Showing 156001 words to 159000 words out of 359620 words

Chapter 53 - Triplets Book 3 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2025

akan sun sayar da rayukansu, ba su tsoron a mutu ko ayi rai, jininsu a tafashe yake a ko da yaushe, sun sami horo iya horo na wuce misali.

Rai a matukar ɓace ya yage rigar jikinsa domin tana takura mashi wajen jibgarsu yadda ya kamata, haka ya cigaba da ba su a jikinsu.

Shi kuma Aseef sarkin tausayi, bai ma damu da wani hali Areef ɗin yake ciki ba, bayan kuma shi ya jangwalo faɗar, miƙe wa ya yi abinsa ya riƙo hannunta yana yi mata sannu. Duk ilahirin jikinta sai kerma yake yi, dama a tsorace take, ganin suna faɗa kuma yasa ta kara tsorata sosai, ta fara kuka.

Hannunta ya ja suka karisa wajen motarsu yana faɗin "Kada ki ji komai tsab Areef ɗina zai yi masu dukan mutuwa, ke dai yanzu shiga mota bari ya gama jibgansu ya zo mu maida ke gidanku..." Bai kai karshen maganar ba ya ga an wurgo mutun kusa da shi, ai kuwa a guje shima ya shige cikin mota yana faɗin "Ya Subhanallah, Allah ka rufamin asiri da irin wannan duka na Areef, ka kama mutane sai jibga kake yi kamar an aiko ka, ni dai ina daga ciki, ka tabbatar ka ba su jikinsu sosai kafin ka zo mu wuce, amma fa ka yi sauri dan ina kewar My Rimsha wlh, zan je na kirata video call". Da yake ita Jehan ɗin ta ɗan bugu kuma ga tashin hankali da take ci, sai bata ma sauraron abin da suke faɗe, ta dafe kanta da hannayenta dukka biyu, ban da wash babu wani abin da take furtawa, kan nata ne dama ya bugu da jikin motar tasu.

Lilis Areef ya yi wa ƴan'sandan kafin ya taho ya shiga cikin motar, a kujerar gaba ya zauna yana ɗan dafe wajen ciwonsa, dan ɗaga hannunsa da ya yi ta yin nan ya ɗan ji zafin ciwon ba kaɗan ba.

Yana shiga Aseef ya ja motar suka koma gida, da yake ma basu da nisa da gidan, daga in da suke suna hangen gidan, dan fitowarsu kenan suka ci karo da ita. Sai da suka shiga cikin gida kuma Aseef ɗin ya ce "Areef ai da mun fara mayar da ita gidansu kafin mu dawo ko?" Fita daga cikin motar Areef ɗin ya yi ba tare da ya yi magana ba, burinsa kawai ya karisa cikin gida ya shafa maganinsa ya kuma sha na shansa dan ya fama ciwon nasa.

Dawo da kallonsa kanta ya yi, har lokacin tana dafe da kanta ta yi shiru da alama bata dawo dai'dai ba, "Ni ba zan ji daɗin kai ki gida ni kaɗai ba, amma ki zo mu shiga ciki, idan Areef ya ɗan ji sauki sai mu kai ki gida, daga nan dai zuwa 9 zai ji dai'dai In Sha Allah, yanzu ki fito mu je ciki". Shiru bata amsa mishi ba, kada ku manta da turanci yake magana. Ganin bata amsa bane yasa ya fito tare da buɗe gidan bayan ya riƙo hannunta zuwa cikin gida, da kyar ta iya fitowa daga cikin motar, ba musu ta bi shi kamar wasu yaya da kanwa, kai tsaye ɗakin da su Imran suka baro a sama ya kai ta, da farko ya so kaita ɗakin Rimsha, sai kuma ya tuna Rimsha daban ce basu haɗa ta da kowa, dan haka sai ya kaita tsohon ɗakin Imran da suka fara zama.

