Showing 12001 words to 15000 words out of 359620 words
shegun Stones masu bala'in kyalli, kuma stones ɗin sun daku da jikin lace ɗin sosai, lace ne mai shegen tsada, sai wani walwali yake, manya manyan abubuwan hannu na gold ta sanya mata a hannu wadda sun kasance nata ne da ta jima da saya ta ajiyewa matar ɗan nata kwaya ɗaya tilo a duniya zai aura, bakaramin kyau Aafia ta yi ba, sai dai idanunta da suka yi ja, alamar ta ci kuka ta ƙoshi, wani dankareren sarkar gold Ummin ta sake ɗaukowa ta sanya mata a wuya, sannan ta bata duk wasu kayan gyara da HJY BATULA ta haɗawa jelly bata gama shanyewa ba, ba musu ta ƙarɓa ta sha, komai Ummi ta ce mata, bata cewa A'a, sun zama kamar raƙumi da akala, a takaice dai, da kayan da aka sayawa Amarya jelly, da shi aka yi wa Aafia amfani, humra masu shagen daɗin kamshi Ummi ta sanya mata.
Amarya fa masha Allah, ta yi kyau tamkar ka sace ta ka gudu da ita, sai tashin kamshi take yi, mayafi Ummi ta rufa mata sannan ta riƙo hannunta suka nufi bedroom ɗin Nawid.
Da sallama suka shiga cikin ɗakin, sai hawaye Aafia take yi kasa kasa a cikin mayafin, domin kuwa yanzu a duniya babu abin da take tsoro biyun namiji, tamkar yadda take tsoron mutuwa, haka take tsoron haɗa ido da angon nan nata, jikinta sai kerma yake yi, Allah sarki baiwar Allah, ta ɗanɗani bakar azaba a hannun ƴan kidnaping, abin ya zauna a zuciyarta, hakan ya haifar mata da razana a cikin ƙwaƙwalwarta, wannan yasa kuma take mutuwar tsohon maza, ciki kuma har da angon nata, wato Dr Nawid, mutumin da take mutuwar so, yau ya zama mallakinta amma tana ji tamkar kabari aka kawota shiga ɗakin nan nasa da suka yi.
Lokacin da suka shigo yana zaune a gaban laptop nasa yana aiki, ya yi wanka yana sanye cikin kayan barci masu kyau brown colar, idanunsa na sanye da medicated glass, hannunsa na riƙe da pen ga kuma tarin takardu a gabansa, laptop ɗin nasa kuma tana ɗaure saman table dake tsakiyar bedroom ɗin nasa, shi kuma yana zaune saman wata sofa irin wadda ake sanya guda biyu a cikin bedroom ɗin nan.
Jin sallamar Ummi yasa ya ɗago kansa yana amsawa, cike da kulawa ya yi Maganar.
Karisowa cikin ɗakin suka yi, a gefensa Ummi ta zaunar da Aafia, ɗan gyara zama ya yi ta yadda Aafia ɗin zata zauna da kyau, sannan ita kuma Ummi ta koma ɗayar sofar ta zauna.
Wani irin razana A'AFIA ta yi lokacin da Ummi ta zaunar da ita kusa da shi, jikinta har wani kerma ya fara yi, kasa ta yi da kanta tana cigaba da hawayenta, abin gwanin ban tausayi, daga Nawid har Ummi ba wanda ya lura da tana hawaye, saboda mayafin ya rufe mata fuska, kuma ta sunkuyar da kanta kasa.
Nasiha sosai Ummi ta yi masu kafin ta yi masu sallama ta fice daga ɗakin. Ji Aafia tayi tamkar ta tashi ta bi bayanta, amma ba halin yin hakan, saboda bata da amsan da zata basu idan suka tambayeta lafiya.
Ummi na fita ya juyo da kallonsa kanta, cike da kulawa ya ce "Sannunki?". Shiru ta ɗan yi kafin ta ce "Ina wuni?" Ta faɗa cikin muryar kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro.
