Showing 294001 words to 297000 words out of 359620 words
ba zaki yi abu ba kuma ki ce zaki yi, ni sa'anki ne? Ko don ina yawan wasa dake ne yasa kike ƙoƙarin gaya mini duk wani abin da ya zo bakinki?". Shiru ta ɗan yi kafin ta ce "Kayi hakuri". Ta yi maganar sam bata kalli in da yake ba, sa kai ya yi ya wuce zuwa cikin bedroom ɗin abinsa, shi ma bai sake bi ta kanta ba, idan baku manta ba babu abin da TRIPLETS suka tsana a duniya irin raini, basu son raini ko kaɗan, kullum yana wasa da ita baya damuwa da duk abin da take gaya mishi saboda yasan bada gaske take yi ba, cikin wasa take yi ita ma kamar yanda yake yi, amma yau kuma da gaske ta gaya mishi maganar shiyasa abin ya bashi haushi, ta raina shi kenan da har zai ce mata ga abin da baya so kuma ta ce sai ta yi, yanda ta yi magana da gasken nan yasan sai ta yin ne dan yasan wace ce ita, shiyasa ya gaya mata abin da ya gaya mata shi ma ya kuma ɓata rai.
Chains ɗin ya ɗauko ya zo ya wuceta tana tsaye ya fice zuwa bedroom ɗin Lion ba tare da ya kalli in da take ba, ajiyesu ya je ya yi sannan ya koma bedroom ɗin Aseef ya ɗauko na Akilar ya zo ya haɗa, ita kuma Akila har lokacin tana sume, Aseef kuma ya samu barci bawan Allah, daddyn Rimsha ya kwantar mishi da kansa a saman sofa tare da gyara mishi kwanciyar sannan ya wuce nasa bedroom ɗin.
Areef bayan ya kai chain ɗin ya dawo cikin bedroom ɗin a in da ya haɗe hannunsa da kyau ya ɗauki Aseef ɗin cak daga saman sofa zuwa saman bed kusa da matarsa, dan yafi sofar tsawo, wuyarsa zai yi ciwo a yanayin kwanciyar da ya yi, shi ne yasa ya ɗauke shi, su daddy duk sun koma bedroom nasu dan a bar Akila ta huta kada su dameta da hayaniya, daddyn ne ma bayan ya gama dubata ya ce a kyaleta ta huta, shi ne dalilin da yasa suka fice bakiɗayansu.
Bedroom ɗin daddyn Rimsha ya nufa dan su ɗan yi hira bayan ya gama gyarawa Aseef da Akilar kwanciya, har da ja musu bargo ya yi dan ya lura kamar sanyi suke ji.
Bakinsa ɗauke da sallama ya shiga cikin ɗakin, kwance ya isko Jehan saman cinyar daddy cikin yaren Hausa tana gayawa daddyn abin da ta yi wa Areef ɗin yau, ta ce daddy ya bashi hakuri dan ya ɓata rai sosai, duk yanda yake bala'in kaunarta amma yau ya shareta dan ya nuna mata kuskurenta na raini da take neman kawowa a tsakaninsu, sam ita ma bata ji daɗin abin da ta yi ɗin ba, shi ne take gayawa daddy har idanunta sun ciko da kwallah. Saman bed ɗin ya hau yana faɗin "Uncle sannu da ƙoƙari". Murmushin ya yi kafin ya ce "Areef Jehan zata je gidan yayana Deen ta gaishe su, please ka kai min ita ka ji?".
Kallonta ya yi kafin ya ce "Uncle this your daughter ƴar rigima ce, yanzu kuma me zata je yi a gidan mutane? Salon ta je tana ɗaure musu fuska tare da basu command tamkar wata Captain na sojoji ko? Serious uncle ina ji a jikina duk yanda aka yi wannan yarinyar jininmu ce, kana ganinta tamkar ita take bin Lion a haihuwa, wannan da namiji ne banbancinta da Lion kaɗan ne, to kaga mu Lion abin a jininmu yake, gadon faɗar muka yi daga wajen daddynmu, ita kuma ya akayi ta zama irinmu, bata magana, ga bala'in tsare gida, ga faɗa da bala'in zuciya, iya bada command, son girma, kai komai ma".
