Showing 147001 words to 150000 words out of 359620 words
Allah ya isa ban yafe ba, sai Allah ya tsayar da mu ranar da bata da abin da zata biyani face ladarta*
Dedicated to Maman Yasmin💋
E39-40💋
Cikin sanyin murya cike da tsoro ta ce "Yaya Saif ga tea". Bai amsa ba kuma bai ɗago ya kalleta ba har His excellency ya ɗaga kiran nasa, kara wayar ya yi a kunnensa ya fara magana a nitse cikin kwanciyar hankali, yana fitar da words one by one, zuba mishi idanu ta yi tana kallon yadda yake motsa kyawawan lallausan red lips nasa, ba zaka taɓa cewa shi yake maganar ba, magana cike da class.
Bayan ya kammala ya ajiye wayar a gefe tare da yin kasa da kansa kamar mai tunanin wani abin, daddaɗar kamshi su kaninfarin da chitta dake cikin tea ɗin sai dukan hancinsa yake yi, har ga Allah kamshin ta yi mugun yi mishi daɗi, ita kuma tana tsaye kamar wata soja, wani irin kara suka ji tamkar fashewar glass a palon kasa, a guje ta watso ta haye saman mattress ɗin ta ɓuya a bayansa, har da kankame shi ta yi, mamaki ne ya kama shi, wai wannan wace iriyar yarinya ce, tsoronta ya yi yawa, ko motsawa bai yi ba. Sun ɗan ɗauki lokaci a haka kafin ya yunkura zai miƙe dan ya je ya ga menene ya fashe a palon.
Kankame shi sosai ta yi, ba ƙaramin haushi ta bashi ba, ya tsani mutun matsoraci, a ɗan fusace ya juyo tare da fisgota da karfi, gabaɗaya ta tafi sai saman faffaɗar kirjinsa, damko wuyarta ya yi yana ƙoƙarin fara magana, zaro idanunta waje ta yi a matukar tsorace, ba ƙaramin kyau razananniyar face ɗin nata ta yi mishi ba, musaman ma da ta zaro idanun nan nata, ga su sleeping eyes dara dara, ga su farare tas kamar audiga, ya tsani ganin matsoraci, amma yau fuskar matsoraciya ta burge shi, tsoron ya yi wa face ɗin nata kyau, sake ta ya yi tare da miƙewa ya nufi palon kasan, ita kuma kwanciya ta yi a wajen ta takure waje guda, jikinta sai wani kerma yake yi.
Babu kowa palon kasa, daga in da yake tsaye ya hango cikin kitchen, ashe cup É—in daddy da ta É—auka bata mai da drawer da kyau ta rufe ba, kuma ta jawo tray É—in cups É—in baki baki dan tsawonta bai karisa kaiwa can ba, to shi ne tray É—in ya faÉ—o gabaÉ—aya glass cups É—in suka fashe, guntun tsaki ya ja tare da juyawa ya koma saman.
A in da ya tashi ya koma ya zauna, cup ɗin tea ɗaya ya ɗauka cikin natsuwa ya ɗan zuba sugar kaɗan ya fara sha, dan kamshin tea ɗin ya yi mugun tafiya da shi, haka zalika ɗanɗanon tea ɗin ta yi mishi daɗi, kuma yunwa yake ji sosai yasa shi ya sha, idan baku manta ba, bai ci abincin daren jiya ba. Ba ƙaramin daɗi ta ji ba, Lion ya sha tea ɗin da ta girka mishi, har wani nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke, tare da miƙewa zaune a tsakiyar mattress ɗin tana ɗan satar kallon shi, da yake suna kusan a jerene waje guda, sai dai da ɗan rata a tsakaninsu.
Wayarsa ce ta fara kara alamar shigowar kira, yana dubawa sai yaga Aseef ne, nisawa ya yi, ba ƙaramin daɗin kiran nan ya ji ba, yana kewarsu sosai da sosai, ɗaukar kiran ya yi, suna haɗe su dukkansu biyu kwance a saman bed nasa, cool murmushi Aseef ya saki, shi dai Areef bai da yawan fara'a, amma akwai kyan zuciya kamar me, zuciyar zinari ke gare shi, ba kowa da kowa yake samun ni'ima da baiwar zuciya irin makamanciyar tasa ba.
