Showing 198001 words to 201000 words out of 359620 words
60/60 kamar yadda ta ci.
Juyowa Mark ɗin ya yi garesu, sun rungumi juna sai murna suke yi, can kasa kasa ya yi magana "Shikenan ina naki paper Rashmee?". Nan take face nata ya sauya, cikin sanyi murya ta ce "Ni yaki bani na rubuta, tun ranar da na dawo school na roke shi amma yaki bani, dama ni bana nan aka yi test ɗin". Juyowa gare shi ya yi, tun kafin ya yi magana tuni ya fito mata da question paper ya miƙa mata hannunsa har rawa yake yi, karɓa ta yi tana murna, da hannu Mark ya nuna mata saman sofa akan ta zauna ta rubuta da wuri su wuce gida zai je ya yi girki.
Tana tsaka da rubuta wa daddyn Anaya ya zo ɗaukarta, Zaira ce ta shigo office ɗin kiranta dan wata student ta gayawa daddyn ta gansu sun shiga office ɗin Mr Emmanuel, cike da murna ta sake rungumar Rimshar tare da bata kiss a kumatu tana murna, tsabar farinciki Juyowa ta yi ta rungumi Mark ɗin ma da yake tsaye kamar Robot tare da furta mishi ta gode sosai, Allah sarki ita ɗin ma bata ɗauki rungumar a matsayin laifi ba, ba ilimin addini sai zallar boko babu surki.
Har cikin ransa ya ji wannan rugumarsa da ta yi, babu wata mace da ta taɓa zuwa kusa da shi ma bare har ya kai ga sun yi musabaha ta hannu da hannu ma bare kuma runguma, babu wannan macen, yau Anaya ta rungume shi, har wani shock ya ji a jikinsa, sakinsa ta yi tare da juyawa cike da murna tana yi wa Rimsha bye bye, juyawa shi ma ya yi ya bita da kallo yana mamakin irin tsantsar murnar dake kan face nata, kamar wadda aka yi wa wani hamshaƙin kyauta na gani na faɗa, bai san cewa ta ɗauki boko ne da matukar mahimmanci fiye da tunanin mai tunani ba, wannan paper tun ranar da Mr Emmanuel ya bata ta kasa nunawa daddynta dan tana tsoron ya ga ta ci zero, ba zai yi farinciki ba, haka mum ɗinta, to yanzu kuma an gyara mata marking ɗin, ai dole ta yi murna over.
Ita kuma Rimsha tana son zuwa su gaisa da daddyn Anaya, sai dai ba dama, Mark na jiranta ta gama rubuta test da wuri su wuce, bata ji daɗin hakan ba sam, ta so ganin daddyn Anayar, dan Zaira ta ce daddy da uncle Shitu ne suka zo a tare, sam ba haka ta so ba, amma dole tahakura.
Shi kuma sai da Anayar ta kurewa ganinsa ya dawo da kallonsa kan abinda Rimsha take rubutawa, ya yi mamakin ganin yadda take tsara amsar kamar wata computer, ya jinjinawa kaifin basira da kwakwalwarta ba kaɗan ba.
Sai 12:40 ta kammala, lokacin kuma hadari ya haɗu sosai a garin, miƙawa Mr Emmanuel ta yi, da sauri ya karɓa ya bata marking yadda ya dace tare da shigar da list, sannan ne Mark ya ce suje, tasa ta gaba ya yi suka wuce, binsu da kallo Mr Emmanuel ɗin ya yi yana sauke ajiyar zuciya, sai dai fa a cikin zuciyarsa ya kudurci niyar tun da suka yi mishi haka shi kuma wlh sai ya lalata Rimsha da Anayar baki ɗaya, ko da kuwa zai mutu sai dai ya mutu sai ya san hanyar da zai bi wajen ganin ya cimma burinsa na lalatasu ɗin, to ance mai son abinka ya fika wayo, Allah dai yasa mu dace.
Lokacin da suka fito student ɗaiɗaiku ne suka rage a cikin school ɗin, dayawansu iyayensu sun zo sun ɗauke su, saura waƴan da iyayensu ke lattin zuwa.
