Showing 27001 words to 30000 words out of 359620 words

Chapter 10 - Triplets Book 3 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

1955

yi, Allah ma yasa baya ganinta, da sai ya ce ta haukace.

Da yake yau ya ji yunwa sosai, bai wani tsaya ɓata lokaci ba, tana tura mashi abincin ya fara ɗeba yana kaiwa ɗan bakinsa a nutse, ita kuwa zama ta yi a gefensa tana tunanin da ace yanzu kawai ya fara bata abincin nan a baki mana, ai da ta ji daɗi.

(Kai Rimsha duniya)

Shi kuwa tamkar ma bai san da mutun a cikin ɗakin ba, laptop nasa dake a ɗaure saman gado ne sauti dariyar Aseef ya fara fitowa dafa ciki, ba tare da ya ɗago kai ba ya ce ta miƙo mashi laptop ɗin, okey ta amsa mashi da shi, a nutsu ta miƙe ta ɗauko mashi.

Saman sofa ta gefensa ya ɗaura laptop ɗin, ita ma tana iya kallon screen ɗin, saboda tana gefensa ɗan nesa da shi, kusan a jere suke za'a ce.

Zuba ma laptop ɗin ido ta yi, shi kuma yana cin abinci yana sauraron shirmen Aseef da Musharraf, wai Aseef na koyar Hausa, shi ne suke ta dariya, idan Musharraf ya faɗi wani word Aseef ya kwashe da darita kamar zautatce, wai kalmar ta bashi dariya, idan kuma Musharraf ya ce ya maimaita kalmar, to fa idan ya faɗeta sai Musharraf ya kwashe da wata mahaukaciyar dariya, domin kuwa harshen Aseef a naɗe take, ba yarensa bane, so baya taɓa faɗa daidai, komai sai ya canza mata muhalli.

Rimsha kuwa, daddynta kawai take kallo, yadda yake ta dariya abinsa, suna zaune a wajen basket ball na gidan nasu, Aseef na sanye da wando three quarter, sai farar singlet, shi kuma Daddy, yana sanye ne da full dressing ba ƙanana kamar Aseef ba, sun yi kyau ba kaɗan ba, daddy fa ya kara haske sosai, ainahin hasken fatarsa ta kara bayyana, saboda yanayin kasarsu, akwai sanyi sosai.

A ɓangaren Lion kuwa, har cikin ransa yake jin matukar daɗin abin da suke yi, ko ba komai cikin kaso 100 na damuwar da Aseef yake shiga na ciwon nan nasa, daddy na rage mashi kaso 80 daga ciki, a zahirin gaskiya Aseef yana jin matukar raɗaɗi idan har ya tuna cewa ƴan uwansa dukka sun gama karatu, shi babu abin da ya sani, wani lokaci har hawaye yake yi, sai dai daddyn Rimsha yana ƙoƙari wajen nuna mashi ya yarda da kaddararsa, kowa da yadda kaddara take zuwa mashi, hakan kuma yasa daddyn yake zama ya ɓata lokacinsa da komai da komai, ya zage dantse yana koyawa mashi abubuwa, harta assignment idan a ka basu, daddy na kula da shi, domin daddy degree ne ke fareshi shi, so sai ya zama tamkar uncle nashi mai yi mashi lesson, hakan kuma ba ƙaramin daɗi da farinciki ya sanya Areef da Saif ba, abin da yasa ma kenan Lion bai hukunta Rimsha ɗazun ba, ya daure ya yafe mata sabida Imran da kuma babanta.

Tana ta kallon Daddynta har ya kammala cin abinci bata sani ba, zazzakar sexy voice nasa ta ji yana faɗin ta bashi ruwa, ta shagala da kallonsu ta mance kula da shi, a hanzarce ta zuba mashi ruwan ta miƙa mashi, karɓa ya zo yi hannunsu ya gogi na juna, ai bata san time da ta saki ruwan ba, Allah dai yasa shi ya riƙe cup ɗin, badan haka ba, da ta yi mashi wanka da ruwan. Bai bi ta kanta ba, ya kai cup ɗin saitin ɗan bakinsa.

Sai da ya sha rabin ruwan, sannan ya ajiye, bata gaji da ganin daddynta ba, amma haka ba dan ta so ba, ta tattare kayan ta nufi waje, miƙewa ya yi ya koma saman sofa set mai zaman mutun 2 yana mai matukar jin ƙoshi, ga shi yana cikin farinciki dariyar da Daddy yake sanya Aseef, tamkar Tv haka ya mai dasu yake kallon shirmen nasu, sai dai fa duk da wannan daɗi, fuskarsa a turnuƙe kamar kullum.

