Showing 114001 words to 117000 words out of 359620 words
mance da A'isha, an rufe musu babinta, sai murna jenan take yi zasu fita sayayya da mummynsu wato Hajiyar daɗi, tashin hankali da ba'a sanya mishi rana.
Masu karatu shin ku a tunaninku me ya sami D.P.O ne?, ko dai ta mance wace ce ita ne? Anya lafiya kuwa? Akwai cakwakiya gaskiya, in dai haka ne Hajiyar daɗi ta ɗauki hakkin jama'a sosai a kanta, da alama rufewa mutane baki take yi, ba ji ba gani, dole sai maganarta kawai kowa zai bi, sai Allah ne kaɗai yasan adadin mutanen dake cikin gidan nan wadda basu son zaman gidan, Allah ne kaɗai yasan adadin matan da suke kuka a cikin zuƙatansu basu son wannan harka, wlh ba kowa zai so yin harkan nan ba, kunga ita ma Jehan bata zo da niyar son wannan harka ba, hasalima yakarsu ta yi niyar yi, amma sai ga shi reshe ta juye da mujiya, da alama ta koma tana supporting nasu fa, ko ya makomanta zai kasance cikin wannan bakin gida? Mu dai je zuwa, mu waiwayi gidan Abba mu dawo.
GIDAN ABBA💋
A bakin kofar palo mai gadi ya ajiyewa Akila trolley tsarabar da Aseef ya kawo mata, da kanta ta ja zuwa cikin palon, yadda ta bar Ammie hakan ta dawo ta same ta, tsakiyar palon ta jawo akwatin ta kawo shi, zuba mata idanu Ammie ta yi tana kallon ikon Allah, bayan ta ajiye akwatin ta koma ta ɗauko kwalin goribarta, shima a tsakiyar palon ta ajiye shi, sai wani sakin uban murmushi take yi baki yaki rufuwa, har lokacin Ammie bata tanka ta ba.
"Ammie heartbeat ne ya kawo mini wannan tsaraba fa". "To Akila heartbeat kuma?" Gyaɗa mata kai ta yi baki yaki rufuwa, "Waye shi heartbeat ɗin?" Kusa da ita ta zo ta zaune tare da kwantar da kanta a saman cinyar Ammien nata tana faɗin "Ammie zan baki labarinsa daga baya, yanzu dai ya ce zai zo ya gaishe ki idan ya sake dawowa, har da Abba ya ce zai je ya gaidar, bari dai na buɗe tsarabar nasa in gani". Ta kai karshen maganar tare da miƙewa ta nufi trolleyn, zuba mata idanu kawai Ammie ta yi tana mamakin ƴar tata, wannan murmushi dake a kan fuskar ya isa ya bayyanar da tsantsar kaunar masoyin nata da take yi.
Kwantar da trolley ta yi, tare da zuge zip ɗin, da wata katuwar teddy ta fara cin karo, teddyn nan ta haɗu tamkar ɗan mutun, fari tas da ita, a gaban teddyn daidai wajen wuyarta an yi rubutu da jan kala, Heartbeat+ Heartbeat, wani irin haɗaɗɗen murmushi ne ya kubce mata, yasan abin da take so ashe, ya santa da teddy akwai amana, ga wannan teddy ma ta tsaru iya tsuruwa, da alama shi ya bada yadda yake so aka buga mishi, sai kamshin perfume ɗin Lion take yi, tsabar murna, jikinta har rawa yake yi wajen ciro teddyn daga ledarta, ta wani rungume a kirjinta tamkar Heartbeat ɗin nata ta rungumi, da yake Ammie ta san halinta da shegen kaunar teddy's, sai bata yi mamaki ba, in dai a kan teddy ne fin haka ma zata yi, a wajenta wannan teddy ya fi mata komai dake cikin akwaitin, da kyar ta yarda ta ajiye shi ta fara fito da sauran kayan.
