Showing 123001 words to 126000 words out of 359620 words

Chapter 42 - Triplets Book 3 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2043

kallonsu, tun ɗazun ta tashi daga barci dan zata je school, makarantar yana ranta, shiyasa bata yi wani barcin kirki ba ta farka, yau Lion ya yi mata wani masifaffe kuma azababben kyau ba kaɗan ba, ta kafe shi da idu har suka bar gidan, nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta juya zuwa toilet.

A gurguje ta yi wanka tare da fitowa ta shirya cikin uniform nata, ba ƙaramin kyau ta yi ba, a palon kasa ta isko Areef yana tsaye yana waya, da alama da daddynsu yake magana, gefensa ta zo ta tsaya tana jiran ya kammala, after some minutes, ya Kammala wayar tare da riƙo hannunta cikin nasa yana faɗin "Kyakkyawar gimbiyar TRIPLETS ya aka yi ne?". "Good morning lovely brother". Ɗan leƙo face nata ya yi, ta yi kyau sosai da sosai, "Shikenan an gama shiri muje ko?" Kai ta gyaɗa mishi alamar e "To yanzu dai zo muje saman table na koya miki cin abincin kasarmu kafin mu tafi ko?". Ba zata iya yi mishi musu ba, kai ta gyaɗa mishi tana faɗin Okey.

Abincin da Mark ya shirya musu ya fara zuba mata ɗaya daga ciki, sai bin shi da ido take yi, "Me yasa ki kuka daren jiya kuma?" Ɗan zaro idanu waje ta yi, tana mamakin waye ya gaya mishi ta yi kuka kuma, "Ki dai'na mamaki idanunki suka nuna mini kin yi kuka, yanzu dai gaya mini dalili, da daddare dai nasan ba wanda zai shiga ɗakin ki har ya yi miki wani abin, to me matsalar?". A maimakon ta gaya mishi halin da take ciki na ɓatar ƴar uwarta, dan ko banza ba zai yarda ba sai ya nemota, amma sai ta ɓoye mishi tare da ce mishi karatun Alqur'ani mai girma ta yi ya sanyata kuka, ya gamsu da maganarta, dan ko shi idan yana karatu, yana tuna girman Allah, da wasu bayi dake bijirewa umarni Allah sai ya yi musu kwallah, sai dai a jikinsa yana jin tamkar tana da damuwa, bai cika son matsa mata a kan abu ba, dan haka sai ya kyaleta tare da tura mata abincin da ya zuba a plate ɗin a gabanta a kan ta ci.

"Yaya Areef ina tare zamu ci?" "Haka kike so?" Gyaɗa mishi kai ta yi, okey ya amsa mata da shi tare da ɗauko spoon ya ɗabo first spoon ya kai mata saitin ɗan bakinta yana faɗin "Buɗe baki ki karɓi first spoon na". Bata kai ga buɗe baki ba Aseef da ya fito yanzu ya yi maza ya zo ya cinye yana murmushi, harararsa ya yi kafin ya sake ɗebo mata wani abincin, zama shi kuma ya yi a ɗayar gefenta ya zamana sun sakata a tsakiya, a shagwaɓe ya ce "Sister saura first spoon naki, ɗebo ki bani naci". Ba musu ta ɗebo mishi, dan tasan halinsa sarai, yanzu ba ƙaramin aikin shi bane ya sanya musu kukan shagwaɓa a nan, bayan ta bashi sai ya ɗauko spoon nasa shi ma, ita ya fara bawa kafin Areef, daga nan suka fara ciki a tare, wasa wasa Rimsha bata san time da cikinta ya cika tap da abincin nasu ba, sun mantar da ita me ma take ci, sai hira suke yi mata gwanin ban sha'awa.