Ita kuma kitchen ta mayar da kayan abincin kafin ta fito ta wuce wajen Areef dan su ɗan yi hira, daidai zata shiga ɗakin nasa, Malika ta jata baya tana faɗin kada ta shiga, da mamaki ta tambayi dalili, hannunta Malika ta riƙe suka koma saman sofa suka zauna dan su tattauna.

A nan take gaya mata Areef baya a cikin hayyacinsa yanzu, Sakamakon yakar wanna kunguya ta matsafan da aka sanya shi a ciki, to abin sai a hankali, idan ta shiga Areef zai iya kasheta, su kyale shi shi kaɗai ɗin dai.

A tsorace ta tambayeta shin ko Areef ɗin zai sami lafiya. "Rimsha Areef da izinin Allah ya ma sami lafiya ya gama, Kinga wannan yaki da ake yi, azzaluman nan sun tattaru ne a jikin Areef ɗin ne, dan su yi garkuwa da shi ko zasu tsira, amma hakan ba zai yi wu ba, yanzu dai sun yi nasarar shiga jikin nasa, amma fa nan da ƴan mintuna dole su sake shi ko suna so ko basu ko, domin Saif ya baza malamai ta ko'ina suna yi masu sauƙar Al Qur'ani mai girma tare da addua'o'i, ai dolene ma su rabu da Areef, ko da kuwa uwa ɗaya a ka Haife su".

Shiru Rimsha ta ɗan yi, kafin nan ta miƙe da sauri ta nufi sama tana faɗawa Malika bari ta je ta yi sallah saboda Areef, bari ta yi nafila ita ma ta rokar mashi Allah da ya kuɓutar da shi lafiya, tsabar sauri bama ta jira amsar Malika ɗin ba, a hanzarce ta faɗa cikin bedroom nata.

Kai tsaye toilet ta nufa, bayan ta ɗauro alwala ta fito sai ta shiffiɗa dadduma tare da sanya hijabi ta tada Sallah.

Ita kuma Malika miƙewa ta yi ta fito harabar gidan, ƴan dube dube ta yi kafin ta ɓace ɓat.

A ɓangaren gidan Abbi kuwa.

kamar yadda Abbi ya faɗa haka aka yi, tun safe suka shirya suka ɗauki Hanan suka nufi Katsina, Aunty da ita da Hjy Batula kuma, suka shirya Jelly suka nufi gidan babban yayansu, wato dai Abban Imran.

Hjy Batula ce ta ja motar, Aunty na gidan gaba ita kuma jelly tana gidan baya, sai taunar chewing gum take yi, Hjy Batula ta ce ta yasar da chewing gum ɗin nan, kada ta kuskura ta shiga gidan surukuwa da shi, ta ce to sai sun isa gidan sarakuwar tukun nan ta yasar.

A waje suka yi parking na mota, suka fito, Aunty ta riƙo hannunta, ita kuma Hjy Batula tana ƙoƙarin ɗage glasa ɗin motar da sauransu, da Motar Irfan suka zo.

Bayan ta fito ne suka nufi cikin gidan, mai gadi bai hanasu shiga ba, domin ya ga kamannin Hjy Batula da Abba. Ciki suka wuce, har lokacin jelly bata yasar da chewing gum ɗin ba, ta dai ɓoye a bakinta, ta daina taunarsa.

A palo suka isko Ammie zaune tana kallo a Tv, bakinsu ɗauke da sallama suka shigo, jin sallamarsu yasa ta juyowa domin taga suwaye ne.

Ganin Hjy Batula yasa ta ɗaure fuska sosai tana binsu da kallon banza. Ita kuwa jelly tun da suka shigo take karewa palon kallo, baki abin magana ta kasa hakuri sai da ta ce "Gwaggon Batula wannan wani irin gidan kazanta ne haka? Jibi ko'ina da datti, amma dai masu gidan guragu ne basu da kafa da hannu ko?". Aunty ce ta rufe mata baki tana girgiza mata kai.

Hannunta ta sanya ta zame na Auntyn daga bakin nata. "Ke Aunty gaskiya ce baki so na faɗa ko me? Wlh gidan nan gidan datti ne, buhun datti ne masu wannan gida, jibi kura wajen Tv nan, kuma a haka a ka kunna Tvn? Aunty wlh datti cuta ce, kazanta tana mugun yi wa lafiya Illah".

Dafe kai Aunty ta yi domin tasan kaɗan ma ta gani in dai jelly ce, ita kuma Hjy Batula kasa kasa ta ce mata ta rufewa mutane baki.

Ammie dai sai binsu da idanunta kawai take yi, bata ce masu ko sannu ba, bata yi masu iso ba, dan ra'ayin kansu, suka iso ciki.

