Showing 57001 words to 60000 words out of 359620 words
karama, amma kuma ita kowa yake durkusawa dan girmamawa, har sai da ta zauna a saman kujerarta suma suka zazzauna a nasu kujerun.
Tana zama bai fi da minti 5 ba, mahaifiyarta ta fito, wadda ita kuma dattijuwa ce da a kalla zata iya kai 45 to 50 years haka, da kallo ɗaya zaka yi mata kasan cewa yes tabbas ita ta haifi Queen, ba komai zai sanya ka yi tunanin hakan ba face muguwar kamannin dake a kan fuskokinsu.
Tana takawa bodyguards guda biyu suna take mata baya kamar dai yadda suka rako QUEEN, har sai da ta zauna bodyguard ɗin suka juya zuwa ta bayansu suka tsaitsaya dan tabbatar da tsaro a kansu.
Cikin yarensu mahaifiyar QUEEN ta buɗe musu taron, kowa yana zauna saman tsadaddun kujerun, sun sha kwalliya na ƙin karawa, suna da yawa sosai, a kallah sojijin ko in ce dakarun QUEEN zasu iya kai su 50 haka, dukkansu babu wani yare na daban a ciki, duk yarensu ne, hakan zai tabbatar maka da ba ƙaramin shiri suka yi wa wannan bakin azzalumin gidan ba.
Cikin yaren su suka gudanar da komai, sun ɗauki tsawon lokacin suna magana, wadda a kallah zai kai awa uku zuwa biyar haka, sai tattauna suke yi, da alama suna kara yin shawara ta yadda zasu kara buɗa gidan ne, ta yadda zasu inganta shi ya kara girma fiye da tunanin mai tunani, shi ne abin da suke tattaunawa, kowa yana kawo shawararsa a kan ga yadda zasu yi.
QUEEN dai shiru bata ce ko uppan ba, mahaifiyar ta ke magana, daga karshe ma mahaifiyar tata ce ta yanke shawarar ga matsayar da zasu tafi a kan shi dan su kara faɗaɗa gidan nasu...... BASU SAN CEWA ALLAH BAI YI ALKAWARIN TALLAFAWA AZZALUMAI BA, ALLAH BAYA BARCI, YANA GANIN KOMAI DAKE FARUWA, WANNAN TSINANNEN GIDA BA ZAI CIGABA BA, YA DAI CIGABA A BAYA, SUN CI LOKACIN SU DA DAMARSU A BAYA, A YANZU IN SHA ALLAH SAI YA RUGUJE, BA ZASU SAKE YIN MASARA BA, BA ZASU SAKE KASHE KOWA BA, BA ZASU SAKE TSAFI DA KOWA BA, AZZALUMAI TSINANNU.
Duk wannan taron da suka yi babu Duna babu alamar sa, wai shin ina duna ɗin? Ina suka kai shi? To muje dai zuwa, koma me zamu ji a gaba.
Sai da dare ya tsala sosai suka tashi taron nasu, sun ci sun sha, sun ƙoshi sun yi hani'an, an cashe anyi murna sun sha sharholiya, abin ba'a cewa komai.
Sai bayan sun tashi taron mafiya yawa daga cikinsu suka koma kamanninsu na matsafan dan sun ce yafi yi musu daɗi, wasu kuma sun zauna a ainahin kamannin da suke da shi na kyawawan matasa.
QUEEN ma bata koma kamannin tsafi ba tukunnan, haka ita ma mahaifiyarta, da alama su kam basu son wannan tsiffa tasu ta matsafar, to koma yaya ne zamu ji a gaba,.
Da ainahin kamanninta Queen ta bar wajen zuwa katafaren daular yin barcinta, tana barin wajen taro ya watse, kowa ya wuce bakin aikinsa.
TO KUN JI ABIN DA YAKE FARUWA A DAULAR MUTUWA, BARI MU LEƘA WASHINGTON DC DAN JIN YA AKE CIKI NE.
WASHINGTON DC💋
Tafiya suke yi a cikin mota, Aseef da kansa yake tuƙa motar, shi kuma Musharraf yana gefensa suna hira.
