Showing 246001 words to 249000 words out of 359620 words
ma ya miƙe yana faɗin "Jiba idanunta a wajen kamar na Aseef, sai ka ce ball, amma suna mugun yi mini kyau fa". Ko sannu bata ce mishi ba ta nufi waje dan ta je wajen daddynta, rufa mata baya ya yi yana faɗin "Wow baby ko ta baya ma ke haɗaɗɗiya ce, gaskiya kin iya tafiya fa, see beautiful shape!" Tsayawa ta yi ta fasa tafiyar haushi kamar ta shake mishi wuya ta yi ta kifa mishi maruka a wannan jajir ɗin kumatun nasa ko zata huce, ashe dama tafiyarta yake kallo dan iskanci, wannan mutumin ɗan iska ne gaskiya, ta faɗa a cikin zuciyarta tana wani zabga mishi harara.
Shi kuwa murmushi ya sakar mata yana jin wani irin tsantsar nishaɗi idan yana tsokanar ta, da gangan ya ce mata hakan dan kawai yaga tana hararsa tana juya dara daran fararen idanun nan nata, ba ƙaramin tafiya da imaninsa suke yi ba idan tana hararsa, so yana ɗaya daga cikin dalilan da yasa yake yawan tsokanarta, da hararar.
"Mu je mana". Ya faɗa yana karewa kirjinta kallo, ga shi babu hijabi a jikinta, daga ita sai doguwar rigar abaya, sai dai ita tana sanya breziya, yanzu ma ta yi amfani da guda ɗaya cikin wanda Akila ta taɓa ɗaukawa Rimsha lokacin da Imran ya kaisu shopping, Rimsha bata taɓa bi ta kansu ba, dan bata sakawa, da vest kawai take amfani, amma ita tana sanyawa dan breast nata sun ciko sosai, dama kun san tana da halittarsu sosai ita ma, so shiyasa take sakawa, hakan kuma ba ƙaramin kyau ya kara mata ba, ya kara bayyanar mata da shape nata, bata sanya ɗankwali ba, dan idan baku manta ba Jehan bata son ɗankwali sai idan ya zama dole, idan baku manta ba kullum faɗarta da mummy kenan a kan ɗankwali, so yanzu ma ta saki kyakkywar gashin nata ba ta ɗaure ba.
Ganin yana karewa kirjinta kallo ne yasa bata da zaɓi dole ta cigaba da tafiya dan ta gujewa kallon da yake yi mata ɗin, cool murmushi ya saki yana mai jin tsantsar kaunarta har cikin ransa, yana son ƴar diramar nan tasa so na wuce misali.
Rufa mata baya ya yi har zuwa bedroom ɗin daddy. Daddy da Rimsha suna saman bed suna hira, yana zaune Rimsha ta tada kai da cikyarsa. Da sauri ta haye gadon tana faɗin Rimsha ta tashi mata bari ta kwanta idan ya so ita kuma sai ta kwanta ta kafofin daddyn, yau ga karfin hali.
Juyowa Rimshar ta yi ta rungumi daddyn tana faɗi wlh bazata tashi ba, ai ko addinin musulunci ya yi hani da ka sami mutun a waje yana zaune ka ce ya tashi ka zauna, koda kuwa ka girme shi to bai kamata ka tashe shi ba, yin hakan zalinci ne, addinin musulunci kuma baya goyon bayan zalunci, ya yi hani da shi, kuma ya tsawatar da babbar murya, dan haka ita gaskiya bazata tashi ba dan magana ake ta addini bata girma ba.
A kule ta ce "To sarkin wa'azi, ban nemi ki yi mini wa'azi a nan ba, dan haka ni ki tashi ko kuma wlh naja kafarki ya yasar dake a kasa, dama can ai ni nake kwanciya a cinyar daddy da Gwaggo, ke kuma mummy wata rana ki haɗa da Gwaggo, dan haka wlh ki tashi tun wuri". Shi dai daddy sai murmushi yake yi abinsa, wato har yanzu da suka girma ma ba zasu dai'na wannan faɗar ba, abu tun suna yara, kamar wasu tom and Jerry. Kai uba mai daɗi kenan, Allah ka sakawa iyayenmu da gidan aljanna.