Murmushi daddy ya yi yana faɗin "Ita ma gado wajen kakanta ta yi ai, da kuma ƴan uwan mummynmu su uncle Trump, uncle Alex iyayen bala'i". "To shikenan Uncle ta shirya mu tafi ko?". Ya yi maganar yana kallonta.
Cikin harshen Hausa daddy ya ce mata "Tashi kije ki shirya sai ki zo ku tafi gidan Abbi ki gaishe su, idan kuna tafiya a hanya sai ki bashi hakuri, yana da saukin kai kuma zai hakura, ki daina yi mishi gardama Jehan, Areef ba zai taɓa cutar dake ba, kuma yana sonki da gaske, wlh babu wata mace da ta isa ta tsaya tana yi mishi abin da kike yi mishi yana hakura, so ki daina kin ji? Ki rinƙa girmama shi, ki dai'na idan ya yi magana ki ce zaki bashi amsa ko da ma cikin wasa ne, kin ji ko? Ai ya fiki shekaru nesa ba kusa ba, so ki rinƙa girmama babba".
Jinjina kai ta yi tana ɗan turo baki ta ce to daddy tare da miƙewa dan ta je ta shirya. Tana fita daddy ya dubi Areef ɗin ya fara magana cikin natsuwa "Nasan kana hakuri da halin Jehan, amma ka kara hakuri ka ji?". Murmushi ya yi yana faɗin "Uncle ni fa bata taɓa yi mini wani abin da ba dai'dai ba, ni halin nata ma mugun burgeni yake yi, na san cewa a haka take, shiyasa nake ƙoƙarin canzata izuwa yanda kowa yake rayuwa, ta dai'na takura kanta tana ɗaure fuska, murmushi rahmace kuma baiwa ce, ta dai'na gudun mutane tana zama ita kaɗai a ɗaki, shi ne yasa nake son na koya mata wasa da dariya, so ni bana jin komai a kan abin da yake a tsakaninmu, ni nabi ta hakan, idan ina so zan iya canza hanya, dan haka kada ka damu our daddy".
Ajiyar zuciya ya sauke yana kwarara musu ruwan albarka, Amin Amin ya rinƙa amsawa da shi, a haka ta dawo ta samesu, wayar daddy ta karɓa kafin ta ce su je, okey ya amsa mata tare da miƙewa ya fito suna yi wa daddy sallama, sai kallonta yake yi da waƴan nan dara daran ash eyes ɗin nasa, ba karya ta yi kyau sosai na wuce misali, doguwar riga dai ta sanya kamar ɗazun, sai dai na yanzu ash color ne tare da yafa mayafin a kanta.
Gidan gaba na motar ta shiga ta zauna, kallon sama ya yi yana kallon yanda wani bakinkirin ɗin hadari yake tasowa, ɗan kallonta ya yi kafin ya shiga cikin motar ya zauna a mazaunin driver, yanzu ya sami sauki yana iya tuki da kansa. Kunna motar ya yi suka nufi waje, tun kafin su iso gateman ya wangale musu gate ɗin, cikin natsuwa ya danna hancin motar waje.
Sai shakar daddaɗar kamshin perfume nasa take yi, sun yi tafiya mai nisa tsakaninsu da gida kafin ya ce mata "Ina ne gidan? Ko dai gidansu Prof ne?". Tana ta aikin danna wayar daddy da ta karɓa, hankalinta baya a kansa, sam bata ji abin da ya ce ba, kashe motar ya yi a gefen hanya tare da juyo da kallonsa bakiɗaya a kanta, sai latsa waya take yi tana buga game.