"Kana ji uncle Hosain? Dama ai na gaya maka, sai na kwashi rabin kuɗin account ɗin uncle T na yi ta sadaka da su, ko Allah zai dube shi da idon rahama yasa ya musulunta, wannan kafurar zuciya ta ragu, to in gaya maka yau a account nasa na kwashi kuɗi na zuba a nawa, nan da anjuma zaka ji ya kirani akan me zan yi da uban kuɗin da na ɗeban nan, ai tun da suka sanar da ni sirrin bankin su, wlh ko ba su so sai sunyi sadaka, musamman ma uncle T da Uncle Herry, basu taɓa kyauta wa wani ba, sai pastor, shi kawai suke bawa kuɗin su".
Dariya Musharraf ya yi sosai kafin ya tsagaita ya ce "Wlh Aseef ka zama lashe money, ina ga nan gaba kaɗan sai sun canza gabaɗaya tsarin bankinsu saboda kai, duk sai ka talauta mutane ko? To kai ma dai Allah ya sanya ka gama karatun nan lafiya ka fara aiki ka tara naka kuɗin, sai ka fita daga layin lashe moneys".
Yana ƙoƙarin juya kan motar ya sauƙa daga kan titin da suke izuwa titin kasa ya ce "Uncle ba zaka gane bane, basu yin sadaka ne shiyasa nake yi masu, kuma ai kuɗin su ba zai kare ba tun da kullun wasu ne suke shigowa, duk cikin mu fa, daga Saif sai Areef ne kawai suke yin sadaka, shi ma daddy da kake ganin nan, wlh pastor kawai yake bawa kuɗinsa, bayan pastor kuma sai ni da nake cin kuɗin, ko suna so ko ba su so, kuma dole su bani na ci". Kara faɗaɗa murmushinsa ya yi "My Aseef ka cigaba da yi musu addu'a, In Sha Allah everything will be okey nan ba da jimawa ba".
Ɗan ɗaure fuska kaɗan ya yi. "Uncle Hossain wlh wannan bakar zuciya da kake gani, ni nasan daga wajen wannan Roshan ɗin suka gado shi, ko ban ji tarihin kakan nan namuba, nasan shi ne mai shegen bakar zuciya tamkar shaiɗanun farko, kai uncle Hossain baka ji sunansa bane? Wai fa Roshan, daga ji kasan anyi tsiya ba na wasa ba, ni ban ma son jin tarihinsa, ban son sanin komai, dan nasan bakin mugune da wani idanunsa a wajen, ya ma yi Sa'a Allah yasa idanunsa irin na Lion blue color, dan hakan yasa nake raga mashi, ba da ban haka ba, da sai na ce Allah ya kara mishi azaba tun da bai musulta ba ya mutu". Yana magana yana ɗaure fuska.
(Kai jama'a to me kakansu kuma ya yi mishi da ya kare mishi tanaji har haka?🤔 Allah ya shirya Aseef Wlh, wai da ya ce Allah ya kara mishi azaba🤣 to ai ka riga da ka faɗa sai dai kar a kara🤣)
"ASEEF abin da nake so da kai kana jina?" Gyaɗa mishi kai ya yi ba tare da ya yi magana ba. "Yauwa, musulmi ba zai taɓa zama cikakken musulmi har ya shiga aljanna ba sai yana kiyaye harshensa, Annabi da kansa ya yi wa duk wandan ya kiyaye abu biyu zuwa uku alkawarin shiga aljanna babu fashi, na farko, ka kiyaye abun dake tsakanin hakwaranka na sama da na kasa, wato harshe kenan, idan har kana iya kiyaye harshenka, to ana sa ran ka samu babban rabo, abu na biyu ka kiyaye abun dake tsakanin kafafunka, wato al'auranka, muddin ka kiyaye gabanka baka aikata zina ba, muna yi maka kyakkyawar zaton da samun Rahmar Ubangiji, abu na uku gani, ka kiyaye idanunka wajen zuwa lallai sai ka leƙa abin da ya zama haramun, misali kallon fina finan banza da tsiraicin wani, mutane biyu kawai Allah ya yafewa da su kalli tsiraicin juna, mata da miji, bayansu duk wanda zai zo a baya tofa akwai matsala, uwa tana iya yi wa ƴaƴanta wanka suna yara ta kalli tsiraicin su kafin sukai munzalin haramta ita ma a gareta, idan ba ya zama dole ba, Aseef ina son ka san wani abu guda wadda duk wanda ya sanya hakan a ransa dole ya tuba ya koma ga Allah, ina son