Showing 243001 words to 246000 words out of 359620 words

Chapter 82 - Triplets Book 3 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2053

sojojin Lion basu shiga musu ɗaki dan rashin yarda da mutane da suke yi, sun tsani mata, mace bata taɓa raɓarsu ba, yau rana tsaka mace a ɗakin Michael tana gyara mishi gado, ai dole ya ji ko ƴar uban wanene?!.

Murya na rawa ta amsa mishi da ita matar Heartbeat ne, dan a gaskiya ba karya Akila bata rike sunan Aseef ba, sau ɗaya ya taɓa gaya mata sunansa, kuma ta manta, Heartbeat take kiransa tun farko, kuma sunan ne ya zauna a bakinta, dan haka sai ta ce ita matar Heartbeat ne.

Da yake shi ma daddyn haka yake kiran Michael ɗin nasa, wato Heartbeat, sai ya gane wato ita matar Michael ne, tab lallai akwai rikici. Cikin fushi ya ɗauketa da wani wawan mari wanda ya sanyata juyi ta faɗa saman gadon, wani irin azababben ihu ta saki dan ta maru ba karya, nan take yatsun daddy biyar reras suka fito ɓaro ɓaro a saman kumatunta, dan ita ma a Nigeria fara ce tas, a gabansu ne take baka dan su babu mix a jininsu tarr suke.

Jay, Uncle Herry da suke tsaye a bayansa duk sun ji daɗin abin da daddy ya yi dan suma suna kyamar bakaƙen fata, shi kuma John har cikin ransa bai ji daɗi ba, dan kuwa tun da ya ganta a ɗakin Michael yasan cewa Michael yana sonta kenan, to duk abin da Michael yake so shi ma yana so, ba ruwansa da kabilarci or faɗar addini, shi dai yana kaunar Michael dan tare suka taso, komai tare suke yi a baya, dan haka kaunar a jini take.

To masu karatu a yanzu dai dole mu mayarwa da su Michael sunansu na farko, domin su daddy basu san sun musulunta ba, kuma kunga dama basu son su daddyn su sani, bamu san dalilinsu ba, za dai muji komai a gaba, yanzu dai shi daddy Michael yake kira, so dole bakinsa zamu rubuta ba namu ba.

Da sauri John ya karisa wajen da take kwance ta dafe kumatunta tana kuka, cikin sauri ya sanya hannu ya ɗan ɗagota yana faɗin "Haba daddy why zaka mareta haka? You know fa tun da ka ganta a nan Michael yana sonta ne, to kuma bai kamata ka daki abin da Michael yake so ba gaskiya, ni wlh ina sonta tun da Michael yana sonta".

Wani irin mahaukacin tsawa ya dakawa John ɗin wanda ya sanya shi razana har ya saki hannunta da ya riƙe, wannan tsawar ce kuma ta sanya Aseef dake toilet ya ji abin da yake faruwa, tsaida ruwan da yake zuba ya yi yana son jin menene yake faruwa?.

Faɗa daddy ya fara yi a kan lallai Akila ta tashi ta bar gidan nan yanzu! Babbar magana, Me ya kawo hakan? Duk tsana ce? To ina ga kuma ya ji shi ma Lion ya auri bakar fatar? Akila da take fara tas kamar Naurat ma ya kira ta baka ina ga kuma Rimsha da take da kala mai tsada a duniya wato chocolate color? Ita kam kamar gawayi zai kalleta kenan? Ina ga ita tsanar da zai yi mata ma sai yafi na kowa, dan ita ce kawai chocolate a cikinsu dake gidan, Jehan ma fara ce tas irin farar fatar Naurat, e lallai da akwai case ba kaɗan ba, dan kuwa bana jin Aseef dai zai rabu da Akila, bama zai yiwu ba, dan ana rabasu mutuwa zai yi, sai dai Akila ta hakura ta jure azaban daddy, dan yadda ya tsanesun nan zasu wahala da alama!!.