Kamar abin haɗin baki, har suna rige rigen tambayar ina Rimsha, Lion ya ɗan yi mamaki, wai ba za su tambaye shi ya yake ba, ya ya isa garin da ba nasu ba, ya ya kwana, sai ina Rimsha suke tambaya?, Ko gaisawa basu yi ba, su dai ina Rimsha kawai, lallai Rimsha ba ƙaramin samun damar mallake zuciyar ƴan uwansa ta yi ba,.
Shiru ya yi musu bai tanka ba, turo baki Aseef ya yi tare da saka mishi kukan shagwaɓa a kan lallai shi sai an nuna mishi Rimsha. "Ka sha maganinka Areef?" Shi ne abin da ya ce dasu, gyaɗa mishi kai ya yi yana mai kara tambayarsa dan Allah ina Rimsharsu take. "Yau ya kamata ka cire bandejin dake wajen ciwon ai, yanzu komai normal ne". Ya sake faɗa a sanyaye, tamkar bai ji tambayarsa Rimsha da suke yi ɗin ba, amsa mishi da okey Areef ɗin ya yi tare da sake tambayarsa ina Rimsha a karo na uku.
Shiru ya yi bai amsa ba, cikin zoyala Areef É—in ya sake cewa "Wai Saif me ya faru ne na ganka kamar sabon ango? Sai wani kyalli face naka take yi, ko dai garin Abujan ne ta yi daÉ—i sosai?". Kwashewa da dariya Aseef ya yi yana faÉ—in "Ni dan Allah ka nuna mini my Rimsha, ita nake son gani, idan ba haka ba, wlh bani ba cin abinci yau". Ya san halin Aseef sarai, zai aikata ya ki cin abincin.
Dogon numfashi ya ja tare da sauƙewa a hankali, ya fahimci ba za su barshi ya yi numfashin or ya sha iska ba matikar bai nuna musu in da take ba, da alama kuma idan bai nuna musu ita ɗin ba, ko abinci ba zasu ci ba, yadda suka kafe da sanyin safiyar nan suke wani tambayarsa ita, wannan kenan dan ita suka kira shi ba dan lafiyarsa ba, ita suka kira su kallah ba wai su tambaye shi ko ya isa lafiya ba, lallai ma sun shahara, yanzu Rimsha ta zama kamar kishiyarsa a zuciyarsu.
Gently ya ɗan waigo tare da ɗago dara daran blue eyes nasa ya sauƙesu a kanta, tana zaune shiru kamar mai tunanin wani abin, ba karya ta yi kyau sosai cikin kayan jikin nan nata, gabaɗaya shape nata sun bayyana, ga shi ba'a magana in dai wajen shape ne, akwai shi sosai, ƙasa ta yi da kanta dan kada su haɗa idanu, yatsun hannunta ta fara wasa da shi kamar wata mara gaskiya, zazzaƙar sexy voice nasa ne ya ratsa dodan kunnenta, calmly ya furta ta zo nan, ba musu ta matso gefen shi sosai tana wani yin kasa da kai, Aseef yana ganinta ya furta "Our Queen!" Shi kuma Areef ajiyar zuciya ya sauke.
Jin muryar Aseef yasa ta ɗago kanta, wani irin kyakkyawar kayatatcen cool murmushi ta saki wadda sai da dimple nata suka yi wani irin lotsawa na musamman, siririn wishiryarta dake tsakanin fararen hakwaranta ya bayyana, ba zaka taɓa cewa abinci ko wani abin ya taɓa ratsa cikin hakwaran nan nata ba saboda haskensu, sai kyalli suke yi, suna shan wankewa ne da kayan wanke baki masu inganci, shiyasa suke tas.
