Showing 222001 words to 225000 words out of 359620 words

Chapter 75 - Triplets Book 3 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

1980

ɗin ya yi alamar duk ɗaya ne, a tare suka ji bugun zuciyar, a zafafe ya dawo wajen bed ɗin, dan wannan bugawar da zuciyarsu ta yi a tare tana da nasaba da Aseef, saboda duk abin da ya sami ɗayansu sai sun ji hakan a tare, shiyasa ma ya dawo dan ya duba ko dai Aseef ɗin bai mutu bane.

Duba shi ya fara yi a zafafe babu kama hannun yaro, shi ma Areef hayewa saman bed ɗin ya yi suka fara bincikarsa ko zasu gano wani abin.

Daddyn Rimsha kuma zuwa ya yi ya riƙo Akila dan kada ta hanasu yin aiki, sai kuka take yi, duk rashin son hayaniya ta Lion yau ya daure yana jin kukan AKila bai yi magana ba, domin kuwa Aseef yana mahaukacin sonta, dole su kula da ita dan ɗan uwansu, dama idan baku manta ba Rimsha ta taɓa gayawa Akilar, in dai ɗaya daga cikin TRIPLETS yana sonta ya aureta, to dukkansu uku zasu so ta har da shi ma Lion ɗin, dan suna son abin da ɗayansu yake so, bare kuma yanzu da take matar Aseef ɗin, ai dole sun danne su shanye, bugu da kari ga irin rabuwar yankar kauna da aka yi musu, ai kukanta mai hujja ne, dole ta yi, dole suma su danne su barta ta yi ko zata samu sauki a ranta.

Sun ɗan ɗauki lokaci suna bincikar Aseef ɗin, amma ina babu wata alama da take nuna yana raye, can kamar daga sama suka ji saukar hannunsa, nan take numfashin ya fara fita da sauri da sauri kirjinsa na harbawa da karfi karfi, a zafafe Areef ya diro kasa daga saman bed ɗin ya nufi wajen drawers dake wajen mirror dan ya kawo oxygen su saka mishi numfashin ta daidaita, ya kuwa yi sa'a suna da shi, dan suna tafiya da abubuwa irin haka saboda tsaro, duk wasu kayan taimakon gaggawa da ta shafi lafiya suna tafiya da shi dan yanayin aikinsu, tana iya yiwuwa a harbi wani daga cikinsu da bindiga ko makamancin haka, to shi ne dalilin da yasa duk in da zasu je suke ɗaban kayan kula da lafiya na agajin gaggawa.

Sanya mishi Lion ya karɓa ya yi dan numfashin ta dai'dai ta, sun kuwa yi sa'a ta daidaita, sai dai bai buɗe idanu ba, kamar ma bai farka ba, sun dai tabbatar yana raye bai mutu ba, kifa kai Areef ya yi a bayan Lion yana sauke numfashi tare da zuba ɗinbin godiya ga ubangiji da ya sanya Aseef bai mutu ba, da ya mutu ai da sun shaga uku, Juyowa Lion ɗin ya yi suka rungumi juna, Allah ne kaɗai yasan irin farincikin dake cikin zukatansu a yanzu.

Sosai suka kankame juna, har ƴar washewa idanun Lion ya yi, bayin Allah suna mutuwar kaunar junansu, ita ma Akila shiru ta yi dan ganin Aseef yana numfashi, daddyn Rimsha ba'a magana, murna a wajensa ya wuce misali, Allah sarki ita kam Rimsha tana cikin bedroom nata kwance a jikin Jehan tana ruwan hawaye bata san me yake faruwa ba, bata san cewa doguwar suma mai kama da mutuwa Aseef ya yi ba, ta ɗauka ya mutu baiwar Allah, abokin shagwaɓarta da zuba hira, sun yi sabo sosai da shi, shiyasa take kuka har haka, sai rarrashinta Jehan take yi dan ta yi mugun bata tausayi.

