Showing 120001 words to 123000 words out of 359620 words

Chapter 41 - Triplets Book 3 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

1964

nake so, ni dole a aura mini ke".

"Ni Heartbeat serious nake gaya miki, ki dai'na wasa". Ya yi maganar tamkar zai fashe mata da kuka, sake kwaikwayarsa ta yi, daga muryar har maganar da ya yi, "Ni Heartbeat serious nake gaya miki, ki dai'na wasa". "Uhm uhm kai heartbeat ki dai'na kwaikwayona nace miki ko?" Sake kwaikwayon na shi ta yi, kuka ya saka mata tare da katse kiran.

Cool murmushi ta saki tana faɗin "Ɗan rigima kawai, nima ai na iya". Ta kai karshen maganar tare da fara kiran layin nasa tun da ya buɗe mata, wayar ta yi ringing har ta katse bai ɗaga ba, tana katsewa sai ga shi ya biyo kiran nata, "Ɗan rigima" ta faɗa kafin ta ɗauki kiran.

"My heartbeat i want to see your face now". Shi ne abin da ya faɗa bayan ta ɗaga kiran, "Video call?" Ta tambaye shi, yes ya bata amsa, "Okey in kira ka ne ko zaka kira ni?" "No bari ni na kira ki". Okey ta amsa mishi da shi, juya kiran ya yi zuwa video call, cikin zumuɗi ta ɗaga, dan ita ma tana mugun son ta kalli face nasa, bata gajiya sam sam ga ganinsa, ya haɗu ne ta ko'ina, irin mijin da take burin aura kenan su kashe juna amma da soyayya da kauna tare da shagwaɓa.

Kayatatcen murmushi suka sakarwa junansu lokacin da suka sauke idanu a kan juna, cikin sanyin murya ta ce "My shagwaɓati ka yi kyau sosai, kasarmu ta karɓe ka".

"Ba dole Kasarku ta karɓe ni ba, tun da kina cikin kasar, yanzu dai ɗan yi kasa da bargon nan bari naga face naki da kyau". Kara jawo bargon sama ta yi har zuwa wajen idanunta, cikin sigar zolaya da shagwaɓa ta ce "Ni kunyarka nake ji". Rumtse idanu ya yi, kasa kasa ya furta "Wato ba zaki dai'na yi mini irin wannan wasa bako? For sure watarana sai kin saka ni zuwa gidanku 2 na dare".

Ɗan zato idanu waje ta yi "To ai da gaske kunyarka nake ji my shagwaɓati". Turo mata ɗan bakin nan nasa ya yi "Uhm uhm wai fisabillilahi ba zaki bari ba? So kike yi ki sanya ni kuka ko?" Ɗan gangaro da bargon zuwa kirjinta ta yi, tana murmushi tare da faɗin "Sarkin rigimana to ai gani nan ka ganni, yanzu dai ba shikenan ba?". Shiru ya yi bai yi magana ba, ya zuba mata idanuwansa babu ko kyaftawa, "Lafiya kake kallona haka?". Gera ɗaya ya ɗaga mata tare da kashe mata ido ɗaya, ɗan zaro idanu ta yi tana kallonsa, "Wai me ya faru ne shagwaɓati? Kayi magana mana". Nisawa ya yi tare da shagwaɓe fuska kamar zai yi kuka, bai ce mata komai ba.

"Shagwaɓati wai ba zaka yi magana ba?". Ji yake yi tamkar ya jawota ya rungume, shi kaɗan yasan me yake ji a cikin zuciyarsa, ta yi matukar tafiya da imaninsa, ya tsareta da waƴan nan idanuwan nasa, a hankali ya lumshe su ya sake buɗewa a kan face ɗin nata, ba ƙaramin rikita ta ya yi ba yadda ya lumshe idanun, sai ya kara kyau over, tsantsar madarar kyau ne ya bayyana, ga zara zaran eyelashes nasa wadda suke tamkar ya kara dana kanti saboda tsawo, sak irin na Lion, kuma irin na Josephine.

