Showing 270001 words to 273000 words out of 359620 words
Yaya Saif ko?". Hararar wasa ya wurga mata yana faɗin "Ni ma a nan ba wuya kike bani ba ne? Wato ita ma koya mata yanda zata wahalar mini da my pleasure na kike yi ko? Allah ba zan yarda ba!". Zata sake yin wani magana ya haɗe bakinsu waje guda, dukan wasa ta fara kai mishi a kirjinsa tana ƙoƙarin kwace bakinta, ƴan rigima biyu aka haɗa a wajen ne, sun iya rigima ba kaɗan ba.
Jin abin nasu azimun ne yasa Rimsha ta lallaɓa ta katse kiranta cikin rufin asiri tare da miƙewa ta koma saman bed ɗin ta kwanta kusa da shi cike da tsoron abin da zai iya aikata mata, tuni ya jima da yin barci abinsa, hakan ce tasa ta miƙe ta yi kwanciyar rigingine tare da zubawa face nasa idanu, sam bata san shi bashi da nauyin barci ba, bata san duk motsinta yana ji ba. A hankali kamar wata ɓarauniya cikin sanɗo ta kai yatsarta saman lips nasa ta ɗan taɓa, ganin bai motsa bane yasa ta ɗan sake taɓawa, duk yana jinta sai dai barci ya sha kansa ya kasa buɗe idanu.
Matso da face nata daf da nasa ta yi, sumbatar lallausan kumatunsa ta yi, shiru bai motsa ba, nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta sake kai ɗan bakin nata saman nasa lallausan lips ɗin, a tunaninta yana zuba barci, sumbatar lallausan laɓɓansa ta so ta yi, sai da ya barta ta kawo ɗan bakin nata zata sumbacesa ya waro dara daran idanunsa waje, gasu sun yi jawur saboda barci, a sukwane ta miƙe dan ta diro kasa daga gadon ta gudu, hannu yasa ya rikota tare da jawota ta faɗa saman faffaɗar kirjinsa, runtse idanunta ta yi tana faɗin ta tuba ba zata sake ba, nadama ta fara yi na menene ma ya kawota wajensa?.
(Ni kuwa na ce shagwarar Akila ya kawo ki mana)
Hannunsa ɗaya ya ɗaura a saman bayanta tare da mayar da idanunsa ya lumshe, dan barci yake ji over, ganin hakan ba abin da zai yi mata yasa ta kwantar da kanta a saman kirjin nasa tana shaƙar daddaɗar kamshin perfume nasa, a hankali ya cusa hannunsa cikin gashin kanta yana ɗan watsawa idanunsa a lumshe, barci yake ji sosai amma tana neman hana shi yin barcin nasa.
A ɓangaren gidan Abbo kuwa, bari mu leka mu dawo, kafin nan wata kila Lion ya yi barci ya taso ko kuma Rimsha ta hana shi yi, bari dai mu je gidan Abbon mu dawo sai muga me ake ciki.
A saman sofa Dr Nawid ya kwana, zamu koma baya ne dan jin me ya wakana, bayan ya yi sallar asuba sam bai mayar da barci ba, wanka ya yi tare da yin shirin zuwa office dan baya da bukatar cigaba da jimawa a cikin gidan, idan yana kallon face ɗin Aafia ransa yana kara ɓaci, kishi tana motsawa.
Bayan ya kammala shirinsa zai fita ne ta sauko daga saman bed ɗin ta sha gabansa tare da zube gwiwowinta a kasa tana ruwan hawaye tana bashi hakuri, da kyar ya iya magana saboda ɓacin rai. "Hakurin me kuma zaki bani A'afia? Ni tambaya ɗaya nayi miki, ki gaya mini a ina kika kai budurcinki? Kin ki ki bani amsa, to me kuma kike son na sake ce miki?".