A bakin gado ya zaunar da ita, sai kallonta yake yi, shi dai ko ma yaya yasan wannan dai tabbas tana da alaƙa da uncle Hosain ɗinsa, dan sun yi kama over, amma dai bari Areef ya samu ya dawo dai'dai shi ma ya ganta dole zai ga kamannin, sai tunane tunane yake yi, bai ma san lokacin da ta kwanta ba sai dai ɗago kai ya yi ya ganta tana sharar barcin wahala, ɗago dara daran brawn eyes nasa ya yi ya sauƙesu a kan Ac dake ɗakin, rage mata gudun ya yi kafin ya rufa mata bargo zuwa cikinta ya juya ya fita zuwa wajen Areef dan ya ga a wani hali yake ciki.

Ɗakin Lion ya nufa, Areef ɗin na toilet yana wanka, ga A box a saman bedside drawer ya ajiye, da alama ya yi dressing na ciwon nasa ne kafin ya shiga wanka, saman bed ya haye tare da jawo wayarsa dan ya kira Lion ya zuba mishi shagwaɓa kaɗan, ya takura mishi. Har zai fara kiran number kuma sai ya tuna Heartbeat na can tana jiran zuwansu, dan haka sai ya fasa kiran Lion ɗin ya kirata dan ya sanar da ita sai gobe da safe zasu zo, tun da Areef ya ɗan ji ciwo.

Bugu ɗaya ta ɗauka cikin zumuɗi a shagwaɓe ta fara magana "Hello my shagwaɓati kun iso ne?" Dogon numfashi ya ja tare da saukewa a hankali, yadda ta yi maganar ta tafi da shi ba kaɗan ba, "Heartbeat ki yi hakuri ba zamu sami damar zuwa yau ba sai gobe". Kuka ta saka mishi a kan lallai ita wlh ba zata yarda ba, in dai yana son farincikinta to yazo yanzun nan, shiru ya yi yana sauraron shagwaɓar da take zuba mishi har sai da ta kai aya, sannan ya fara magana a nutse "Heartbeat muna hanyar zuwa fa muka sami accident, mun buge wata ƴarinya ce wadda tasa dole muka juyo zuwa gida, so please ki yi hakuri zuwa gobe kinji ko my rigimati?".

Zubur ta miƙe daga kwanciyar da take tana dafe kirji tare da zaro idanu waje, "Amma dai baku ji ciwo bako?" Ta tambaya hankali a tashe, "Calm down My heartbeat, babu abin da ya same mu, Allah ya tsare yarinyar ce kawai muka ɗan jiwa ciwo, ita ma ba sosai bane, shi ne muka dawo gida dan mu dubata". Shiru ta ɗan yi kafin ta ce "Ya yarinyar take to? Babban mata ce ko dai karama?". Da yake shi bai san kishin mata ya yake ba, sai ya zauna ya zayyana mata yadda ya ga Jehan ɗin tas, budurwa ce kamar ita ga kuma irin kayan da ta sanya, kyakkyawace sosai mai kama da uncle ɗinsa, da sauransu. Kuka ta sa mishi tana faɗin Wlh sun ɓata kada ya sake kiranta tun da har da riƙe irin kayan da yarinyar ta saka, kenan ma wato ya yi ta kallon yarinyar ko? To wlh ba zata yafe mishi kallon wata da ya yi ba, tana kuka tana surutai, shi kam yau yaga bala'i, dan bai san mata haka suke da kishi ba, dafe kansa ya yi tare da fara rarrashinta dan bashi da mafita.

Kin yarda ta yi ta katse kiranta tana kuka hawaye bibbiyu, sake kiran nata ya yi, kin ɗagawa ta yi, ta yi fushi da shi, tamkar zai yi kuka, duk ta rikita shi, ba zai iya jurar tashin hankalinta ko ɓacin ranta ba, zai iya ɗaukar komai amma banda wannan.