Nan ta sake cin karo da wani haɗaɗe flowers mai girma, ya kusa kai girman teddyn nata, flowers yana nan round, an shirya shi datsan datsan, ba karya shi ma ya yi, dukka kayan cikin akwaitin nan kamshin perfume ɗin Lion suke yi, perfume ɗin da idan ya kama kaya baya saki, sai dai abin mamaki Ammie bata ce bata son kamshin ba, sai ma shaka da take yi tana lumshe idanu, amma kuma da alama kamshin ya canza abubuwa da dama daga cikin gidan, duk wasu aljanu dake kusa sun gudu, har wani haske gidan ya kara yi, to me hakan yake nufi? Ita dai Ammie duk abin da waƴan nan dodannin basu so, suna sawa ita ma ta ji bata so, to ya akayi take son wannan kamshin, su kuma sun gudu da suka jita? Akwai ayar tambaya a nan gaskiya, ba mai amsa mana kuma sai ita Ammien da kanta, mu dai je zuwa.
A jikin flower an rubuta i really love you my heartbeat, da farin kala aka yi rubutun, shi kuma flower ja ne, a wannan karon Ammie ta kasa hakuri sai da ta ce "Heartbeat hala Bature ne ya kawo miki wannan kyauta?".
Cikin sauri da mamaki ta gyaɗa kai tana faɗin "Ammie shi ne ya aka yi kika gane to?". Karo na farko da ta saki cool murmushi, cak Akila ta tsaya tana kallonta, yau tsawon shekaru 15 kenan rabon da taga Ammiensu tana murmushi, kullum fuskarta a ɗaure, tun tana yarinya da take mata wasa da dariya, daga ta fara girma Shikenan duk wata annuri ta kau daga fuskar mahaifiyar tasu, Allah sarki abin tausayi.
"Akila kenan ai soyayya da Bature daban yake da kowa a duniyar nan, su duk in da zasu yi soyayya baza su ɓuya ba, haka zalika kyautarsu a soyayya bata ɓuya, abin da zance miki na karshe shi ne ki shirya wajen tara flowers, dan zaki samesu babu adadi, idan ba Bature ba waye zai tsaya irin wannan soyayya, bahaushe zai wani sayo miki flower ne? Ai su ɓata lokaci da shirme ne a wajensu, yanzu idan kika ji uban tsadar wannan flower dake hannunki sai kin tsorata, da za'a canza kuɗi da kuɗin Nigeria, sai ya saya miki ƙaramin gida, tab ai ni nina san Bature, ke baki san tarihin Abbanki ba ko,? Lokacin da muke soyayya da shi, bashi da babbar kyauta biyun flower, a lokacin ma kakanku tana nan, kinga shi ma Abbanku har ya yi girma ya yi wayo yana cikin turawa kafin su dawo nan, to yanzu ne zama cikin Hausawa ya sauya shi, amma duk wani ɗabiunsa a baya irin nasu ne, shima Bature ne ai kinga ni".
Zaro wannan dara daran idanun nasu na gado ta yi, tana mamaki, ba abin da yafi bata dariya da mamaki wai Abbanta ma soyayyar flower ya yi, dan iya shege sai ta rufe idanu tana imagine ga Abba nan ya zo ya duƙa yana miƙawa Ammie flower, kamar wata zararriya haka ta tuntsure da dariya har da faɗuwa kasa, Ammie kamar wata aljana, ta san me take yi wa dariyar, sai ta shareta tamkar bata sani ba.
Sai da ta yi mai isarta ta tsagaita tare da ajiye flower ta cigaba dan fitar da sauran kayan, set na wasu ɗankara dankaran shegun chain ta fitar, a jere suke guda goma sha biyu, dukkansu na zallar madarar zinari ne babu mix, sai wani irin bala'in kyalli suke yi, suna ɗaukar ido ba karya, ko wanne da irin design nasa, ita kanta Ammie ta tsorata da ganinsu, tsadar bala'i gaske suke da shi, ko wani guda ɗaya bala'in tsada ke gare shi, ga shi har goma sha biyu set ɗin baki ɗaya ya saya mata, innalillahi wa inna ilaihir rajiun, ai Ammie bata san lokacin da ta tambayeta da ɗan waye take soyayya ba, ɗan shugaban kasa ne ko waye, da yake ita Akilar bata san tsadar chain ɗin ba, sai bata wani ɗaga hankalinta sosai da ganinsu ba,.