Hayewa saman gadon shi ma ya yi yana faɗin "Our Queen maza tashi ki bani waje dan dukkanku yanzu ba kafarku ba ne, nawa ne ni kaɗai". Ba musu ta miƙe ta bashi waje, kwanciya ya yi abinsa, shafa lallausan gashinsa daddyn ya fara yi suka fara zuba hira, miƙewa Rimshar ta yi ta nufi waje abinta dan ta leƙo masoyinta tana kewarsa.
Ita kuma Jehan haushi kamar ta kifawa Areef ɗin mari, haka ta matso ta kwantar da kanta a kafaɗar daddyn tana turo baki, daddy dai yana ganin ikon Allah wajen ƴan diramar nan tasa, wato Areef da Jehan sai Allah, yanzu da gangan ya ce zai kwanta a cinyar daddyn dan yaga ta ce zata kwanta, saboda neman tsokana ya wani haye ya kwanta, sam ya manta magana zasu yi da Lion da Aseef, ya zo yana ta neman tsokanar Jehan.
A ɓangaren su Aseef kuwa, lokacin da suka shiga bedroom ɗin na Lion, saman bed ya haye tare da sakin Akilar yana mai cigaba da yi mata sannu, saman bedside drawer ta zauna tana ɓoye fuska dan bata son ganinsa ba riga, wani irin kunyarsa take ji, sosai ya lura da hakan, sai ya ce ta zo.
Ba musu ta haye saman bed ɗin, jawota saman kirjin nasa ya yi yana faɗin "Kunyar kallon mijinki a haka kike ji?". Gyaɗa mishi kai ta yi tana sake ɓoye fuska, "Au kin manta cewa kafin muyi aure kin yi alkawarin zaki yi mini wanka kuma tare zamu rinƙa yi dake kullum ne?". Dukan wasa ta kai mishi a kirjin nasa, cikin tsantsar shagwaɓa ta fara magana kasa kasa kamar mai raɗa.
"To ai ba yanzu ba, sai gaba". Kai tsaye ya ce mata "Sai nayi disvirgin naki?". Zaro idanu ta yi tana mamakin rashin kunya irin tasu, wai su kwata kwata basu san kunya ba, magana sam bata yi musu nauyin faɗa?
(Ni kuwa nace ai Aseef ma mai sauki ne yana da ɗan sauran nasa kunya da kika koya mishi, rashin kunya ai sai Lion da Areef)
"Baki bani amsa ba?". Ya yi maganar yana ɗago haɓarta dan su fiskancin juna, shiru ta yi tare da rufe idanunta dan har ga Allah bata da amsar da zata bashi, ya sanya ma ta kara jin kunyarsa sosai.
"In dai sai nayi disvirgin naki ne zaki fara yi mini soyayyar da kika faɗa to ni gaskiya dole yau zan yi hakan". Ya yi maganar a shagwaɓe sosai, wasa ta fara yi da yatsunta a saman kirjin nasa tana turo baki tare da faɗin "Ni dai Heartbeat ka dai'na faɗin haka dan Allah, Allah bana so". "Bakin so me?" Ya tambaya yana ɗan kama hannun nata ya mayar saman breast nasa.
"Maganar da kake yi mana, bana so ka bari". "Baki son nayi disvirgin naki?". Gyaɗa mishi kai ta yi alamar e, "Why to?" Babu komai ta bashi amsa, "Serious?" Ya yi maganar cikin wata iriyar murya dake nuna tsantar tsokana ta masoya, jinjina mishi kai ta yi almar e da gaske take yi.
"Tom shikenan naji ba zan yi yau ba, amma gaba zanyi idan na sami lafiya, dan gaskiya ba zan iya kyaleki ba, ina son in karɓi virgin ɗina sosai". Yatsa ta ɗaura a saman lips nasa alamar ya yi shiru, ta yi hakan tana gyara kwanciyar a jikin nasa da kyau, ɗan bakin nasa ya buɗe tare da capko yatsar nata ya fara ɗan ciza a hankali yana shafa bayanta har zuwa kumatunta in da ta sha marin daddy.