To mu ɗan koma baya kaɗan, a daren jiya, ba iya Rimsha ce kawai ta yi mafarkin Jehan na cikin wani hali ba, har ta daddynsu, mummynsu, Gwaggo duk sun yi, hakan yasa gabaɗayansu suka kwana a saman dadduma suna kaiwa Allah kukansu, musamman ma daddynsu da yafi kowa shiga tashin hankali, dan shi nashi mafarkin a tsantsar mummunar yanayi Jehan ɗin ta zo mishi, ya tsorata sosai, wai gata nan tana kuka an mata fyaɗe, tana kwance cikin jini, ga sarka a hannu da kafa an ɗaureta ana zaneta da wasu irin dogayen bulalu masu shiga jiki, duk in da aka zana mata sai wajen ya yi jajir ya tara jini, da yake ita fara ce tas, kunsan duk Uba na gari ya ga yarsa cikin wannan hali ko a mafarki ne ma dole hankalinsa ya yi mummunar tashi ba kaɗan ba, hakan yasa yau ya tashi da azumi a bakinsa dan ya roka mata Allah da ya tsareta a duk in da take, yasan in makamancin haka ya faru da ita zai iya mutuwa saboda bugawar zuciya, wlh bawan Allah nan har wani ƴar rama ya yi, duk ya yi sanyi jikinsa ya mutu, kuka ne kawai bai yi ba.

A ɓangaren mummy da gwaggo ma hakan ne, da azumi a bakinsu suka tashi, duk da su mafarkinta da suka yi bai kai na daddy muni ba, bayin Allah basu kaiwa kowa kukansu sai ubangijin taliƙai, da abu ya damesu zasu ɗauro alwala su kaiwa Allah damuwarsa, shiyasa a kullum suke cin nasara a kan makiya, badan suna addu'a ba ai da an rufe bakinsu, da Rimsha ba zata iya fitowa daga Daular Mutuwa ba, karfin addu'a ya fito da ita, shi ya juyar da hankalin duna har ya taimaka musu suka fita, suka yi breaking na record ɗin Daular Mutuwar, haka shi ma daddy, badan karfin addu'a ba da an jima da kashe shi, su ma su mum ɗin hakan ne, uncle Shitu, dukkansu karfin addu'a ke cetarsu a ko da yaushe, to yanzu ga Jehan ma sun dukufu a kanta, yadda suka dukufan nan kuwa wane uwar Hajiyar daɗi dan ubanta, tsafinta ya yi kaɗan, masu kai kara wajen Ubangiji sun fi yawa, karfin addu'ar bayin Allah ya fi karfinta, Allah dai ya basu Nasara, Amin. Mu cigaba da labari.

Bayan sun kammala cin abincin Areef ya riƙo hannunta yana kallon jakar bayanta, suka nufi waje, shi kuma Aseef sai da ya koma bedroom nasa ya ɗauko wayarsa da key ɗin mota ya fito, a cikin motar ya iskosu zaune suna jiransa, sai hira suke zubawa kamar wasu kawaye, mazaunin driver ya shiga, bai kai ga tada motar ba sai ga Imran da jelly su fito, gidan baya suka shiga, Areef na ya kirasu akan su tafi tare, suna shiga Aseef ya yi wa motar key, gaisuwa Rimsha ta fara ɗagawa Imran, da fara'a sosai a kan face nasa ya amsa, tare da tambayarta ya take, ita ma sai murmushi take yi ta amsa.

"Aunty jalila ina kwana?" Ta ɗagawa jelly gaisuwa, cikin mutunci Jellyn ta amsa mata, da alama ta natsu ne, tana bala'in tsoron TRIPLETS, bare ma kuma da taga Rimshar na zaune kusa da Areef ɗin a kujerar gaba, sai ta kara natsuwa sit kamar bata a wajen, shi kansa Imran sai da ya sha ruwan mamakin me yasa ta natsu sit daga shigowarsu cikin motar, kamar zai yi magana sai kuma ya danne, sai wani kankame shi take yi tana satar kallon Areef da tamkar bai san da zamanta a cikin motar ba, idan ta kalli Areef ɗin sai ta sake juyawa ga Aseef ta kasa banbance waye ne a cikinsu ya yi yunkurin marinta rannan.

