Showing 48001 words to 51000 words out of 359620 words
gaya maki ba wanda yake zama a kujerar Dr sai shi kaɗai, dan haka ki dawo wajen da patient ke zama ki zauna, idan ba haka ba ranki in ya yi dubu zai ɓaci yanzun nan". Har lokacin Aafia bata ɗago ta kalleta ba, sai ma ɗauko wayarta da ta yi tana latsawa.
Bahijja ta fusata iya fusata, tun da ta kalli Aafia dama ta ji ta tsaneta, bata sonta, tana tsoron ta ce zata yi mata wani abu kuma, ya zamana suna da kusanci sosai da Dr ya yi mata hukunci, hakan yasa ta zauna a patient chair tana cika tana batsewa, ba dan ta so ba ta hakura.
Ita kuwa Aafia ko a jininta, ranta fes, sai ma massage ta yi wa Nawid akan tana son shan black tea kafin ya shigo, yana ganin massage ɗin shi ma ya yi wa Bahijja massage a kan ta haɗawa matarsa Black tea ta bata kafin ya zo.
Ba ƙaramin razana ta yi ba lokacin data ga massage ɗin nasa, wai a haɗa wa matarsa tea, kenan Aafia matar sa ce? Ta tambayi kanta, "Kai ina ba matarsa bace, sai dai wadda yake son aura, tun da bamu ji ance ya yi aure ba" ta sake faɗa a cikin zuciyarta tare da miƙewa ta nufi wajen wani kyakkyawar show glass dake cikin office ɗin, kayan tea ne kala kala a ciki.
Ruwan zafi ta fara jonawa a hitter, kafin ta haɗa komai da zata buƙata a cikin cup mai shegen kyau.
Duk abin da take yi Aafia tana jinta, kawai ɗagowa ta kalleta ne tana ganin kamar bata kai wannan matsayi ba, ta fi karfi kula irinsu Bahijja, dama idan baku mance wace ce Aafia ba, kun san ta akwai ta da jiji da kai, abin da ya faru da ita ne ma yasa ta yi sanyi, ta dawo kamar ba ita ba.
Cikin girmamawa Bahijja ta miƙo mata cup ɗin tea ɗin bayan ta kammala haɗawa kenan, bata karɓa ba, sai ta nuna mata saman table ɗin a kan ta ajiye a wajen, hakan ma sai da ta ɗauki ƴan sakanni kafin ta nuna mata ɗin.
Haushi tamkar Bahijja ta yanka mata mari, wata ƴar siririya da ita kamar bulala ƴar yarinya da ita Dr ya kawota tana yi masu iskanci, cewar Bahijja a cikin zuciyarta.
Ba yadda zata yi, haka ta ajiye mata tare da komawa mazauninta, ta zauna tana mai huci, ko kala Aafia bata ce da ita ba.
Suna a haka har aka yi sallar mangariba da isha, a cikin office ɗin Aafia ta yi sallah kasan cewar akwai komai a ciki, ita kuma Bahijja nata office ɗin na P.A da yake kafin ka shigo cikin office ɗin Nawid ɗin, to a nan nata office ɗin yake, a nan ta je ta yi sallah ta dawo, domin Nawid ya ce ta kula mashi da mata sai ya gama aikinsa ya dawo sannan ta wuce, kada ta kuskura ko ƙuda ya taɓa mashi mata............... To fa🤔
Suna zaune shiru kamar kura me, Aafia ta jingina kai da jikin kujerar tare da lumshe idanu kamar mai barci, ita kuma Bahijja tana ta kare mata kallo, tana son taga dame Aafia ta fita ne?. Mata kenan matsalar mu kenan, kowa so take a ce tafi kowa, da zarar mata sun haɗu zasu fara kallon junansu dan suka da me wata tafi su, kowa da irin rayuwarsa, kowa da kalar baiwar da Allah ya yi Mashi, naki baiwar daban, ita ma tata daban, wata kilama baiwarki ta fi tata tsada, kowa da abin da yafi a halitta da kuma rayuwarsa, so bai kamata ki haɗa kanki da kowa ba, ki sanya a zuciyarki ke fa ta dabance, ke kaɗai ce babu irin ki, sai ki zauna lafiya, kada ki duba kowa, ki sanya kawai ko kin duba ba irinki bace, ki kasance mai duba rayuwarki kullun ba na wasu ba, hakan ne zai baki damar ki zauna lafiya cikin kwanciyar hankali, Allah yasa mu gyara.
