Showing 87001 words to 90000 words out of 359620 words

Chapter 30 - Triplets Book 3 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

1989

kula da soyayyansu da abin da suke so hakan suke a zahiri ba, ta ɗauka a iya Tv ne, bata san a zahiri ma hakan suke ba, in dai suna son abu, to suna bashi tsantsan kula da iya iyawarsu.

Sai bayan ya kammala kakkaɓe mata ya miƙe ne ita ma ta ɗan duka ta goge mishi wajen gwiwowinsa daya zube su kasa, ba ƙaramin daɗi ya ji ba, har da sauke wani nauyayyar ajiyar zuciya ya yi lokacin da ta fara kakkaɓe mishi.

Bayan ta Kammala ta miƙe tsaye suna fuskantar juna, ganin ta kafe shi da dara daran nan nata na gado ne yasa ya ɗan kyasta mata yatsunsa guda biyu a saman face nata, ɗan runtse idanun nata ta yi tana murmushi.

"Kyakkyawa son kowa kin wanda ya rasa". Ya faɗa yana murmushi, ita dai har yanzu bata yarda ba, idan ya ce ita kyakkywace, dan tana ganin ai daga cikin ƴan uwansa Turawa ya fito, a wawtarta da shirmenta, tana ganin daga kan turawa kyau ya kare, bata san cewa a ko'ina akwai kyawawan gaske ba, kamar dai ita ɗin, sai a tara turawa 50 ba'a a sami mai kyanta a cikinsu ba, hasken fatar kawai zasu fita da shi, kyau kam iya kyau Allah ya zubawa jinin Dr Salman da barrister Naurat, Ba fulatani da Baturiya, ya kuke tunanin haɗin zai fita, ai kunga suma madaran kyau ne a wajen.

Turo ɗan bakin nan nata kamar biro ta yi, cikin shagwaɓa ta ce "Ni Heartbeat ka dai'na ce mini kyakkyawan nan, dan nasan kawai kana faɗa ne dan ka ji daɗin bakin ka". Shima turo mata ɗan bakin nasa ya yi, tare da shagwaɓe murya "No serious nake gaya miki, you are so very gorgeous more than your expectations wlh". Shiru kawai ta yi ba dan ta yarda ba.

Sake kyasta mata yatsun sa guda biyu ya yi a fuska "Ga fa goribar ki a mota, na sanya Areef ya nemo mini tun kafin nazo, shi kuma ya sanya Prof ya nemo, a takaice dai ga shi nan na kawo miki, amma me ake yi da shi?". Jim ta ɗan yi tana maimaita sunan Areef, idan bata manta ba, idan kuma ƙwaƙwalwarta ya bata daidai sunan Areef Rimsha ta kira wadda ta ambata a matsayin masoyin ɓoye, to amma me yasa yanzu kuma ya ce ya sanya Areef ya memo mishi goriba, to shi kuma waye? Ko dai su dukka sunansu Areef Areef ne? Abin ya ɗan ɗaure mata kai.

Shi kuwa bai lura da yanayin da ta shiga na tunani ba, sai hira yake yi mata. "My heartbeat dan Allah yanzu zaka iya gaya mini sunanka?" Ta tambaya tana mai da kallonta kasa. Kai tsaye ya ce mata Aseef, maimaita sunan ta yi, sai ta ji da Aseef da Areef ai ba banbanci, hakan yana nufin ita ce bata ji sunan da Rimsha ta kira da kyau bane koyaya ne? Ta sake shiga ruɗu, sunan sunzo kusan iri ɗaya, wai me yake faruwa ne? Ta kasa gane komai.

To fa Akila ta kasa gane komai, shawara kawai ki bisu a duk yadda suka zo miki, idan ma kin gansu dukkansu biyu, duk sunan da yazo bakinki, in ma Aseef or Areef duk maka musu kawai, ai dole su amsa tun da suka rikita mini ƙwaƙwalwa, Allah sarki Baiwar Allah sai ma kin gansu su biyun da black glass, a nan ne zaki yi ainahin rikicewa, a dai Nigeria idan ba Rimsha da Imran ba, ba mai iya banbanta su.......🤣 Ita ma Rimsha Allah ne kaɗai yasan baiwar dake gareta, yasa take iya banbantasu, shi kuma Imran ya sansu tun ba'a kai haka ba.

