Showing 192001 words to 195000 words out of 359620 words

Chapter 65 - Triplets Book 3 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2051

daɗi sosai.

Almost 5 mins suna a haka, da yake tea ɗin akwai zafi a hankali take sha, Juyowa ya yi suna fuskantar juna tare da juyo da laptop nasa mai ɗauke da wani hoto, "Kin san wannan fuskar?" Ya tambayeta, shiru ta yi tana kallon mutumin, shi kuma ya tsareta da idanu yana kallon sleeping eyes nata, sai dai kuma nazari yake yi a kan face ɗin nata, "A'a ban san shi ba". Dama ya san da wuya ta san shi, dan ita ko Media bata damu da hawa ba, daga karatun boko sai na Islamiyya, shi ne kawai abin da take yi kullum, ko kallon film bata damu da yi sosai ba, idan kaga tana kallo to labarai ake yi a kan jaruminta GAR wato shi kenan.

Ɗago dara daran sleeping eyes nata ta yi dan ta saci kallonsa, kai tsaye sai cikin idanunsa suka sauka, dan kuwa ita yake kallo, ya rasa me yasa yake son kallon face nata, ɗan saukar da idanunta kaɗan ta yi izuwa saman lips nasa, shi kam yana mamakin yawan kallon lips nasa da take yi idan suna kallon juna, hannu ya kai gently ya karɓi cup ɗin tea ɗin hannunta tare da kaiwa ɗan bakinsa, mamaki ne ya kamata, dama zai sha ne? Ta tambayi kanta, bata taɓa tunanin hakan ba, kai gaskiya ba zata manta wannan rana ba a cikin rayuwarta. Ganin ta saki baki tana kallonsa ne yasa ya kyasta mata yatsunsa a saman fuska, ƴar firgita ta yi tare da turo mishi ɗan bakin nan nata, sai ya yi mata kamar da Aseef sarkin shagwaɓa take tare, ita ma bari ta zuba mishi nata shagwaɓar, ta manta da GAR take tare ba Aseef ɗin ba.

Shi kuma tun ranar da ya kare mata kallon a Abuja in da ƴan ta'addan nan suka biyosu, tun lokacin take burge shi sosai, komai ta yi kyau yake yi mata, yarinyar akwai shiga rai, zanensa da ya gani ta yi kuma ba ƙaramin kara burgesa ta yi ba, Allah sarki komai taurin zuciya tana son mai kyautata mata, kyautatawa ke sanya duk taurin zuciya ta yi laushi, ai dole ma ta burgeka, dan ma baka san cewa har a Daular Mutuwa ta rinƙa zana fuskarka ba, ai da sai ta burgeka fiye da hakan ma, bugu da kari ga TRIPLETS naka abin kaunarka suna bala'in kaunarta, ai dole ta burgeka.

Kurɓa ɗaya ya yi wa tea ɗin ya miƙo mata kayanta, dan ta sanya madara a ciki, shi kuma baya so, bai son madara a cewarsa tana da karni sosai, dama kamshin su kaninfari ya ɗebesa ya sha. "Yaya Saif in haɗa maka wani ne?". Shiru ya yi bai tanka ta ba, zubawa laɓɓanta idanu ya yi, yadda ta motsasu gabaɗaya dimples nata sai da suka lotsa, ba ƙaramin ɗaukar hankalinsa suka yi ba, ɗan sunkuyar da kanta kasa ta yi tana wasa da ƴan ƴatsun hannunta, zubawa kyakkyawar dark black curly hairnta idanu ya yi yana kare musu kallo, sai sheƙi yake yi yana ɗaukar hankalin mai kallo, ga wasu gashi baki siɗif kwance a saman goshinta ya yi mata kamar hula ta kifa, ga saje ɗan siriri gwanin burgewa a gefe da gefen kunnenta, kawar da kallonsa ya yi daga kan nata zuwa kan laptop nasa.