"Am so sorry my rigimati". Ya faɗa tare da cire yatsar tata daga bakin nasa, nisawa ta yi kafin ta ce mishi babu komai ai daddynsa tamkar daddynta yake, so yana da damar da zai iya dukanta kamar yanda zai dake shi shi ma, dan haka kada ya damu ita ta yafewa daddyn tun lokacin.
Rungumeta ya yi sosai yana mai jin tsantar farinciki tare da jin wani azababben kaunarta yana kara ratsa shi, ita ma rungume shi ta yi tana murmushi.
"Can I kiss you?". Ya yi mata maganar cikin raɗa a kunne, ɗan ɗagowa ta yi suna kallon juna, zubawa lips nasa idanu ta yi, sun kara ja sosai alamar ya ɗan cizasu saboda daɗin rungumarsa da ta yi. Gera ɗaya ya ɗaga mata yana faɗin "Do you love it?" Ya yi maganar yana nuna mata lips ɗin nasa.
Kai ta gyaɗa mishi alamar e tana son lips ɗin nasa, dan ba karya suna da kyau sosai, akwai abubuwa da ya kasace a jikin TRIPLETS iri ɗaya ne sak babu banbanci, ciki har da kafarsu, lips nasu da sauransu, dama kunsan dole a sami hakan dan mahaifa ɗaya ba wasa ba, hakan yasa duk wanda ya gansu sai ya ji lips nasu ya burge shi, dan fa ba karya akwai kyau, shiyasa Rimsha take yawan kallon na Lion, sai dai ita fa Rimsha na Lion ɗin ne kawai yake burgeta, bata taɓa ɗaga ido ta kalli na TRIPLETS nasa ba, ita dai nasa kawai. SO KENAN, NA KOWA BAYA BURGETA SAI NASA, YANZU KUMA SUN ZAMA MALLAKINTA BA TARE DA TA SANI BA.
Yana ƙoƙarin fara kissing nata Lion ya yi musu knocking na kofar, sauka gadon ta yi ta je ta buɗe mishi, ko kallon in da take bai yi ba ya shige cikin ɗakin, bayansa ta biyo ta zo ta zauna a saman bedside drawer.
"Kai my rigimati, ni kizo ki kwanta a jikina kamar ɗazun hai". Ya yi maganar a shagwaɓe, ɗan satar kallon Lion dake ƙoƙarin fito da A box daga mazauninsa ta yi, kafin ta grigiza mishi kai alamar a'a bazata zo ba tun da Lion yana nan.
Kukan shagwaɓa ya saka mata yana faɗin "Wai ke meyasa kike yin wannan abin ne? Ni fa bana son wannan kunyar". Shiru ta yi bata yi magana ba. A gefensa Lion ɗin ya zauna tare da fara duba shi bai ce musu ko sannu ba, dan shi bashi ne a gabansa ba, lafiyar ɗan uwan nasa ne a gabansa, shi ne abin da ya fi damunsa.
Haka suka kasance har ya kammala duba shi tare da yi mishi alluran barci sannan ya miƙe ya fice gabaɗaya daga bedroom ɗin ya koma garden dan ya kwanta ya huta. Yana fita ita ma ta haye saman bed ɗin kusa da mijin nata ta kwanta, dan tana tsoron ta koma bedroom nasu daddy ya sake dawowa.
💋AFTER SOME HOURS❤️
Da misalin karfe 8 na dare, taci wankanta ta tsara kwalliya kamar me, ta yi kyau sosai, sai tashin kamshi take yi, yau barci take ji sosai saboda ta gaji, ga shi gobe akwai school zasu yi Exams na karshe, jibi partynsu, dan haka sai ta sanya kayan barcinta riga da wando launin white color masu masifan kyau, akan idan ta dawo daga wajen Lion kawai ta kwanta abinta ba sai ta tsaya shiri ba, kayan barcin jikinsu yana da tsantsi sosai ga laushi, hijabi har zuwa gwiwarta ta ɗauko ta sanya a jikin nata tare da kara fesa perfume nata sannan ta fito ta nufi kitchen dan ta ɗauki abincin Lion ta kai mishi, ita kuma Jehan tana wajen daddy suna hira, Aseef ya koma bedroom nasa shi da Heartbeat, Areef yana bedroom ɗin daddynsa suna hira.