"Heartbeat ban san me zance miki bane, shiyasa na yi shiru, idan nace zan yi magana zan iya yin kuka, kina rikitani sosai my one and only". Kara kudundunewa ta yi a cikin bargon, murya kasa kasa kamar wani nayi mata laɓe ta ce "Heartbeat kai ne kake rikita ni dayawa wlh, ban san ya zan kwatanta maka yanayin kyanka ba, ni na rasa ma me zan ce". Sake lumshe idanunsa ya yi zuciyarsa na kara macewa a kanta, ya kara narke mata sosai.

"My shagwaɓati idan kana lumshe idanun nan naka kana kara birkita mini ƙwaƙwalwa fa". A tsananin shagwaɓe ta yi maganar, nisawa ya yi, cikin sanyin murya ya fara magana "Rufe idanunki bari na baki wani surprise". Okey ta amsa mishi tare da datse idanun nata, waro idanunsa ya yi a hankali, zuba mata idanun ya yi sosai yana kare mata kallo, ga shi kuma high neck t-shirt ne a jikinta, rigar ta kamata sosai, kana iya ganin shape nata sosai, kanta babu ɗankwali, ta saki gashin nan nata da ya sha gyara sai kyalli yake yi, ga kamshin shampoo ta sai tashi yake yi, ya ɗauki ƴan sakanni yana kallon face nata kafin a hankali ya dawo da kallonsa izuwa kirjinta daidai in da ta tsaida bargon nata, ɗan daidai tsakiyar breast nata, zuba musu idanu ya yi na second goma, daga bisani ya mai da kallonsa izuwa saman kanta.

Ya shagala da kallonta zazzakar muryarta ta katse mishi tunani da cewa "My shagwaɓati in buɗe idanun nawa ne?" Dogon numfashi ya ja tare da sauƙewa a hankali "Ban gama kare miki kallo ba ai, ɗan ja mini bargon nan ƙasa mana". Cikin sauri ta waro idanunta a cikin nasa, kashe mata shanyayyum idanun nan nasa ɗaya ya yi, idanun sun zama tamkar wadda ya sha wani abin ko kuma yake jin barci, turo baki ta yi tare da saka mishi kukan shagwaɓa akan ita ba zata yarda ba, dan me zai kare mata kallo, rarrashinta ya fara yi yana ce mata sorry, sai da ta ɗan wahalar da shi kafin ta yarda ta yi shirun.

"My rigimati ba, ki cigaba da bani wahala, baby's ɗina zasu rama mini, ƴar rigima kawai". "Kai kuma ɗan shagwaɓa kawai, nima ai baby's ɗin nawa zasu rama mini, Allah yasa first born na ya fika shagwaɓa, ya rama mini abin da kake yi mini". Kafeta ya yi da ido bai yi magana ba, "Zan so ganin ranar da baby's ɗina zasu takura maka, su rama mini duk shagwaɓar da kake yi mini".

"Ni da ke waye yafi wani Shagwaɓa?". Yadda ya yi maganar ba zaka taɓa cewa shi ya yi taba, ba zaka yi tunanin ya motsa lallausan lips nasa ba, a hankali ya fitar da words ɗin, ya yi maganar kuma yana yi mata signal da gera ɗaya, abin gwanin ban sha'awa.

"Kai mana, ai ka fini iya shagwaɓa, kai karshe ne a wannan fannin". Girgiza kai kawai ya yi, shi kaɗai yasan me yake ji yadda yake kwancen nan, tana sane sarai da halin da ya shiga, tun da ta buɗe idanunta lokacin da ya ce ta rufe, tun a sannan ta fahimci ya shiga wani yanayi, shiyasa ma yake kasa yin magana, idan ta yi mishi magana, sai dai ya bita da ido, sai ta yi sau biyu yake amsa ɗaya, ga shi ya kasa kawar da kallonsa daga kanta, a nata shirmen kuma, da ƙaramin tunaninta, idan ta barshi yana kallonta suka cigaba da yin video call ɗin, zai sami natsuwa, dan haka take kallo a film, sai ta yi tunanin hakan ne a gaske, bata san cewa kara mishi raɗaɗi take yi ba, musamman ma idan ta yi magana, har cikin ransa yake ji, idan ta motsa laɓɓanta har wani shock yake ji, wani irin sanyi ne ke kara ratsa shi tana karuwa mishi har cikin tsakiyar kansa, bawan Allah yana cikin yanayi, ga ruwan sama.