Suna a haka har Dr ya shigo, jin shigowarsa yasa Bahijja ta ɗago kai tana bin shi da kallo, ita kuma Aafia bata motsa ba.
"Mrs Nawid kin yi barci ne?". Sai lokacin ta waro idanunta a kansa. Cool murmushi ya sakar mata "Am sorry na barki zaune ko? Amin afuwa ba zan kara ba, aikin ne ya bani wahala yau, yanzu dai muje gida ko? Dan naga har karfe 9 ta yi". Ya kai karshen maganar yana zame hand gloves da suke hannayensa.
"Yaya Nawid jikina ya mutu barci nake ji, ba zan iya tashi ba fa". Tayi maganar cikin sanyin murya.
Tamkar wasu Tv haka Bahijja ta mai da su, abin haushi kamar ta shaƙe Aafia har sai ta mutu sannan ta saketa take ji, shi kuwa tamkar bai ga Bahijja ɗin ba, ta matarsa kawai yake yi.
"To idan ma ba zaki iya tashi ba, ai ni zan iya ɗaukarki cak ko?". Yana magana yana nufar in da take. "Yaya Nawid ina da nauyi fa". Ƴar dariya ya yi kafin ya ce "A hakan? Yadda kike yar siririyar nan? To idan ma kina da nauyi, ni kuma ina da karfi" Gyaɗa mashi kai ta yi alamar e tana da nauyi duk da take ƴar siririyar.
"To bari na gwada maki ki gani ina da karfi". Hannu yasa yana ƙoƙarin ɗaukarta, cikin sauri ta ce "Wasa nake yi, zan iya tafiya". Girgiza kai ya yi yana faɗin "A'a ni ban yarda ba, dan haka kawai ɗaukarki zanyi gara ma ki tsaya". Yau Bahijja dai taga ikon Allah, tambayar kanta take yi, dama Dr haka yake? Dama yana dariya? Dama yana magana har haka? Wato sune dama yake ɗaurewa fuska kenan? Lallai yau taga abin mamaki.
Shi kuwa ɗaukarta ya yi kamar yadda ya faɗa suka nufi waje, daidai zai fita ya ce da Bahijja ta rufe mashi office da duk abin da ya dace shi ya wuce gida, daga haka ya fice da ita a kafaɗarsa. Da Ido kawai Bahijja ke binsu da shi har suka fita.
Tun da ya fito duk in da ya wuce nurses sai sun kalle shi sun sake waigawa, ba ƙaramin mamaki ya basu ba, sai tambayar kansu suke yi akan yaushe ya yi aure, dayawa daga cikinsu dai sun san bashi da kanwa, shi kaɗai ne wajen Umminsa, to a ina ya samo wannan yarinyar kuma?.
Shi kam bai bi ta kan kowa ba, kai tsaye motarsa ya wuce da ita, sai ɓoye fuska na rashin kunya take yi. A gidan gaba ya zaunar da ita, ya zagayo mazaunin driver ya shiga.
Kasancewar parking space ɗin akwai ɗan duhu, babu haske sosai, sai bai kunna hasken motar ba, ya lallaɓa a cikin duhu ya jawota jikinsa, sosai ya matseta tare da zura hannunsa ta samar wuyar rigarta zuwa ciki.
Bata hana shi ba, kuma bata tashi daga jikin nasa ba, breast nata ya kama ya fara shafasu a hankali yana wasa da su, hannayenta tasa dukka biyu ta rungumo shi, hakan ba ƙaramin daɗi ya yi mashi ba, yanzu ta yi accepted na shi kenan, nan take ya fara wasa da ita sosai son ranshi, bata hana shi ba kuma bata taya shi ba, ta yi shiru tana sauraronsa.
Har sai da agogon hannunsa ta buga masu karfe 10 ya yi, sannan ya saketa yana mai da numfashi tare da lumshe idanu, ita ma sauke numfashi take yi a hankali hankali, alamar ta karɓi saƙon nasa.