Sai hira Areef da Rimsha suke yi suna dariya har suka iso school ɗin, shi kam Aseef yana tuƙi yana latsa waya, Heartbeat na kashe shi da love, tana kudundune a cikin bargo ta lafe a gado sai zuba mishi iya shege take yi, duk ya birkice mata, da kyar ma ya iya tuƙa motar har suka isa. A parking space na makarantar suka tsaya, dawo da kallonsa kan Rimsha Areef ya yi cikin sanyin murya ya fara magana "Ki kula mana da kanki sosai, zamu dawo mu ɗauke ki idan time ya yi, ki je class mu bari mu duba shigaban makarantar naku".

Da yake ba da wannan motar ta saba zuwa ba, sai Anaya bata san ita aka kawo ba, motar Imran Anaya ta sani, tana class, amma kafin ta shiga class ɗin taga tsayuwar motar, sai dai bata kai kallonta wajen ba, dan tasan bata san motar ba, da alama ita ma Anaya bata shiga abin da bai shafe ta ba.

"Yaya Areef zan yi kewarku sosai". Ta faɗa a ɗan shagwaɓe, leƙo face nata ya yi, cikin zolaya ya ce "Za'ayi kewarmu ne ko za'ayi kewar Saif?" Rufe fuska ta yi da hannayenta tana faɗin "A'a dukkanku dai". "Au ashe dai shi ma Saif za'ayi kewarsa kenan?" Cewar Aseef, shi ma cikin zolaya ya yi maganar, "E mana yaya Aseef, zan yi kewarsa sosai, dan ma na ganshi ɗazun kafin ya fita". Murmushi suka yi a tare har da Imran, a nan ne kuma jelly ta fahimci ita Rimsha ba son Imran take yi ba, tana da wadda take so kenan, gabaɗaya sai ta ji babu daɗi abin da ta yi mata, dama an ce rashin sani ya fi dare duhu, to ita jelly abin da ya faru kenan tsakaninta da Rimshan tashin sani.

Sumbata Areef ya yi mata a lallausan kumatunta yana faɗin "Nima zan yi kewarki sosai, ina jin kamar ba zan iya wuni guda ban ganki ba". Wani irin kunya ta ji, su kuma kun sani ba sai na sake faɗa ba, sumbatar mutun or kiss ba wani abu bane a wajensu ga koma waye, shiyasa ma ya sumbace ta ɗin.
Ganin ta yi shiru ne yasa ya ce "Ba zaki sumbace ni ba nima? Haka zaki tafi mu rabu?". Bata da zaɓi, dole ita ma ta juya ta sumbace shi a kumatu, tana kokarin cewa Areef ya fita bari ita ma ta fita dan ita ce a ciki, sai ta ji saukar wani sumbata a kumatunta na Aseef, juyowa shi ma ta yi tare da bashi sumbatar, cool murmushi ya sakar mata kafin ya buɗe kofar motar ya fita yana faɗa mata ta kula musu da kanta sosai.

Kusan a tare mazan suka fita daga motar, dan su je office ɗin shugaban makarantar, ita kuma jelly tana ciki tana jiransu, Rimsha na ƙoƙarin fita jelly ta riƙo hannunta tare da ce mata "Ki yi hakuri da abubuwan da suka faru kin ji Rimsha?". Cool murmushi ta sakar mata kafin ta ce "Babu komai Aunty Jalila, ni daman ban riƙe ki a cikin zuciyata ba, nasan rashin fahimta ce". Rungumar juna suka yi kafin nan ta saketa ta fita tana yi mata bye bye, da ido jelly take binta da shi babu ko kyaftawa, yau taga Rimsha ta yi mata kama da daddynta, Allah sarki bata san ƴar uwarta bace, dole akwai kama ta jini.

Class nasu ta nufa, da sallama kasa kasa ta shiga, wani ihu Anaya ta yi tare da tahowa da gudu ta rungumeta tana dariya, "Dama na ce yau In Sha Allah zaki zo". Ita ma dariyar take yi, ƴan class sai binsu da kallo suke yi, dan sun san halinsu a tare, Anaya na bala'in Kaunar Rimsha haka ita ma Rimshar.