A hankali ya lumshe dara daran idanunsa, tare da kara jawo pillow ya kara rungumewa a jirjinsa sosai, zuba mishi idanu ta yi tana kare mishi kallo daga face nasa har zuwa kyakkyawar lallausan wuyarsa, ita kanta lips nasa kyau suke yi mata ba karya, mai do da kallonta izuwa kyakkyawar brown sajen dake kwance a gefen kumatunsa ta yi, ya gyara sajen ta zama ƴar siriya, gwanin burgewa, gashin gerarsa sun kusa haɗewa saboda cika, gasu gazar gazar a kwance luf, da yake ba da hannunsa ya riƙe wayar ba, ya jinginata ne da jikin pillow dake kusa da shi, hakan ne ya basu damar ganin juna da kyau da kyau.

A hankali sautin saukar numfashinsa irin na mai barci ya fara ratsa dodan kunnenta, alamar ya yi barci, ajiyar zuciya ta sauke yau ta sami damar kare mishi kallo tsab, ji take yi tamkar ta sanya hannu ta shafi kyakkyawar fuskar nan tasa ko zata ji sauƙi a ranta, kunsan idan mutun ya lumshe idanu to gashin idanunsa suna kara bayyana sosai, to shi ma dai haka nasa suka yi, sun bayyana sosai, ba ƙaramin tafiya da imaninta suka yi ba. Ta ɗauki almost 30 mins tana kallon shi kafin ita ma barci ɓarawo ya yi awon gaba da ita, sun bar wayoyin nasu a kunne........ SOYAYYA RUWAN ZUMA.

After some days.

GIDAN LION💋

Misalin karfe biyu na dare, duniya gabaɗaya ya yi shiru, mafiya yawan bayin Allah suna barci, kalilan masu kwaɗayin ni'imar Allah, kuma masu wayo suna a kan dadduma suna sallah or karatun Alqur'ani mai girma, cikinsu kuma har da Lion, Aseef, Areef, da kuma Imran, ita kuma Rimsha yau wani irin azababben barci mai matukar nauyin gaske ne ya ɗauketa, tun da ta yi sallar issha ta ɓige da yin wannan barci, da kyar ma ta iya dawowa saman gado, dan tun daga kan dadduma ta fara barcin, ko abinci bata ci ba, Areef ya zo tambayarta me zata ci yau, sai ya samu tana barci, bawan Allah bai tashe ta ba, ya kyale.

Daidai lokacin da agogo ta buga karfe 2 daidai, a wani irin haukace ta farka daga barci tana ambatar sunan Jehan!! Jehan!! tamkar ba lafiya ba, sai zufa take haɗawa tamkar wadda ta yi tsere da dawakai masu uban gudu a tsakiyar rana, salati ta fara yi tare da karanta

يَنْفُثُ عَن يَسَارِهِ (ثَلاثاً).
يَسْتَعِيْذُ بِااللهِ مِنَ الشَّيْطَانِ، وَ مِنْ شَرِّ مَا رَأَى (ثَلاثَ مَرَّاتٍ).
لَا يُحَدِّثُ بِهَا أحَداً.
يتحَوَّلُ عَنْ جَنْبِهِ الَّذِي كَانَ عَلَيْهِ


Addu'a ce mai matuƙar muhimmanci idan mutun ya yi mummunar mafarki, Allah zai kareka daga faɗawa irin wannan mafarki tare da kawo maka saukin a cikin zuciyarka, mummunar mafarki ta yi a kan ƴar uwar tata, gani ta yi gata can cikin ukuba da wahala ta rayuwa, hawaye ta fara yi domin kewarta ya dawo mata, komai ya dawo mata sabo, nan take kuma tsoro ya dira mata a ranta, dan yadda ta kalli fuskar Jehan a cikin mafarkin nan ba ƙaramin ɗaga mata hankali tare da tsoratata ya yi ba.

Almost 10 mins tana hawaye, can kome ta tuna, sai ta diro kasa da sauri tare da ɗaukar wayarta ta kunna wutar wayar, toilet ta nufa, a gurguje ta ɗauro alwala, dadduma ta fitar tare da shinfiɗawa, ta zura zumbulelen hijabi har kasa a saman kayan barcin nata, cikin natsuwa ta tada sallah, tana yi tana kuka tana rokon Allah da ya kare mata ƴar uwarta a duk in da take, a sujjadarta ta karshe ta zubawa Allah kirari tare da yi wa jenan addu'a ba kaɗan ba, tana yi tana ruwan hawaye tamkar an buɗe famfo, sai da ta ji zuciyarta ya ɗan sami natsuwa kafin ta rufe da salatin annabi ta ɗago daga sujjadar tare da fara yin tahiya.