Sun ɗauki ƴan mintoci a haka, wadda a kalla zasu kai 10mins. Da kyar ya iya jan motar suka nufi gida.
WANNAN KENAN A ƁANGAREN SU A'AFIA, BARI MU LEƘA ƁANGAREN SU LION WATA KILA KAFIN MU DAWO SU AAFIA SUN ISA GIDA.
GIDAN LION💋
Yau dai Akila da Rimsha sun sha hira kamar ba gobe. Sai misalin karfe 2 da rabi Rimsha ta ce da Akila ta shiga ɗaki ta kwanta ta jira ta, bari ta kaiwa Lion abinci, to ta amsa mata da shi tare da miƙewa ta nufi cikin ɗakin.
Ita kuma ta nufi Kitchen dan ɗaukar abincin. Kamar kullum, wanke hannayenta ta fara yi kafin tazo ta ɗauki abincin, tana tafiya tana addu'ar Allah yasa ta kai lafiya ta kuma dawo lafiya.
A bakin kofar ta tsaya ta yo sallama, daga ciki Areef ya amsa sallamar tata tare da bata izinin shigowa, tattara dukkan natsuwar da Allah ya bata ta yi, ta kutsa cikin ɗakin tana kara yi mashi sallama.
Imran, Areef, kwance suke a saman gadon Lion suna hira, while shi kuma oga yana zaune saman sofa yana bincike a cikin laptop nasa.
In da ta saba ajiye mashi abincin ta nufa, a nutse ta ajiye mashi tare da ɗagowa ta gaida Areef da Imran, da fara'a suka amsa, dirowa kasa Imran ya yi yana faɗin bari ya je ya ɗauko mata abincinta daga gidan Akil, dan tun ɗazun AKil ya yi mashi massage akan Umaisha ta gama abinci ya zo ya ɗauka mata.
Cikin zolaya Areef ya ce zai bishi domin yau ya kalli bakin ƴan uwan Prof da bai sani ba, a zafafe Lion ya ɗago da dara daran blue eyes nasa, tare da wurga mashi wani mugun kallo, alamar baka da hankali ne zaka fita?. Dariya ya kwashe da shi, dama dan saboda Lion ɗin ya ɗago ya yi maganar, yasan ba ta yadda za'ayi ya fita da wannan ciwon nasa haka, amma kuma kafarsa na bala'in kaikayi, yana burin fita, har tausayawa kansa yake yi akan idan ya samu lafiya kalar yawon da zai yi, sai ya kewaye gabaɗaya States na Naija, zai je wajajen tarihi da saurasu, har ya gama tsara kalar yawon da zai yi, addu'ar samun lafiya kawai yanzu yake yi........( To fa lallai Areef ya shirya karewa kasarmu kallo)
Shi dai Imran bai ce komai ba, ya sa kai ya wuce abinsa, ita kuma Rimsha zama ta yi tana jiran Oga ya sauƙo ta zuba mashi abincin.
Sai da ya ɗauki almost 30 mins yana latsa laptop ɗin, ita kuma tana zaune shiru. A hankali cikin natsuwa ya ɗaura laptop ɗin saman hannun sofa tare da miƙewa ya sauƙo kasa, a in da ya saba zama ya zauna.
Ta kasar ido ta saci kallonsa, pajama ce launin fara tas a jikinsa, ya kulle gashin kan nan nasa a bayan wuyarsa, wannan fitinannen daddaɗar kamshin nasa dai kamar kullun take, ba canzawa.
Yana zama shima Areef ya sauƙo daga saman gadon, ya kariso in da suke yana Murmushi. Abincin ta fara zuba mashi kamar yadda ta saba.
"Our Queen zuba mini nima, amma tare zaki zuba mana dake". Cewar Areef, ya yi maganar yana zama kusa da ɗan uwan nasa, shima dai pajama ash color ce a jikinsa.
"Yaya Areef ni ai ban iya cin kalar abincinku ba". Ta yi maganar tana turawa Lion abincinsa da ta gama zuba mashi.
