Showing 276001 words to 279000 words out of 359620 words

Chapter 93 - Triplets Book 3 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

1987

abin da ya damesa, dama ita ce ta san kunya, shi dai bai san wannan ba. Ganin da gaske ya cire riga ai bata san lokacin data zunduma ihu ta datse idanunta gam ba, juyowa ya yi yana kallonta, tunani yake yi wai wannan yarinyar bata da matsala a cikin ƙwaƙwalwarta kuwa?.

Ihunta ya sanya Brady shigowa cikin toilet ɗin da gudu yana wani girgiza, jikin Lion ɗin ya haye yana son jin me ake wa ihu, rungumesa ya yi suka nufi wajen baf ɗin nata dan su duba ko lafiya take ihu haka.

Wani ihun ta sake kurmawa ganin suna nufota, sam bai tsaya da tafiyar da yake yi ba har ya isa in da take ɗin, ta datse idanu gam ta kuma ɓoye tula tulanta da hannu ta dungule jiki waje guda, cikin ruwan ya zubawa idanu dan ya ga ko wani abin ne a ciki, ganin ba komai ne yasa ya dawo da kallonsa kanta, "Are you okey kuwa?". Ya faɗa a sanyaye.

Cikin kuka ta ce "Ni dan Allah yaya Saif ka tafi". Juyawa ya yi abinsa Brady na makale a kirjinsa, komawa ya yi wajen baf ɗin wankansa, tare da cewa Brady ya sauka mishi a jiki bari ya yi wanka lokacin sallah na wucewa, hannu tasa ta kunna ruwa mai sanyi dan ya cika mata baf ɗin sosai ta lume a ciki.

Bai sake bi ta kanta ba ya cire singlet nasa, ganin ainahin kyakkyawa kuma kakkarfan suran jikinsa a waje yasa bata san lokacin da ta ce "Yaya Saif dan Allah ka bari na gama wanka ka ji ko? Wlh zan iya mutu idan ka ce zaka yi wanka ina nan". Tana magana idanunta a rufe ruf, shi kam yana mamaki har yana tunanin wlh Rimsha bata da lafiya, dole a duba lafiyar ƙwaƙwalwarta, bai san cewa kunya take ji ba, ita akwai kunya ta jinin fulanin Bauchi wato Dr Salman a jikinta, ga kuma mummynta mutanen Maiduguri, ita ba irin shi ba ce, tana da kunya sosai, ba zata iya ganin wannan ɗanyen aiki ba.

Da farko kamar ba zai fasa abin da ya yi niya ba, jin tana kuka kasa kasa mai tsuma zuciyar mai sauraro ne yasa ya fasa yin wankar, yau karo na farko a rayuwarsa da ya yi niyar yin abu kuma ya fasa, yau ita ce rana ta farko da aka ce mishi ba'a son abu kuma bai aikata ba, idan baku manta ba, duk abin da ba'a so shi yake aikatawa, to yau dai Rimsha ta ce bata so kuma ya hakura bai aikata ba, tun da yake a rayuwarsa shekaru talatin cikin talatin da ɗaya bai taɓa ja baya a maganarsa ba sai yau ɗin, babbar magana...... E lallai mata sarakuna ne, mace sarauniya ce, yau dai akan mace ya canza ra'ayi, a kan mace ya fasa yin abin da ya yi niya har ma ya fara aikatawa, ina daddynsa? Ina su Areef? Yau su zo suga ikon Allah, yau da daddynsa na nan sai ya ce wannan ba Romeonsa ba ne, an canza shi ne.

Waje ya nufa, yana fitowa kuma ya bar ɗakin bakiɗaya, ita kuma yana fita ta fara wanka da saur sauri kamar ya ce mata zai dawo ne.