Kai tsaye motarsu suka nufa, gidan baya ta shiga, shi kuma ya wuce mazaunin driver. Suna fita school ɗin aka fara yayyafin ruwan sama, wani irin farinciki ne ya dira mata a ranta lokacin da ta ga ruwa, ji ta yi tamkar ta ce mishi ya tsaya ta shiga cikin ruwan dan Allah, sai dai tana tsoro sosai, dan ma yau sun yi babbar sa'a da har ya yi musu magana kuma ya tsaya musu a kan matsalarsu har komai ya warware, dannewa ta yi har suka isa gida.
Yana yin parking ba motar, tun bai gama kashe ta ba, da sauri ta ajiye school bag nata da ɗan hijabinta da bai gama rufe kirji ba a saman kujerar motar, a hanzarce ta buɗe kofar motar ta fito, har tana haɗawa da gudu wajen shigewa cikin ruwan, juyi ta fara yi a ciki tana tsalle.
Shi kuma Mark wayarsa ya ciro ya fara latsawa dan baya jin zai iya fita a cikin ruwan nan, zuba ruwan yake yi sosai, gabaɗaya ilahirin sojojin dake gidan suna tsaye a host na gidan, ga ruwan saman very fresh.
Sai juyi take kamar wata ƴar tsana, bata ankaraba Juyowa da zata yi sai ji ta yi buge mutun, da yake ta yi ta juyi ya yi mata kamar ajijiya, sai jiri ya ɗebeta zata faɗi kasa, wuyar rigarta ya riƙo yana kallon face nata, dawowarsa kenan, tana can tana juyi bata ma ga shigowar motarsu ba, sauri yake yi ba zai iya jiran ruwa ya ɗauke bane yasa ya fito daga cikin motar ya keto ta cikin ruwan dan ya shiga cikin gida, wasu takardu yake son ɗauka zai sake fita ne, su ya dawo ɗauka ya koma shiyasa yake sauri.
Da yake ruwa na zuba mata a fuska ta kasa buɗe idanunta ma bare taga wanene, ga shi kuma bai ɗago da ita ba, ya dai riƙe wuyar rigar tata, sai dai kuma har cikin ranta ta ji cewa yes tabbas shi ne, dan idan ba shi ba babu mai riƙeta a wuyar riga idan zata faɗi, idan Areef ne hannunta yake riƙewa ko kuma ya rungumota, shi kam Aseef ma gabaɗaya yake rungumota a jikinsa, bayan su ukun nan kuma gabaɗaya gidan ko da daga sama bene zata faɗo babu mai ɗaura hannunsa a jikinta, ta rasa meyasa sojijin gidan gabaɗaya suke respect nata over, duk da dama basu kallon mutane, amma ita rashin kallonta da suke yi ma na daban ne, kamar waƴan da aka yi wa warning a kanta, ba ta san cewa ba wanda ya yi musu warning, kawai suna bala'in tsoron ogan nasu ne, suna kuma mugun respecting nasa fiye da tunanin mai tunani, kamar yadda suke yi masa kuma haka suke yi wa su Aseef, duk wanda Lion ɗin ya ɗaga idanu ya kallah har ma ya zauna inuwa ɗaya da shi to haka suke respecting nasa, ko da sunan wasa basu kuskura su kusanci abin da ya kasance Lion ɗin yana amfani da shi, hakan yasa suke nesanta kansu da koda kallonta ne, dan suna ganinta tare da su Aseef sosai, ga shi suna rungumeta suna wasa da dariya, abin da basu taɓa yi da wata mace ba a rayuwarsu, sannan kuma yanzu tana zama tare da Lion ɗin dan aikin da yake yi, hakan yasa gabaɗaya sojojin suka ɗauketa a matsayin ko budurwar ɗaya daga cikin TRIPLETS ɗin ne, ko kuma matar ɗaya daga ciki ne ma, shiyasa suke bata wannan respect ɗin.
Zuba mata idanu sosai ya yi yana kallon yadda ruwan nan yake sauka mata a kan face nata, wani irin azababben kyau lips nata suka yi mishi, yadda ruwan yake sauka a kansu yasa suka kara pink over kamar ta sanya lips stick, irin lips na kakanta Naurat sak, ga su da laushi kamar fure, ƴan kanana da su, na kasa ya fi na sama girma kaɗan.