Idan kana son addu'ar ka ta karɓu cikin ƙanƙanin lokaci, annabi (S.A.W) ya ce kayi ta cikin sujjada, idan ka kafa goshi a kasa, Allah ya fi saurin karɓarta, dan zata tafi ne tare da sallarka, sannan yana da kyau kafin kayi addu'a ka fara zubawa Allah kirari, Allah kai ne Arrahaman mai rahma a kan bayi, kai ne algaffaru mai gafartawa bayin ka, ya Ubangiji na babu wanda ya isa ya bani abin da baka bani ba, babu kuma wanda ya isa ya hana abin da ka bani, babu abin da ya isa ya motsa a dukka faɗin sammai da ƙassai ba tare da izininka ba ya Allah, ina tawassuli da sunanka tsarkaka, bani da tsumi bani da dabara, na miƙa wuyata a gare ka ina rokon da ka biya mini buƙata ta kaza, irin wannan makamancin kirarin, ya kamata ku rinƙa yi wa Ubangiji, akwai wasu da dama, na muku misali ne da iya wannan, dan dayawa basu san yadda ake yi wa Ubangiji kirari ba, ita kanta rokar biyan buƙata dayawa basu san ya akeyi ba, wasu kawai su zo ne su faɗi bukatarsu tamkar a gaban ƴaƴansu suke, ko iyayenka idan kana son abu a wajensu sai ka rusunar da kai bare Ubangijin talikai, mai kowa mai komai, sannan ana son kafin ka fara addu'a ka fara buɗeta da salatin annabi, wasu malamai sun ce a tsakiyar addu'ar ma ana karanta salatin annabi, amma dai a karshe ma da salatin annabi ake rufewa, matikar kayi irin wannan babu jimawa zaka samu biyan buƙata, Allah kasa mu cikin wanda Annabi zai ceta a ranar gobe kiyama, Allah ka kara mana ilimi mai albarka mai amfani.

Tun da ta farka bata sake mayar da barci ba har sai da ta yi sallar asuba, da yake ta kwana tana sallah, sai barci ya cika mata idanu, tana yin sallar asuba ta ɓige da barci a saman dadduma, fuskarta gabaɗaya jaga jaga da kusasshen hawaye, idanuwanta har sun ɗan kumbura saboda kuka.

AREEF

Misalin karfe 6:30 fitowa ya yi daga ɗakinsa zuwa bedroom ɗin Aseef, da sallama ɗauke a bakinsa ya shigo cikin ɗakin, can naɗe saman bed nasa ya hango shi, ya wani kankame pillow a kirjinsa, ga ɗaya kuma ya tashi kansa da ita, ɗaya a tsakanin kafafunsa, sai zuba barci yake yi cikin kwanciyar hankali, da alama daren jiya ya kwana yana waya bai yi barci ba, sai yanzu yake biyan barcin.

A hankali ya kariso cikin ɗakin izuwa bakin gadon, zubawa ɗan uwan nasa idanu sosai ya yi yana kallon shi yadda yake barci furkarsa ɗauke da annuri, sai kyalli yake yi yana wani kwailin, kamar mai mafarkin wani abin. Ya ɗan jima a haka yana tunanin ya tashe shi ne ko kada ya tashe shi.

Can wani abin ya faɗo mishi cikin tunaninsa a in da ya saki cool murmushi kafin ya haye saman gadon tare da sanya hannu a hankali ya zame pillow dake a tsakanin kafafun shi, sai guntse dariyar mugunta yake yi domin yasan yau za su kwashi ƴan kallo ba kaɗan ba, idan ya yi mishi abin da yake da niyar yin nan.