ka saurareni da kyau, Ubangiji bai bawa kowa daman sanin aikinsa ya karɓu ko bai karɓu ba, ka kwana kana sallah, kana azumi, zakka, hajji, ba abin da baka yi a manya manyan ayyuka Alkhari, sadaka, amma kada ka kuskura ka saki jikin cewa wannan aikin naka tana karɓuwa, domin me? Saboda baka sani ba wata kila akwai in da ka tabka babban kuskuren da ya shafe dukkan ayyukan alkharin nan naka, idan bawa yana da hankali bai kamata ya saki jiki da duniya ba, saboda baka da tabbacin abin da aka turoka a duniyan ka yi shi mai kyau kuma an karɓa, Aseef muddin aikinka bai karɓuba ka shiga uku ka lalace, bari kaji Annabi da kansa akwai lokacin da Allah ya sauƙar mishi da aya ya daka mishi warning akan yana shiga abin da bai kamata ya shiga ba, a lokacin sai da annabi ya shiga tsananin tashin hankali na abin da ya faru, to shi kaga ɗan gata ne, Allah yana son shi da Rahma har hakan ta faru, zaka iya zuwa kana tapka babban kuskure da zai goge duk wani aikinka ba tare da ka sani ba, Sahabban annabi ban cire maka ko ɗaya ba, harta waƴan da suka san makomansu ɗin, waƴan da suka san aljanna zasu tafi irinsu Sayyidina Abubakar, Omar, Usman, Ali, ɗalhatu binu Ubaidullahi, abu ubidu binu zarrai da sauransu, su kansu idan aka kira lahira jikinsu kerma yake yi, kuka suke yi suna kara neman gafara da sassauci wajen ubangiji, wannan kawai bai isa yasa bawa ya kasance cikin tashin hankali a kullun ba? Manyan Sahabban da suka san yes aljanna zasu tafi, suna kuka idan suka ji annabi ya fara magana a kan lahira, to mu da ko rabin su a aikin Alkhari bamu yi ba, sai kaga bawa ya samu waje ya kwanta ana kiran sallah yana zaune tamkar wani kurma, ya ilahi ya lillahi, wlh bai kamata bawa ya zauna cikin kwanciyar hankali har ma ya yi tunanin cutar da wani ba, mutuwa gaskiya ce, tashin alkiyama gaskiya ce, yau ina kakaninmu? Wasu ina iyayenmu? Ina kannenmu? Wasu ina yayyunmu? Idan ka juya kaga matsalar dake a kewaye da kai ma kawan ya isa ya sanya ka kara jin tsoron Allah ka girgiza, ya isa ya sanya ka kara komawa ga Allah dan samun rabauta, kafin Annbi ya rasu, da Sahabbai suka tambaye shi ya Rasulullah yaushe za'ayi tashin alkiyama, ya ce da su sanin gaibu sai lillahi, Allah ne kaɗai ya barwa kansa sani, amma akwai misali da Ubangiji ya yi mini, zan yi muku shi dan ku kotanta, mikar da yatsun hannunsa gabaɗaya ya yi, kun dai san yatsun hannu ɗaya ta fi ɗaya, sai ya ɗauki babba ta tsakiya da kuma manuniyar yatsa, ya mikar da su sosai, ya ce da sahabbansa abin da ta regewa duniya ta tashi bai wuce ɗan wannan fifikon dake tsakanin yatsarsa ta tsakiya da kuma manuniya ba, ku duba ɗan ratan dake tsakanin yatsunnan, a lokacin annabi yace abin da ta ragewa duniya kenan, bare kuma yanzu da ya yi shekara 1445 da yin wannan maganar, to ku lissafa abin da ya saura kenan, a lokacin da Sahabbai suka ji wannan magana, hankalinsu ya yi mummunar tashi, masu kuka suna yi, annabi ya yi ƙoƙarin kwantar musu da hankali ta hanyar nunawa su sayyidina Abubakar cewa su fa ƴan aljanna ne, amma ina sunki yin shiru, suka ce idan ba sun ga kansu a cikin aljanna ba, sun karɓi takardansu da hannun dama, baza su taɓa daina kuka suna neman gafara da sassauci wajen ubangiji ba, ɗan adam ako da yaushe mai kuskure ne, tana iya yiwuwa su je su aikata wani abin da zai shefe musu aikin alkharinsu na baya, to su da suke Sahabbai ma kenan, ina ga mu da ba ɗaya kanwar biyu? Sai kaga mutun sai wani