Wunin ranar dai a cikin bedroom ɗin suka wuni, Akila taki yarda ta matsa daga jikin gadon, gani take yi idan ta tashi wani abin zai same shi, shi kuma har lokacin bai farfaɗo ba, yana dai numfashi, Lion, Areef duk basu matsa daga wajen ba, suma suna ganin kamar idan suka matsa wani abin zai same shi, cikin ƙanƙanin lokaci labari ya sake isanwa Mutanen Washington DC akan Aseef bai mutu ba, nan ne fa su John suka ce su gaskiya za su zo su ganshi da idanunsu, Lion bai hanasu zuwa ba, daddy ma da bai san me yake faruwa ba ya kafe sai ya biyo su John sun zo tare, shi ma Lion ya barshi yazo dan ya lura hakurin daddyn nasa ya fara karewa a kan rashinsu a kusa da shi, kada ciwonsa ta yi ta kara cigaba, yanzu sun fara murna sauki ya samu, to kada a koma gidan jiya gara ya bar shi ya zo ɗin, shi ne yasa ya kyale su suzo tare, shi kuma Tga sai ya kara samun sauki nan da next week.

Da misalin karfe 6 na yamma, duk sun haɗu a cikin bedroom ɗin Lion, harta su Rimsha sun zo, Lion, Areef suna saman bed kusa da ɗan uwansu, ita kuma Akila tana zaune saman bedside drawer tana ta kallon mijin nata ba ko kyafta idanu, hayaniya ne ya fara tashi a waje, sojoji ne da su Abba sun biyo AKila, Abba ne da Abbi sai daddyn Jelly, Irfan da kuma Akil da ya yi musu jagora, sojojin sun hanasu shiga gidan ne, shi kuma Abba ɗan zafin rai ya ce dole sai ya shiga ya je ya ɗauko ƴarsa.

Jin hayaniyar yasa Areef miƙewa ya nufi wajen, dai'dai lokacin kuma ɗaya daga cikin sojojin ya ɗaga bindiga zai harbi Abba a kafa dan ya ce sai ya shiga, daka musu tsawa Areef ɗin ya yi yana faɗin suna hauka ne zasu harbi mutun basu san waye shi ba? Laifin me ya yi musu zasu harbe shi? Sorry sir suka fara ce mishi.

Bai sake bi ta kansu ba ya yi wa su Abba iso zuwa cikin gidan cikin mutunci yana mai basu hakurin abin da sojojin suka yi musu

❤️❤️TRIPLETS❤️❤️




E57-58💋




Bai sake bi ta kansu ba ya yi wa su Abba iso zuwa cikin gidan, cikin mutunci yana mai basu hakurin abin da sojojin suka yi musu, a palon kasa ya sauƙesu, dan bai san da me suka zo ba, kada su je palon sama ya zamana da ɗaga murya suka zo Lion ya jiyo su suna ɗaga murya ya zo ya kwaɓe komai, dan kaɗan daga aikinsa idan suka ɗaga murya ya sanya a basu hukunci mai tsanani, bayan kuma shi ya je ya ɗauko musu yarinya kamar shi ya haifa musu ita, so yanzu sun rigada sun zama family ɗaya tun da dai Akila da Aseef aure ya ɗauru ba warwarewa, yana da kyau su daraja iyayen Akilar, kuma yana da kyau su basu kulawa tun da suna da damar da kuma power yin hakan.

Zama shi ma ya yi cikin sanyin murya ya ɗagawa Abba da Abbi gaisuwa, fuska ba yabo ba fallasa suka amsa, miƙawa daddyn Jelly hannu ya yi dan su gaisa saboda suna kusa da juna, ya raina daddyn Jelly yana yi mishi kallon matashi dan ya ganshi ɗan kwalisah, yana yi mishi kallo kamar su yake, bai san ba haka bane, daddyn Jelly ya girmesu da almost shekaru 8, kawai yana da karamin jiki ne da kuma kyau irin na Naurat, shi ne har da wani miƙa mishi hannu ya yi dan yana ganin ai duk sa'annin juna ne su.