"Heartbeat Ammie ta ce kada na jima, zan koma gida ba dan ina son rabuwa da kai ba, sai dan kada na tsallake maganar mahaifiyata, ka kula mini da kanka, zamu yi waya ko? Yanzu ai zaka dai'na ɓoye mini number ko?". Jim ya ɗan yi kafin ya wuce ya buɗe bayan motarsa ya fito mata da kwalin goribarta da kuma kawatin da ya yi mata tsaraba, already Rimsha ta jima da yin barci abinta, kwata kwata Akila bata san cewa tare yazo da Rimsha ba, shi kuma hira ta yi daɗi ya manta ya gayawa Akila ɗin tare suke da Rimshar.

"Heartbeat ya kamata ka je ka gaida Ammie fa idan ka sake zuwa". Yana jawo akwatin zuwa gabanta ya ce "Okey zan je idan na sake zuwa, yanzu dai ga kayanki, zaki iya ɗauka ne ko dai na kai miki ciki?".

Kada ku manta duk maganar da suke yi cikin harshen turanci suke yinsa, sannan karin wani haske, kada ku manta da Naurat da Dr Salman da farko a kasar Russia suke zaune, a can a ka haifi su Abba, to suma basu jin hausa sai da suka dawo Nigeria, hakan yasa su Jehan babu hausa a bakinsu sosai, dan iyayen nasu ma basu cika yin hausar ba, to suma su Akila turanci ya fi zama a bakinsu sama da Hausa, amma kuma sunfi kaunar yaren Hausa sama da turancin, shiyasa suke magana da Hausar idan suka haɗu da su Aafia, dan sun ce Hausa tafi musu ko wace yare a duniya, a takaice dai family'n Dr Salman duk gayyan ƴan yin turanci ne, na yi muku bayani ne dan kada ku ce to a ina suke jin American English da suke magana da TRIPLETS, to suma tushensu dai English ɗin turawan ne, shi suka iya, fatan kun gane?.

Da sauri ta buɗe kwalin goribar dan ta tabbatar da gaskiya, tabbas kuwa goriba ce da aduwa very fresh a ciki, gwanin ban sha'awa, ɗagowa ta yi tana kallon shi, while shima ita yake kallo.

"Me ake yi da su My heartbeat?" Ya tambaya yana zura hannu a cikin aljihun wandonsa. "Ci ake yi". Waro dara daran brawn eyes nasa ya yi yana kallon goribar, maimaita kalmar ci ya yi a filli, jinjina mishi kai ta yi tana mai tabbatar mishi da ci kuwa.

Hannu ya miƙe mata, a kan ta bashi guda ɗaya, bari ya ci ya ji, shi da abincin Nigeria mai shegen daɗi da Musharraf yake girkawa a Washington DC ma, ya kasa ci bare kuma goriba.
Da farko kin bashi ta yi, sai da ya fara zuba mata shagwaɓa kamar zai yi kuka, sannan ta ɗauko goriba ɗaya aduwa ɗaya ta miƙa mishi, karɓa ya yi tare da kaiwa bakinsa da nufin ya gutsiri goribar, dan a wanke take kuma tana cikin leda kafin a sanyata cikin kwalin, sannan a cikin fridge Areef ya sanyata, a tunaninsa fruits ne kamar irinsu Apple, shiyasa ya sanya Mark ya wanketa tas, aka zuba a leda sannan aka sanya a cikin fridge ɗin, wai dan karta ruɓe kafin Aseef ɗin yazo.

(Wayyo cikina, goruba yaga gata, har da fridge 🤣 Wayyo rashin sani yafi dare duhu🤣🥱)

A tunaninsa laushi take da shi kamar apple, sai da ya kai bakinsa sai ya ji abu kamar dutse, da sauri ya fitar yana furta subhanallah, ya tsuke ɗan bakin nan nasa, tare da haɗa geran sama da ta katsa, tsabar dariyar mugunta Akila bata san lokaci da ta yi baya tana ƙoƙarin faɗuwa ba.