Shagwaɓe murya ya yi yana faɗin "Our Queen ina missing naki over wlh, yau ba zanci first spoon naki bafa". Ita ma shagwaɓe murya ta yi kamar dai yadda ya yi mata magana, tamkar zata yi kuka ta ce "Nima ina kewarku sosai, Yaya Areef dan Allah ku shigo mota kawai ku biyo mu, zan fi jin daɗi, yanzu wlh ina tsoron gidan sosai, akwai wasu mutane, dan Allah kuzo zan fi jin sanyi". Yadda tayi maganar sai da ta sanya Lion ɗin waigowa ya kalleta, ga shi tana magana dimple nata na wani irin lotsawa, duk wanda ya kalleta sai ta burge shi, ga shagwaɓa da take zubawa Aseef, abin ba'a cewa komai, yau har cikin zuciyarsa sai da ya ji ta burge shi, kawar da kallonsa ya yi daga kan nata tare da cigaba da shan tea ɗin nasa ya kawar da wayar daga face nasa zuwa saitin tata.
"Kina so mu zo ne my Rimsha?" Cewar Areef, da sauri ta gyaɗa mishi kai alamar e, "To shikenan zamu zo, amma ke da kike tare da Lion me abin tsoro? Kada ki damu, ni nasan waye ɗan uwana, yana kaunarmu kuma yana kaunar dik abin da muke kauna, muna kaunarki ya sani, ba zai taɓa watsa mana kasa a idanu ba, yana son ganin mu cikin farinciki fiye da kansa, so ki kwantar da hankalinki, dole zai baki farinciki dan yasan idan ya yi hakan kamar mu ya yi wa, in kin yi farinciki tamkar mune muka yi, akasin hakan ma, mune muka yi"......... A nan wajen Areef ya yi amfani da basira ne ya ɗaure Lion da magana, ya gayawa Rimsha Lion yana sonsu fiye da kansa, dan haka zai kula da ita, ya san cewa idan ya faɗi hakan, kenan suna da kwarin gwiwa sosai a kan shi, hakan zai sa Lion ɗin ya bata kulawa dan kada ya watsawa ƴan uwan nasa kasa a idanu, Areef ba dai basira ba, akwai basirar na wuce misali.
Zata yi magana Lion ya miƙa mata waƴar tare da miƙewa ya bar wajen zuwa ɗakin daddynta, yana tafiya Areef ya ce "Kina ji sister?" Gyaɗa mishi kai ta yi alamar e tana ji, "Lion ba ya cin abincin restaurant, ba ma zai taɓa ci ba komai wuya komai daɗi, duk in da zai je in dai ba mai yi mishi girki, to Maltina da kyau sune kawai suke zama abincinsa, dan su hannun baya taɓa cikinsu a cewarsa, kinga kwai ma ko an dafa ai ba'a taɓa cikin ba sai bayan, bayan kuma ɓarewa za'ayi a zubar, dan haka ki rinƙa dafa mishi kwai, dan Allah kada ki bari ɗan uwana ya zauna da yunwa, wlh bashi da juriyar yunwa, sai dai baya cin abinci sosai, iya Maltina idan ya sha, yana iya ƙoshi, amma idan lokacin cin abincinsa ya yi zai shiga damuwa dan baya jure yunwa, ki rinƙa bashi Maltina da kwai, na san ba zai iya cin abincinku na Nigeria ba, dan haka ba sai kin sha wahalar girkawa ba kin ji ko?" "To yaya Areef amma yanzu da na bashi tea namu na nan ya sha wlh, ka ga cup nashi ma har ya kusa shanyewa, kaɗan ya rage".
Ba Areef kawai ba, har ta Aseef sai da ya zaro idanu waje, anya kuwa,? Aseef ya tambayi kansa da kansa a cikin zuciyarsa, Areef kuwa cewa ya yi "Ba abin mamaki bane dan ya sha, na san yunwa yake ji shiyasa ya sha, na gaya miki baya da juriyar yunwa ko kaɗan, dole zai sha dan bashi da mafita, ba zai iya cin abincin waje ba duk wuya duk daɗi, yanzu kuna da Maltina a gidan naku ne ko babu?". Ɗan waigawa ta yi tana kallon shi yana nufota ya fito daga bedroom na daddynta, "Yaya Areef babu, babu Maltina kuma babu wuta a gidan". Zai yi magana Lion ya miƙa mata hannu a kan ta bashi wayarsa, babu musu ta miƙa mishi cikin girmamawa a kuma nitse.