Cigaba da kiranta ya yi, amma taki ɗauka, sai sharɓar kuka take yi kamar ba gobe, ɗauko wayar Areef ya yi ya kirata da shi, call na farko bata ɗauka ba saboda taga new number ne, sai a karo na biyu ta ɗauka, ban da shessheƙar kuka babu abin da yake jiyowa daga cikin wayar, cikin sanyin murya ya fara magana

"Am really sorry my heartbeat, you knew ni ba zan taɓa kula kowa ba sai ke, bani da wani interest a kan wata mace sai ke, please ba zan iya jure kukan ki ba, zaki haifar mini da babbar matsala a cikin zuciyata, ki dai'na dan Allah". Kun sani na sani turawa basu yin mata biyu, mace ɗaya ce, sai dai masu bin matan banza zaki samesu da wata ta waje, amma matar aure ɗaya ce, kawai rigima ce irin ta heartbeat, da kuma tana tunanin zai iya canzata ya auri wata, tun da dama kunga tana tantama a kan son da yake yi mata, tana ganin kamar bata kai ya so taɓa, bata da wani abin da ya kai ya so ta domin shi, da sun yi aure ba zata damu ba dan tasan ba kishiya, yanzu kuwa zata iya damuwa dan a girlfriend nasa take, yana iya canzawa.

Shiru ta dai'na kukan, amma bata yi mishi magana ba, "My rigimati zaki sha chocolate na kawo miki yanzu?". Ya faɗa a shagwaɓe, shiru taki amsa mishi, "Muyi Video call?" Nan ma shiru ta yi bata amsa ba, juya kiran ya yi zuwa video call.

Sai da kiran ya kusa ya katsewa ta ɗauka, tana kwance ta tada kai da pillow tana wani turo baki tare da kumbura kumatu. "My rigimati, kaga ɗan bakinta a wajen sai rigima, yanzu dai sai da kika yi mini asarar hawayena ko? Ba komai zan rama ne, bari na zo da safe sai na matse ɗan bakin nan, ki cigaba da turo mini shi". Shiru ta ki kula shi kuma taki ɗagowa su haɗa idanu.

"Haba mana my rigimati, wai ba zaki ɗago ki kalle ni ba? Haba mana ƴar kyakkyawata, ƴar babyna, kaga hancinta kamar karas idanu kamar madara masu kyan gaske, ga wani ɗan siririn saje a gefe zai yi mini daɗin wasa da shi". Kukan shagwaɓa ta saka mishi tana faɗin "Ni Allah ka bari bana so". Narke mata murya ya yi tamkar zai yi kuka ya ce "Ni gaskiya ba zan bari ba, ni da kayana dan na yaba sai ya zama wani abin,? Bakiga ma da kika yi maganar nan ba yadda ɗan bakin nan ya yi mini kyau kamar in jawo ki in tsotse kayana kamar sweet". Hararar wasa ta wurga mishi ta kasan idanu, tana murmushi kasa kasa, ya iya magana idan ya yi niyar yi, idan kuma baya jin yin maganar sai ya yi ta binta da okey or not, amma gwani ne wajen iya zuba kalaman soyayya, ya san duk ta yadda zai bi ya kwantar mata da hankali idan ta ɓata rai.

"Kin san me nake tunani My heartbeat?" Girgiza mishi kai ta yi alamar a'a bata sani ba, "Ranar da na mallake ki ko? Akwai wani abu". Kawar mishi da zancen ta yi da cewa "Ina Areef?" Dan tasan halinsa sarai yanzu zai kawo mata wasu maganganun da zasu sakata jin kunya, shi kuma hakan ba laifi bane a wajensa, bata ganin laifinsa dan ya yi ire-iren wannan magana, saboda tasan halin Turawa ne hakan, tana yi mishi uzuri sannan tana ƙoƙarin koya mishi dai'na yin hakan tana kuma ƙoƙarin canza mishi topic na magana idan ya ɗauko zancen, ta san yanzu ba ƙaramin aikinsa bane ya ce mata idan ya malllaketa, ranar da aka kawota a gaban kowa zai yi mata kaza zai yi mata kaza su kiss da sauruansu, ita kuma kunyar irin maganganun take ji sosai shiyasa bata so.

"Areef yana toilet yana wanka". Bawan Allah da yake shi wankansa ba irin na kowa bane, dole ya bi komai a hankali saboda ciwonsa yasa yake jimawa a toilet idan ya shiga.