"Lafiya Ammie kike tambayata da waye nake soyayya?". "Akila kin san tsadar chain ɗin hannunki nan kuwa?" Girgiza kai ta yi tana faɗin "Ammie ba ɗan shugaban kasa bane, amma jikan shugaban kasa ne, kuma ke baki ganin news ma bare nace zan yi miki kwatancen shi ki gane shi, da kina kallon Tv ne idan na kira miki sunan ɗan uwansa zaki iya saninsu". Hannu tasa ta karɓi chains ɗin tana kara kare musu kallo, farkon soyayyarta da Abba ya saya mata irin shi guda ɗaya, ita kuma Akila set baki ɗaya tabɗijam.
Cigaba da watsa tarukucen kayan ta yi, a nan ta sake fito da diamond Ring mai bala'in tsada, kafin ta fitar da wani tambarin Heartbeat mai bala'in kyau fari tas, tamkar balo balo a ka hura, haka heart ɗin yake, amma ba balo balo bane, yana da karfin da ba zai fasu ta daɗi ba har sai dai idan yanka shi za'ayi, Heartbeat+Heartbeat ne a rubuce a gaban heart ɗin, an yi rubutun da jan kala, rungume heart ɗin ta yi a kirjinta, ita duk tsadar waɗan nan abubuwa basu wani dameta ba, tafi kaunar teddy, Heart, da kuma flower nan, sun fi shiga ranta, Heartbeat nata ya san abin da take so da wanda bata so.
Miƙewa ta yi da sauri ta nufi bedroom nata ta bar Ammie da tulin kaya a gaba, har zata shiga sai kuma ta dawo ta ɗauki teddynta, sai murmushi take yi ta haye saman bed nata tare da fito da wayarta, massage ta yi mishi a WhatsApp a kan ya kirata yanzu.
Ba'afi minti ɗaya da shigar massage ɗin ba, sai ga kiransa da numbersa na ainahi ba unknown number ba, cikin zumuɗi ta ɗaga kiran, a shagwaɓe ta fara magana.
"Heartbeat, heartbeat Allah har na fara kewarka over". Cikin shagwaɓa shi ma ya fara magana "In zo in ɗauko ki mu dawo gidan mu ne?" Da yake su Turawa a wajensu dan budurwa ta dawo gidan saurayi da zama ba wani laifi bane, bai san nan kam Nigeria bane, kasar musulci, ko za'ayi hakan ma sai dai a ɓoye kuma ba da sanin iyaye ba, a takaice dai sai wadda iyaye suka yi wa baki ne zata yi hakan, wadda aka cewa jeki kya gani, Allah ka tsaremu da jin wannan mummunar kalma daga bakin iyayenmu masu albarka Amin.
"A'a Heartbeat ka zo dai mu yi hira, idan mun gama sai ka yi wa Abbana magana".
"Heartbeat ina nan zuwa wajen Abba, dole ne kuma nazo nayi magana da shi, dan gaskiya ba zan iya komawa ba tare da aurenki ba". Cool murmushi ta saki tana ɓuye fuska "Amma Heartbeat in tambaye ka mana?". Yana daga kwance ya miƙe zaune yana faɗin "To ina jinki". "Yanzu me kake yi?" "Ina kwance daga ni sai shot and single, kizo mu kwanta tare". Rufe fuska ta yi, ko me ya aiketa ta tambaye shi Oho, ai ga shi nan ta sami amsa daidai da tambayarta.
Kawar da zancen ta yi da cewa "Heartbeat dan Allah zaka iya gaya mini me yasa kake sona?". "Kyau, saboda kyanki mana". Ya bata amsa a full voice nasa, ba shagwaɓa a cikinta ko kaɗan. "Heartbeat kyau kuma?" Jinjina mata kai ya yi yana faɗin "Eh mana, nasan idan na gaya miki wani abu akasin haka, nasan zuciyarki ba zata yarda ba, so kawai ki riƙe wannan amsar, ni kuma na barwa kaina sanin me yasa nake sonki, da kuma irin son da nake yi miki ɗin". "Dan Allah Heartbeat ka gaya mini, wlh zan yarda da kai, ina son nasan asalin dalilin da yasa kake so na ne".