Bayan ta kammala ta ɗauro towel nasa ta fito waje, sauri sauri ta shafa Lotions nata tare da sanya perfume, wani ɗan ƙaramin wandon jeans ta ɗauko wanda ba zai wuce zuwa gwiwarta ba, sai ƴar riga ce mara nauyi, har lokacin bai dawo ɗakin ba, shiryawa ta yi cikin kayan nata sannan ta fara duba cikin akwaitin babu hijabi sam, kamar zata yi kuka ta ɗauko wani sabon bed sheet daga cikin drawer dake cikin ɗakin ta rufe jikinta ta yi sallah, bayan ta kammala ne ta zauna tana addu'a tare da yi wa iyayenta fatan Allah ya tsaresu a duk in da suke, haka shi ma Lion ta yi mishi addu'a sosai kafin ta miƙe tare da naɗe bed sheet ɗin ta mayar cikin drawer.

Saman sofa ta zauna tana tunanin ko ta kira number Anaya ne ta ji ya take, da wannan tunani ta ɗauko wayarta da sauri ta fara kiran number, amma ina a kashe dan kuwa a office ɗin Mr Emmanuel ta baro wayar, tamkar zata yi kuka ta mayar da wayar tata ta ajiye.

Tana ajiyewa ta fara jin saukar ruwan sama, har lokacin Lion bai dawo cikin ɗakin ba, wani irin tsallen murna ta yi tare da fitowa waje da gudu, sam ita ta manta da dressing dake jikinta, kowa yasan tsakanin Rimsha da ruwan sama akwai amana, kanta babu ɗankwali ga wandon jikinta zuwa iya gwiwa, sannan shi ma rigar tata mai ƙaramin hannu ne a iya kafaɗa, ga shi ba shi da wani kaurin kirki, kuma ba laifinta bane, irin kayan ne kawai a cikin akwatin, dan su ta ɗauko a wajen shopping da suka je da su Areef, shi kuma ya kwasa ya zuba mata kawai ba tare da ya san ma wasu irin kaya ba ne.

Cikin ruwan ta shiga har da leko da kanta ta cikin tekun tana yi wa ruwan sama magana kamar wata zararriya, kasan jirgin cikin ruwan kenan ta rinƙa leƙo kanta kamar zata tafi ta faɗa cikin tekun ta kai ta kai, ga ruwan saman yana jiƙata, sai murna take yi tana dariya kamar wata zautatciya.

Almost 10 mins tana a haka, kamar daga ta ji daddaɗar kamshin perfume nasa, a hanzarce ta juyo dan ta kalli kofar ɗakinsu, caraf suka yi 4 eyes yana tsaye a bayanta yana kallonta, ga ruwan sama shi ma yana jiƙa shi, ƴar waige waige ta fara yi, gabaɗaya sojojin nasa da ta fito ta samu a wajen basu nan, tsoron yanda ta ga fuskarsa ne ya kamata, sam babu alamar wasa a tattare da shi, ya haɗe gerar sama da ta kasa alamar yana cikin ɓacin rai.

Takowa ya yi ya nufota, baya baya ta fara yi jikinta na kerma, ta sha jinin jikinta, ya ji haushi sosai lokacin da ya fito ya sameta tana wanka a cikin ruwan ga kuma sojojinsa a tsaye, duk da cewa aikinsu kawai suke yi basu bi ta kanta ba, amma abin ya bakanta mishi rai, dole ya yi mata hukunci dan gobe kada ta kara. Sai da ta kai karshen jirgin ta gefe ne ta tsaya tana zare idanu, ta yi narai narai da idanun kamar zata yi kuka.

Yana zuwa wajen ya damko gashin kanta tare da janta zuwa wajen matakalar shiga jirgin, sauke matakalar kasa ya yi izuwa cikin ruwan, taku biyu ya yi a saman step ɗin, sai da ya je bakin ruwan, sannan ya juyar da ita tare da turata cikin ruwan, bata kai ga faɗawa ba cikin sauri ya riko hannunta kamar zata faɗa cikin tekun, wani azababben ihu ta kurma tare da kankame hannunsa da karfe, kasa kasa ya ce "Ba ruwa kike so ba? Ai sai ki shi ga". Girgiza mishi kai ta fara yi tana kuka kamar ranta zai fita, ƴar kaniya ta ga mutuwa muraranta.