"Tom gaskiya ya kamata nayi hira da shi ko ta wayane yau tun da baku sami damar zuwa ba". Okey ya amsa mata da shi, "To ɗago ki kalleni". Make mishi kafaɗa ta yi alamar a'a b zata ɗago ba, "Please mana my heartbeat". Ya faɗa a tsananin shagwaɓe, "To ka rufe idanunka idan kana son ganin na ɗago kai". Ba musu ya rufe idanun nasa, dama a yunwace da son kallon face nasa take, dan haka sai ta ɗago ta zuba mishi idanu tana kallon face nasa kamar ta kai hannu ta shafa, shi kuma ya datse idanunsa gam dan bin abin da take so, saboda farincikinta.

"My shagwaɓati ka kara kyau sosai, Allah har wani kyalli face naka take yi". Waro dara daran brawn eyes nasa ya yi kai tsaye sai cikin nata, lokacin guda suka sakarwa da juna wani kayatatcen murmushi mai sanya zuciyoyin masoya nishaɗi ya kuma mantar da su a wani duniya suke, "I really love you my wife to be In Sha Allah". Ya faɗa yana kashe mata ido ɗaya, wani irin kallon soyayya ta wurga mishi mai ɗan ɗauke da harara kaɗan irin na masoya tana faɗin "My shagwaɓati ina ganin daga mum, dad, Triplets a masu sonka sai ni,". Cikin zoyala ya ce "Au dama baki fi Triplets sona ba?".

Gyaɗa mishi kai ta yi tana faɗin "E mana, yanzu idan nace maka nafi Triplets naka sonka zaka yarda?" Girgiza mata kai ya yi alamar a'a ba zai yarda ba, dan duk wanda zai so shi, to fa wlh yazo a bayansu Lion, "To ka gani ai, ba yadda za'ayi in yi maka karya, gaskiya na gaya maka". Zuba mata idanu ya yi yana kallon yadda take motsa lips nata da suke pink color, ga shi ta sanya lips balm, sai suka kara wani kyalli sosai, ba ƙaramin ɗaukar hankalinsa suka yi ba, yana bala'in son ya yi kissing nata.

"Me kake kallon haka kuma?" Nisawa ya yi kafin ya ce "Babu komai kawai dai ina son na yi miki kiss ne". Turo mishi ɗan bakin nata ta yi tana faɗin "To Bismillah". Wani irin dogon numfashi yaja tare da saukewa a hankali kafin ya lumshe dara daran idanunsa, shi kaɗai yasan me yake ji, gyara kwanciyarsa ya yi tare da rungumo pillow yana faɗin "Ni kike yi wa kwalele ko? Zaki sani bari na riƙe ki". Yadda ya yi maganar tamkar baya son motsa laɓɓansa, can kasa kasa ya yi ta, murmushi ta yi yana ce mishi sorry ba zata kara ba, shiru ya yi bai tankata ba, dan ta jefa shi cikin yanayi, haka suka cigaba da hirarsu cike da nishaɗi suna farantawa juna rai, sai dai baya wani yin magana sosai, daga yes sai no yake binta da shi.

A ɓangaren Lion kuwa, wato Abuja.

A razane ta farka daga barcin da take yi tana kurma ihu, mummunar mafarki ta yi wai ga kartin jiya sun dawo sun kamata, dirowa kasa ta yi daga samar sofar, tare da nufar gadonsa, baya nan, sake tsorata ta yi, a guje ta watsa ta nufi waje, sai dukan uku uku kirjinta yake yi, ya jima da farkawa daga barci har ya yi wasu uzurorin gabansa.

Palo ta nufa, a dai'dai tsakiyar benen suka yi karo da shi ta buga kanta a tsayayyen faffaɗar kirjin nan nasa, baya baya ta yi tana kara kurma ihu, duk a tsananin firgice take, zuba mata idanu ya yi yana kallon yadda take firgicen ga idanunta a datse, mamaki ma yake wai me ya sameta ne haka? Ita da ya bari take zuba barci cikin kwanciyar hankali, anya kanta ɗaya kuwa? Ya tambayi kansa, dama zai haura sama ne ya je ya yi alwala azahar ta yi, ya yi sallah.