"Jeki dressing room ki kawo mini trolley da muka yi tafiya da shi". Okey ta amsa tare da miƙewa, binta da kallo ta wutsiyar idanunsa ya yi, komai nata gwanin burgewa, sai dai shi fa yaki yardanwa zuciyarsa tana burgesa, kokarin tursasa zuciyar tasa ma yake yi da ta dai'na cewa tana burgesa ɗin. TAB LALLAI KANA DA BABBAR AIKI IN DAI KUWA HAKA NE!! AI ITA ZUCIYA BA'A TURSASA MATA, DOLE ABI YADDA TAKE SO KO TA HANA MUTUN YIN BARCI!.

Kawo mishi Trolley ta yi, buɗewa ya yi tare da fito da hotunan da ya kwaso daga Abuja, ta sha ruwan mamakin ganin hotunan, tunani ma take yi a kan a ina ya samosu? Dan ita bata san da zaman hotunan a gidansu ba.

Hoton Naurat ya ɗauko tare da ɗago idanu yana kallon Rimshar, suna kama kuwa, ya sha ruwan mamakin ganin hakan, jini ba wasa ba, a wannan lokaci Aseef ya shigo ya samesu, kusa da su ya zo ya zauna yana bin hotunan da kallo, su dayawan da a kallah zasu kai 45, ba shi da lokacin ɓatawa wajen ganinsu dan haka sai ya duba na Naurat da Azharuddeen Bature da kuma na Rimshar, ya kwashi sauran ya mayar cikin akwatin.

"Yaya Saif in tafi?" Ta faɗa tana ɗago ido dan ta saci kallonsa, yana ƙoƙarin snapping ɗin hoton Naurat da ya ɗauko yanzu a wayarsa ya jinjina mata kai alamar tana iya tafiya ba tare da ya yi magana ba kuma bai ɗago ya kalleta ba.

Aseef ne ya riƙo hannunta yana faɗin "Ki tafi zuwa ina dan kinga na zo ko?" Ya kai karshen maganar tare da ɗan jawota jikinsa yana cigaba da cewa "Yanzu kin dai'na kulani sosai ko? Shikenan ai tun da ga Jehan ta zo zan koma abota da ita". Ya yi maganar a shagwaɓe. Hannu ta kai saman gashin kansa tana faɗin "Yaya Aseef da gaske ban dai'na kula ka ba, kai ne dai yanzu baka kulani". Ɗan rankwafo mata da kai sosai ya yi dan ta cigaba da watsa mishi gashin yana faɗin "No ba wani nan dan kin ji nace ga Jehan ko? Kishi kike yi ko? To na gano ki".

"Yaya Aseef wai meyasa kake son yanke gashin nan naka ne? Ka rinƙa barin shi kamar nasu yaya Areef da yaya Saif mana, wlh ba ƙaramin kyau zai yi maka ba". "No ni damuna yake yi ai, idan ya yi yawa yana takura mini". Cigaba da watsa gashin nasa ta yi, a hankali ta ɗago idanu dan ta saci kallon masoyin nata, karaf suka haɗa idanu, wani irin mugun kallo ya wurga mata wadda ya sanyata sakin gashin ba shirin, dama tana magana ne tana satar kallon shi, dan tana bala'in jin daɗin kallon face nasa, gently ya ce ta fita mishi a ɗaki tana toshe mishi kunne da magana, tana damunsa.

Miƙewa ta yi da nufin ta fita, hannunta Aseef ya riƙo yana faɗin "Jani na miƙe mu fita tare zan je wajen Areef". Ɗan satar kallon Lion ɗin ta sake yi, kansa yana duke yana aikin dake gabansa, a shagwaɓe ta ce "Yaya Aseef ba zan iya janka ba, dan kayi nauyi, wash Allah na". Dariya ya kwashe da shi yana faɗin "Raguwa kawai, bata da karfin komai". Sake turo baki ta yi zata yi magana Lion ya daka mata wata uwar tsawa wadda ya sanyata ficewa da sauri "Get out i said!!". A ɗari ta fice, shi kuma Aseef kukan shagwaɓa ya saka mishi yana faɗin "Wai Lion me haka ne? Na ce ta ɗaga ni ka zo ka koreta". Banza da shi ya yi bai tanka ba, ya cigaba da abin da yake yi kayansa.