Maganar da ta yi tasa ya gane tana kuka, dan haka sai ya juyo da kyau suna fuskantar juna, hannu ya sanya ta buɗe mayafin nata, cikin sanyin murya ya fara magana "Kiyi hakuri, nasan wata kila kema baki so na, wata kila akwai wanda kike so, kila ma har kunyi alkawarin aure, amma ina son kiyi hakuri mu yi wa iyayenmu biyayya, Ummina tana masifar sonki, ke kuma Abbinki yana suna da har ya bani ke, ba zan taɓa mantawa da shi ba, ki dai'na kuka, na miki alkawarin zan riƙe ki hannu bibbiyu, ba zan taɓa saki cikin kunci ba, duk duniya idan kika cire iyayena, yayanki Prof shi ne mutun na uku da nake so, to ko dan Imran zan sanya ki farinciki, yanzu dai dan Allah ki daina kuka kin ji ko? Abar batun dangantakar da yake tsakanin Ummi da Aunty Hadiza, ke kanwata ce domin da ni da Prof duk ɗaya ne, dan haka ki ɗauke ni a matsayin Prof Kinji?".
Kara tsananta kukan nata ta yi sosai, domin ita kaɗan tasan ciwon da yake a cikin zuciyarta.
Dogon numfashi ya ja tare da sauƙewa a hankali, kafin ya sanya hannu ya riƙo hannayenta, yana ƙoƙarin yin magana, a razane ta kwace hannayen nata, jikinta ya kara tsananta kermar da yake yi.
Bai damu ba, domin yasan waye Imran, yasan shi da addini sosai, so yana tunanin gabaɗaya kannensa haka suke, shiyasa da ta kwace hannunta sai ya yi tunanin ko dan irin faɗan da ake musu a gida tun suna yara akan kada su bari namiji ya taɓa su ne.
Cire medicated glass ɗin face nasa ya yi, sannan ya ajiye pen ɗin hannunsa, cikin natsuwa ya fara yi mata nasiha tare da nuna mata cewa shi mijinta ne, ko ya taɓata ba wani matsala, dan haka kada ta damu, har lokacin kukanta kawai take yi bata kula shi ba, da alama kuma bata cikin natsuwarta.
Ganin hakan yasa ya jawota jikinsa ya rungumeta yana ɗan bubbuga bayanta, jin nasihar da ya yi mata ne yasa bata tashi daga jikin nasa ba, ta kwanta ta cigaba da kukan da take yi.
"A'AFIA baki so nane yasa kike yin wannan kuka haka?" Ya yi maganar can kasa kasan maƙoshinsa, tayi kuka sosai, ta kasa magana, sai dai kuma ta ɗan rage kukan nata yanzu.
Hannu yasa ya ɗago haɓarta yana kallon face nata, idanunta a runtse, shiru ya ɗan yi na ƴan mintoci kafin ya ce "Dan Allah me zan yi maki ki dai'na wannan kukan ne? Ni bana son kukan nan, ke amana ce a wajena, sannan kanwata ce ke, kuma matata, idan baki so na ne, ki gaya mani, ni nasan ta yadda zanyi wa Ummi bayanin ta fahimceni, kuma nasan shima Prof nasan zai fahimceni, sannan Abbinki ma zai fahimta, auren dole bashi da wata faida, ni nasan zama da wanda baka so babban ciwo ne, ba kowace zuciya zata iya jurewa ba, to kada ki damu, idan baki sona ko kuma kina da wanda kike so, ki gaya mani kinji kanwata?". Ya kai karshen maganar yana cire mata mayafin jikinta.
Girgiza mashi kai ta fara yi, amma dai ta kasa buɗe baki ta yi magana.
"Bakiso na ne kike girgiza kai?".
Sake girgiza mashi kai ta yi a karo na biyu.
"Kina sona?" Nan kuma shiru ta yi mashi bata motsa ba. Shiru shima ya ɗan yi kafin ya zame mata mayafin nata gabaɗaya ya ajiye a gefe.
"To meyasa kike kuka?". Sake girgiza mashi kai ta yi, bai takura mata lallai sai ta yi magana ba, domin kuwa yasan ba zata iya yin magana ba, saboda kukan da taci ta ƙoshi.
Bayanta ya fara shafawa a hankali hankali yana jin yanayi mai daɗi a tattare da shi, ita kuma tun tana sassauta kukan nata har ta dai'na gabaɗaya, sai ajiyar zuciya na wadda ta ci kuka take sauƙewa.
Sun ɗan jima a haka, har barci ya fara ɗaukar ta, "Muje ki kwanta a gado ko?" Can kasa kasa ta jiyo voice nasa.