Raɓawa gefenta ya yi yana mai wucewa sama abinsa, har gobe ɗaukar ƙaramar yarinya yake yi mata, bai taɓa ɗaukarta a mace ba, shiyasa baya damuwa sosai yake taɓa ta kamar jiya kenan da ya ɗauketa. Da gudu ta bi bayansa dan a tsorace take, toilet ɗin daddy ya nufa, alwala ya ɗauro tare da fitowa, ga mamakinsa sai yaga ta shinfiɗa mishi dadduma, ya ji daɗin hakan a cikin zuciya, amma a fili kuma shiru, ba wata alamar da ya nuna hakan.

Bayan sun yi sallar baki ɗayansu, fita ya yi zuwa palo ya barota a cikin ɗakin tana askar, har zai wuce zuwa palon kasa sai kuma ya ce bari ya duba sauran ɗakunan dake cikin gidan, maybe akwai abin da zata amfane shi a bincikensa. Ɗakin mum ya fara shiga, ƴan dube dube ya yi, babu wani abin tuhuma, har zai fita sai ya tuna bai buɗe drawer mirror ba, dawowa ya yi ya buɗe, hotunane a cike a ciki, tun daga kan iyayen Naurat, iyayen Dr Salman har zuwa Rimsha wadda ta kasance Auta a cikin family'n Dr Salman ɗin, duk cikinsu ita ce karama, autar kowa ce, idan baku manta ba, daddynta yana bibiyar rayuwar ƴan uwansa sosai har yana taimaka musu, to a nanne ya samo hotunansu da su da ƴaƴansu, su Imran dukka, su basu san nashi ƴaƴan ba, amma shi ya san su bakiɗaya.

Bashi da lokacin tsayawa kallon hutuna, dan haka sai ya kwashesu a kan idan ya koma Kaduna ya natsu zai duba, da haka ya fita zuwa ɗakin dake kusa dana mum ɗin, wanda kuma ya kasance nasu Rimshan ne kenan.

Ya sha ruwan mamakin ganin uban zanen face nasa a cikin duk wata drawer da ya buɗe a cikin ɗakin, ɗaukar zane ɗaya ya yi yana dubawa, sak shi aka zana har da sanya mishi blue color a idanunsa ta yi kamar blue eyes, tunawa ya yi da sunanta dake saman kirjinta, to me hakan yake nufi kenan? Ya tambayi kansa, dan shi bai yarda Rimsha ta san soyayya ba, ƴar baby yake ɗaukarta wadda bata wuce goyo wajen iyayenta ba, bai ma ɗauka ita ce ta yi waƴan nan zane ba, dan yana ganin kamar bata kai iya zane har haka ba, babban abin kuma daya ɗaure mishi kai shi ne dukka zanen sun jima, alamu sun nuna ba yanzu aka yi su ba, to ya akayi suka san face nasa kafin ya zo? Ya sake tambayarsa kansa da kansa, shiru ya yi yana tunanin shin waye ne ma ya yi zanukan nan bakiɗaya?.

Drawer kayanta da ya buɗe ne ya ci karo da wata katuwar cardboard paper fara tas, an nannaɗeta da kyau sosai, an yi mata ajiya na musamman. Zarota ya yi tare da buɗewa, zanen face nasan ne dai a jiki, sai dai kuma a jikin wannan cardboard paper ya sami amsa a kan wacece ta yi zanen, dan kuwa bayan ta zana face nasa da girma, sai ta zana nata face ɗin karami a kasa dai'dai wajen wuyarsa ta gefen dama, daga gefen hagu kuma ta yi rubutu da biro da manyan baki kamar haka GAR MY PLEASURE MY WORLD, I REALLY LIKE TO SEE YOUR FACE, AM SURE, SOON I WILL SEE YOU IN SHA ALLAH. Ba karamin mugu mugun kyau handwriting nata ya yi mishi ba, ƴar karama da ita sai good handwriting kamar me, shi bai wani ɗauki zancen da ke rubuce da mahimmanci ba, dan ba sanin me soyayya ya yi ba.

Calmly ya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login