Cikin kuka ta ce "Zan gaya maka, amma ka zauna dan Allah muyi magana a nutse". Bai musa mata ba ya koma ya zauna a saman sofa yana kallonta, kusa da shi ita ma ta zauna amma a kasa saman carpet, tana kuka kamar ranta zai fita ta fara bashi labarin duk abin da ya faru daga farko har karshe, tunawa ya yi da lokacin da Umminsa ta ce mishi kidnappers sun kama ƴar gidan babarsa Hjy Hadiza, kenan dama Aafia ce? Ya tambayi kansa, yes yasan da zancen an kamata, kuma yasan lokacin da aka karɓota Ummi ta bashi labari, da yake tana yawan bashi labarin ƴan uwanta idan suka zauna, hakan yasa yake da labarinsu duk da bai taɓa zuwa in da suke ba, har cikin ransa ya ji sanyi kuma ya ji tausayinta, amma sai ya ce to ta kira mishi daddyn Jelly bari ya yi magana da shi, ba musu ta kira mishi shi a waya ta bashi.
Cikin girmamawa ya gaishe shi kafin ya ɗaura mishi da dalilin da yasa ya kira shi, tabbatar mishi da hakan daddyn Jelly ya yi tare kuma da bashi hakuri na mantawa da suka yi basu gaya mishi ba, har lokacin tana kuka sosai, wani mugun tausayinta ne ya kama shi, katse kiran ya yi bayan sun yi sallama da daddyn, saukowa kasa saman carpet ɗin shi ma ya yi tare da rungumota yana bata hakuri yana kuma rarrashinta, da yasan haka ne ai ba zai yi abin da ya yi mata ba, rungume shi ita ma ta yi tana mai cigaba da kukanta sosai.
A cikin kunne ya raɗa mata ta yi kuka sosai dan ta rage ciwon dake cikin zuciyarta, ya yi maganar yana kara rungumeta da kyau.
Sai da ya barta ta yi kuka kamar na minti goma sannan ya hau rarrashinta yana faɗin to kukan ya isa haka yanzu kam, ai ta yi na kuɗinta, sam ta kasa dai'na kukan nata, da ya ga dai ba zata dai'na ba sai ya ɗago haɓarta ya haɗe bakinsu waje guda tare da sanya hannunsa yana goge mata hawaye idanun nata, shiru ta yi tana wani irin jan numfashi irin na wanda ta sha kuka ta ƙoshi.
Sai da ya yi kissing nata sosai sannan ya saketa tare da ce mata ta shirya ta raka shi office, a zahirin gaskiya gwadata yake son ya je ya yi gudun kar a samu matsala ta wata cuta ko makamancin haka, tun da fyaɗe ne, kuma ba ita kaɗai suka taɓa yi wa ba, suna yi wa mata da yawa, so ba za'a rasa cuta a jikinsu ba, amma sam bai bari ta gane abin da zai yi mata ba kenan, dan baya son ya sake ganinta cikin damuwa, shi yasan ta ƴan da zai bi da ita ya ɗebi jininta ba tare da ta kawo wani tunani a cikin zuciyarta ba.
Kasa tashi ta yi saboda duk karfin jikinta ya kare, ga shi yanzu suka tashi barci bata ci komai ba, ta kuma zo ta ci kuka kamar ba gobe. Miƙewa ya yi tare da cire suit dake jikinsa ya ɗauketa cak zuwa cikin toilet ɗin, da kansa ya haɗa mata ruwan wanka tare da cewa zata iya yi ne ko sai ya yi mata?. Da sauri ta ce zata iya yi, murmushi ya yi tare da juyawa ya fita ya bata waje.
Wankar ta yi, shi kuma yana fitowa wajen Ummi ya nufa, tana kitchen tana ƙoƙarin haɗa musu breakfast, tayata aikin ya fara yi suna gaisawa, cike da damuwa ta tambaye shi ya jikin Aafia? Da sauki ya bata amsa yana juya mata miyarta, abin gwanin burgewa, yanzu A'afia ta koya mishi shiga kitchen yana taya Ummi aiki, ya zamana ko ita Aafia bata a kitchen ɗin, to shi zai shiga ya taya mahaifiyar tasa, sune ake kira da nice family, Abbo kuwa ya mantar da su shi ma kwata kwata a rayuwarsu, babu wanda ya yi yunkurin nemansa, sun rufe babinsa.