Kasa miƙewa tayi daga jikin nasa, domin kuwa duk jikinta a mace, zuba mata ido ya yi yana mai jin wani irin yanayi da ba zai iya fassara shi ba a tattare da shi.
"Kanwata, a nan kike son kwanciya ne?" Ya sake magana kasa kasa kamar mai raɗa.
Ɗan motsawa kaɗan ta yi ba tare da ta yi magana ba. "To shikenan ɗan ɗaga kaɗan bari na ɗauke ki mu haura saman gado ko?".
Jin abin da ya ce yasa ta yunkura da iya karfinta dukkan, a sukwane ta miƙe daga jikin nasa, nan take wani irin muguwar tsoro ya kamata, abin da ya faru da ita a baya ne ya fara dawo mata, nan take ta birkice mashi, ta fara yin wani irin abu kamar bata da lafiya.
A wannan karon sosai ya yi mamakinta, zuba mata idanu ya yi, tana ƙoƙarin miƙewa, cikin sauri ya riƙota yana kallon face nata.
Kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro ta sa mashi, sai ƙoƙarin kwace hannunta take yi, dan ta gudu, ko ina zata je?.
Miƙewa tsaye ya yi har lokacin yana kallonta, kasancewar shi na babban likita, sai kwakwalwarsa ta fara hasasho mashi matsalarta, domin kuwa wannan abin da take yi, ya yi kama da yarinyar da aka yi wa fyaɗe ta karfin tsiya, wadda hakan kuma dama yana birkita masu kwakwalwa.
Cikin sauri ya kori shaiɗan tare da kawar da wannan tunani daga ƙwaƙwalwarsa, dan dai shi yana yi wa familyn Imran kallon salihan bayi, ya yi imanin da wuya a sami hakan a cikin jinin Prof, kuma ko da an samu ma, ya yi Imani ba za su ɓoye wa mijin da yarinyar zata aura ba, abin da bai sani ba, shi ne, gabaɗaya family'n ma mutun uku ne suka san da zancen, kuma da alama suma mutun ukun nan sun mance da zancen ma baki ɗaya. BABBAR MAGANA
Jawota jikinsa ya yi ya rungume tare fara gaya mata kalamai wadda za su sanyaya mata rai, ya yi amfani da matsayinsa na cikakken namiji mai ilimi da hankali, kuma ya fita shekaru.
Tun tana tureshi har ta hakura ta lafe a jikin nashi, mamaki yake akan me yake damunta, ya san dai a shekarun tan nan kam, tasan me ake nufi da aure, sannan kuma tana da ilimi sosai, amma tana yi mashi wasu irin abubuwa da suka ɗar sa mashi ? (Alamar tambaya) a ransa.
Cikin dabara ya yi mata wayo suka koma saman gado, a tare suka kwanta tana jikinsa. Sai lallaɓata yake yi kamar wata kwai a saman tray, Bawan Allah ya rungumi kaddararsa, to amma matsalar idan ya gano ba budurwa bace ita ya kenan?.
Suna kwanciya, ba jimawa ta yi barci, sai faman sauƙe ajiyar zuciya take yi a cikin barcin nata.
Shi kuma, sai faman shafa bayanta yake yi, yana ɗan bubbugata kamar ƴar baby.
Sun jima a haka kafin nan ya lura da uban zufar da take haɗawa saboda lace ɗin jikinta.
Cikin dabara ya sanya hannu ya ɗauko remote ɗin Ac. Ya kara gudun, sannan ya mai da remote ɗin, a hankali ya fara bin kayan jikinta da kallo, lace ɗin ya yi mata nauyi ta kwana da su.
Cikin dabara ya sanya hannu ya zuge zip ɗin rigar kasa, domin ya rabata da su, ko zata ɗan ji daɗin barcin, har lokacin kuma, tana kwance a jikinsa.
Bayan ya zuge zip ɗin kasa, cikin dabara ya mai da ita saman gadon ya kwantar da ita, sannan ya miƙe zaune, hannunsa har kerma yake yi wajen sanya hannunsa ya cire mata rigar tata, ya ɗaura mata a saman bedside drawer, juyowa da zai yi da nufin ya cire mata zanin, karaf sai saman kirjinta idanun nasa suka sauƙa.