Wucewa suka yi suka je suka zauna a mazauninsu, dama kowa da kujerarsa, sai dai suna kusa sosai da juna, "Rimsha ya kamata ki je ki roƙi uncles su baki test ɗin da suka wuce daga na last Monday zuwa yau fa ki yi, dan kinga suna da yawa, almost test 7 fa". Cewar Anaya.

Shiru ta ɗan yi kafin ta ce "Anaya ni English and mathematics nafi ji, yanzu dai ki rakani office ɗin Mr Emmanuel bari na roƙe shi ya bani English na yi, wlh ranar da kika gaya mini anyi test na English da kyar na iya barci". Murmushi ta yi tana faɗin "Kai Rimsha saboda English ɗin kika fi iyawa ba? Dole ki damu ai, amma gaskiya ni ba zan je office ɗin Mr Emmanuel ba, dan kin san halinsa sarai da bala'i, yanzu idan munje mu biyu ma yana iya kin baki ya ce waye ya ce muzo mu biyu, kin san fa ba'a shiga mishi office bibbiyu, mutun ɗaya ne, kema ki yi addu'a kafin ki je, bakin mugu azzalumi, sannan kuma uncle Faisal na jiranki, ba idan ya kiraki baki ɗauka ba, zaki yi bayani". Guntun tsaki ta ja tare da miƙewa ta miƙawa Anaya ɗin school bag nata tana turo baki ta nufi waje, haushin uncle Faisal ɗin nan take ji, kamar ta yi ta kifa mishi mari, a wawa, wawa take kallon shi ma, dan kawai yana nan shiru shiru da shi.

Tana fita ta hango motar su Areef ya bar makarantar, ajiyar zuciya ta sauke tare da wucewa ta nufi office ɗin, a bakin kofa ta yi excuse kasa kasa tare da tura kofar ta shiga, wani irin mahaukacin birki ta ja babu shiri, zaro idanuwanta waje ta yi tana kallon abin da kwakwalwarta ya kasa ɗauka, Mr Emmanuel tare da wata student ƴar ss 2 ne ko 3 suna romancing na juna, ya cire mata rigar uniform yana wasa da breast nata, ita kuma yarinyar sai wasa da gabansa take yi, matashiyar budurwa ce wadda zata iya kai 19 to 20 years haka, gata kyakkyawa ba laifi, fara ce tas, kuma da alama musulma ce, dan kunsan hasken musulci baya ɓuya a fuskar bawa.

A wani irin razane suka ɗaugo kai jin an buɗe kofar, guntun tsaki yarinyar ya ja tare da ɗaukar rigar uniform nata tana maidawa jikinta, da gudu Rimsha ta juya tana ruwan hawaye, to me abin kuka? Binta da kallo Mr Emmanuel ya yi, ita kuma yarinyar sai faman mayar da kayanta take yi, damko rigar uniform ɗin nata ya yi, cikin murya mai kama da na ƴan shaye shayen da turanci ya ce "Ina zaki je Fadila? Ai ban gama ba". Kara jan dogon tsaki ta yi tana faɗin "Mr Emmanuel ka bari sai an shiga class zan sato hanya nazo". Shafa breast ɗin nata dake tsaye kyam ya yi tare da lumshe idanu, kamar wani tsohon maye yana wani lashe baki. Ba dan ya so ba ya barta ta fice daga office ɗin bayan ta gama mayar da kayanta kenan.