Bayan ta fito daga wanka, shiryawa cikin Abaya launin Navy blue da zanen fari ta gaban ta yi, ta sanya ɗan hijabinta na please call me fari a kanta, ta fito waje, a kitchen ta iskosu, cikin girmamawa ta gaishe da Ummi, sai yi mata sannu ya jiki Ummi take yi, satar kallon shi ta yi, kashe mata ido ɗaya ya yi yana yi mata alamar ta amsa kawai, amsawa da lafiya ta ji sauki ta yi tana wani sunkuyar da kai kasa, sosai Ummi ta ji daɗi tare da yi musu fatan alkhari, sai dai ta fahimci Aafia ɗin ta yi kuka, amma da yake tasan ciwon mata, dama anayi ana kuka ne, sai ta mayar ai duk ciwon ne ya saka ta kuka, dan haka sai bata nemi jin ba'asin kukan ba.
A tare suka yi aikin suka kammala, Ummi ta yi ta yi da Aafia a kan ta koma cikin bedroom nata ta kwanta, amma ta ce a'a zata yi aiki, shi ma Dr yana son ta yi aikin dan ta ɗan jinjiga jinin jikinta saboda ya sami abin da yake so. Sai karfe 7 dai'dai suka kammala girke girke nasu tare da wucewa palo dan su yi breakfast cikin jin daɗi.
Bayan sun kammala suka yi wa Ummi sallama kamar kullum har bakin kofar palo ta rakasu a in da ta yi musu addua'o'i sosai sannan ta dawo cikin, sai sunkuyar da kai kasa Aafia take yi dan kunyarsa take ji sosai, sarai ya lura da hakan shiyasa da ya yi parking na motar tasa a cikin hospital ɗin bai fita ba, ya tsaya ya zuba mata idanu, sai wani ƴan kame kame take yi, daga karshe dai sai ta yi ƙoƙarin buɗe motar ta fito tun da shi bai fita ba.
Jawota jikinsa ya yi yana faɗin "Ina zaki je bayan mijinki bai fita ba?" Yana magana yana shafa bayanta, "Office naka zan je". Ta bashi amsa, a hankali ta yi maganar. "Wajen waye zaki je a office ɗin tun da ni ina nan?". Shiru ta yi bata bashi amsa ba, dan bata san me zata ce ba. A'afia, ya ambaci sunanta, na'am ta amsa mishi kasa kasa. "Kiyi hakuri da abin da ya faru kinji? Ki saki jikinki kamar da komai ya wuce, rashin sani ne ya jawo nayi miki irin wasu tambayoyi da yanzu ni kai'na bana son tunasu".
Nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta bashi hakuri ita ma a kan rashin gaya mishi da bata yi ba. "Zan sami kiss ɗaya kafin mu tafi?". Sam baya ji a jikinsa ta ɗauki wata cuta, shiyasa ma yake wasu abubuwa da ita, kwararren likita ne, so bai ga alamar cuta a tattare da ita ba, kawai dai zai gwada ta saboda tsaro ne, dan kuma tabbatarwa.
"Kai yaya Nawid ai ni ban iya kiss ba". "Sai na sake koya miki ko?" Gyaɗa mishi kai ta yi alamar e, hannu ya kai ya ɗago haɓarta suna fuskantar juna. "Duba idonta a wajen, har kin rame kwana ɗaya, a kan ki na fara son mace siririya fa, da sam basu burgeni, amma yanzu idan kika yi kwalliya sai naga kin fi masu kiba kyau sosai, kwalliya tafi zama a wajen masu jiki irin naki".
Juya idanunta sama ta yi tana faɗin "Cigaba da zugani, idan ka tashi ka auro ƴar lukuta, wata kila ma idan nayi kwalliyar daurewa kawai kake yi kana kallona ba dan na burgeka ba". Ƴatsa ɗaya yasa ya buge mata baki yana faɗin "Haka zaki ce?" Shiru ta yi bata kula shi ba. "Oh gimbiyata to yi hakuri na tuba". "Gaskiya ba zan hakura ba sai na rama". Ta faɗa a sanyaye.