Tana fita bedroom nata ta wuce, jikinta har wani karma yake yi, ta tsorata da jin yadda ya daka mata tsawa har haka, bai taɓa yi mata tsawa haka ba sai yau, bata taɓa jin muryarsa da sauti ta fita ba sai yau. Wanka ta yi tare da yin shirin barci ta kwanta tana tunanin zata je school gobe, murna cike fal ranta.

Shi kuma Aseef da ya gama zuba shagwaɓarsa son ransa Lion ɗin bai kula shi ba, sai ya miƙe ya nufi ɗakin Areef, bai san cewa Lion kam ransa a ɓace ma yake ba, ko me ya ɓata mishi rai cikin ɗan ƙanƙanin lokaci haka? Ko dai aikin da yake yi ne ya gano wani abin da bata yi mishi daɗi ba? Shiyasa yaki kula shagwaɓatin nasu, dan yasan idan ya buɗe baki zai iya marinsa ma. TO FA BABBAR MAGANA MARI KUMA? SHAGWAƁATIN NAMU? KAI LION BAKA SON ZAMAN LAFIYA.

ASEEF

Ga mamakinsa sai ya kalli bedroom na Areef ba kowa, toilet ya nufa dan ya leƙo ko dan uwan nasa yana ciki, nan ma babu kowa (Kai da yanzu yana ciki toilet ɗin haka zai leƙa shi kenan?🤔)

Waje ya nufo dan ya tambayi Mark, nan wani soja ya ce mishi gaskiya bai ga Mark ɗin ba, waya ya ciro ya kira number ɗan uwan nasa, tare da duba time almost karfe 11 yanzu, to ina Areef zai je a daren nan haka? Ga kuma ba wani ƙoshin lafiya ke gare shi ba?.

Bugu ɗaya ya ɗaga, a gurguje ya ce mishi, ya je wani waje ne shi da Mark amma ba zai jima ba yana nan dawowa, okey ya amsa tare da yi mishi addu'ar a dawo lafiya sannan ya wuce nasa bedroom ɗin, wanka ya yi kafin ya yi shirin yin barci, sannan ya jawo wayarsa tare da lalauɓo number heartbeat nasa dan su kwantarwa da juna hankalinki su sha soyayyarsu.

A ɓangaren su Jehan kuwa, ba yadda Ameera bata yi da ita ba akan ta zo su je karɓar abinci lokacin da ake rabon abincin, amma ina ta kafe a kan ita ba zata je ba, kuma Allah ya kiyaye ta ci wannan abincin, abin kyama, haka Ameeran ta hakura ta kyaleta tare da nufar wajen karɓar abincin, ita kuma ta wuni da yunwa, da daddare ma haka ta zauna ba abinci, ta ki yarda ta ci abincin nasu, ga yunwa kuma tana ji kamar ta mutu, amma saboda kafiya da taurin zuciyar bala'i ta hana kanta ci.

Su kuwa suka ci abincinsu tas kafin su haye gado ba sallah bare salati suka kwanta, ita kuwa sai da ta je ta yi wanka a toilet na prison ɗin, ba laifi akwai tsabta sosai toilet ɗin, matan suna wankewa, bayan ta yi wanka ta ɗauro alwala, kayan da Rimsha ta kawo mata ta sanya ɗaya daga ciki tare da tambayar Ameera ina ne gabas, nuna mata ta yi ta zumbula hijabinta ta tada sallah, da ta yi mangariba ta idar bata tashi a wajen ba har sai da ta yi issha, ta jima zaune tana askar tare da addua'o'i kala kala dan neman taimakon Ubangiji, sai misalin karfe 9 ta haye saman gadonta bayan ta naɗe daddumar ta mayar cikin jakar, kafin ma ta shigo da jakar sai da gandurobobin suka cajeta fes sannan suka bata. kwanciya ta yi cikinta na mata murɗan yunwa, har wani jiri jiri take gani.