Miƙawa Irfan da Akil ma hannu ya yi suka gaisa, Abba ne ya fara cewa sun zo ɗaukar Akila ce, cikin nuna ko in kula ya ce "Akila ai matar aure ce, ba ta yadda za'ayi ta fita ba tare da izinin Aseef ba, amma kuyi hakuri idan Aseef ɗin ya farka zan gaya mishi ya kawo muku ita har gida ku ganta". Har cikin ransa Abba ya ji daɗi da ƴarsa ta auri zaɓinta, amma kuma sai ya ɓoye tare da ɗaure fuska yana faɗin "Ban gane matar aure ba? Waye ya isa ya ɗaurawa ƴata aure ba da izinina ba? Ai hakan sam ba zai yiwu ba, idan ma an ɗaura dole a warware kuma bai ma ɗauru ba tun da ni ubanta ban bayar ba, kuma babu waliyi".

Karɓar zancen Abbi ya yi da cewa "Tayaya za'ayi ma ace an ɗaurawa yarinya aure ba tare da izinin iyayenta ba? Wannan aure bai yiwu ba, kawai ku bamu ƴarmu mu tafi dan ba hanayina ko wani abin bane ya kawo mu". Akil dai shiru ya zuba musu idanu, dan shi ransa fes kanwarsa ta auri zaɓin ranta, shi ai sun faranta mishi rai, yadda yake mugun kaunar Heartbeat ɗin nan, ai baya son ɓacin ranta sam, so dan haka shi bama zai saka baki ba.

Shiru Areef ya yi yana jinsu suna ta surfa zance son ransu, su dai dole a kira musu Akila su tafi da ita, ya rasa me zai ce musu bawan Allah, sai kawai ya bisu da ido, shi dai ba zai iya yi musu rashin kunya ba, ba kuma zai gaya musu magana mara daɗi ba, shiyasa ya bisu da idanu kawai.

Tamkar saukar aradu suka ji sexy voice ɗin Lion yana faɗin "Ina da bukar ku yi mini shiru ban son hayaniya!" Ya yi maganar yana saukowa kasan, bin shi da idanu suka yi har ya sauko zuwa kasan, daddyn Rimsha tare da Imran ma a tare suka sauko, Jehan da Rimsha suma a tare suka sauko.

Nufar hanyar fita daga palon Lion ɗin ya yi ba tare da ya sake ganin in da suke ba. "Lion sun zo suna son tafiya da matar Aseef ne fa". Cewar Areef, tamkar bai ji me Areef ɗin ya faɗa ba ya cigaba da tafiyarsa.

Sai da ya kai bakin kofar fita daga palon sannan ya ce "To ba sai su ɗauke ɗin in gani ba". Ya kai karshen maganar yana ƙoƙarin sa kai ya fita. "Wai taya za'ayi ace kun ɗaurawa yarinya aure ba tare da yardar iyayenta bane? To ku sani auren bai yiwu ba, dan bata da waliyi, dole ku bamu ƴarmu". Cewar Abbi, Juyowa Lion ɗin ya yi yana kare wa Abbin kallo, ganin bai ma ga in da zai mara a face ɗin Abbin bane yasa ya kawar da kallonsa, dan a cewarsa idan ya mari Abbin zai suma ko mutuwa.

"Zaku iya tafiya dan bana son abin da zai takurawa Aseef a yanzu, yarinya kuma ta riga da ta yi aure, idan kunga ta fita daga gidan nan, to ita da mijinta ne!". Shi ne abin da Lion ɗin ya ce da su. "Wlh ba zai yiwu ba, dole sai kun bamu ƴar mu, babu wanda ya isa ya tsara mana ga abin da zamu yi a rayuwarmu, dan haka baku isa ku ce ga abin da zamu yi ko abin da ƴarmu zata yi ba". Cewar Abbi. Shiru ya yi bai sake magana ba, dan shi maganarsa mai tsada ce, ba mai arha da zai tsaya bada amsa a kan komai da suka faɗa ba.