Shiru ya zuba mata ido yana kallonta yadda take barcinta, ga kirjin nata masha Allah. Ya ɗan ɗauki lokaci a haka kafin ya daure ya kawar da kansa, ya cire mata sarkar wuyarta da abin hannu cikin dabara, sannan ya kai hannunsa ya zame mata zanin jikinta tare da kashe wutar ɗakin wai dan ma kada ya ganta ta ɗaga mashi hankali, domin baya son kusantar ta a yau, ya lura tana tsorace da shi sosai, ya fi son ya barta har sai ta saki jiki da shi sosai, sannan duk abin da zai faru ya faru.
Kwanciya ya yi ɗan nesa da ita tare da jawo bargo ya shiga domin shi sanyi yake ji, ba komai bane kuma ya ja mashi jin sanyi fa ce yanayin na sha'awa da ya tsinci kansa a ciki, juya mata baya ya yi tare da yin addu'ar barci, sannan ya juyo ya tofa mata, kafin ya yi wa kansa, daga nan ya ce asuba ta gari.
Yana kwanciya ba jimawa barci ta yi awon gaba da shi.
GIDAN LION💋
Tana tsaka da barcinta, can cikin ƙwaƙwalwarta ta fara jiyo karar wayarta, a hankali hankali ta fara jiyo ringin ɗin, ɗan motsawa ta yi tare da gyara kwanciyarta, ta kara jawo lallausan pillow ta rungume a kirjinta, tana mai cigaba da barcinta.
Sake kiran wayar aka yi a karo na biyu, a wannan karon har tsakiyar kanta ta jiyo ringing ɗin wayar.
Slowly ta faro dara daran fararen sleeping eyes nata waje, wadda suka ɗan sauya launi saboda barci.
Cikin sauri ta miƙe zaune ganin yadda rana ta take, wani irin sara mata kanta ya yi, cikin sauri ta dafe kan nata tana karato Alhamdulilahil lazi ahyana bada ma'amatani wa ilaihin nushur....
Ta kai karshen addua'o'in nata tare da sauke idanunta akan wayarta dake saman bedside drawer yake ta faman ringing yana neman agaji.
Jikinta duk a mace, hannu ta kai ta ɗauko wayar, My lovely Anaya shi ne sunan da ya bayyana a kan screen ɗin wayar, ɗan washe idanunta ta yi tare da ɗan motsa ɗan bakin nan nata kamar zata yi magana, hakan kuma yasa dimple nata gabaɗaya suka lotsa sosai.
Nauyayyar ajiyar zuciya ta sauƙe kafin ta ɗauki kiran, ta kara wayar a kunnenta.
Daga ɗayar ɓangaren Anaya ta sauƙe nauyayyar ajiyar zuciya kafin ta ce "Hello Beautyn Uncle Faisal". Guntun tsaki ta ja kafin ta ce "Anaya bana son magana dake fa".
Dariya ta yi tana faɗin "To nima bana son maganar ai, Yanzu na dawo daga school, kuma yau wlh uncle Shitu ne ya zo ya ɗauke mu, na so kiga uncle Shitun nan, saboda na gaya maki yana sonmu sosai, Musamman ni, ya ce ina mashi kama da wata ƴarsa da ta rasu".