Tana fita ya lumshe idanu yana tunano Rimsha a cikin zuciyarsa, tun ranar da ya ɗaura waƴan nan shegun idanu nasa a kanta ita da Anaya yake haɗiye yawu, ya yi ƙoƙarin jan Anaya da wannan shashancin, sai dai bai sami dama ba, dan kullum tana tare da Rimsha, kuma kullum suna cikin class basu cika fita sosai ba, yasan idan ya fara da Anaya zai yi nasara, dan da alama bata da ilimin addini sosai, kuma akwai yarinta sosai a kanta, ita kuma Rimsha ba sai na gaya muku ba, ta san komai dan mummynsu babu kunya babu ɓoye ɓoye ta sanar musu da komai, ta faɗaɗa musu ilimi dan gujewa irin hakan, shiyasa ake son uwa ta rinƙa jan ƴaƴanta a jiki, ya zama daga bakinta suka san komai ba daga bakin kawaye or wani waje ba, baya son idan ya tinkari Anaya Rimsha ta sani, ya fi son kafin ta sani ya rigada ya lalata Anaya ɗin, Shiyasa bai yi wargin tinkararsu lokacin da suke tare ba, ya bari yana jiran wata ƴar dama, lokacin da Rimsha ta daina zuwa school, kwata kwata baya samun damar ganin Anaya ɗin, sai ya zo class nasu karantar da su, bata fitowa, bata da abokiyar hira, da an tashi breakfast ko ya aika a kirata ba zasu ganta ba, a dokar makarantar kuma ba'a yarda wani malami ya kira ɗaliba lokacin da suke class ba, sai dai ita ɗalibar ta fita a sace, idan aka kamata kuma zata yi bayani, a takaice dai Mr Emmanuel Anaya yake son fara lalatawa kafin Rimsha, dan idan Rimsha ta san kudurinsa, zata zuga Anaya ta kuma tsawatar mata a kan kada ta yarda da shi, tsab ya gama karantarsu jira yake ya sami ƴar dama ya cinma burinsa.

Rimsha tana barin office na shi class nasu ta nufa, tana tafiya tana hawaye, abin ba ƙaramin ƙona mata rai ya yi ba, ace wannan kafurin yana lalata ƴar musulma, ta ji zafin hakan ba kaɗan ba, shi ne kuma abin da ya sanyata hawaye, sai da ta zo kofar class nasu ta tsaya tare da goge hawayenta tsab kafin ta shiga ciki, saman chairnta ta je zauna tana kasa da kanta dan kada Anaya ta gane ta yi kuka.

"Rimsha me ya faru ne? Me ya same ki? Mr Emmanuel ya yi miki muguntar tasa ko? Azzalumin wannan mutumin akwai bakin mugu, ya ce ba zan baki ki rubuta bako? Ko dai dukanki ya yi ne". Cewar Anaya.

Girgiza kai ta yi tare da miƙewa da sauri ta riƙo hannun Anaya ɗin suka nufi waje, binsu da kallo ƴan class suka yi har suka fice, suna fita suka haɗu da Uncle Faisal, gaisuwa suka ɗaga mishi, da fara'a ya amsa tare da tambayar Rimsha ya jiki, satar kallon Anaya ta yi tana mamakin ita kuma yaushe ta yi rashin lafiya? Kashe mata ido ɗaya Anaya ɗin ta yi alamar ita ce ta ce mishi bata da lafiya ne yasa bata zo school ba kwana biyu, ganin hakan yasa ta amsa mishi da ta ji sauki.

"Ayya Allah ya kara sauki, na yi ta kiran numberki da Anaya ta bani dan na yi miki sannu ya jiki, sai dai kuma baki ɗauka ba". Kasa ta yi da kanta tana faɗin "Wayar ce bata a hannuna, tana hannun yayana ne, bai cika bani ita ba, Shiyasa ban ɗauka ba". "Okey tom shikenan yanzu dai ina zaku je?". Ƴan kame kame suka fara yi, dan suma basu san in da zasu je ba, ganin hakan yasa ya yi tunanin ko toilet zasu je ne, dan haka sai ya wuce yana faɗin "To ku kula dai sosai, kuma ku dawo da wuri dan kunga lokacin shiga class ya yi, muna da class daku yanzu, daga nan ma class naku zan shiga". Okey suka amsa mishi da shi tare da wucewa suka nufi ta hanyar toilets ɗin, shi kuma ya wuce cikin class nasu.

A kusa da toilet suka tsaya shiru, sai kallonta Anaya take yi da mamaki, ita kuma ta rasa ta ya zata gayawa Anaya ɗin abin da take son gaya mata, suna tsaye a wajen sai ga Fadila ta nufo su, wani irin faɗuwar gaba ta ji lokacin da idanuwanta suka sauƙa a kan Fadila ɗin.

Daga ɗan nesa da su ta tsaya, da hannu ta yi musu alama a kan su zo nan, ba musu suka nufeta dan senior su ce, dole


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login