Shi kam Mark ajiye wayarsa ya yi tare da zubawa ogan nasa idanu yana faɗin "Da alama oga ya faɗa tarkon mace fa, ji yadda yake kallonta babu ko kyaftawa, amma gaskiya so bata yi mishi adalci ba, wannan ƴar yarinyar haka da bata wuce goyo ba". Sai zancen zuci yake yi shi kaɗai a cikin mota yana kallon ikon god, tunanin rungumarsa da Anaya ta yi ɗazun ne ya faɗo mishi a ransa, shiru ya yi yana jin yadda ya jita a jikinsa, wani irin yanayi ya ji har tsakiyar kansa, face ɗinta ya fara tunanowa a cikin ƙwaƙwalwarsa, ga sanyin ruwan sama na kara ratsa shu, nan take ya faɗa wani yanayi na soyayya. TAB OGA DA YARONSA FA SUNA RUWA, AMMA FA SUNKI YARDAWA KANSU DA HAKAN, DAN YARA SUKE ƊAUKAR SU RIMSHA, E KAM AKWAI AIKI BABBA MA KUWA, GA DAI YARINYA TA SANYA MARK TUNANI, SHI KUMA OGA YA TSARE YARINYA DA IDANU.
A hankali ta motsa laɓɓanta tare da ɗan turosu gaba alamar shagwaɓa, nan take dimples nata suka yi wani irin lotsawa sosai, har cikin zuciyarsa ya ji hakan. Ganin ba zai ɗagota bane yasa ta yi kokarin ɗagowa da kanta duk da tasan a yadda ta riƙeta ɗin ba zata iya ɗagowar ba, amma ta kwatanta, hakan ya sanya ya fisgota da karfi ta faɗa saman faffaɗar kirjinsa, hannu ta sanya tana ƙoƙarin sharce ruwan face nata dan ta buɗe idanu ta kalli waye ne, duk da ta san shi ne, dan wannan faffaɗar kirjin shi kaɗai ne mai irinsa a cikin TRIPLETS, daga shi sai Areef mai bi masa, fisgota ɗin da ya yi kuma ya sanya gashin kanta dake jike sharkaf yana zubar da ruwa ya watsu mata har saman kirjin nasa, ɗan dagowan nan da ta yi dan ta sharce ruwan face nata sai gabaɗaya gashin nata suka dawo face nata, sun rufe mata idanu, abin gwanin burgewa.
Gently ya kai hannunsa ya kawar mata da gashin zuwa gefen kunnenta tare da sakinta ya nufi cikin gida, Juyowa ta yi tana kallonsa, har ya ɗan yi gaba kuma ko me ya tuna ya juyo, taku biyu ya yi ya dawo in da yake tsaye, ta yi mutuwar tsaye tana kallonsa, gashin kan nata ya zo ya damke tare da tasata a gaba a kan ta wuce zuwa cikin gida, ta fita daga cikin ruwan.
Ai kuwa kukan shagwaɓa ta saka mishi dan ita gaskiya duk bala'i bata son a rabata da ruwan saman nan, gara mata ya daketa, amma dai ya barta a cikin ruwan nan sai an ɗauke. Ganin bai kulata bane da gaske ciki zai wuce da ita yasa ta juyo da kyau ta rungume shi sosai tare da kankame shi tana yi mishi kukan shagwaɓa, tun da Areef ya gaya mata Lion ba zai taɓa dukanta ba ta saki jiki da shi sosai, tana zuba mishi shagwaɓa san ranta, yanzu ta san shi baya dukan mata, ya fi karfin sanya hannunsa a jikin mace dan duka, amma kuma yana bada punishment ai idan bai yi duka ba.
Kin kulata ya yi tamkar bai san tana yi ba, amma fa a zahirin gaskiya yana bala'in jin daɗin shagwaɓarta over, musamman ma idan ta haɗu da Aseef a ɗakinsa, ai abin ba'a magana, ba ƙaramin burgesa suke yi ba idan suna yi, sai dai ba zaka taɓa gane yana burgesa ɗin ba, saboda dama kun san shi ba'a taɓa gane halin da yake ciki.