Can misalin ƙarfe 11:20 ta sauko daga saman gadonta dan ta je ta ɗauro alwala ta zo ta yi sallar nafila, dan yunwa ya hanata barci Baiwar Allah. Toilet ta nufa, sarki ta yi tare da ɗauro alwala ta fito, dai'dai zata shiga hanyar da zai kaita ɗakinsu babu kowa a wajen, ko tsoro bata ji ba, ga shi dare ne kowa ya kule cikin ɗakinsa, kamar daga sama ta ga mutun a gabanta, da yake akwai hasken wata sosai, sai ta gane waye ne, kallon gefen ido ta yi mishi kafin ta kara ɗaure fuska sosai tana faɗin "Malam lafiya zaka wani zo ka tare mini gabana?". Yatsa ya ɗaura mata a saman lips nata yana faɗin "Not malam it's babyn baby". Kallon uku goma ta watsa mishi kafin ta ce "Bani hanya na wuce!". Matsowa kusa da ita sosai ya yi "Babu in da zaki wuce ki je, wai ke baki murmushi ne sai faɗa kullum ki ka iya?". Banza ta yi da shi bata sake tankawa ba.

Raɓawa gefensa ta yi zata wuce, cikin sauri ya sake shan gabanta, har cikin ranta tana bala'in tsoronsa, dan ganin fuskarsa ma razana ta yake yi, idan baku manta ba, TRIPLETS akwai kwarjini sosai, amma saboda dakiya irin tata ne take dannewa ta nuna kamar ma bata ji komai ba, daga ta ciki kuma, har wani dukan uku uku kirjinta yake yi na bala'in tsoronsa.

"Wai kai me na tare maka ne da zaka zo ka takura mini?". Matsowa kusa sosai ya yi da ita, har yana iya jiyo sautin numfashinta, "Tambayar me kika yi mini kike yi? To ki saurara, me yasa kika shiga cikin tunanina kika watsa mini lissafin ƙwaƙwalwata? Ya zama komai nake yi sai na kallin wannan kyakkyawa kuma fusataccen fuskar taki mai kama da unclena? Ga idanun nan naki sun saka ni a gaba da tunani, na kasa barci sai su nake tunawa, shi ne yasa nazo in ganki, ni anya ma ba zan ɗauke ki kawai mu tafi ba? Kai na fara jin hakan a raina, amma dai yanzu faɗa mini ke kina tunanin face na?". Wani muguwar harara ta watsa mishi kafin ta ce "Waye kai da zan yi tunaninka? Kuma sai na rasa waye ma zan yi tunani sai kai? Lallai baka da aiki, ni ka bani hanya na wuce hai!!". With full confidence take yin maganar.

"Komai kika yi ni burgeni kike yi, ji yadda kike tsaro magana kamar wata brigadier general na sojoji, ji ɗan bakinta a wajen ban da tsiwa babu abin da ta iya, idan kika cigaba da yi mini haka for sure sai na shanye wannan ɗan bakin, ni ki gaya mini kalamai masu daɗi bari na wuce zuwa gida hai!". Ya kai karshen maganar yana ɗaure fuska, tunani ta fara yi to ko dai ta yi mishi ihu ne? Amma kuma ai tun da ya shigo har in da take hakan ya nuna cewa gandurobobin sun san da zuwansa, so ko ta yi ihu ba amfani, wannan bala'in dame ta yi kama? Zai wani takura mata, dan iskanci wai sunansa babyn baby.

Tana can tana tunani bata ankara ba sai jinta ta yi a jikinsa ya jawota yana faɗin "Zaki gaya mini kalamai masu sanya mutun love and romance dream ne ko dai ya ya?". Duk da tsoronsa da take ji bai hanata wage baki zata yi mishi ihu dan ya sake ta ba, ta san yadda ya riƙeta ɗin nan ba zata iya kwace kanta ba, kada ku manta su rungumar mace a wajensu ba laifi bane.