"To shikenan na yarda rama sai mu tafi". Ya kai karshen maganar tare da ɗago mata bakinsa a kan ta rama, "To ka rufe idanunka". "To ai kema idanunki a buɗe nayi miki". Turo baki ta yi tana faɗin "A'a ni ban yarda ba sai ka rufe idanu". Ba musu ya rufe yana faɗin na rufe, sumbata ta kai mishi a saman bakin nasa tana ƙoƙarin zamewa ya capkota, dama yasan abin da zata yi mishi kenan, ƴar kara ta saka mishi dan bata yi zaton zai kamata ba, shi kuwa tas ya san me zata yi ne ya kuma shirya ta yanda zai rikota ɗin, kissing nata ya fara yi tare da rungumeta sosai a jikinsa, duk abin da suke yi su Bahijja suna sama ta window office nasa suna kallonsu, da yake asibitin hawa uku ne, shi office nasa tana can sama kololuwa, ita kam Bahijja tamkar ta haɗiyi zuciya ta mutu take ji dan bakin ciki, mamaki ma suke yi wai dama Dr ɗan love ne kenan? Ya zuba son ransa a gida sun zo nan ɗin ma ba zai raɓu da matar tasa ba, wannan anyi jarababbe in ji Bahijja................. Ba wani jarababbe kishi kawai take yi dan bata samu ba😌🤣💃
Sai da ya yi kissing na kayansa son ransa kafin ya saketa yana faɗin su je, fitowa ta yi kusan a tare suka fito, rufe motar ya yi ta karɓa mishi jakarsa, shi kuma ya riko hannunta suka nufi ciki, sai kallonsu jama'a suke yi saboda sun yi dace da juna ba kaɗan ba, jini ba wasa ba har wani kama suke yi, sai da ya kusa shiga office ɗin ne su Bahijja suka haɗa malaman jikinsu waje guda, ta koma office nata na bakin kofar shiga office ɗin nasa zuciyarta cike da bakin ciki.
Ko da suka zo shiga ko kallon in da take Aafia bata yi ba, sam jininsu bai haɗu ba ko kaɗan, cikin girmamawa ta gaishe da Dr kafin ta ce "Aunty ina kwana" sannunki kawai A'afia ta ce mata sannan suka shige ciki. Dabara ya yi mata ya ɗebi jininta da nufin zai yi mata test a kan wata cuta da ta shigo yanzu, har da ce mata shi ma zai yi wa kansa, gudun ya kawar mata da zargi haka ya ja jininsa a gabanta ba dan zai yi amfani da shi ba, sai dan kawai kada ya sa ta ji wani irin a cikin zuciyarta, ya fi so ta manta da komai.
Laboratory ya nufa yana faɗa mata yana zuwa ta jira shi, yana zuwa ya ajiye nasa jinin a gefe ya fara aiki a kan nata dan shi ne a gabansa ba nasa ba, tsab ya gwadata, babu wata cuta dake tattare da ita, hamdala ya yi ga Allah cike da farinciki ya dawo office ɗin nasa, yana zuwa ya rungumeta yana jin tsantsar farinciki, ta yi mamakin irin murnar da yake yi, ita ma sai ta rungume shi suka cigaba da abin da suka saba, yau kuma tun da ta rako shi office ɗin ai shekenan, aiki kuma a lalace zai yi shi.
Idan muka koma gidan Lion kuwa, zaune Jehan take a palon sama ita kaɗai tana tunanin duniya, Areef da daddynta sun fita........