"Areef zan fita ne, sai na dawo". Ya kai karshen maganar tare da katse kiran ba tare da ya jira amsarsu ba, pistol gun da ya ajiye daren jiya ya ɗauka ya nufi hanyar palon kasa dan ya sauƙa fita zai yi zuwa unguwa. Zazzaƙar muryarta ne ya katse shi tare da sanya shi juyowa babu shiri. "Yaya Saif tsoro nake ji, dan Allah kada ka fita ka barni, ina jin tsoron gidan sosai". Ta yi maganar a nutse, a shagwaɓe, can kasa kasa kuma, sannan ta yi maganar tana sunkuyar da kai katsa dan bata son kallon face nasa bare ma taga action ɗin da zai ɗauka.
Shiru ya ɗan kalleta na ƴan sakanni, maganar Areef ne ta dawo mishi kunnansa, yana son mu fiye da kansa kuma yana son farincikinmu, ba zai taɓa bari ki shiga kunci ba, dan yasan idan kin yi farinciki to tamkar mune muka yi, tuna hakan yasa ya juya ya cigaba da tafiya, binshi da kallo ta yi idanunta sun ciko tab da kwallah, tana bala'in tsoron zaman gidan ita kaɗai, bai juyo ba kuma bai yi mata magana ba har ya sauƙa ya fita daga palon baki ɗaya, juyowa ta yi ta balcony tana kallon shi ya zo wajen motarsa, shiru ya ɗan tsaya bai shiga ba, can kuma sai ya ɗago kansa sama kamar yasan tana kallon shi, da hannu ya yi mata alama a kan ta zo su tafi, da sauri ta miƙe, tsabar murna bata ma san lokacin da hawayen da suka cika mata idanu suka zubo ba, ɗakinsu ta koma ta ɗauko ɗan ƙaramin farin hijabi ta sanya a saman kanta, ta yi kyau over, baiwar Allah ko tea ɗin ma ita bata sha ba, kuma tana jin yunwa sosai kamar ta mutu, amma ba halin ta ce zata tsaya shan tea ɗin, dan ba zai jirata ba.
Ta wutsiyar idanunsa yake kallonta tun da ta fito, sai da ta kariso gabansa, calmly ya ce ta buÉ—e musu gate, da okey ta amsa mishi tare da wucewa ta je ta buÉ—e gate É—in, shi kuma ya shiga motar ya tada ta, waje ya nufa, bayan ta fita ne ya tsaya yana jiranta, sai da ta rufe gate É—in sannan ta zo da sauri ta shiga gidan gaba, sai tashin kamshi take yi.
Da gudu ya ja motar, bayan sun kusa kaiwa babbar gate ne ya ciro face mask ya sanya a face nasa, dan yasan idan sun isa gate ɗin sai ya sauƙe glass ɗin motar, miƙa mata face mask ɗaya ya yi a kan ta saka, dan baya son su tsayar da su tambayarta yaushe ta dawo da sauransu, dan ba wanda bai san ƴaƴan Nawazudden ba a wajen, suma masu tsaron babbar gate ɗin sun santa tun da kullum daddy na kaisu school.
Haka kuwa aka yi, da suka zo sai da aka tsayar da su, suka yi binciken da zasu yi sannan suka fice, suna fita ya kunna goggle map a wayarsa ya ɗauki hanya kawai abinsa, sun yi nisa da tafiyar da suke yi sai ya lura ana bin bayansu, wata bakar mota ce ta fara biyo su tun ɗazun, ɗan juyowa ya yi ya kalleta ta cikin mirror, sarkin tsoro sai kallon hanya take yi, kasa kasa ya ce ta ɗaura seat belt nata, okey ta amsa tare da ɗaura wa, shi ma ɗaurawa ya yi tare da canza hanya daga kan hanyar da yake ya sauƙa izuwa ɗayar hanyar ya kuma kara gudun motar sosai, bata wani damu ba, dan dama bata san ina zasu je ba.