Ganin Abin yana neman kwaɓewa ne yasa Areef ya yi saurin cewa "Please uncles ku kwantar da hankakinku mu fahimci juna, komai ai mai sauki ne". Cikin kunar rai Abba ya ce "Babu zancen mu kwantar da hankali a nan". Dan ba karya ya ji babu daɗi abin da Lion ya yi musu, a cewar Abban ai ya rainasu ne, basu san cewa shi a haka yake ɗaukar kowa bama, su yama yi musu da sauki dan sun bawa ɗan uwansa abin da ya fi so, da wasu can ne wlh basu isa su shigo cikin gidansa har cikin palo suce zasu saka magana a saman nasa maganar ba, wane kaniyarsu, amma su koba komai sanadiyarsu Aseef zai yi farinciki, dama kuma shi Lion baya rena alkhari kuma baya mantawa, shiyasa ya ɗauki zane ɗaya daga cikin wanda Rimsha ta yi mishi ya ajiye a wajensa dan baya rena alkhari kuma baya mantawa.

Abbi zai sake yin magana daddyn Rimsha ya yi saurin taresu cikin yaren Tatar wato yaren mahaifiyarsu Naurat dan ma kada su Rimsha su ji abin da zai faɗa, "Yaya Babba dan Allah ya isa haka, kuyi hakuri kada ku sanya wannan abin a ranku, kada ku yi abin ya zama wani babban case, waƴan nan da kuke gani haka suke, haka Allah ya yi su, idan kuka matsa kune zaku sha wahala, dan baku da wani abin da zaku yi sai hakuri, dan Allah ku bar maganar nan haka ya isa, ku yi hakuri, ni Hossain nina basu auren AKila, ni ne waliyinta, ko ban kai na aurar da ƴarka bane yaya?". Babbar magana, zuba mishi idanu suka yi sun kasa magana.

Miƙewa daddyn Jelly ya yi yana faɗin "Yaya Hossain, dama na faɗa musu wlh kai ne His excellency Nawazudden, amma shi ne ka ce mana ba kai bane ko?". Ɗan kawar da kansa ya yi yana faɗin "Yanzu ma dan farincikin Aseef yasa na gaya muku ni ne ai, yanzu tun da kunsan waliyin AKila sai ku kyale mini Aseef na ya huta, kun kusa kashe mini shi, da shikenan ya mutu fa, da kuwa sai kun biya dan da ba zan yafe muku ba!" Ya yi maganar on a serious note.

Abba da Abbi dai sun kasa yin magana, dan kuwa sun rasa da bakin da zasu fara yi mishi magana har su nemi gafararsa, shi kuma Lion wucewa ya yi ya fita abinsa.

Ganin su Abbi sun kasa yin magana ne yasa ya ce "Yaya lafiya kuwa?" Shiru suka yi ba wanda ya yi magana, karisowa kusa da su ya yi yana sake tambayarsu me yasa suka yi shiru, su kuwa abin da ya faru a baya ne ya dawo musu sabo, kallon Jehan da Rimsha dake tsaye ya yi cikin harshen turanci ya ce "Kuzo ga bappanunku yau kam na bayyana muku su". Kallon Rimsha Jehan ta yi da mamaki, ita kuwa ko a jikinta, dan idan bamu manta ba kafin daddy ya kowa Washington DC ya gaya mata Imran yayanta ne, dan haka ta sani, sai bata wani damu ba.

Karisowa wajen suka yi, ita dai Jehan tana ta mamaki, wai dama daddynsu yana da ƴan uwa ne? Ita ta ɗauka ma shi maraya ne bashi da kowa kamar yadda mutane suke faɗe, yau dai ga shi ya nuna musu su.

Kusa da Abbi Rimsha ta zo ta zauna dan shi ta sani, shi ne take zuwa gidansa da Imran, bata san Abba ba, rungumeta Abbin ya yi tamkar zai yi kuka, ita kuwa Jehan taki zuwa wajen kowa, ta tsaya a tsakiyar palon tana binsu da idanu, hannu Abba ya miƙa mata a kan ta zo, ɗan juyawa ta yi dan ta kalli daddynta caraf suka haɗa ido da Areef, kashe mata ido ɗaya ya yi yana faɗin "Me kike wani kallona? Da wani idonki a wajen". Guntun tsaki ta ja kafin ta karisa wajen Abban tana faɗin "To me zan kallah a tattare da kai dama, mummunar fuska ko me?". Daddynta ne ya yi saurin cewa "Ke baby wlh ki kiyayeni, bai fiki kyau bane da zaki ce mishi mummuna?".