Bata kai ga faɗuwa ba ya yi maza ya riƙo hannunta ɗaya, har lokacin yana tsuke da ɗan bakin nan, ya je ya gabtari dutse ta kusa cire mishi hakwara a cewarsa, gata da shegen bauri kamar me, bai yi Sa'a ba, ya sami mai bauri a maimaikon zaki, tufarwa ya fara yi yana goge bakinsa da hannunsa, har lokacin sai dariya take yi mishi.

A shagwaɓe ya ce "Heartbeat stop laughing for me now". Yadda ya yi maganar ma, dariya ya kara bata, har da sanya hannu ta dafe cikinta saboda dariyar.

Turo ɗan bakin ya yi yana ƙoƙarin saka mata kukan shagwaɓa, cikin sauri ta tsayar da dariyar tana faɗin "Am so so sorryyyyyyyyyy my heartbeat". Turo ɗan bakin ya karayi sosai, bai ce da ita komai ba, sai aikin zubar da yawu yake yi, tana son ta yi dariya, tana tsoron rigimarsa kuma, haka ta danne ta yi shiru suka yi sallama, ba dan sun so rabuwa da juna ba, sai dan kada Ammie ta yi faɗa.

Har bakin gate ya ja mata trolley tsarabar da ya yi mata, ya kai mata, ita kuma ta ɗauki kwalin goribarta,.
A bakin gate ɗin ma tsayuwa suka yi na ƴan mintoci da a kallah zasu kai 20 haka, kwata kwata basu son rabuwa da juna, umarni ya yi wa mai gadin a kan ya shigar mata da trolley da kuma kwalin goribar dukka cikin gida, hannayenta dukka biyu ya riƙo cikin nasa, abin ku da turawa, su yin hakan a wajensu ba wani abu bane, anyi sa'a ma da bai ce zai rungumeta ba, ita ma kuma bata hana shi riƙe hannayen nata da yake yi ba, ta biye mishi kawai, dan tana ganin ba zai wuce yin hakan ba, a iya hannu kawai zai tsaya.

Cike da kulawa da tsantsar kaunarta ya fara magana "My heartbeat zan yi kewarki, ji nake yi tamkar ba zan iya wannan rabuwa da zamu yi ba, ni gaskiya ba zan iya jimawa sosai ba, tun da nazo Kasarku kafin mu koma ayi mana aure kawai, ki gayawa daddynki, zanzo na ganshi, ya saka mini lokaci, amma kafin nan zan yi magana da Pleasures ɗina".

Kasa ta yi da kanta tana amsa mishi da okey, gabaɗaya ta koya mishi kunya, a wajenta ya koya, har yake jin kunyar TRIPLETS nasa. Daga haka ya saki hannayen nata tare da binta da idanu har ta shige cikin gida, nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya juya zuwa wajen motarsa.

Lokacin da ya shigo cikin motar Rimsha sai zuba barcinta take yi kamar ba gobe, ƴar murmushi ya yi tare da shafa lallausan kyakkyawar gashin kannan nasa yana furta mata kalmar sorry kasa kasa. Cikin natsuwa ya tada motar ya nufi gida, lokacin yamma ta yi sosai, almost karfe 6.

Lokacin da suka koma gida, Imran da jelly sun dawo, Areef yana zaune a saman ɗaya daga cikin kujerun shan iska dake wajen pool na gidan, Lion yana cikin bedroom nasa, haka suma Imran da jelly ɗin, suna cikin bedroom nasu, sai iya shege kala kala jelly ke zuba mishi, bawan Allah shi kuma sai biye mata yake yi, dan ba yadda ya iya da ita.