Yana ƙoƙarin kai pillow saman fuskar ɗan uwan nasa ya toshe mishi numfashi, cak ya riƙe pillow da hannu ɗaya idanunsa a rufe kamar mai barci. Guntun tsaki ya ja kafin ya ce "Dama in the first place dana shigo na yi tunanin baka yi barci ba, oya stand up". Wani kayatatcen murmushi ya saki ba tare da ya buɗe ido ba ya fara magana tamkar mai sambatun magagin barci "Heartbeat i really love you so much, kada ki manta ki rufe kofa kada Areef ɗan gulma ya leƙo, kin san...." Bai barshi ya karisa ba, ya kai mashi duka yana faɗin "Waye kuma ɗan gulma?".

Wani irin miƙewa ya yi ya rungume shi yana faɗin "Kai mana, muna tsaka da soyayya da heartbeat zaka tashe ni ko? To yanzu ba gulmar ka zo yi bane?" Hararar wasa ya watsa mishi tare da sauƙowa daga gadon ya nufi waje, "Ka shirya by 7 zamu kai sister school, zan je naga school ɗin, bari nayi magana da Prof ina zuwa". Okey ya amsa mishi da shi tare da komawa ya kwanta yana murmushi kamar wadda aka cewa ga amaryar ka can ana kawo maka ita.

A ɓangaren Lion kuwa, yau ya zuba kwalliya ta musamman, da alama akwai in da zai je, ya yi wani azababben kyau na wuce misali, kananan kaya ne a jikin nasa kamar kullum, sai dai waƴan nan daga ganinsu kasan sun amsa sunansu kaya ba karya, masu shegen tsada ne, yanzu yana yawan barin sarkarsa a waje samar sigarsa mai mai kon a ta ciki, da alama hakan ta fi yi mishi daɗi, Brady na goye a bayansa, sun fito tsakiyar palo sama kenan Brady ya yi tsalle ya diro kasa yana daka haushi, zuba mishi idanu Lion ɗin ya yi yana kare mishi kallo, cikin harshen turanci ya yi mishi magana a kan su tafi komai na gidan nan kamshin perfume nasa yake yi, saboda ya gane me Brady ɗin yake yi wa haushi, kamshin perfume nasa ya ji yo a ɗakin Rimsha na wancan rigar sanyi, to shi ne yake haushin shi ba zai tafi ba sai ya fito da rigar, tamkar rigar sane ɗan kaniya.

Da kyar ya yarda ya biyo Lion ɗin suka sauƙa kasa, babu kowa a palon kasan sai Mark dake kitchen, jin kamshin perfume ɗin ogan nasa ta karu a palon ne yasa ya gane ogan nasa ya fito, ɗauko kayan abincin da ya gama haɗawa ya yi izuwa palo, a saman dinning table ya shirya su kafin ya juyo izuwa wajen ogan nasa, shiru suka yi dukkansu biyu, dama already kun sani, dukkansu sarakan zama shiru ne, zasu iya shekara su biyun nan ba tare da sun ce da junansu uppan ba, kuma suna tare waje guda, hakan suke kamar wasu kurame, ga Mark kullum cikin bakar glass yana rufe sexy Hazel eyes nasa, dan idanun nasa zaka tara turawa 1000 baka sami biyu masu irin idon ba, idanun yana nan tamkar green eyes ne, sai dai bai kai green eyes shiga color ba, combination ne na green da brown, sune suka bada Hazel, yana da bala'in kyau sosai, ga shi shima akwa mangan idanu ga karfin gani, kullum yana cikin black glass abinsa, sai ka rantse baya kallon komai, saboda sau ɗaya yake kallon abu baya kuma mai da kallonsa sai in an sami kuskure, to shi ogansa ma baya kallon abin, Lion zaku jima tare da shi ba tare da ya ɗago ya ganka ba, daga motsin mugun yake iya zayyana shi a ransa, idan kuna tare yau da gobe, yanayin yadda mutun yake motsi a kusa da shi, ta hakan ya gane Rimsha tana da bala'in rawar kai, bata da natsuwa.

Sun jima tsaye a haka kafin Lion ya yi gaba ba tare da ya ce da Mark ɗin uppan ba, rufa mishi baya Mark ɗin ya yi, motarsa ya je ya shiga, sai tsalle Brady yake yi, da alama daɗi yake ji zasu je yawo, gidan gaba Mark ya shiga tare da yi wa motar key suka bar gidan, tana tsaye a jikin window ɗakinta tana


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login