Gudu ya yi ta shararawa har suka fita bayan gari, a É—an wani daji ya paka motar tasa tare da ce mata ta zauna a ciki kada ta fita, dama yasan in dai suka fita sai an bi bayansu, da gangan ya ce ta buÉ—e mishi gate, dan ta fito a waje ne ta shiga motar tasa, yana son kowa ya san ta dawo, idan suka sani kuma sai an biyo bayansu, wannan dalilin yasa ya É—auko pistol gun nasa.
Ta cikin mirror yake kallon wannan bakar motar, É—an nesa da nasu suma suka paka, suma bakar glass ce da motar tasu, baka iya ganin mutanen da suke ciki, baya son fita, dan kada su gudu, yana da tabbacin basu san shi ne a cikin motar ba, Rimsha suka biyo, dan ita ce ya shiga motar a waje, shi tun daga cikin gida ya shiga, ita kuwa sarkin tsoro tuni ta tsorata ganinsu a daji, jikinta har wani karma ya fara yi, ta manta ita Æ´ar soyayya ce, yau ga daji daÉ—in soyayya amma kuma jikinta na kerma.
Tana can tana tunani zazzakar sexy voice nasa ya katse mata tunani da cewa "Cire face mask na fuskarki ki fita ki zagaya wajen bishiyoyin ɗan bayan mun can ina zuwa". Ba musu ta cire ta kuma fita, ya yi mata haka ne, dan yana son mutanen su fito, yana son sanin ko su waye ne, tabbas idan ya fito suka ganshi zasu gudu in basu riƙe makamai ba, idan kuma suka gudu da wuya su sake biyo Rimshar ta wannan hanya, sai dai su canza salo, hakan kuma zai sanya shi ya jima a garin nan, baya son wuce kwana uku bai gama komai ya koma ba, idan ita ta fita, zasu yi tunanin bari su lallaɓa su kasheta su cika aikinsu, dan shi ɗan ta'adda kullum gani yake yi zai yi nasara, baya taɓa hangen zai faɗi, shiyasa basu nadama sai sunga mutuwa ɓaro ɓaro.
Tana fita ta nufi wasu bishiyoyi dogaye da suke É—an nesa da motarsu ta É—an bayar motar amma, ma'ana tsakanin motarsu da na waÆ´an da suka biyo su, mutane huÉ—u ne suka biyosu, dukkansu fuskokinsu sanye da mask, ga kuma bakaken suit kamar zasu je church or party, suna ganin fitowarta É—aya daga cikinsu ya ce "Oga wlh ita ce, yanzu saura mu san ita da waye a cikin motar, mahaifiyarta ce ko waye?".
Wanda aka kira da ogan ya amsa da cewa "Dole ita da mahaifiyarta ce mana, kun san dai Nawazudden kam ya jima a lahira, shi ma Shitu hakane, dama ita da Mahaifiyarta da ƴar uwarta suka rage, kuma kunsan Nawazudden ba shi da ƴan uwa, duk waƴan da suka san shi sun ce shi kaɗai suka sani, maraya ne tsintatcen mage, zuwa Abuja neman aikin yi fa ya yi, ɗan cirani ne bai da kowa, ita ma matar tasa marainiya ce basu da kowa, amma ba zamu yi gangancin tinkarar motarsu ba har sai mun san dame suke tafe, yanzu dai ku sauƙa mu kashe yarinyar, idan muka bita cikin dajin muka kasheta kunga dole mahaifiyar tata koma wace ce ta fito idan ta ji shiru yarinyar bata dawo ba, dole na cikin motar ta fito dan zuwa nemanta, kunga a nan ne zamu gane da waye suke tafe, sai mu haɗesu duk mu kashe, yanzu ku fita mu je". To suka amsa tare da buɗe kofofin motar suka fito, jahilci ya fi hauka, ya Allah ka bamu ilimi mai albarka mai amfani, kowa ya tsaya ya nemi ilimi, idan ba jahilci ba, ta ya za'ayi ku kalli mota danƙareriyar har haka ta faka a cikin daji kuma kuyi tunanin su ba'a shirye suka zo ba? Tabbas jahilai ke yin ta'addanci, mai ilimi wadda yasan me yake yi, yasan Allah da