Kwaikwayon voice nata ya yi yana faɗin "To ai koya miki ci zanyi my Rimsha". Bata san time da dariya ya kubce mata ba, ba iya basajan wajen aiki kawai ya iya ba, ashe har da kwaikwayon murya ya iya, dan kuwa sak siririn voice ɗin nan nata ya yi, shi dai Lion tamkar babu shi a cikin ɗakin, abincinsa kawai yake ci cikin kwanciyar hankali.
"Dariyar me kike yi mini? Dan na kwaikwayi zazzakar muryar nan taki ko?". Girgiza mashi kai ta yi alamar a'a. "Kinsan me my Rimsha?". A'a ta bashi amsa.
"Kina da murya mai shegen daɗi, idan kina magana bana son ki daina, just like uncle Musharraf voice naki yake, shima haka voice nasa yake da zaki, sai dai fa kina magana a sanyaye kamar Lion, ke da Lion sam baku son buɗe baki ku yi magana sosai, i don't know why, ko dai bakinku na yi maku zafi ne idan kuka ɗaga murya?". Yana magana yana satar kallon ɗan uwan nasa, wadda tamkar babu shi a cikin ɗakin.
Zuba mashi abincin ta yi ta tura mashi a gabansa tana faɗin "Yaya Areef nifa wlh kawai ban san ya akayi maganata take a haka ba".
Sai da ya bari ta gama zu ba masu abincin, ta turo masu, sannan ya kira Aseef video call dan su takurawa Lion, yau sai sun sanya shi ya canza magana, dole ya barta ta koma school, yarinya yar karama ace ba zata rinƙa zuwa school ba, cutar ta zaayi.
Ya danna video call ɗin yana faɗin "A'a akwai dalili dai, sai ku rinƙa magana kamar baku son yi?".
Bugu ɗaya Aseef ya katse kiran ya kirashi, hakan zai tabbar maka da cewa haɗa baki suka yi, sun shiryawa Lion kitimurmura, kuma da alama da wuya ya tsallake masu yau, dan sune rauninsa dama.
"Da gaske yaya Areef......" Bata kai karshen maganar ba zazzaƙar sexy voice nasa ya daki dodan kunnenta. "Get out". Sun cika mashi kunne da surutu, ba damar ya kori Areef, amma ita yana da damar korinta.
Cikin sauri ta miƙe ta nufi waje, tana jiyo voice ɗin Areef yana faɗin "After 30 mins ki zo ki kwashe kayan abincin". Okey ta amsa da shi tare da ficewa abinta.
Kada ku mance da Turanci suke magana.
Duk abin da ya faru, Aseef yana jinsu, dan Areef ya yi picking call ɗin. Jawo ɗan ƙaramin kyakkyawar table dake wajen ya yi tare da ɗaura wayar, ya jingina wayar da tissue pack, ta yadda Aseef zai ji daɗin ganinsu su biyun dukka da kyau.
"My bloods wlh kewarku zata iya yi mini illah fa, please ku dawo ko kuma ni na taho, saura mani Exam har guda huɗu fa, ni gaskiya almost 2 weeks suka rage ba zan iya jira ba, ya yi mini nisa".
Lion bai san time da Areef ya kira Aseef ɗin ba, jin zazzakar murya ɗan uwan nasa yasa shi ya ɗago blue eyes nasa daga kan abincin da yake ci zuwa kan wayar.
Zubawa Aseef ɗin idanu ya yi yana kallon yar ramar da ya yi, da alama dai yana yawan tunanin ƴan uwan nasa sosai, Allah sarki bawan Allah, tun da suka taso basu taɓa rabuwa su yi nisa har haka ba sai wannan karon, duk ya shiga damuwa sosai, dan ma Musharraf na rage mashi damuwar, amma duk da haka sai da damuwar ta fito ta hanyar sanya shi rama.
"Our pleasure muma muna kewar ka sosai, ban taɓa shiga damuwa sosai irin na wannan karon ba, seriously tamkar na rasa wani ɓangare na jikina haka nake ji, amma dai ka kammala Exam ɗin, 2 weeks ai kamar yau ne". Cewar Lion kenan, kuma tun da yake sai yau ya taɓa yin magana makamanciyar hakan, ya yi ne kuma dan ya kwantarwa da ɗan uwan nasa hankali ya samu ya natsu ya rubuta Exams nasa cikin kwanciyar hankali, sannan kuma har ga Allah yana kewar ɗan uwana nasa over, abin na damunsa a rai, dan dai kawai bai da yawan magana ne yasa ba zaka fahimci hakan ba.