Sake hannun nata ya yi dan ta faɗa cikin tekun yana faɗin ta sake shi ta faɗa ciki sai ta yi wankan da kyau, ina ai rike shi ta yi gam tana ihu kamar maƙoshinta zai ɓalle, jin ihunta yasa Mark fitowa daga cikin bedroom nasa, ganin ita da Lion ɗin ne yasa ya koma cikin sanɗa dan ma kada ogan nasa ya gan shi.

Har cikin ransa ta bashi tausayi yanda take ihu ta kuma ƙanƙame shi kamar zata shige jikin hannun nasa, ga kuma ruwan sama na sauka a saman face nata, amma idan ya tuna yanda ta fito tana wanka ga sojojinsa a wajen sai ya ji wani kululun bakin ciki a cikin zuciyarsa, a fusace ya damki gashin kanta da gaske ya yi yunkurin jefata cikin ruwan, a sukwane ta saki hannun nasa ta rungume shi, tun da ya ɗan ɗagota kaɗan, zata iya rungumar shi, shi ne ta rungume shi tana kuka.

Ƙoƙarin raba jikinsa da ita ya yi dan ya jefata cikin ruwan ko da sau ɗaya ne ta ɗanɗani azaba gobe ba zata sake ba, sai ta sha azaba zai cirota, amma ina taki sakinsa, sosai ta rike shi tana ihu tana faɗin wlh ta tuba daga yau ba zata sake shiga cikin ruwan sama ba, ita har abada ma ta tsani ruwa, sosai take kuka tamkar ranta zai fita.

Kasa jure kukan nata ya yi, ya kasa dannewa ba dan ya so ba ya haura da ita zuwa tsakiyar jirgin in da ta tsaya ɗazun take wanka, ɗage matakalar ya yi sama yana ɗan shafa bayanta alamar rarrashi.

Ta shige kirjinsa sosai tana wani irin marayar kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, ɗagota cancak ya yi zuwa saman kirjinsa, kwantar da kanta a saman kafaɗarsa ta yi tana wani irin wahalallen numfashi, ɗan juyo da face nasa ya yi suna fuskantar juna, zuba mata idanu ya yi yana kallon yanda ta lafe shiru idanu a rufe.

"Meesha". Ya ambaci sunanta, kin amsawa ta yi dan ba zata iya ba, hannu ya kai ya tattara mata gashinta da ya barbazu mata har saman face nata, sake ambatar sunan nata ya yi, har lokacin bata amsa ba, matso da face nasa daf da tata ya yi yana mai sake ambatar sunan tata, tana jinsa amma taki amsawa, dan ya bata haushi ba kaɗan ba, a cikin zuciyarta ta ce wlh ba zata dai'na shiga ruwan sama ba ya kasheta idan yana so.

Tana can tana tunani sai jin saukar hannunsa a saman kumatunta ta yi, ɗan shafawa ya yi kafin ya dawo da yatsansa guda ɗaya saman lips nata da suka yi pink sosai saboda ruwan saman dake zuwa a kansu, wani irin laushi ya ji lips ɗin nata sun kara yi saboda ruwa ya jiƙasu.

Dawo da ita ta gabansa ya yi tare da ɗaurata a saman wani kyakkyawan chair dake wajen kusa da su, a hankali ya haɗe fuskokinsu waje guda, can kasan maƙoshinsa ya fara magana a nutse "Meesha meyasa kika cika son ruwa har haka ne? Kuma ruwan ma bana pool ba, ba na toilet ki yi wanka kamar kowa ba, a'a ruwan sama mai sanyi har haka why?" Yana magana yana kallon idanunta dake rufe gam.

Turo ɗan bakin nan nata ta yi, a tsananin shagwaɓe ta fara magana "Kai yaya Saif ni ma fa ban sani ba, kawai ina son ruwan ne, kuma yana yi mini daɗin shiga, Allah ko dare idan ana ruwa shiga nake yi, daddy ma hakura ya yi ya kyaleni ina shiga". Yanda take magana tana kara turo baki.