E69-70
Idan muka koma gidan Lion kuwa, zaune Jehan take a palon sama ita kaɗai tana tunanin duniya, Areef da daddynta sun fita, Aseef da Akila suna cikin ɗakin, sai zubawa juna shagwaɓa suke yi, Akila ta ce ya kaita wajen Ammienta, shi kuma ya ce sai ta yarda ya yi mata wanka sannan zai kai ta, diramar da suke yi kenan sama da 40 mins, idan ta fara kuka sai ya rarrasheta, idan ta yi shiru ta ce zasu je, sai ya ce a'a sai ta yarda, idan ta sake saka mishi kuka shi ma sai ya saka mata ya kwanta ya ce ya yi fushi, haka zata yi ta aikin rarrashi har ya sake hakura, abin nasu kamar wasan yara, sam yanzu baya kula Areef, yana can yana zuba love ɗin sa, shi ma Areef ɗin bai zauna ba two days, yana faman busy ga tsokanar babyn nasa da yake yi, duk bayan ƴan mintuna sai ya tsokane ta.
Sam yau ta ji babu daɗin da bata ji ɗuriyarsa ba, sun jima da fita da daddy, yau bai tsokane ta ba, sai ta ji babu daɗi, tana zaune a palon sama tana shan yoghurt mai sanyi, kamar daga sama ta ga mutun ya hauro saman zai shiga bedroom ɗin Lion, kallo ɗaya ta yi mishi ta kawar da kanta tare da cigaba da abin da take yi.
"Who are you?" Muryarsa tamkar saukar aradu haka ta ji shi, ɗago idanu ta yi tana kallon cikin blue eyes nasa babu ko ɗar a tattare da ita, ta sani ko ba'a faɗa mata ba, daga ganin shi tasan daddynsu Areef ne, dan kuwa akwai kamanin, amma da yake ya nuna mata rainin wayo sai ta yi banza da shi kamar bata a wajen, tsawa ya daka mata yana mai sake tambayarta wace ce ita, mikewa ta yi ta ɗauki yogurt nata ta nufi bedroom ɗin daddynta dan a cewarta bata da lokacin bashi amsa, saboda idan baku manta ba, ita mutun ce da idan ka bita a hankali zaku zauna lafiya, amma idan ka nuna mata rainin wayo da izza ko isa, to ko bata yi maka rashin kunya ba, zata mai da kai mahaukaci, sai ka yi ta magana ba zata tanka ba, idan ka cika matsa mata ma, sai ta tashi ta baka waje, idan ƴan rashin mutuncinta suna kusa kuma, sai ta sauke maka kwando kwando kafin ta wuce, to shi dai daddy ya yi sa'a bata yi mishi rashin mutuncin ba, ta ɗauki yogurt nata ta wuce ta bashi waje, saboda tsoron ƴaƴansa ne yasa bata kula shi ba, tasan idan ta yi mishi rashin kunya ko mari ɗaya Areef ya yi mata ba zata tashi ba, sai ta kama kanta.
Baki ya buɗe yana ganin ikon Allah, yau yaga mace mai irin halin Lion a cewarsa, banbancin ba yawa, ji har da wani ɗaure fuska kamar wata ubansa, abin ya bashi mamaki, shiru ya yi kamar mai tunanin wani abin. Ya jima tsaye a wajen kafin ya shige cikin bedroom ɗin na Lion, dan yasan shi dai yanzu ba yanda zai yi da bakaƙen fatan nan, tun da Lion ya ce ba zasu bar gidan ba, to zaman lafiyarsa kawai ya fita harkarsu, idan ya matsa to wlh zai ja wa kansa matsalar da ba zai iya ɗauka ba, shi ne ya haɗa malaman jikinsa baya shiga harkarsu daddyn Rimshan sam, sai dai yana nan yana tunanin ta yanda zai raba ƴaƴan nasa da waƴan nan mutane wato bakaken fata.
Da misalin karfe 8 na dare, daddyn Rimsha, Areef, da kuma Jehan suna zauna a palon sama suna hira, sun dawo daga unguwar da suka je, gidan daddy na nan Kadunan suka je suka duba, dan Areef ya ce da Tga idan zai zo ya zo mishi da takardan yarjejeniyar da Lion da daddy suka yi akan lallai daddy zai yi shekaru huɗu a karkashin Lion ɗin, so ya kawo mishi takardan da hannunsa zai yage ta kafin Lion