jiji da kai yake yi yana faɗi kamar ba nan da ɗan lokaci kaɗan cikin kasa zan koma ba, jama'a duk wasu masifa da suka zo a cikin Al Qur'ani mai girma da hadisan Manzon (S.A.W) da suke nuna almomin tashin alkiyama ne, to wlh sai bayyana suke yi, me ba'ayi yanzu? An maida zina abin kwalliya! An mai da luwaɗi gasa! An mai da lesbian sana'a! Saɓon Allah ya zama har tinƙawo da shi ake yi! Uba ya nemi ƴa ya kwanta da ita, yaya ya yi wa kanwarsa ciki, makwabci ya yi wa ƴar makwabcinsa ciki, mata su kashe mazansu a kan shirmen banza, ba'a ɗauki ran a bakin komai ba, matan aure suna zina, Maza na cin amanar matansu, namiji ya auri yarinya kuma ya zagayo ya yi wa kanwarta ciki, wasu ma tamkar a garin dabbobi suke, ka auri yarinya sannan ka kwanta da uwarta, ya ilahi ya lillahi, me ba'ayi?! Cutar mutane an mai da shi yanzu tamkar wani ilimi, har koyan danfara ake yi, karya na gudu kana bin shi a guje sai ka kamo shi, dole dole sai anyi karya, zalunci da hasada na gudu kuna binsu ku kamo su, dole dole sai an zalunci jama'a, kashe mutane kamar kiyashi ya zama contract! Gasa ta gina manya manyan gine gine a duniya ta bayyana, wadda annabi da bakinsa ya faɗa tana daga cikin manya manyan almomi na tashin alkiyama, masifu kala kala sai bayyana suke yi, shi kansa wannan faɗa ta yahudawa da musulmai ya zo mana a cikin Al Qur'ani mai girma? Kafin tashin Alkiyama sai anyi shi, duk wasu alamomi sun bayyana, jama'a muji tsoron Allah, mu tsaya tsayin daka dan gina lahirarmu, bai kamata hankalinmu ya kwanta mu saki jiki da duniya ba, har sai ranar da muka karɓi takardanmu da hannun dama, mu lizimci yin istigifari dan idan munyi laifi ma Allah ya yafe mana, a kowace rana ku rinƙa tuna mutuwa fiye da yadda kake tunanin abinci, dan mutuwa tafi abincin saurin zuwa, idan kwana ya kare ko tafiya kake zaka tsallaka babbar titi sai an zare ranka, second ɗaya mala'ika azarailu baya karawa bawa wajen zare rai, ko a ina yake kuwa, shi kuma abinci kana iya jira har sai an kammala, to dan haka mu lura, mu tuba mu koma ga Allah, zunubanmu ya yi yawa, Allah gafurun rahim ne, amma ku sani a yanzu ne kuke da damar tuba kafin lokaci ya kure, a lahira ko kabari ba'a tuba, iya duniya Allah yake karɓar tuba".... Yana magana yana hawaye bibbiyu, duk dakiyar zuciya irin na daddyn Rimsha sai da ya yi hawaye ba kaɗan ba, haka zalika shi ma Aseef, paka motar ya yi a gefen titi tun lokacin da daddyn Rimsha ya fara maganar, ya kifa kansa da jikin steering motar, hawaye yake yi sosai, wani na bin wani, duk sai ya ji duniyar ma ta ishe shi, ya ji jikinsa gabaɗaya ya mutu, me bawa zai nema a duniyar nan da ta wuce lahirarsa? Me zai tsayar da bawa yin wasu shirme a duniyar nan? Ya ilahi ya lillahi, gaskiya duk wanda ya zo duniya, ya mutu ya tafi wuta to tabbas shi ya so, shi yaga dama, kuma ya zama babban mai asara number ɗaya a duniya, dan Allah ya bamu lokaci da kuma dama, Allah Arrahaman ne, mai rahma a kan bayinsa, tabbas wannan hakane, Allah ne kaɗai zaka yi babban laifi ya kuma baka damar tuba ka koma gare shi, ka sake yi ya sake baka damar tuba, duk dan ka samu rahmarsa, ba wanda zai yi wa bawa haka sai mahaliccinsa, wani ma nan a unguwarku idan yana jin haushinka, haka kawai sai ya ɗauki gaba da kai ba gaira ba dalili, idan kayi kuskure yi mashi laifi kaɗan, to ka shiga uku, ba zai taɓa yafe maka ba, sai ya ɗau fansa, kunga ya tabbata idan ka mutu ka shiga wuta kai kaso.