Bayan ya yi parking na motar ne ya juyo da kallonsa a kanta, a hankali ta fara motsawa kafin ta buɗe dara daran sleeping eyes nata masu ɗauke da barci, ganin su a gida yasa ta juyo gefe dan ta ga a ina take, karaf suka yi idu huɗu, cool murmushi ya sakar mata yana furta kalmar sorry, murmushi ta mai da mishi ita ma kafin ta ce "Yaya Aseef am waiting for you ne fa, ina son ka gama magana da Aunty Akila, i wan to talk to her, amma shi ne ka dawo dani gida bamu yi magana ba ko?". Ɗan kama kunnansa ya yi yana mai kara maimaita mata kalmar sorry tare da ɗaurawa da gobe zai kaita ai kada ta damu, okey ta amsa mishi da shi kafin ta buɗe kofar motar ta fito waje.

Shi me fitowa ya yi tare da nufar wajen pool ɗin dan ya hango Areef a wajen, ita kuma cikin gida ta nufa, dan ta je wajen Imran duk da cewa ba wani shiri sosai suke yi da jelly ba, jelly na kishi da ita, da farko suna zaman lafiya, daga baya da ta fahimci Imran yana bawa Rimshan kulawa sosai, duk wani motsi idan ta yi sai ya tambayeta me take so, tun daga nan jelly ɗin ta fara kishi da ita, ta ja baya da ita sosai, idan ma Rimshar na yi mata magana bata cika wani amsawa ba, sai tayi kamar bata ji ba, hakan yasa Rimshar bata cika shiga harkan ta ba, bata son ma su haɗu sai idan ya zama dole, dan ba zata iya masifar jelly ba, kuma koba komai jelly ta girmeta, ta bata a kallah shekaru 2, sa'ar jehan ce ita, shiyasa bata biye mata, kuma ita Rimsha dama bata iya faɗa ba, bata iya masifa ba, ita dai a barta da soyayya kawai, shi ta fi iyawa, shima ɗin Akila ke kara koya mata.

ASEEF

Da sauri ya karisa ya rungumi ɗan uwan nasa yana faɗin ya yi kewarsa, ture shi Areef ɗin ya yi yana faɗin "Sai yanzu ne kayi kewa na ɗin ko? Tun ɗazun baka yi ba wato? Tukun nan ma ina ka je? Ina ne mai mahimmancin da ya fi maka zama tare da mu a ranar da kazo, bayan kasan muna kawarka sosai? Koma inane ba zaka iya hakura sai gobe ba ko? To yau munyi hannun riga". Ya kai karshen maganar yana mai da kallonsa a kan wayarsa da yake latsawa.

Shiru Aseef ɗin ya ɗan yi, yana tunanin abin da zai gaya mishi da zata sanya shi dariya, yasan bai kyauta ba, yasan suna kewarsa sosai da sosai, amma haka ya tsallakesu ya tafi wajen Akila, ya kasa hakura sai gobe ya je ya ganta, kuma da ya je ya kasa barin wajen nata da wuri, da farko ya yi niyar idan ya je ba zai wuce ya yi minti 30 ba ya dawo, sai kuma gobe ya je su ga juna da kyau, amma ya je ya yi almost 2 hours a wajen nata, sam ba haka ya so ba, yanzu haka yasan Lion ma bai ji daɗi ba, dan yasan shi ne bugun zuciyarsu, kuma farincikinsu.

"Wlh Areef she is gorgeous". Ya faɗa yana murmushi tare da goya hannayensa a saman kirjinsa.

Da sauri Areef ɗin ya miƙe yana faɗin "Who is she please?". Wani kallon gefen ido ya wurga mishi dama yasan idan ya kawo wannan zance ɗan uwan nasa zai sauƙo. "Wlh she is gorgeous". Ya sake maimaita maganar ta ɗazun.

Cikin zumuɗi ya sake tambayarsa wace ce kyakkyawar, kuma a ina take, son ta yake yi ne ko ya ya. Kara faɗaɗa murmushin nasa ya yi kafin ya sake cewa "Wlh she is gorgeous".

Ɗaure fuska sosai Areef ya yi dan ya fahimci iskanci sabo Aseef yake ji da shi, zai wani tsaya yana gaya mashi she is gorgeous, to waye gorgeous ɗin an tambaye shi yana ta kara maimaita magana ɗaya, ga shi shi kuma a ƙage yake da ya ji wace ce wannan da Aseef yake yabonta haka.