Cikin sauri ya toshe mata baki yana faɗin "Masifaffiya kawai, ni ki natsu ko dai wlh na shanye bakin nan naki, maza yanzu ki ce I love you my baby tare da wasu kalamai dan na samu na tafi Aseef sai kirana yake yi, ya damu sosai dan ina waje, bai san ina wajen wadda ta takura tunanina bane". Ya kai karshen maganar tare da sakinta ya kuma zame hannunsa daga bakin nata, dan ya fara shiga wani yanayi, da gudu ta raɓa gefensa ta wuce tana mai jin haushinsa, a kan me zai wani rungumeta? Har da ce mishi mugu azzalumi ta yi, shi kuwa juyowa ya yi tare da goya hannayensa a saman faffaɗar kirjinsa yana binta da kallo har ta shiga ɗakinsu, murmushi kaɗan ya yi kafin ya ce "Sarkin faɗa, zaki dai'na ne, na rinƙa takura miki kenan, waye ya ce kiyi kama da uncle na? Ai tun da kika yi kama da shi kin shiga uku da ni, ba dai kin nuna baki so abin da nake yi miki ba? To mu zuba mu gani". Ya kai karshen maganar tare da juyawa ya nufi office ɗin shugaban gandurobobin, sallama ya yi mishi kafin ya ce da Mark da yake zaune su tafi, gaba ya yi Mark ɗin ya rufa mishi baya suka nufi motarsu.

Gida kai tsaye suka wuce, a lokacin kuma Aseef bawan Allah ya gama rarrashin AKila, dan sai kuka take yi mishi, ta sanar da shi cewa su Abbi zasu dawo gidansu da zama gobe dan shirye shiryen bikin tun da goben saura kwana shidda kenan, ya shiga tashin hankali na wuce misali, amma haka ya daure ya danne ya yi ta rarrashinta tare da bata hakuri ya kuma kara mata kwarin gwiwa a kan su kaiwa Allah kukansu, su kuma bashi zaɓi, In Sha Allah komai zai zo musu da sauki, da kyar dai ya samu ta ɗan kwantar da hankalinta har suka ɗan yi hira, bayan sun yi sallama misalin karfe 1 kenan, barci gabaɗaya ya kaurace daga idanun bawan Allah nan, ya shiga tsananin damuwa ya rasa mafita, gaskiya shi ba zai iya rabuwa da ita ba, koma yaya ne, dole ya san abin yi a kan hakan.

Ko da Areef ya dawo, bai bari ya gane halin da yake ciki ba, da ya ji motsin shi ma, barcin karya ya yi, hakan yasa Areef ɗin ya shigo ya yi mishi addu'a kawai ya juya zuwa nashi bedroom ɗin, sai da ya yi wanka ya yi shiri cikin kayan barci kafin ya kwanta zuciyarsa cike da tunanin Jehan ƴar diramarsa, da haka barci ya kwashe shi ba tare da ya leƙa Lion ba.

A ɓangaren Lion kuwa..........

❤️❤️TRIPLETS❤️❤️



*Duk wace ta karanta mini littafina ba tare da ta biyani hakkina ba Allah ya isa ban yafe ba, sai Allah ya tsayar da mu ranar da bata da abin da zata biyani face ladarta*



E51-52💋


A ɓangaren Lion kuwa, ba shi ya kwanta barci ba har sai da ya tabbatar ya kammala da case ɗin nan, sai da ya san ya gano wanene yasa a nemo mishi Rimsha, sannan ne ya tattare komai ya kashe laptop ɗin tare da miƙewa ta nufi toilet, wanka ya yi tare da fitowa ya shirya cikin kayan barcinsa masu bala'in kyau da tsada, ya feshe jikinsa da perfume nasa mai kwantar da hankalin mai shaƙa, zai wuce zuwa saman bed nasa sai ya kalli trolley da ya ce Rimsha ta ɗauko mishi ɗazun, dan haka sai ya ɗauki trolley da nufin ya mayar dressing room, bayan ya shiga dressing room ɗin sai ya lura zip ɗin trolleyn bata rufu da kyau ba, zugeta gabaɗaya ya sake yi ya buɗe, zanensa da ta yi wanda ya ɗauko daga Abuja ya buɗe yana kallo, ba karya fa ya zanu a zanen kamar ka kira shi ya amsa, shafa fusataccen fuskarsa ya yi kafin ya dawo da kallonsa kan face nata dake jikin zanen, ba karya ita ma ta zanu na wuce misali, zubawa sleeping eyes nata idanu ya yi na ƴan sakanni kafin ya mayar da shi ciki ya ja zip ɗin ya juya zuwa cikin bedroom ɗin.

Saman bed nasa ya haye tare da jawo bargo zuwa saitin cikinsa, ya kara gudun Ac kafin ya kashe wutar


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login