Harshensa ya fitar tare da ɗaurawa saman lips ɗin nata ba tare da ya sake yin magana ba, hannu ta kai ta saƙalo wuyarsa idanun nata a rufe har lokacin, wannan saƙalo wuyar nasa da ta yi tamakar ta kunna shi ne, cikin natsuwa ya kama lips nata ya fara kissing ga ruwan sama na sauka a kansu, shiru ta yi tana tunano zantukan Akila tun kan lecture da ta rinƙa bawa su jelly, Umaisha da ita kanta, daɗi ta ji sosai yau dai GAR mijinta ne na sunnah, tuna hakan yasa ta fara yin wasa da hannunta a wuyar nasa, sai dai fa tabbas tana tsoronsa har yau har gobe, amma da yake ta kudurta a ranta tana son shi, ga kuma yarinta a kanta, ga rashin mummynta, ta yi aure babu uwa a kusa da zata gaya mata abin da ya dace ta yi, hakan yasa kawai take amfani da duk abin da ya zo mata a cikin ƙwaƙwalwarta, dan ma tana da kwakwalwa da basira bata manta abubuwa, duk wasu karatu da mummy ta koya mata bata manta ba, sai dai ai mummyn bata yi mata karatu a kan aure ba, so bata san komai ta wannan ɓangaren ba sai wanda Akila ta koya mata, ta ɗauka a iya soyayyar kawai ake tsayawa, shi kawai za'ayi ta zubawa kamar ba gobe.

Wani irin azababben shock ya ji sosai lokacin da ta fara shafa mishi wuyarsa, waro dara daran blue eyes nasa waje sosai ya yi a kan face nata, sai ya kallima idanunta a rufe ruf take abin, tuni ya sauketa daga saman chair ɗin ya dawo da ita saman kirjinsa tare da cigaba da kissing nata babu kama hannun yaro, gabaɗayansu jinsu suke yi tamkar ba'a duniya suke ba, bedroom nasu ya koma da ita tare da zame ɗan bakin nasa daga tatan.

Sai zubar ruwa suke yi, sauketa a tsakiyar ɗakin ya yi tare nufar trolleys ɗinsa ya fito da kayansa pajama launin white ya nufi toilet.

Ita ma kayan jikinta ta cire a hanzarce kafin ya fito ta canza zuwa wasu ƙananan kayan, sannan ta ɗauko mopper ta goge ɗakin.

Yana fitowa ya haye saman gado ya kwanta tare da jawo bargo ya kara gudun Ac, kansa ciwo yake yi mishi saboda ruwan saman da ta dakesa.

Bayan ta gama wayarta ta ɗauka ta koma saman sofa ta kwanta tare da fara kallon hotunansa dake cikin wayar tana kara jin tsantsar kaunarsa, da gudu Brady ya shigo cikin ɗakin, zai haye saman bed sai ya kalli hoton Lion a wayarta tana kallo, da gudu ya haye jikinta tare da kwace wayar tata, ihu ta kurma tare da miƙewa dan sam bata ga shigowarsa ba, shi kuwa dirowa kasa ya yi wayar tana a bakinsa ya haye saman bed ya bawa Lion wayar dan ya ga hotonsa da take kallo.

Ita kuwa wani marayar kuka ta saka dan ta tsorata ba karya, kun san idan abu ya razana mutun sosai, daga baya ya fahimci abin bai kamata ya razana ba, akwai wani irin kukan da yake saki mai tsuma zuciyar mai sauraro, to ita ma hakan ta yi. Shi kuma Lion karɓar wayar ya yi yana ganin hoton nasa da take kallo, Brady ya tona mata asiri.