Hannu ya kai ya karɓi wayar dai'dai lokacin kuma ruwan sama ta ɓarke tammar da bakin kwarya, ɗago idanu ta yi tana kallonsa, kashe mata ido ɗaya ya yi yana faɗin "Sai ki bar mijinki shi kaɗai yana ta magana ke kuma kina latsa waya ko? To maza gaya mini hanyar gidan mu tafi kin ga ruwan saman nan da karfi da kuma iska ya zo". A kule ta ce "Nima ai ban san gidan ba". Ta ji haushin ya kwace mata waya ne tana tsaka da buga game. "Baki san gidan ba kuma?". Ya tambaya da mamaki, banza ta yi da shi bata sake yin magana ba.
Kunna motar ya yi suka cigaba da tafiya ba tare da ya bata wayar daddyn ba, wani irin azababben iska da ruwa mai karfi ake yi wanda ya sanya shi dole ya yi parking na motar a gefen hanya dan gudun haɗari, baya iya ganin gabansa saboda iska da karfin ruwan.
Jingina ya yi da jikin kujerar motar yana sauke numfashi a hankali. "Malam ka bani wayata". Ta faɗa cikin no respect, sam yaki kulata dan yanda ta yi maganar bai yi mishi daɗi ba, duk da yasan cewa ita haka take magana cikin nuna isa, amma yana da kyau ya fara gyara mata magana idan ta yi, idan ba haka ba akwai matsala babba.
Sai magana take yi mishi ya sherata bai kulata ba, da taga ba zai kulata ba, sai ta yi yunkurin buɗe motar ta fita mishi daga cikin motarsa dan a cewarta ai ya raina ta ne, ko dan yana ganin ta shiga motarsa ne, ai a gida bai taɓa yi mata hakan ba, yanzu kuma wato dan yasan ba'a gida bane kuma ta shiga motarsa, shi ne zai yi mata walaƙanci......... Mata kenan, shi kuma yau ta haka ta fassara shi, bawan Allah ba hakan yake nufi ba shi kuma.
Ganin kofar motar a rufene yasa ta juyo a fusace ranta a ɓace, dama kunsanta da saurin hawa ga zuciyar bala'in, Areef ya rainata yau, ba zata sake shiga motarsa ba, a kule ta ce "Ka buɗe mini motar nan na fita". Ta faɗa cikin ɓacin rai.
Ɗan zaro ido waje ya yi kafin ya ce "Baki da hankali ne da zaki fita a cikin wannan uban ruwan sama dake zuba kamar da bakin kwarya? Kuma baki ganin a kan hanya muke ne? Kina fa sane iska da kuma karfin ruwan saman nan ya sanya muka dakata da tafiya har sai ruwan ya tsagaita".
Sosai ta ɗaure fuska tana faɗin "Ka buɗe mani mota ni dai na ce".
Shiru ya jingina kansa da jikin headboard na kujerar motar yana shakan daddaɗar kamshin perfume nata dake kwantar mishi da hankali, yaki sake tankata.
Ganin hakan yasa ta yi kokarin buɗe kofar motar domin ta fita waje, dawo da kallonsa kanta ya yi yana kare mata kallo tare da mamakin yaushe yarinyar nan ta zama mai shegen gardama ta kuma raina shi har haka ne?.
Ganin da gaske take yi sai ta fita yasa ya sakar mata kunamarsu na TRIPLETS a daidai hannun marfin motar.
Ihu ta kurma tare da sake hannun motar ta faɗa jikinsa tana kuka, sosai ta kankame shi tare da runtse idanunta gam, kunamar ya ɗaga mata hankali, ta tsorata ba karya.
Wani irin yanayi mai wuyar fassarawa ya ji a jikinsa, gabaɗaya ya kasa motsawa, sam bai yi zaton zata faɗa jikinsa haka ba, ya zaci jaruma ce bata tsoron komai, ashe damisar kwalice, ga tsoro ga ban tsoro. Ita kuma sai kara kankame shi take yi tare da sakin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro.
Kaɗan kaɗan ya ke jiyo sautin kukan nata har ta fara ratsa shi da kyau, nauyayyar ajiyar zuciya ya sauƙe kafin ya sanya hannunsa ya ɗago haɓarta suna fuskantar juna, can kasan maƙoshinsa ya fara magana a nutse. "Am so so sorry my baby, ban taɓa tunanin zaki tsorata haka ba, shiyasa ma na sakar miki kunamar, kuma saboda na san ba zata cijeki bane, amma dai ki yi hakuri, na tuba ba zan kara ba".