Murmushi Areef ɗin ya yi kafin ya ce "Yes my uncle i love you so much, gaya mata na fita kyau, ita ma ta sani ai, har da satar kallona take yi taga fine guy, bata san ina ganin duk abin da take yi ba ne ai?". Turo baki ta yi tare da miƙewa daga wajen Abban zata bar palon dan sun ɓata mata rai, cikin sauri daddyn Jelly ya riƙota yana faɗin "Rabu da su hai, sun taɓa ganin namiji yafi mace kyau ne? Ai ke karshe ce a kyau, baki ga idonsa kamar ball bane?".

Ɗan yake ta yi kafin ta ce "Yes nima ga bappana zai karɓa mini". Rimsha ne ta karɓi zancen da cewa "Wlh bappa yaya Areef ya fita kyau, jiba kanta kato fa, shi kuma nasa daidai, ga gashinta kamar na Gwaggo ba kyau, idonta kamar na......". Bata kai karshen ba daddyn Jelly ya wurga mata harara yana faɗin "Saboda tafiki kyau ne kike kishi ko?".

"No uncle gaskiya baby bata fi Our Queen kyau ba, ita fa Queen ita kaɗai ce, daga ita babu wata kyakkyawa a duniya, kawai fa babyn nan dan ta yi sa'a ne nake kulata, kuma ta yi sa'a ta ɗan yi kama da uncle shi ne ta yi kyau". Cewar Areef, miƙewa Jehan ɗin ta yi fuuuu kamar wata kunfa ta fita daga palon tana faɗin zata kama Rismha ne, wlh sai ta cire mata hakoran gaba, ta zama bata da hakori, dariya Abbi ya yi yana jin tsantsar farinciki a ransa.

Nisawa Abba ya yi tare da fara ƙoƙarin bawa daddyn Rimsha hakuri, dakatar da shi daddyn ya yi yana faɗin "Komai ya wuce, dan haka a barshi a ya wucen kawai, please kada ku dawo da komai, bana son tuna komai, ni har ga Allah na yafe muku, so ku manta da komai". Jinjina mishi kai suka yi, Akil da Irfan dai sai binsu da idanu kawai suke yi, shi kuma Imran tun ɗazun ya fita amsa wayar jelly da ta kira shi da layin Ammie, dan har yanzu bata da waya.

Hira suka fara zubawa, sam daddyn Rimsha yaki yarda su dawo mishi da abin da ya wuce, sun so ya gaya musu a ina ya yi rayuwa, bayan barinsa gida ina ya je, amma ya nuna sam baya son maganar, dan haka sai suka kyale shi sai zuwa gaba idan ya saki jiki da su sosai, sai su tambaye shi.

A ɓangaren cikin bedroom na Lion kuwa, wato wajen Aseef, su Lion suna fita Akila ta matso kusa da mijin nata, dai'dai saitin kunnensa ta kai ɗan bakinta, a hankali ta fara yi mishi magana kamar mai raɗa. "My shagwaɓati, please ka tashi kaji? Ka tashi ka kalleni in ganka, ina kewar muryarka, tun fa da safe da naji ban sake ji ba, kana so ne na yi rashin lafiya? To ni dai gaskiya ka tashi ko nayi maka kuka, kuma idan na fara kuka ba zan yi shiru ba, ina son jin shagwaɓarka mijina, ni gaskiya ka tashi". Da yake Lion ya sanar da Areef ya ɗaura musu aure a gabanta tana ji, shi ne ta san cewa mijinta ne, ba dan haka ba bazata sani ba, dan a lokacin da aka ɗaura auren tana sume bata sani ba, bawa Areef labari da ya yi ne ta ji.

Ɗan kwanto da kanta a saman kirjinsa ta yi tana mai kara cigaba da magana "Wai ba zaka tashi ba har sai na fara kukan gaske ne? Yanzu fa kai mallakina ne, nima


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login