Sosai suke kuka duk cikinsu babu mai iya rarrashin wani, sun jima a haka kafin Musharraf ya ɗauki robar ruwa ya fita ya wanke fuskarsa ya dawo.
Yana dawowa ya hau rarrashin Aseef, da kyar ya samu ya yi shiru, sai shessheƙar kuka tare da ajiyar zuciya yake sauƙewa, idanuwansa sunyi jawur kamar wuta, abinku da farar fata, har wani ja kumatunsa ya yi, tamkar wadda a ka wawwankawa marika.
Sun ɗauki almost 1 hour a wajen kafin su dawo daidai, kunna motar Aseef ya yi suka nufi in da zasu je, wato white house.
Yau duk fara'a irin ta Aseef, da yake yi wa sojoji da ƴan'sandan white house dariya da kyauta, yau dai ba wanda ya ga hakwaransa a waje, kyauta dai kamar yadda ya saba ya zube masu kuɗaɗe ba kaɗan ba, duk sai mamaki suke yi, sun sha jinin jikinsu ganin yanayin da suka jima basu ganshi a ciki ba, wato yanayi na ɗaure fuska, tun lokacin ciwon shi da yake ɗaure fuska, babu damar tambayarsa ko lafiya, haka suka haƙura suka fara raba kuɗin da ya basu.
Yau bai shiga fadar shugaban kasa ba, kai tsaye cikin gida ya nufa abinsa, bai jira a yi mishi iso ba, ya wuce izuwa babbar palo ya yi zamansa saman wata danƙareriyar sofa, masu bala'in kyau da ɗaukar idanu, sofar ta haɗu iya haɗuwa, a gefensa Musharraf ya zauna suka yi shiru, yau ba hira da dariya, dama shi Aseef akwai wata guntuwar zazzaɓi a jikinsa, sai abin ta haɗu mishi, kansa ya fara yi mishi ciwo, haka ya daure ya kwanta a saman sofar tare da tada kai da cinyar Musharraf, kyakkyawar gashin kansa Musharraf ɗin ya fara shafa mishi yana yi addua'o'i tare da tofa shi, sau da dama haka suke yi, duk lokacin da Aseef zai tada kai da cinyarsa, tofa sai ya yi ta tofa mishi addua'o'i sosai da sosai, kuma ga shi Aseef ɗin bashi da wani wajen kwanciya biyun cinyar Musharraf ɗin.
Suna a haka wata kyakkyawar budurwa ta sauƙo daga sama, kyakkyawa ce sosai, farace tas, daga gani kuma tana da alaƙa da su, dan kuwa kamannin His excellency ne a kan face nata, da alama jikarsa ce, kamar yadda suma su Lion ɗin suke jikokinsa, ba karya tana da kyau kam, idanunta farare tas tamkar madara, sai dai ƴar siriri ya ce sosai, kunsan zubin turawa dama, sirarane sosai, to haka ita ma take, tana sanye da wasu shegun kananan kaya, kun dai san yadda dressing nasu yake, wando da riga ne da suka kamata, a kafarta kuwa, wasu shegun high heel ne masu matukar kyau da tsada, da ganinta zata yi jiji da kai ba kaɗan ba, hannunta na riƙe da wata danƙareriyar wayarta, sai wani ɗan siririn jaka wadda ba zai wuci ɗaukar iya ATM card ba.
Ta gabansu ta zo zata wuce ba tare da ta ɗago ta kalli su waye a wajen ba, kallonta na a kan wayarta, da alama dai wannan izza da jiji da kan nasu na gado ne, a jininsu yake, dan kuwa ita ma