Ƙoƙarin zubawa kasa ta yi ta zauna dan ya saketa, da hannu ɗaya yasa ya ɗauketa cak ya saɓa a kafaɗa ya nufi cikin palo abinsa, duk abin da suke yi gabaɗaya sojijin nasa suna kallonsu, sai dai basu yi mamaki ba, dan jiya ma sun ga fin haka yadda suka gansu tare a garden yana bincike tana zaune a kusa da shi, daga karshe ta yi barci tare da kwantar da kanta a saman kafaɗarsa, da ya ga haka sai ya gyara mata kwanciya zuwa saman cikyarsa ya cigaba da aikin da yake yi, dan kada wuyarta ta yi ciwo ne ya yi mata hakan, so sun ga komai jiya da yamma, bayan ya kammala aikin da yake yi kuma ya ɗauketa cak zuwa cikin palo, a saman sofa ya kwantar da ita kafin ya wuce cikin bedroom nasa, a cewarsa yanzu lafiyarta tana da matukar muhimmanci a gare shi ya kula da shi dan akwai tafiyar da zasu yi nan da kwana bakwai, shiyasa yake bata kulawa, a hankali shakuwa tana shiga tsakaninsu ba tare da ya sani ba, ita kam dama ai ta jima a ciki.
Sama ya haura da ita, kai tsaye bedroom nasa ya nufa, sai kukan shagwaɓa take zuba mishi tamkar babu shi a wajen, sam bai kula ta ba, jikinsu duk sai zubar da ruwa yake yi. A tsakiyar bedroom nasa ya sauketa tare da kara ɗaure fusataccen fuskar nan tasa sosai kamar hadari, cike da bada umarni ya fara magana a nitse cikin sanyin murya "Idan na sake ganinki a cikin ruwan sama sai ranki ya yi mummunar ɓaci, ki je ki kawo mini birth certificate na ƴar uwarki bari na gani". Natsuwa ta yi tsit dan bata ga alamar wasa a tattare da face nasa ba, har gobe kuma tana mutuwar tsoronsa, sai dai tana dannewa ne sakamakon kwarin gwiwa da take samu daga Aseef, Areef da kuma Akila, suna karfafa mata gwiwa sosai tare da kara gaya mata ta daina jin tsoronsa dan ba zai taɓa dukanta ba, baya dukan mata, ta rinƙa yi mishi abubuwa da zai rinƙa sanya shi magana, a haka idan ya saba da ita, to fa duk ranar da bai ganta ba dole zai shiga damuwa, zai ce yau dai ba wanda zata saka shi magana, hakan zai sanya ya ji ba zai iya yin nesa da ita ba, daga haka kuma shakuwa ce zata shiga tsakaninsu mai karfi, da alama kuma shawarsu Areef ta yi aiki, dan kuwa shakuwar tana ta kara yawaita sosai a tsakaninsu.
Juyawa ta yi da nufin ta fita tsantsin ruwan jikinsu da ya zuba a tiles ɗin ne ya ɗebeta dama ga kafarta da ruwa, tafiya ta yi luuuu zata faɗi, a zafafe ya tareta ta faɗa saman faffaɗar kirjinsa ta baya, dan idan ya barta ta yi wannan mummunar faɗuwa da wuya idan ba zata samu karaya ba, ba'a saiti ta tafi zata faɗi ɗin ba, so dole tasa ya tareta dan kada ta karye ta ja mishi dakatar da tafiyar da zai yi.
Nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ɗan juyo kaɗan, da yake gabaɗaya ta jike sharkaf, sai ya zamana kayan jikin nata sun manneta sosai, hakan yasa gabaɗaya ilahirin albarkatun jikinta suka bayyana, ɗan zuba mata idanu ya yi yana kallon shafaffen plat tummynta, tamkar bata taɓa zuba abinci a ciki ba.