Jin kukanta yasa ya ce da Brady ya je ya kira mishi ita, dirowa kasa ya yi ya nufota, hannunta ya zo yana ƙoƙarin kamawa da bakinsa ya ja ta dan ya kaita wajen Lion ɗin, ihu ta sake kurmawa tare da miƙewa tsaye ta haye saman bed ɗin da gudu, dan tasan ba in da zata je ta tsiranwa Brady sai wajen Lion ɗin dai, shi kaɗai ne mai dakatar da shi, a tunaninta cizonta ya zo yi, bata san aikoshi akayi ya kirata ba.

Tana zuwa ta haye jikinsa ta ƙanƙame shi tana kuka, rungumeta ya yi tare da kiran Brady dan ya zo ya haɗasu su zama abokan ko zai huta da wannan bala'in nasu, ya gaji da rabasu faɗa. Da gudu ya haye bed ɗin, shafa jikinsa ya fara yi kasa kasa ya furta "Meesha". Cikin kuka ta amsa mishi da na'am, "Ɗago kai ku gaisa da Brady daga yau ku zama friend". Girgiza kai ta fara yi tana kuka ta ce "Bana so, ni kam bana son shi yaya Saif, dan Allah ka ce ya tafi, wlh bana son ganin shi, wayyo daddyna, mummyna, gwaggona, Jehan, wlh bana son shi".

Shiru ya ɗan yi kafin ya ce da Brady ya kyaleta zuwa anjuma idan ta gama kukan kila ta yarda su zama abokai, dan dole ne idan yana son zaman lafiya a cikin jirgin nan to ya cirewa Rimsha tsoron karen nan, idan ba haka ba, wata rana zata iya faɗawa cikin tekun nan saboda tsoro da razana, so dole ya cire mata tsoron da su zauna lafiya.

Sauka kasa Bradyn ya yi ya nufi wajen Mark abinsa, ita kuma har lokacin kuka take yi ta kankame mijin nata gam kamar nace zan kwace mata shi, hannu ya ɗaura saman bayanta yana ɗan bubbugata alamar rarrashi...........

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥

KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔
ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne.

KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA,
INFECTION KILLER,
COLACCA,
SAI KAYAN GYARA PAGE.
KACA KACA.
YALLAGWADA.
JIGIDA.
RUWA RUWA.
BANI BANI.
WOMEN JELL BATA BATA.
DAFIN KAXA.
TANTABARA.
XABUWA.
CICCIƁI.
AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER
09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH,
BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI.


❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥


TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️

👊FATEEMA ZAHRA MUSA (PRINCESS TEEMA OR STAR LADY)✊


*Domin samun karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 0816 139 0581*


71-72


Sauka kasa Bradyn ya yi ya nufi wajen Mark abinsa, ita kuma har lokacin kuka take yi ta kankame mijin nata gam kamar nace zan kwace mata shi, hannu ya ɗaura saman bayanta yana ɗan bubbugata alamar rarrashi. Meesha, ya amsaci sunanta a hankali, cikin kuka ta amsa mishi da na'am.

"Why baki son ku zama friend da Brady?" Hannunta ɗaya ta ɗaura a saman kirjin nasa tana faɗin "Wlh mugu ne, baka ga ranar abin da ya yi wa su yaya Areef ba ne? Ni nasan ko mun zama friend watarana sai ya cijeni tun da ya jiwa yaya Areef da suka saba ma ciwo". "To amma ai baya yiwa mutun komai har sai idan ni na ce ya yi, ko Areef ɗin da ya jiwa ciwo ma ai ni nasaka shi ko?". Yana magana yana shafa bayanta da hannu ɗaya, ɗayan hannun nasa kuma ya kai saman face nata yana goge mata hawayen nata.

"Uhm ni gaskiya yaya Saif bana son shi koma dai yaya". Cigaba da share mata hawayen ya yi yana faɗin "It's okey, tashi to tun da Bradyn ya tafi". Make mishi kafaɗa ta yi ba tare da ta yi magana ba "Bazaki tashi ba?". Jinjina mishi kai ta yi alamar e bazata tashi ba. "Why ba zaki tashi ba?". Tamkar zata ce saboda jikin mijinta ne, sai kuma ta fasa ta ce


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login