Jin cewa kunamarsa ce kuma da gangan ya sakarmata ya sa ta miƙe daga jikinsa a zafafe, rai a matuƙar ɓace ta sanya hannunta ta buɗe Kofar ta fice abinta.
Ganin ta fita a cikin wannan uban ruwan saman yasa ya yi saurin buɗe kofar motar shi ma ya fito waje tare da bin bayanta da gudu yana faɗin "Dan Allah ki yi hakuri, na amince ki yi mini duk hukuncin da zaki yi mini amma kada ki hukunta mini kanki da shiga cikin wannan ruwan sama mai bala'in sanyin, dan Allah ki dawo, na yarda baki so na, muje a haka, ni dai ki zo ki shiga mota mu koma gida". Gabanta ya tare tana wannan surutan.
Rai a matuƙar ɓace, kun san ta dama da shegiyar kafiya kamar kafuran farko, bata san ta yi magana ta canza ba, hakan yasa ta ce "Ka bani hanya na wuce ko kuma wlh na zabga maka mari". A zahirin gaskiya kamar dai yadda kuka sani ne, mugun tsoron shi take yi, dakiya ce kawai irin tata take nuna mishi bata tsoron komai, amma daga ta ciki, idan suka haɗa ido har wani fitsari take ji saboda tsoro, ko a mafarki ba zata iya kuskuren marin shi ba.
Da yake su dukawa mace ƙaramin abune a wajensu wanda ma ya zama masu kamar jiki, ko flowers za su bata sai sun duƙa sai dai masu girman kai a cikinsu irin masu zuciyar Lion, sune ba su duƙawa, irin su ma ai mace da na miji ma duk ba su ishe su kallo ba.
Zube gwiwowinsa a kasa a gabanta ya yi tare da riƙe kunnuwansa da hannayensa yana faɗin "Am so so sorry, na gaya miki ba zan kara ba ko? Please ki yafe mini".
Raɓawa ta yi ta gefensa zata wuce abinta. Cikin sauri ya miƙe ya tare gabanta yana faɗin "Yanzu idan kika tafi a cikin ruwan nan ina zaki je? Kin san dai baki san hanyar gida bako? To ko dan haka ki yi hakuri na mai dake, ko dan uncle na kinji ko?".
Kin yi mishi magana ta yi tare da sake raɓawa ta gefensa ta wuce, a zafafe ya sureta ta baya kamar ƴar baby ya yi wajen mota da ita, abin da bata wuce ya ɗaga ta da hannu ɗaya ba ta tsaya tana ɓata mashi lokaci ruwan sama na dukansu.
Sai bugun shi take yi a hannunsa akan ya sauƙeta, amma ina yaki har sai da ya kaita wajen motar, ya sauƙeta tare da buɗe kofar motar ya turata ciki ya rufo kofar.
Yana ƙoƙarin zagayawa ta ɗayar kofar sai ya ga tana ƙoƙarin buɗewa ta fito, da sauri ya sake dawowa wajen kofar tata, ya sanya hannu ya maida karfin ya rufe tare da jingina bayansa a jikin marfin ruwan sama na dukansa daga tsakiyar kansa, bawan Allah ya gwammaci ruwan sama ta yi mishi duka akan ya barta ta fito ruwa ya daketa.
Almost 10 mins yana jingine da jikin marfin motar ruwa na dukar tsakiyar kansa, ita kuma tana ciki ta yi shiru, ta rasa abin yi.
Ganin zai illata kansa da gaske ne yasa ta ji tsoron hakan, jikinta ya yi mugun sanyi, wani irin so yake yi mata haka? ya gwammace shi ya cutu har haka akan ita ta fita ruwan ya taɓata, lallai wannan ya kai masoyin da dole ko wace zuciya ta yi maraba da shi, shi ne irin masoyin da ko wace zuciya take begen samu a duniyar nan.