Suna isowa idanun jelly suka sauƙa a kan Ammie ɗin. Zuba mata idanu ta yi tana kallonta, sanye take da wani dogon riga irin na barcin nan, kayan duk datti, sai ta yi kama da mai aikin gidan ne ba matar gida ba, wata mai aikin ma, ba zata iya zama cikin uban datti haka ba.

Zama suka yi a saman sofa ba tare da an basu izni ba.


Sanin hali yasa Hjy Batula bata tsaya yin wani dogon turanci ba, faka faka kawai ta sanar da Ammien abin da yake tafe da su, ai kuwa wani mahaukacin tsalle Ammie ta yi, ta dire ta ce idan akwai wanda ya isa ya yi wa ɗan ta aure shegiya take, uban mutun ya yi kaɗan, ai ba uban da ya ɗauka mata cikin ɗan ya yi mata naƙuda, ya rene mata shi har ya girma, dan haka kuma babu uban da ya isha ya yi wa ƴaƴanta abin da bai yi mata ba, wlh tun suna shaida juna su fitar mata da jelly daga cikin gidan nan, idan ba haka ba ta sumar da ƴa, yanzu ta sanya su suyi danasanin saninta a rayuwarsu.

Aunty kam ta tsorata dan bata son hayaniya, Hjy Batula kuwa already ta san hali, dan haka ko ɗar bata yi ba, ita kuma Jelly wani irin ɗaure fuska ta yi, ba mutunci, rai a jagule ta fara magana.

"Wannan mai kama da sumammiyar akuyar fa? Gwaggo Batula wace ce ita da har zata ce a fitar da ni daga cikin gidan nan? Ina cewa shi ne gidansu yaya Imran? Kuma wannan ƴar dattin ba mai aikinsu ba ce? Ko dai a wannan gida masu aiki ma suna da damar yin magana da power kamar haka ne?".

Shiru Aunty ta yi dan tasan halin jelly fin haka ma yi zata yi, dama bata ce zata mari Ammie ba ai an yi sa'a. Ita kuma Hjy Batula buge mata baki ta yi kasa kasa ta ce "Ke Jalila surukarki ce fa, mahaifiyar Imran ce".

Turo bakin nan ta yi kamar biro. "To gwaggo Batula dan ita ta haifi yaya Imran sai ta ce bata son ganina a fitar da nine? To ni dama waye ya ce ma ta so ni? Ni ma ai ba sonta nake yi ba, kuma ba zan zauna ma a gidan nan ba domin daddy ya taɓa gaya mani she is a wicked"

Kalubale gareku iyaye, bai kamata kuna zagin wata ko wani a gaban yara ba, domin baku san wace alaƙa ce zata haɗa ƴaƴanku da waƴan nan mutane ba, gaba tafi baya yawa, wannan haka yake, yanzu dai ga shi nan, daddynta yana zagin Ammie a gabanta, ita kuma ta riƙe, a kwana a tashi ga Ammie ta zama surukuwarta, ku sani duk son da Iman yake yi mata, yafi kaunar farincikin mahaifiyarsa sau dubu, ba zai taɓa yarda ta zagi mahaifiyarsa ba, a kan hakan ana iya kwance wannan aure ma baki ɗaya, to shawara dai ta rage gareku iyaye, ni dai na yi nawa, sai ku kuma ku gyara, dan nasan wannan matsala ce da take damun mu, sai ki ga uwa ta zauna tana zagin makontan ta a gaban ƴaƴanta, kuma ana waje guda, komai ka iya faruwa, ta yi wu ɗan maƙotan ya zo neman aure gidan naku, to ya kenan? Ƴaƴanki ba za su ga uwar da daraja ba, sai ki ga kwana biyu aure ya mutu, ƴa ta raina uwar miji, me ya kawo hakan? Wata kila ta taɓa jin kin ce uwar mijin ƴar datti ce ko ƴar kaza ƴar kaza, babu namijin da zai yarda a raina uwasa da ƴan uwansa, wannan kuskure ne babba muke yi, ya kamata mu gyara.........

❤️❤️TRIPLETS❤️❤️


E7-8


Turo bakin nan ta yi kamar biro. "To gwaggo Batula dan ita ta haifi yaya Imran sai ta ce bata son ganina a fitar da nine? To ni dama waye ya ce ma ta so ni? Ni ma ai ba sonta nake yi ba, kuma ba zan zauna ma a gidan nan ba, dan daddy ya taɓa gaya mani she is wicked".

Sosai Hjy Batula ta buge mata baki da ɗan karfi, kuka ta saka masu, har da birgima a kasa, taɓe maki Ammie ta yi tana ganin ikon Allah, wai wannan mahaukaciyar ce matar ɗan ta? Ta tambayi kanta da kanta.

Ita kuwa Aunty a cikin zuciyarta tana jin da ace Mummy Abla ta kyaleta, bata daketa ba, yanzu ga shi ta sake kwaɓe masu komai.