Jin voice na daddynsa ne yasa ya ajiye brush dake hannunsa, dama already ya gama wanka yana shirya brushs dake wajen ne da AKila ta watsasu da safe bata gyara ba, ruwa kuma yana ta zuba bai kashe ba, dama sai ya gama zai kashe ya fita, jin voice ɗin na daddyn ne yasa ya ajiye brush ɗin tare da ɗauko karamar towel ya ɗaura a saman kansa dan goge gashinsa, dama already ya ɗaura babba a kugunsa.

Da kyar ya fito wajen, har lokacin bai gama warwarewa ba, ya dai samu jirin ta sake shi, yana iya shiga toilet da kansa, amma jikinsa babu wani kwarin kirki.

Ganin abin da yake faruwa ne yasa ya kariso wajen da sauri tare da kama hannun Akilar ya mikar da ita yana kallon face nata yadda yatsun daddy ya fito ɓaro ɓaro, hakan kuma ya yi daidai da shigowar Lion da Areef da ya dawo daga Abuja yanzu, jin daddyn na surfa masifa ne yasa suka shigo dan su ga me yake faruwa.

Rungume matarsa Aseef ya yi yana bata hakuri ba tare da ya ce da daddy komai ba, ya san dai wlh babu abin da ta yi wa daddy ya mare ta, dan haka ba sai ya tambayi ba'asi ba. Daga Lion har Areef sun san cewa wlh babu abin da Akila ta yi wa daddy ya shinfiɗa mata yatsunsa biyar ɗin nan a face nata har haka, already dama sun san shi da tsanar bakaƙen fata, to a tunaninsu hakan ce tasa ya wanke mata fuska da mari, Baiwar Allah har wasu taurari ta gani, ta sha marin Dr William Dangerous Boss.

Tsawa ya dakawa Aseef ɗin a kan ya saketa ta zo ta bar gidan nan, da sauri ya ɗago brawn eyes nasa da suka yi ja ya saukesu a kan Lion dake tsaye yana ganin wannan iko irin na daddy, sai ka ce shi zai zauna da ita.

Areef ne ya katsesu da cewa "Daddy what is happening here? Why are you shouting like that? Kabi komai a hankali mana". A kule ya jiyo ga Areef ɗin yana tambayarsa au tsawa ma kenan yake shi, ihu yake yi ma kenan? E lallai sun raina shi.

"James ina son wannan yarinyar ta bar gidan nan yanzu nan, I don't want to see her close to my son". "Sorry daddy, I can't live without her, gaskiya ni a bar mini matata". Cewar Aseef, ya yi maganar da kyar saboda tsananin ciwo da kansa yake yi mishi.

Ganin yadda yake faman ciza laɓɓansa ne yasa Lion ya fahimci har yanzu fa akwai ciwo a tarrare da shi sosai, so bai kamata su ɗaga mishi hankali ba, dan haka sai ya dubi daddyn nasa ya ce "Daddy babu abin da zai raba Michael da matarsa, yana sonta, ita ma tana son shi, so banga abin da zai rabasu ba, ko da Michael ya ce baya sonta yau, to wlh dole ya zauna da ita dan kuwa tana son shi, a kansa ta kusa mutuwa, bai isa ma ya ce ba zai zauna da ita ba, ko ya dai'na sonta, so daddy kowa ya wuce bedroom nasa bana son wata hayaniya!!".

Tsawa ya daka musu tare da buga saman bedside drawer yana faɗin ba zai yiwu ba, dole yau wannan munafukar yarinyar ta bar gidan nan.

Banza da shi Lion ya yi bai sake yin magana ba tamkar babu shi a wajen, ba zai wani ɓata bakinsa ba wajen yin wani magana, saboda bai ga uban da ya isa ya raba Aseef da matarsa ba, ba daddy ba yau ko Jacop Roshan ne zai fito daga cikin kabari to sai ya barwa Aseef matarsa. Tashin sense, Jacop Roshan da kansa kuma yau? E lallai Lion ya yi nisa.