Bakinta ɗauke da sallama ta shigo cikin ɗakin, shiru babu kowa, a in da ta saba zama ta je ta zauna tare da ajiye abincin tana jiran zuwansa, kamar wanda aka mintsina sai ta ce bari ta buɗe kular yau taga me Mark ya girka musu, dan yanzu abincin Lion ɗin take ci, bata zuwa kitchen ɗiban wani, na kular tasa dai idan ya gama ci shi take ci.
A hankali ta buɗe kular tana leƙawa kamar daga sama taga mutun ya faɗo cikin ɗakin babu ko excuse, ba ƙaramin razana ta yi ba, hakan yasa ta saki marfin kular tare da mikewa kamar wata mara gaskiya.
Ɗaure fuska sosai daddyn ya yi yana kare mata kallo kafin ya daka mata tsawar me ya kawota bedroom ɗin ɗansa? Wacece ita kuma me zata yi mishi a cikin abinci data buɗe? Me tazo yi?.
Baya baya ta farayi dan ta gudu ta fita, daddyn ma ya fara binta tare da kara tambayarta me take yi a cikin ɗakin ɗansa, ta tsorata sosai da ganin shi, musamman da ya zare mata dara daran blue eyes nan nasa irin na Lion ɗin, ga shi kuma an samu akasi ta buɗe kular abincin ne ya shigo, shiyasa ya ce sam wani abin zata yi wa ɗansa, dama bakaƙen fata mugaye ne a cewarsa.
Hawaye ta farayi tana ja da baya bata ankaraba sai ji ta yi ta bugi mutun, ta kasa juyawa ta ga wanene dan saboda bala'in tsoron daddyn, sai dai har cikin ranta ta ji cewa Lion ne, dan daga kamshin perfume nasa ta gane, duk da cewa yanzu su Areef duk da perfume ɗin nasa suke amfani, amma ya fi kama jikinsa shi, idan ya doso waje dole sai kamshin ta bule ko'ina lungu da saƙo.
Tsawa daddyn ya daka mata wanda ya sanyata watsawa a guje da nufin ta fita ɗakin, cikin sauri Lion ɗin ya rikota ta kugunta tare da jawota jikinsa dan ya rabata faɗa da daddyn kada abin da ya faru da Akila na marinta da daddyn ya yi ya faru da ita itama, so is better ya takawa abin birki ya kuma gayawa daddyn cewa shi ya sakata duk wani abin da take yi a cikin bedroom ɗin nasa, dan haka babu ruwansa da ita.
Narai narai ta yi da idanu ta kasa juyowa ta kalli Lion ɗin, ɗan rankwafo da kansa ya yi daidai saitin kunnenta kasa kasa ya ce ta je ta zuba mishi abinci dan yana jin yunwa, ya yi maganar tare da sakinta yana kallon daddyn.
"Dad let's go and eat". Ya faɗa tare da nufar saman bed ya ajiye laptop nasa da duk wasu kayayyaki na mummynsa da ya je ya yi bincike a kansu a garden.
"Romeo ni ba zanci abincin nan ba, kuma kai ma ba zakaci ba, dan ban yarda da abincin ba". Shiru ya yi bai tanka ba, bayan ya gama ajiye kayan ne ya wuce zuwa in da ya saba zama ya zauna, a nitse ya ce "Dad why kake son problem ne? This girl she is our sister, since before now muna tare, and then karamar yarinya ce sosai why are you thinking or expecting cewa zata cutar damu? Me wannan innocent face ɗin ta sani? Gaskiya kana son wahalar da kanka dad, you know cewa tun da ka ganta a bedroom na ai nasan ba zata cutar da mu ɗin bane, so please stop all this thing that you are doing, kazo kawai muci abinci".
Jinjina mishi kai daddyn ya yi alamar ya gamsu da maganarsa yana faɗin "Okey tom i agreed, amma ni zanje naci abinci dasu Herry a saman dinning table kamar yadda muka saba ci". Kai kawai ya gyaɗa mishi ba tare da ya yi magana ba, juyawa ya yi ya fice daga cikin ɗakin ya nufi wajen uncle Herry.