Jiki a mace ta yi mishi knocking na glass ɗin motar, ya ci bakar wahala, idanunsa duk sun yi jawur saboda ruwan saman, kun san dama idan mutun ya shiga cikin ruwa mai yawa sosai haka, to idanunsa suna yin ja sosai.
Slowly ya juyo tare da kifa kansa a jikin glass ɗin motar bayan ya rage tsawonsa kenan, zuba mishi idanu ta yi tana kallon yanda idanun nasa suka sauya, da alama ya wahala over, wani mugun tausayinsa ne ya dira mata a ranta, alama ta yi mishi da hannu akan ya shigo ciki.
Kara rage tsawonsa sosai ya yi, ya dawo daidai da tata yadda take zaune a cikin motar. Ko ya yi magana ba zata ji shi ba saboda glass ɗin a rufe, hakan yasa ya yi amfani da motsa lallausan laɓɓansa ya tambayeta akan ta yi alkawarin idan ya tashi a wajen ba zata fito ba? Cikin sauri ta gyaɗa mashi kai alamar e, cool murmushi ya sakar mata, ɗan sunkuyar da kanta kasa ta yi tana wasa da hannunta.
Da sauri ya bar wajen jikinsa sai zubar da ruwa yake yi, kofar side nasa ya je ya buɗe ya shiga, duk sun jika kujerun motar, wani irin sanyi sosai yake ji, sam bai damu da kan shi ba, ita yake jiyewa saboda ita ma ta jike sosai, tsaki ya ja yana kallon motar tasu, ba irin motarsa na Washington DC ba ne, da yanzu ya canza sanyi zuwa zafi saboda ita.
Shiru suka zauna har ruwan ya ɗan tsagaita, sai satar kallon shi take yi, yana da kyau over, take faɗa a cikin zuciyarta, shi kuma ya lumshe idanu yana tunano irin sanyin da take ji bawan Allah. Da yaga ruwan ya ɗan rage karfi ne sai ya kun motar suka nufi wani tampatsetsen super market, shi kaɗai ya fito daga cikin motar tare da rufeta ya nufi cikin super market ɗin, kaya ya saya suka bashi ɗaki ya canza, sannan ya saya mata doguwar riga da Jacket ya kawo mata, karɓa ta yi tana kallon kayan, sun yi kyau sosai.
Komawa cikin super market ɗin ya yi dan ya bata dama ta canza kayanta, da yake bakin glass ne da motar ta su, bata yi musu ba ta canza dan bala'in sanyi take ji.
After 10 mins ya dawo hannunsa rike da cups guda biyu masu ɗauke da hot coffee da ya saya daga cikin restaurant dake manne da super market ɗin.
Cikin motar ya shiga har lokacin ana ruwan sama, miƙa mata guda ɗaya ya yi, da kamar ba zata karɓa ba, amma tuna cewa daddy ya ce Areef ba zai taɓa cutar da ita ba ne yasa ta karɓa tare da ce mishi thank you, jinjina mata kai kawai ya yi tare da ɗan kurɓar nasa, wani irin azababben amai ne ya ji ya zo mishi, sam ɗanɗanon coffee ɗin da kuma yanayin wajen bai yi mishi ba, buɗe motar ya yi ya fara aikin tikar amai, anyi ruwan sama ya kalli kan hanya ya yi caɓa caɓa shi ne duk hanlinsa ya tashi dan basu son datti ga bala'in kyama, wurgi ya yi da cup ɗin ya yi amai sosai, da mamaki take da kallon shi har ya kammala ya wanke ɗan bakinsa, sannu ta yi mishi ya amsa cike da murna na ta yi mishi magana a nutse, sannan ya kunna motar suka nufi gida tun da dukkansu babu wanda ya san hanyar gidan Abbin, dama zai kira Imran ne ya gaya mishi, to ruwan saman nan tasa ya ce su koma gida kawai.
Ko da suka koma gida ya yi parking a parking space na gidan, tana ƙoƙarin fita dan ta keta ruwan saman ta shiga cikin gida, cikin sauri ya rufe kofar yana kallonta, ita ma