Nisawa Areef ya yi kafin ya ce "Dad please and please ka dai'na faɗin haka, seriously Michael yana son matarsa, and then....." Wani irin razanannen tsawa daddyn ya daka mishi wanda ya sanya shi dakatawa da maganar, sam Areef baya son ganin ran daddyn ya ɓaci, amma kuma yana kure shi, sai danne zuciyarsa yake yi dan kada ya zama ya yi mishi irin abin da Lion yake yi mishi, idan aka ce sun haɗu sun zama iri ɗaya waye zai taushi daddyn kenan? Amma kuma daddyn yana neman kure hakurinsa gaskiya, taya zai yi ya ce shi baya son matar Aseef sai dai su rabu? To shi zai zauna masa da matar ne? Wlh tsohon nan ɗan neman bala'i ne, to sun ce basu son turawa ƴan uwan nasu bakaken fata suke so ana dole ne? Dama ya samu Aseef ɗin ya yi auren ne zai wani takura musu, idan da irin Jay Aseef ɗin ya yi musu ya kawo musu ɗan shege ba shikenan ba?!.

Shi kuwa Aseef ya rungume Akila dake ta faman kuka ta sha mari yau, sai rarrashinta yake yi.

"Michael ɗauketa ku je zuwa bedroom na dan na ga kamar zaka faɗi, idan kun je ka rufe kofar with key". Cewar Lion, dan ya luran Aseef ɗin kamar zai zube kasa saboda rashin kwarin jiki, ga kuma hayaniyar daddy sannan ga Akila a rungume a jikin nasa tana kuka, abubuwan sun yi mishi yawa bawan Allah.

Sam daddy ya hanasu wucewa, shi dai ya kafe lallai baya son bakaken fata, sai da ya ga ran zakunan nasa wato Lion da Areef ya ɓaci, face nasu ta sauya, ya san ba zata yi musu kyau ba, sannan ne ya shafawa kansa ruwan sanyi ya bawa Michael hanya, amma fa ya kuduri niyar wlh sai ya rabasu, dan shi bazai yi mix na jini da kowa ba face ƴan uwansa...... E akwai kura in dai haka ne kam.

Wucewa Aseef ɗin ya yi zuwa bedroom ɗin Lion, a hankali yake tafiya gudun kada ya faɗi, sai shessheƙar kuka Akilar take yi, ita kuma Rimsha tana cikin bedroom nata suna zuba dirama da Jehan a kan zuwa wajen Lion ta yi dare haka, dan jiya a kullace da Rimshar ta yi barci, ta jirata har wajen 11 bata dawo ba har barci ya yi awon gaba da ita, da safe kuma Rimshar ta tafi school basu haɗu ba, dama jiranta take yi ta dawo school sai ta gaya mata uban da take zuwa yi wajensa har dare haka? To shi ne diramar da suke yi, Rimsha dai ta kafe akan ita wlh babu wani abin da take yi bayan kai mishi abinci, ita kuma Jehan ta ce karya take yi munafuka, kai abinci ne sai ta shafe awa huɗu a can, to wlh ba zai yiwu ba, ta shiga hankalinta da kyau idan ba haka ba sai ta yi mata ɗan iskan dukan mutuwa sai dai duk abin da zai faru ya faru.

Da yake ita ma Rimshar akwai zuciyar sai ta ce "Kinga ne Jehan duk wannan magana ba ni zaki yi wa ba, ki je ki sami Yaya Saif ɗin ki gaya mishi, domin shi ne mai tsayar da ni, kuma ni ban isa in ce mishi a'a ba, so kila idan kika yi mishi magana zai ji sai ya dai'na tsayar da ni". "Rimsha ba zan yi mishi magana ba dan bani da wani haɗi da shi! Ke kuma na isa in saka ki kuma in hana ki, wlh idan kika sake wuce minti 30 a wajensa sai ranki ya ɓaci!!". Ta yi maganar cikin fushi da ɓacin rai, dan kuwa abin ya kona mata rai yadda jiya Rimshar ta jima bata dawo ɗaki ba har ta yi barci, wannan ma fa bata san cewa tare a garden ɗin suka kwana ba, ta yi tunanin Rimshar ta dawo cikin dare bayan ta yi barci kenan.