Nisawa Areef ya yi kafin ya ce "Ni ba zan iya misilta kewarka da nake yi ba my blood, baki ba zai iya faɗa ba, a kullun ina ji tamkar na yi fiffige kawai na ganni a tare da kai". Turo baki ya yi zai fara yi masu shagwaɓa.
Har lokacin Lion bai ɗauke idanunsa daga kan wayar ba, ji yake tamkar ya sanya hannu ya fito da ɗan uwan nasa ta cikin wayar su rungumi juna. "Zaka fara yi mana shagwaɓar kenan ko?" Cewar Areef.
"Ni ba wani shagwaɓa da zan yi maku, yanzu dai Lion ina son kayi mini wata alfarma ne ka ji?". Shiru bai yi magana ba, sai dai ya ɗaga mashi gera ɗaya alamar ya ji.
Shiru shima Aseef ɗin ya yi ya rasa ta ina zai fara. "Aseef abin da nake so da kai shi ne, ka daina yawan tunaninmu da kake yi, bana son ganinka a ramen nan, idan kana son sanya ni cikin damuwa kuma shikenan". Cewar Lion ya yi maganar yana mai da spoon ɗin hannunsa ya ajiye a cikin plate ɗin abincin.
"To Shikenan Lion na yi alkawarin zai dai'na duk wata tunani, zan daure yanzu dai please my blood ina son ka bar Rimsha ta rinƙa zuwa school, ma'ana ta daina yi muku aikin safe, ya zamana iya na rana da dare ne kawai zata rinƙa yi muku, kaga yarinya ce, idan aka yi mata wasa da karatu a yanzu to za'a canzawa rayuwarta akalar shi ne, please ni zakayi wa ba kowa ba, idan ka yi hakan zan yi murna sosai wlh". Ya kai karshen maganar cikin sigar shagwaɓa.
Ɗaukar spoon ɗin da Lion ɗin ya ajiye Areef ya yi, ɗibar abincin ya yi tare da kawo wa ɗan uwan nasa a bakinsa, buɗe baki Lion ɗin ya yi ya karɓa yana mai dawo da kallonsa kan Areef ɗin, kamar zai yi magana sai kuma ya fasa, cigaba da bashi abincin a baki Areef ɗin ya yi tamkar wasu mata da miji.
Kuka Aseef ya fara yi musu a kan lallai shi gobe zai zo, ya za'ayi yanzu shi ba mai bashi abinci a baki, shi wlh ba zai yarda ba, ya gaji, yanzu ba mai bashi first spoon fa.
Girgiza kai Lion ya yi, Aseef sai Allah, yana bala'in kaunarsu fiye da tunanin mai tunani.
Shi kuma Areef ɗebo abincin ya yi tare da kawowa saitin wayar yana faɗin "Ɗan nema to maza buɗe bakinka na zuba maka, ba dai first spoon ba? To ga shi nan, har ma da last spoon zaka samu, ɗan babynmu, auntar TRIPLETS, sweetien daddy, pleasure Lion, shagwaɓati kuma damuwati na, ciwon kan Uncle T, ciwon cikin Uncle Herry, matsalar Jonh, addabawa rayuwar Jay, wadda mummy ta fi so, dukka kai kaɗai maza buɗe baki, yi sauri......" Bai kai karshen maganar ba ya yi shiru sakamakon damko gashin kansa da Lion ya yi, da ɗan karfi ya ja mashi gashin nasa.
"Wash Lion me nayi maka kuma? Ko mugunta zaka yi mini ne nima, kamar yadda kake yi wa sauran mutane". Shiru ya ɗan yi kafin ya ce "Me pleasure na ya yi muku da zaka ce mashi ciwon kan Uncle T, ciwon cikin Uncle Herry, me yake yi masu da ya zama ciwon kansu? Me yasa zaka zage shi?". Cewar Lion.
"Kai fa Lion ka iya mugunta, kuma baka son gaskiya, ai ka sani, waye Aseef ya raina biyun Uncle T, ba dole ya rinƙa sanyawa uncle T ɗin ciwon kai