Zuba mishi abincin ta yi ta tura mishi, spoon ya ɗauko ya faraci a nitse ba tare da ya kalli in da take ba, sai dai fa yana tsananin son kallon cikin idanunta, ya yi kewarsu sosai yau, ita ma sai satar kallon shi take yi, tana kewar fine face nasa, sam bai ɗago ya ganta ba har ya kammala cin abincin ya mike ya bar waje ya nufi waje gabaɗaya.
Kayan abincin ta kwashe zuwa waje, kitchen ta mayar da su, ko sannu bata ce da Mark ba, dan ta lura yanzu sam baya son ta rinƙa yi mishi magana, hakan yasa ko sannu bata ce mishi ba ta wuce ta fito abinta.
Bedroom nasu ta yi niyar komawa, tamkar wadda aka cewa ta juya ya kalli cikin bedroom nasa, kai tsaye saman bed nasa ta kallah, kayan da ya ajiye ta gani, sanin cewa baya cikin ɗakin ne yasa bata ji tsoro ba ta shige ciki dan ta kalli menene ya ajiye a wajen.
Gefen bed nasa ta zauna, ko'ina na cikin ɗakin fes yana tashin kamshi, kayan mummyn nasa ta fara dubawa, wannan takarda da yake son sanin wace yarece a rubuce a jiki ta ɗauka tare da hoton Josephine ɗin tana kallo, da yake kowa da yadda yake kallon mutun, sai ita kuma ta kalli Josephine ɗin sak Lion ɗin tamkar an tsaga kara, banbancin kawai kalar kwayar idanu ne, amma ta yi mata muguwar kama da shi, hakan yasa ta fahinci cewa lallai wannan mummynsa ne ko kuma sisters, dan kunga a lokacin da Josephine ɗin ta yi hoton tana budurwa, shiyasa Rimshar ta kirata da sistersa, ta yi kyau sosai a hoton ba karya.
Zubawa sarkar wuyarta idanu ta yi tana kallon shi da mamaki, tunani ta fara yi a kan a ina ta taɓa kallon sarkar nan bayan wuyar TRIPLETS, tabbas sai da ta ganshi yanzu a wuyar Josephine ɗin ne ma ta tuna wlh ta taɓa kallon irin sarkar, to amma a ina? Ta mance dan lokaci bata yi wayo haka ba, matso da hoton sosai ta yi kusa da ita, a nan ne ta fahinci da sarkar wuyar Josephine ɗin da ta wuyar Lion yana da banbanci kaɗan, na wuyar Josephine ɗin akwai rubutu a tsakiyar sannan ya fi nasu girma, tun da Lion yake bai taɓa kurewa hoton kallo har yasan da rubutu a jikin sarkar ba, sai ita yau dan tsabar fitina.
Zubawa rubutun idanu ta yi tana son karanta menene a rubuce a wajen, shiru ta yi tana tariyo sarkar Lion dan shi ma ɗin nasan kamar akwai rubutu wlh, sam dukkansu ba wanda ya taɓa lura da rubutun dake jikin sarkar, dan ba karya rubutun kanane sosai, idan ba ka mayar da hankali sosai ba bazaka gani ba, tabbas tana da bukatar sake kallon sarkar Lion dan taga me aka rubuta, ga dai na Josephine rubutun ba da English bane, da yare ne, hakan na nufin kenan Josephine tana da yare? Dan kuwa wannan sarka dai ita da kanta ta sanya aka buka mata, ba kamar sauran sarkoki yake ba, kuma da alama tabbas akwai dalilin da ya sanya ta sa aka buga mata wannan sarka, alamomi da dama sun nuna hakan, na farko rubutun dake jikin sarkar, na biyu da yare aka yi rubutun, na uku meyasa ta cire tambarin heart na sarka ɗaya ta rike a wajenta, sai ta bawa TRIPLETS babu shi? Meyasa zata yi hakan? Hakan na nufin tabbas akwai sakon da take son isar musu ne wanda ta san da bakinta ba zai isa garesu ba, tasan ba zasu taɓa sauraranta ba idan