Nisawa ya yi kafin ya ce "To Shikenan, babu wani dalili, Allah ne ya jarrabeni da sonki a kallon farko, dan haka saboda Allah nake sonki, adadin son da nake yi miki kuma, ba zai faɗu a bakin nan nawa ba, na barwa zuciyata sanin hakan". Shiru ta ɗan yi kafin ta ce "Wani kalar abinci kafi so?" Shagwaɓe murya ya yi tare da yin kasa sosai da voice ɗin nasa tamkar wani na yi mishi laɓe "Ni ba abincin da nafi so zaki tambaye ni ba" "Me yasa ba abinci zan tambaye ka ba? To me zan tambaye ka?" Ta yi maganar ita ma a shagwaɓe kamar yadda ya yi mata.
Ɗan turo ɗan bakin nan nasa ya yi tamkar yana a gabanta, "Abinci ai bashi da wata faidar ki san me nafi so tun da ba ke zaki rinƙa yi mini girki ba, baki iya irin abincin mu ba ai, muna da masu yi mana girki".
"Haka ne amma ai yana da kyau nasan duk wasu abubuwan da kafi so tun da ni dai ka rigada ka gama sanin nawa ko?" Shiru ya ɗan yi kafin ya ce "Abubuwan da nafi so ai basu da yawa, na farko Triplets na, na biyu uncle Hosain, na uku Prof, na huɗu ke, a aikace kuma karatun Alqur'ani mai girma, sallah azumi, and then ina jin daɗin in ga ina sadaka sosai, abubuwan da nafi a tattare da ke kuma ko in ce a tattare da aure, first soyayya, and then your ball's, your eyes, mouth and rest".
Shiru ta yi, sai jujjuya kalamansa take yi a cikin ƙwaƙwalwarta, wai meyasa Turawa kam basu da kunya ne? Ta tambayi kanta, wai ball's nata yake so, ko a ina ya gansu oho mishi. "What are you thinking?" Ya katse mata tunanin nata. Dogon numfashi ta ja tare da sauƙewa a hankali, "Nothing my heartbeat". "Okey good kin ji abubuwan da nafi, and then ina son kiss sosai, i really like your lips, idan kina magana am feeling like nayi kissing naki". Hannu tasa ta toshe bakinta tana faɗin "Heartbeat mu ai a kasar nan ba'a kissing na mace har sai an ɗaura musu aure". "Serious?" Ya tambayeta ko a jikinsa, jinjina mishi kai ta yi alamar tabbatarwa.
"Okey ba damuwa ai, ke matata ce, very soon zaki zama, mu a kasar mu zaki iya kiss na kowa normal ne, amma tun da ina kasarku zan bi dokanku, zan jure, amma fa idan muna tare ki daina turomin ɗan bakin nan naki, idan ba haka ba, seriously zan yi kissing nashi ba zan iya jurewa ba". Cool murmushi ta saki jin yadda ya yi maganar, a shagwaɓe sosai, ga shi ya yi kasa da murya da alama Areef bai yi nisa da shi ba, ko yana toilet or balcony haka.
"Heartbeat ba dokar kasar mu bace ta hana ayi kissing na mace kafin Aure". "To dokar waye ne hakan?" Yadda yake maganar irin bai damun nan ba, yana cikin farinciki komai normal, "Dokar Allah ce Heartbeat, babu kyau ka taɓa jikin macen da ba muharramarka ba, ba sai budurwarka ba, kowa ma, in dai ba muharramarka bace, babu kyau ka taɓa ta, shi kuma kiss matarka kawai zaka yi wa".
"Tsaya tsaya heartbeat to ai ni har daddyna ina kissing na shi, my TRIPLETS muna sumbatar juna". Nisawa ta yi, cikin jin kunya ta ce "Heartbeat ba irin wancan sumbata da kake yi wa su daddy ba, no ina nufin kiss baki da baki, ka sha lips nata ta sha naka, shi ne matarka kawai ya halakta ka yi wa hakan". Shiru ya ɗan yi wannan maganar tata ta jefa shi cikin wani yanayi, "Heartbeat ya kayi shiru?".