Zura hannunsa ya yi ta saman kugunta a in da ya juyo da ita da kyau suna fuskantar juna, wani irin ɗauke wuta ta yi na wucin gadin jin saukar hannun nasa a kugun nata. Calmly ya fara magana, a hankali yake motsa lips ɗin nasa ta yadda ba zata taɓa tunanin shi ne ma yake maganar ba, dan bakinsa bai motsa ba, shiyasa kullum maganarsa yake can kasa kasa baya ɗaga murya. "Meyasa baki ji ne? Why kika cika rawan kai over haka? Why ba zaki rinƙa abu a hankali ba?". Turo mishi ɗan bakin nan ta yi tana kallon kasa, hannu ya kai ya ɗago haɓarta suna fuskantar juna, idanunta yake son kallah dan ya yi missed nasu, tun safe da ya kalla bai sake kallo ba.
Yana ɗago haɓar tata ta yi maza ta datse idanun nata, ɗan rankwafowa kanta kaɗan ya yi tare da matso da face nasa saitin tata kaɗan, zaro idanunsa waje kaɗan ya yi kafin ya ce "Open your eyes". Ba yadda zata yi haka ta warosu waje, kai tsaye sai cikin nasa, dama ga shi ya zarosu kaɗan, wani irin razana ta yi wadda ya sanya ta kurma ihu sai kuma ta yi shiru diff kamar na ɗauke wutar nepa, har gobe tana tsoron ƙwayar idanunsa sosai, bare ma ya zarosu ai dole ta tsorota, dan idanun nasa har wani kyalli suke yi, bare ma idan ya zarosu waje, ba'a magana dole idan baka saba ganinsu ba ka tsorata.
Da yake bai riketa ba sai ta yi kokarin zubewa kasa, a zafafe ya riƙota da kyau tare da tallaɓota yana mamakin wai ita wannan yarinyar me matsalarta ne? Sai shegen tsoro kamar farar kura, karkaɗa mata ruwan dake dark black curly hairnsa dake ɗiga ya yi a face nata, amma ina shiru hata motsa ba, ɗan zuba mata idanu ya yi na ƴan sakanni kafin ya kwantar da ita a kasa a wajen tare da tsugunnawa a kusa da ita bayan ya ɗauko ruwa daga fridge.
Ga mamakinsa ya zuba mata ruwa sosai, amma shiru bata farfaɗo ba, hakan ya samo asali ne kuma na riƙeta da Malika ta yi ta hanata farkawa, shi bai sani bai, baya ganinta, amma ita tana ganinsa, Malika aljanace mai kirki sosai, musulma ce shiyasa bata gudun perfume ɗinsa, dama shaiɗanun aljanu yake kora ba na kirki ba, ita tana da kirki sosai.
Ya yi ya yi ta farka amma ina shiru, Malika da iya shege ta hanata farkawa da tana son ya hura nata iska ne da bakinsa a cikin bakinta dan dama idan dai bata farka ba bashi da zaɓi dole sai hakan, shiyasa Malikar ta riƙeta, dan tasan muddin ya haɗa bakinsa da nata ya hura mata iska to fa da wuya ya tsallake bai faɗa tarkon sonta ba, dan ya rinƙa tuna wannan abin kenan a ransa, Allah sarki bawan Allah bai sani ba tarko Malika ta kafa mishi dan tana bala'in kaunar Rimshar, ta gaji da kallonta tana wahalar dakon soyayyarsa, yanzu kam ya kamata ace ya fara jinta a ransa, kullum sai ta zauna ta yi ta tunanin yadda zata taimakawa Rimshar a kan soyayyarta, duk ranar da Rimshar ta kasance tare da shi, to da daddare sai ta yi mafarki, tana shan wahalar wannan soyayya ba kaɗan ba, dan dai yarinya ce mai tawakkali yasa ta fawwalawa Allah komai bata nuna damuwarta a fili, ta samu tarbiya na kin karawa wajen mummy da daddy duka, shi kam daddy barin gida ya yi mishi amfani, dan da ya bar gidan bai wani taso da ɗabiun turawan nan kamar Hassan nasa ba, shi ya canza ya fita daban a cikinsu, idan baku manta ba harta Abbi a baya baya wani kula dasu Aafia da tarbiyarsu, zasu yi irin dressing ɗin da suke so suje school baya wani damuwa, bai ma san