Miƙewa Rimshar ta yi tare da riko hannuta zuwa palon sama, dai'dai lokacin kuma Lion da Areef sun hauro sama bayan sun gama case da daddy Areef ya kai shi masauki, shi ne suka nufo bedroom ɗin Lion ɗin dan su tattauna a tsakaninsu su ukun.

Da hannu Rimsha ta nunawa Jehan ɗin Lion tana faɗin "Wannan shi ne yaya Saif, sai ki gaya mishi ya dai'na rikeni ina jimawa a ɗakinsa". Ko kallon in da suke Lion ɗin bai yi ba ya wuce zuwa kofar bedroom nasa yana knocking a hankali dan Aseef ya rufe kofar da key, ita kuwa Jehan ta sha jinin jikinta sosai ganin Lion, ashe bata ga komai a hoto ba, a zahiri ma kwarjininsa yafi yawa, wani irin azababben tsoronsa ne ya dira mata a ranta, dan kuwa bata ga wajen wasa ba, dan ma ko kallonsu bai yi ba, Areef ne ya tsaya yana tambayarsu me yake faruwa? Ba ɓoye ɓoye Rimshar ta gaya mishi abin da yake faruwa.

Da hannu ya yi wa Rimshar alama a kan ta koma bedroom nata bari ya yi magana da Jehan ɗin, a lokacin kuma Akila ta buɗewa Lion kofar bedroom ɗin ya shige abinsa. Wucewa Rimsha ta yi ta koma ciki, juyawa ita ma Jehan ɗin ta yi da nufin ta koma ciki, da sauri ya riko hannunta yana faɗin "Wai ke meyasa kika cika faɗa da neman rigima ne?". Harara ta watsa mishi tare da fisge hannunta ta juya zuwa ɗakin dan ta je ta jibgi Rimsha akan ta kawota gaban Lion, haka kawai ta sanya ta sai faɗuwar gaba take yi tun da ta ganshi, dan haka ba zata kyaleta ba wlh.

Da sauri ya bi bayanta zuwa cikin ɗakin, dan yanda ya kallin ta juya a fusacen nan yasan tana iya aikata wani abin ga Queen nasu. Dai'dai lokacin da ya shigo ta ɗaga hannu zata mari Rimshar dan fa a fusace take, rike hannun nata ya yi tare da ɗaure fuska sosai cikin nuna isa ya ce.

"Ki natsu ko kuma na nitsar dake yanzun nan". Ganin ya ɗaure fuska ya koma kamar Lion ne dama kuma ga bala'in tsoronsa da take ji, hakan yasa ta natsun kamar yadda ya faɗa, dan kuwa wlh tsab zai iya ajiye soyayya a gefe ya gyara mata kuskure idan ta yi, yana da wasa da dariya ga waƴan da ya ga damar yi da su, amma fa idan ka yi mishi ba dai'dai ba abin da baya so, wlh tsab zai canza maka daga Areef zuwa TRIPLETS ɗin General Of The Army, yanzu zai yi maka hukunci.

"Our Queen jeki zuwa wajen daddy ina zuwa nima yanzu". Ya yi maganar tare da sakin hannun Jehan ɗin ya nuna mata waje saman gefen gadon a kan ta zauna, bata musa mishi ba ta zauna, dan tasan ko daddy ta kaiwa karansa bai wuce ya ce mata yayanta ne ta bi abin da ya ce ba, so is better kawai ta bin ya fi.

