɗin "Ai duk abin da yake da mahimmanci a wajenka, to ya zama maka dole ne ka rinƙa gane abin da yake buƙata, ke dai jeki ki karɓo mana kuɗi kizo, zan baki mamaki yau, zan saya miki abubuwan da kike buƙata wadda baki san kina da buƙata ba".

Shiru ta ɗan yi tana tunanin ta yadda zata shiga ɗakin Lion ta ce ya bata kuɗi, ɗan dafa ta ya yi yana faɗin "Ki je babu abin da zai faru". Mamaki ne ya kara kamata, wai shi yaya Areef ɗin nan waye yake gaya mishi abin da yake zuciyar tane? Bata san da babban jam'i hukumar sirri take tare ba.

Jiki ba kwari ta miƙe ta nufi bedroom ɗin na Lion, da sallama ɗauke a bakinta ta shiga, babu kowa a ɗakin, ɗan leke leke ta yi mishi, shiru babu kowa, juyawa ta yi zata fita kenan wayarsa dake saman bed nasa ya fara kara alamar shegowar kira,

Babu ko tsoro ta juyo ta dawo wajen wayar nasa, video call ne, ake kira, My dad shi ne sunan da ya bayyana a kan screen ɗin wayar, ba tsoro bare tunanin me zai je ya zo, kwata kwata ta manta wayar waye zata ɗauka, zuciya ya ɗebeta, shaiɗan ya zugata, ɗaukar wayar tayi, taɓe taɓe ta fara yi har ta yi picking call ɗin, a matukar razane ta saki wayar ya faɗa a kan gadon, hakan ya faru ne kuma sakamakon yin ido huɗu da blue eyes na daddy da ta yi, sai dai kuma bata kawar da kanta daga kallon shi da take yi ba, yana zaune a saman bed nasa, ya yi kewar ɗan nasa ne yasa ya kira, ganin ta yasa ya yi muguwar ɗaure fuska da bai taɓa yin irin shi ba, wani uban tsawa ya daka mata akan ina mai wayar? Me kuma ya haɗa ta da wayar? Cikin tsoro ta fara tattaɓa screen ɗin wayar dan ta katse kiran, hannunta sai kerma yake yi, kirjinta na dukan uku uku, sai yanzu da aikin gama ya rigada ya gama ta tuna da wayar waye ma ta taɓa, hankali a matukar tashe take ta faman katse kiran, sai magana daddy yake yi mata bata amsa ba, da kyar ta samu ta katse kiran tare da kwasawa da gudu ta nufi waje.

Bata zame ko'ina ba sai garden, yadda ta barsu haka ta dawo ta same su, a bakin garden ɗin ta tsaya ta daidai ta natsuwarta kafin ta shiga, bata bari su Areef sun gane abin da ta yi ba, a nutse ta ce mishi Lion baya ɗakin, taɓa Aseef ya yi tare da ce mishi ya je ya ɗauko musu kuɗin su tafi kawai.

Okey ya amsa da shi tare da miƙewa ya nufi cikin gida, shi kuma ya miƙe ya riƙo hannunta suka nufi wajen mota, da shigarsu bai fi 2 mins ba, sai ga Aseef ɗin ya dawo hannunsa riƙe da key ɗin motar da kuma kuɗin, mazaunin driver ya shiga tare da kunna motar, tun kafin su iso gateman ya wangale musu gate ɗin, da gudu ya kutsa hancin motar waje, sai dukan uku uku kirjinta yake yi, addu'a take yi Allah yasa kada Lion ya gane ta ɗauki wayar............ TO SAI DAI MU CE AMIN, AMMA DA KAMAR WUYA DAI.

❤️❤️TRIPLETS❤️❤️



E27-28



"Ina muka nufa Areef?" Cewar Aseef, kallon Rimsha dake ta faman kallon titi ya yi, "Sister ina zamu fara zuwa? Super market ko kuma restaurant?". Jin voice ɗinsa sai da ya sanya gabanta ya yi wani mummunar faɗuwa. "Restaurant" ta bashi amsa tana kallon hanya. "On Monday zaki fara zuwa school ko?" Gyaɗa mishi kai ta yi alamar eh, dogon hancinta ya yana faɗin "To kin dai shirya ko?" E ta bashi amsa, shi kam Aseef sai tuki yake yi yana latsa waya, ga shi sai zabga uban gudu yake yi kamar babu gobe, ɗan uwan nasa kuma bai wani damu da ya hana shi taɓa waya yana tuki ba, ya mance cewa nan fa ba Washington DC bane, a Washington DC ne idan aka ga motocin gidansu sun hau hanya, abubuwan hawa ke kaucewa su basu hanya, shiyasa suke yin duk irin tukin gangancin da suke so a kan hanya, dan babu wani abin hawa da zai keta da gabansu, a nan Nigeria kuwa, basu san gidan jajayen wuya suka zo ba, yo ko doka ce a ka kafa ƴan Nigeria irin haka, ai sai sunci uwar dokar sun kora da ruwan mai sanyi daga fridge, koma uban waye yazo wucewa a kan titi ƴan Naija babu ruwansu wucewa zasu yi, idan ya ga dama ya wuce ko ya tsaya matsalar sa ce, su dai sun rigada sun wuce.