"Aseef ban son iskanci fa, i said who is she ko? Tun ɗazun sai maimaita magana ɗaya kake yi, she is gorgeous, she is gorgeous, to na gaji da jin hakan". Cigaba da murmushinsa ya yi yana faɗin "Wlh she is gorgeous". Areef ya zo har wuya, a fusace ya ɗaga hannu zai kai mashi duka, kaucewa ya yi yana faɗin "Haba mana, kai fa mugu ne, na ce maka wlh she is gorgeous, my cow da na saya jiya a Washington DC mana, wadda Saif ya ce kada a kawo mashi gida, kada na kuskura na zo da ita kasarnan, to ita ce kyakkyawar".

Wani irin harzuƙa Areef ya yi, a guje ya raka shi dan ba zai kyale shi ba, shima da gudu ya wuce zuwa cikin gida, kai tsaye sai bedroom na Lion.

Yana zuwa ya faɗa saman bed yana dariya har da riƙe ciki, idan ya tuna yadda Areef ya ɗaure fuska dan ya ji shanuwa ce kyakkyawar ba abin da yake zata ba, sai ya kara tuntsurewa da dariya.

Saif yana zaune a gefen bed ɗin, jikinsa na sanye da farar jellabiya, ya ɗaure gashin kan nan nasa, fuska dai kamar kullum, a fusace, a ɗaure tamau, tamkar hadari, yau dai rubutu yake yi a cikin wani takarda mai girman gaske, mai kama da diary, sai tashin fitinannen daddaɗar kamshi perfume ɗin nan nasa yake yi, ko kallon in da Aseef ɗin yake bai yi ba.

Shi ma Areef yana shigo kan gadon ya faɗa yana faɗin, "Allah ka tashi muje ka fara frog jump dan ba zan kyaleka ba". "Ni ban iya frog jump ba, amma tun da Lion ya iya zai karɓa mini tun da ni pleasure'nsa ne, ba zai bari na sha wahala ba". Yana magana yana turo baki, jan gashinsa da karfi Areef ɗin ya yi kamar yadda Lion yake yi mishi shima.

A shagwaɓe ya sa ihu yana turo baki tare da kumbura kumatu, ko sannu Lion bai ce musu ba, ganin bai kula su ba yasa Areef hakan bata yi mishi ba, dan ya fi son yaga yana takurawa Lion ɗin sosai, yana sanya shi yin magana. Sakin Aseef ɗin ya yi, ya koma kusa da Lion ɗin dan ya saka shi magana, shi baya son ya ga ɗan uwan nasa yana zaune shiru, ya fi son yaga yana sanya shi magana ko ba yawa.

"Lion wai ya batun bed guda ukun nan ne? Ka sanya a zo a zuba mana su a nan mana, dare fa yana yi". Ko sannu bai ce mishi ba, dan wlh ba zasu zauna mishi a ɗaki ba, yanzu ma ya yake karewa da su bare kuma a ce sun dawo ɗakin, ai hawan jini zasu saka mishi, yasan ko zai mutu sai sunyi ta saka shi magana.

Shima Aseef miƙewa ya yi ya dawo ɗayan gefen ɗan uwan nasa, suka saka shi a tsakiya kamar masu shirin bashi shawara mai mahimmanci, har lokacin bai ɗago ya kallesu ba, Allah ne kaɗai yasan abin da yake tunani da kuma abin da yake cikin zuciyarsa, duk yadda suke da saboda da Lion ba zaka taɓa gane ina ya dasa ba, ba zai taɓa baka wani sign da zai nuna maka alamar in ya dosa ba, sai dai kai kayi ta hasashe dan kanka, harta su dad nasa hasashensa kawai suke yi a kansa, ɗan gara ma Triplets ɗin nasa, suna iya cankan abu daidai a kansa, yanzu haka sai Allah kaɗai yasan me yake rubutawa, ko sun duba ma, ba zasu gane kan zancen ba, tun da ba littafi ne karami ba, shiyasa basu sha wahalar duba abin da yake rubutawa ɗin ba, ga shi da shegen good handwriting kamar computer, ga bala'in iya rubutu da sauri, kafin su karanta layi ɗaya, ya sake rubuta wani layi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login