"Ba da wasa nake miki ba, idan kika yi kuskure dukan Rimsha serious ko ni ban isa in tare miki wannan faɗar ba, dan idan garin nan kap zasu haɗu bana jin zasu iya tare miki, idan kika ga Lion bai sumar dake ba, to sai dai idan Rimshar ce da kanta ta shiga tsakaninku, ki sani Lion yana da damar yi miki duk hukuncin da ya ga dama idan kika taɓa ta saboda matarsa ce, akwai aure a tsakaninsu, so baki da damar dukanta, bare kuma da hujjar taki ta zama a kan dan ta je wajensa ne, to ki sani mijinta ne, ita kanta bata san mijinta bane, kuma ban ce ki gaya mata ba, ki kyaleta kamar yadda uncle ya ce kada a gaya mata, abin da yasa kema na gaya miki, dan ba zan iya juran wani abin ya same ki bane, na san in dai kika taɓata a yadda Lion yake yanzu sonta na ɗawainiya da shi ba tare da ya sani ba, tsab zai iya yi miki illah, ba zan iya juran hakan ba ni kuma shiyasa kawai na gaya miki, tun wuri ma ki sani, dan haka ki cire idanunki a kansu babu ruwanki da su".

Hakika ta tsorata da jin cewa akwai aure a kan Rimsha, abin ya girgiza ta, to ya akayi hakan ta faru? Ta tambayi kanta, lallai kuwa abin da mamaki, baiwar Allah Rimsha ita bata ma sani ba, ga shi daddy ya ce kada a gaya mata, ko meyasa ya ce hakan? Ta sake tambayar kanta.

Ganin ta shiga duniyar tunani ne yasa ya hura mata iskar bakinsa a fuska yana faɗin "Faɗa mini ke kuma yaushe kike son muyi aure?". Kallon uku goma ta wurga mishi kafin ta ce "Me kuma aure? Sunan wani abinci ne? Idan ma abinci ne bana ci, dan daga jin sunan abincin ba zai yi daɗi ba".

Da yake shi ma ɗan yi ne sai ya matso kusa da ita sosai, kasa kasa kamar mai raɗa ya fara magana "Yes sunan abinci ne aure, abinci kuma mai daɗi ma kuwa, kuma ko zaki yi yaya sai kinci, kuma ni zan baki da hannuna, dan haka ki fara shirin aure tun yanzu, bari dai Lion ya je lafiya ya dawo lafiya, daga nan sai aurenmu, yanzu bani da kwanciyar hankali yin aure har sai ɗan uwana ya dawo lafiya, ji wani ɗan bakinta a wajen, zaki ga abinci ne iya ganin idonki masifaffa mafaɗaciya kawai, Allah ko har na hangoki kina goye da baby'sna a bayanki, zakuwa ki yi matukar kyau da hakan, Allah ya sanya ki haifi 5 baby's lokaci guda, dan ni ina matukar son baby's Lion ne baya so, shi ma kawai dan baya son hayaniya ne, amma nasan idan baby's nasa ne dole zai so a nawa tunanin".

Miƙewa ta yi dan ta lura Areef fa ya fita iya iskanci, duk wani mannin haukarta to ya ninkata, ko da me ta zo wlh ya fita, Hmmm ga shi Bature babu kunya ko ɗigo a lamuransu, bugu da kari ya yi rayuwa waje daban daban, ai dole ma taga abin da ya minka haka, idan bata yi hankali ba ma ta biye mishi suna magana, wlh watara sai ya gaya mata abin da yafi karfin ƙwaƙwalwarta, rufin asirinta ɗaya idan yana magana ta yi shiru, idan ba haka ba, duk wani amsa da zata bashi, yadda zai fassara shi daban, dan sai ya kara gishiri da su maggi, ya tsara kalmar da kyau kafin ya bata amsa wanda zai sanyata yin shiru bata shirya ba, ga shegen iya magana a wajensa na wuce misali, kai a takaice komai ya haɗa, idan shiru shiru ne ma tsab zaka samu a wajensa, dan wlh bashi da magana sai da waƴan da yaga dama, maganar tasa ta ganin dama ce, wani lokaci ko da Aseef idan bai ga dama ba baya tanka mishi magana idan yana yi mishi, shi ɗan naga dama ne over.

Ganin ta miƙene yasa shi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login