Restaurant da suka je jiya, shi yauma suka je, yau dai a nan suka ci abincin, sai kallonsu jama'a suke yi, sun ga masu jajayen kunnuwa, fararen tattabaru, kyawawan gaske, kamar dai ko yaushe sai aikin latsa waya yake yi, yana makale da Heartbeat nasa suna hira, ya hanata ko motsawa, Rimsha da Areef sai zuba hira suma suke yi, cikin natsuwa suka ci abinci, sai dai Aseef bai ci ba, ya ce ba zai iya ba, Areef ne kaɗai ya tayata ci.

Bayan sun kammala Areef ya biya kuɗin suka fito daga wajen suka nufi super market, suna tafiya suna hira, sai bata labarin Washington DC Areef yake yi, tana ta murmushi. Tasha ruwan mamaki lokacin da suka je super market ɗin nan, kayayyakin da take mutuwar so Areef ya rinƙa zaɓa mata, sai tunani take yi a kan waye ya gaya mishi abin da take so kenan, har da takalma high heels irin wanda take so ya kwasa mata, ta sha sayayya iya sayayya ba karya, a nan ne Aseef yake gaya mata ai shi ma ya saya mata kaya, har da abin wuya irin nasu da ya ce zai sa a buga mata, to ya bugo ya zo mata da shi, yana cikin wannan akwaitin da ya ce ta ɗauka jiya bata ɗauka ba, ba ƙaramin daɗi ta ji ba, cike da murna ta ce su koma gida, dan ta je ta kalli kayan, to suka amsa mata tare da nufar wajen biyan kuɗi.

Areef ne ya biya, ma'aikatan wajen suka ɗauka masu kayan zuwa wajen motarsu, a gidan baya suka sanya kayan, kamar yadda suka zo, ita da Areef a kujerar gaba, shi kuma Aseef driver, haka suka sake shiga suka nufi gida, sun manta da batun gyaran gashi.

Suna tsaka da tafiya a hanya daddy ya kira number Aseef, ya sha ruwan mamakin ganin call ɗin daddy da safiyar nan, yana can yana tunanin ko lafiya daddy ya kira shi, sai da wayar ta kutsa matsewa, ya yi maza ya ɗauka tare da sanyata a hand-free dan yana tuƙi. "Hello daddy good morning?".

Wani irin mahaukacin tsawa ya daka mishi wadda ya sanya shi taka birki a tsakiyar titi, saura kaɗan motar dake biye da su a bayansu ta dake su, sai Allah yasa ta kauce, daga Rimsha har Areef sai da kansu ya bugu da jikin glass ɗin motar, saboda irin birkin da ya ja babu excuse.

"Michael wace ce ta ɗauki wayar Romeo yanzun da na kira shi?! Na sake ina kiran shi baya ɗagawa, shin a ina ma kuke tukunnan?!!". A razane ya ɗago yana kallonta, dan yasan ita ce ba makawa, daddynsu bai taɓa yi musu magana cikin irin wannan matsanancin siga mai cike da tashin hankali ba, to menene matsalar?.

Nan take shi ma tsantsar bala'in ɓacin rai ya bayyana a saman fuskarsa, tabbas yasan yau ba ƙaramin yaki za'a sha ba a Washington DC, dan kuwa idan daddy ya san suna Nigeria akwai bala'i ba kaɗan ba, sun ce mishi suna Spain ne wajen James, ba zai taɓa yarda su yi nisa har Nigeria ba, fatansu dai Allah yasa kada ciwonsa ya tashi, shi kansa Areef yau idan ransa ya yi dubu to ta ɓata mishi, ina ga kuma Romeo? Shi da ta ɗaga kiran na shi, Aseef jikinsa har rawa yake yi saboda tsantsar ɓacin rai, ji yake yi yau idan bai ɓalla yarinyar nan ba, ba zai sami kwanciyar hankali ba, yarinya bata ji sam, me ya kai ki taɓa waya ke da akace ki karɓo kuɗi?.

"Daddy am coming". Yana kai karshen maganar ba tare da ya jira me daddy zai ce ba ya yi diff ya katse kiran, a fusace ya juyo da kallonsa kanta, cikin ɓacin rai da kakkausar murya ya fara magana "Me yasa kika taɓa wayar Lion? Kin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login