Wani irin bugawa Rimsha ta ji zuciyarta ya yi jin Anaya ta ambaci sunan Uncle Shitu, sai dai yarinta ya hana ta tayi tunani a kan ko dai nasu Uncle Shitun ne, domin ita ma tana tunanin Uncle Shitun nasu ya mutu, hakan yasa bata taɓa kawowa shi ɗin bane, mafiya yawan lokuta Anaya tana yawan yi mata maganar uncle Shitun wadda ya kasance shi ne yake kaisu school wata rana, haka kuma yana zuwa ɗaukarsu wata rana, shi ne yake kula da gidan Hassan, wato daddy Anaya, da yake idan baku mance ba, Hassan baya zama, sai weekend yake dawowa, to hakan yasa ya wakilta uncle Shitu dan kula mashi da gida, abin da yasa ya yi hakan kuma, saboda shi yasan waye uncle Shitu, yasan tarayarsu da Hosaini sa, shiyasa kawai bai damu ba, ya bar mashi ragamar kula mashi da gidansa, ya san uncle Shitu mutun ne mai gaskiya, kuma ita Rimsha bata taɓa cin karo da shi ba, domin kullun ana riga zuwa ɗaukarta, tana tafiya ta bar Anaya a school, haka lokacin zuwa, tana riga Anaya zuwa school ɗin, to da yake ita bata cika son hayaniya ba, da ta zo school zata wuce class nasu ta zauna, hakan yasa ko an kawo Anaya bata ganin waye ya kawota, kuma ba kowa ce Uncle Shitu yake cewa Anaya tana mashi kama da ƴarsa ba face Jehan, dama idan baku manta ba, na gaya maku ba in da Anaya ta bar Jehan a kamanni, ita Anaya bata san tarihinsu Jehan ba, amma daddynta ya sani, kuma ba wanda ya sanar da su, to shima dai uncle Shitu yana tunanin su Jehan sun mutu ne, hakan yasa yake cewa sun rasu. ALLAH SARKI, WANNAN ZALUNCI DAME TA YI KAMA? SUNA RAYE AMMA KOWA YANA TUNANIN ƊAN UWAN NASA YA MUTU, SABODA SUN SAN ABIN DA YA YI NIYAR HALLAKASU BA ABUNE DA ZA SU IYA ZULLE MASHI BA, SHI MA DADDYN RIMSHA YANA TUNANIN SUN MUTU NE YASA YA BAR KASAR BAKI ƊAYA, HAKA SU MUMMY SUNA TUNANIN YA MUTU, JEHAN NA TUNANIN RIMSHA TA MUTU, SU MUMMY SUNA TUNANIN RIMSHA TA MUTU, SANNAN YANZU SUNA TUNANIN ITA MA JENAN TA MUTU, RIMSHA NA TUNANIN SUMA SUN MUTU, WANNAN AZZALUMI DA YA RABASU ALLAH YA SAKA MASU, SABODA ABIN DUNIYA, KAI INNALILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJIUN, YA ALLAH KASA MUFI KARFIN JUƘATANMU. WANNAN KENAN, MU KOMA KAN LABARI.
"Allah sarki Anaya ki gaida mani da uncle Shitu ɗin kin ji, In Sha Allah zamu haɗu"
"E mana Rimsha, ai dole ma, yanzu dai me ya sa baki zuwa school ne?".
Shiru ta ɗan yi domin bata san me zata ce da Anaya ba,.
Jin ta yi shiru ne yasa ta ce "Rimsha, lafiya kuwa?". Ƴar firgita ta yi "Lafiya lou Anaya, In Sha Allah zan zo school gobe kin ji ko?". Jinjina kai ta yi sai dariya take, har ga Allah tana masifar kaunar Rimsha sosai da sosai. HMMM AI JINI BA WASA BA.
Haka suka ta hirar school Anaya tana bata labarin yau Uncle Faisal ya yi ta nemanta, kamar zai yi kuka da bata zo ba, kuma ya ce ta bashi number Rismha ɗin, kuma ta bashi, ya ce zai kira.
Tuna abin da ya faru tsakanin Areef da A'A SALAHUDDEEN yasa Rimsha ta dafe kirji tare da zaro idanu "Anaya me yasa zaki bashi numberta?".
Har lokacin sai murmushi Anaya take yi "Haka kawai mana Rimsha, uncle namu nefa, so kike yi na hana shi number ne?". Shiru ta ɗan yi kafin ta ce "Tom Shikenan, bari na je na yi wanka na yi sallar azahar, domin wlh tun safe nake barci sai kiran wayarki ne ya tasheni, ko sallah ban yi ba, zamu yi waya anjima kin ji ko?" To ta amsa mata da shi, sannan suka yi sallama.
A hankali ta zuro kafafunta kasa ta miƙe ta nufi toilet bayan ta ɗaura wayar saman bedside drawer.
Yau duk wani aikinta Imran ne ya yi, kuma Allah yasa Lion yana tare da AREEF bai ma san waye ya yi aikin ba, kuma bai kai ga cin abincin rana ba, harta gyaran ɗakin su Mark Imran ne ya yi, daɗin abin ɗaya shi ne Lion bai sanya camera a gidan ba bare ya kalli cewa Imran ne ya yi aikin, shi kuma Imran baya son wani abin da zai tasheta daga barci ne, shiyasa ya yi aikin, time da ya shigo ɗakinta yaganta ta sami barci, sai ya wuce kawai ya fara yin aikin nata.
Wanka ta yi a gurguje ta fito ɗaure da