"Babu komai just am feeling like i want to hug you ne". Dama ta san za'ayi hakan, shiyasa ta sake tambayarsa, ta san shi sarai ɗan nema, ranar ma haka suka yi da ita, daga ta ce mishi me yake yi, sai ya ce mata yana kwance rungume da pillow yana tunaninta, tsautsayi ya sa ta ce mishi gata nan zuwa su kwanta, shikenan ya birkice mata wai yana jin feeling, ga shi su basu san kunya ba, baya ɓoye abu, karara ya fito ya gaya mata gaskiyar abin da yake ji, wai a hakan kuma gara shi sau dubu da sauran, shi ta koya mishi kunya, Lion da Areef kam sai addu'a dan kwata kwata basu san hanyar da kunya ta bi bama. Shi ne da magana ita da jin kunya.
"Heartbeat kin iya tausa?" Zazzaƙar muryarsa ya katse mata tunani, "E na iya me ya faru". "Zaki rinƙa yi mini? Ni fa seriously ina son tausa sosai, and then ina son macen da ta iya soyayya da shagwaɓa sosai kamar dai ke ɗin nan" "Kasan me my heartbeat?" A'a ya bata amsa, "Kayi addu'a Allah ya kai mu ranar da zamu mallaki juna, nama alkawari zan maka soyayyar da sai kayi kuka dan daɗi". "Serious?" Jinjina mishi kai ta yi alamar tabbatar mishi da abin da take faɗa.
Kukan shagwaɓa ya sa mata yana faɗin "Ni gaskiya ba zan yarda ba, dole ayi sauri azo a kawo mini ke gida na, duk abin da za'ayi ayi da wuri, ina son soyayya sosai, ina son naga kin zama mallakina". Yana magana yana turo baki tamkar yana a gabanta, ga kukan shagwaɓa da yake yi mata, ita ma kukan shagwaɓar ta sa mishi "Heartbeat nima ina son naga ka zama mallakina ai". "Uhm uhm da gaske kike yi Heartbeat?" Gyaɗa mishi kai ta yi alamar eh da gaske take yi.
"Waye yake kiranka a waya tun ɗazun nake jin kara". Ta faɗa tana turɓune fuska, "Ɗayar wayata ce fa, Haroon ne yake ƙirana". "Waye kuma Haroon?" "Class mate". Shiru ta ɗan yi kafin ta ce "To kaɗauki kiran mana, wata kila wani abin zai gaya maka mai mahimmanci da ya shafi school". Girgiza kai ya yi yana faɗin "Duk wani abin da zai faɗa mini bai kai kwatar hirar da nake yi dake mahinmanci ba, idan ba Lion or Areef bane suka kirani a yanzu ba, ba wanda ya isa ya sani na kula shi a lokacin da nake magana da ke, so ki kyale shi, idan mun gama magana zan kira shi".
"My heartbeat wata kila fa abin yana da mahimmanci sosai tun da ga shi sai kiran ka yake ta yi". Ta yi maganar a shagwaɓe tana Murmushi, har cikin karkashin zuciyarta ta ji daɗin maganarsa, tana jin daɗin irin yadda ya ɗauketa da matukar mahinmanci a rayuwarsa.
"Seriously ba zan ɗauki kiran nan ba, ki kyale shi kawai, yanzu ke so kike yi mahimmancin wani yafi naki? Kin san yadda nake jinki a zuciyata kuwa? Ba zaki gane bane, ke dai Allah ya mallakamin ke ina ga a sannan ne zaki gane irin yadda nake sonki, yanzu ko na yi miki bayani ba zaki ɗauki haske ba". Wani irin ƙayatattacen murmushi ta saki tare da rungume pillow dake kusa da ita, wani irin azababben kaunarsa ne yake kara ninkuwa a cikin zuciyarta, addu'a take yi Allah ya mallaka mata shi, yadda yake son soyayyar nan ga shi ɗan shagwaɓa ɗan soyayya, zasu haukata juna, "Heartbeat" ya ambaci sunanta tamkar zai sa mata kuka, kasa sosai ta yi da murya cikin wani