Tsawa Ammie ta daka masu akan su fice mata daga gida tun ransu bai ɓace ba. Waya Hjy Batula ta ciro wayarta ta kira Abbi dan ta sanar da shi abin da yake faruwa, bugu ɗaya ya ɗauki kiran, ba ɓata lokaci ta sanar da shi ga abin da jellyn ta yi, ita kuma Ammie ga reply da ta bata akan ba zata karɓi jelly ɗin ba.

Shiru Abbi ya ɗan yi kafin ya yi magana kasa kasa dan kar daddyn Jelly ya ji, yasan hakinsa sarai idan ya ji zai ɓata rai ya ce an wulaƙanta mashi ƴa, hakan yasa ya yi magana kasa kasa dan zaman lafiya yake so ba faɗa ba, umarni ya yi masu a kan su dawo da jelly ɗin gida, idan suka dawo daga Katsina za su kira Imran, sai su san abin yi.

To ta amsa da shi, ta yi wa Ammie sallama tare da riƙo hannun jellyn ta miƙar da ita suka nufi waje, wani irin matsiyacin kallon banza Ammie ta bisu da shi, sai da suka ƙurewa ganinta ta koma saman sofa ta zauna tare da ɗauko wayarta.

Number Imran ɗin ta fara laluɓa dan ta kirashi, ta bashi umarnin akan idan ma ya auri jelly to ya saketa ko ta tsine mashi albarka, sai dai kash a kashe ta sami number, ta ji babu daɗi sosai, saman sofa ta ɗaura wayar ta cigaba da kallonta.

Su kuma bayan sun je mota, sosai Hjy Batula ta yi wa Jelly faɗa tare da nasiha, ta kara mata da cewa, in dai bata girmama Ammie ba, to tabbas yaya Imran ba zai taɓa sonta ba, zai dai'na kulata, zai yi watsi da ita, domin yana Kaunar mahaifiyarsa shi ma, shiru ta yi tana sauraron Hjy Batula tamkar wata mumina, yadda kasan an mata sauƙar karatun Al Qur'ani mai girma a kanta, tsit ta yi, sai da mummy Abla ta gama nasihar, ta tada mota dan su tafi.

Suna kama hanya ita kuma Aunty ta ɗaura nata nasihar, dan jelly sai an bita a hankali, ta karfi ba zata taɓa yi wu wa ba, idan ka zare mata ido, ita ma zare maka zata yi, bata da tsoro ko kaɗan, ga uban rashin kunya tamkar a kanta a sauƙe shi.

Kai tsaye gida suka koma da ita, tun Hjy Batula bata gama kashe motar ba, jelly ta fito ta wuce ciki abinta, da ido kawai Hjy Batula ta bita da shi, tana mugun tausayawa Imran, gaskiya daddyn Jelly ya yi kuskure, ya biye wa sanyata farinciki ya koya mata ɗabiar da barin shi yanzu ba karamin abu bane, ya biye mata komai take yi baya yi mata faɗa, kawai dan ta yi farinciki, to ga shi dai karshe abin da ya haifar masu, bata ganin kowa da girma sai shi daddyn nata da kuma Imran, shi ma Imran ya ci albarkacin son da take yi mashi ne yasa take ɗan girmama shi, daba dan haka ba, shi ma da a sahun marenan wayonta zata sanya shi. TAB AIKUWA AKWAI GYARA BA KAƊAN BA.

GIDAN ABBA💋

Kwance take a saman gatonta bayan ta gama cin abicnin dare ta yi sallar isha kenan, ba abin da take jira face kiran sahibinta, abun begenta, farincikinta, ta lula can duniyar tunanin masoyin nata, sanye take da kayan barci a jikinta, doguwar riga ce launin pink color, ta sanya hular rigar a kanta, ƴan kwana biyun nan da tana samin kwanciyar hankali, har wani ƴar kiba ta yi.

Karan ringing na wayarta ne ya daki dodan kunnenta, hakan kuma ya yi sanadiyar dawowarta daga duniyar tunanin sahibin nata da ta faɗa, cikin sauri ta duba kiran, abin mamaki kuma abin al'ajabi kiran Irfan ne yau kuma ya shigo wayar tata, sai kuma a lokacin ne ma ta iya tunawa da wani abu wai sun taɓa yin soyayya da Irfan, nan take ta ji jikinta ya mutu, wani irin rashin daɗi ta ji.

Jikinta a sake duk ya mutu, haka ta ɗauki kiran nashi. "Yaya Irfan barka da dare". Dogon numfashi bawan Allah ya ja, tare kuma da sauƙewa a hankali. "Heartbeat ina kika shiga ne? Meyasami wayarki? Nazo gida ban same ki ba". Yadda yake maganar kamar zai yi kuka, abin gwanin ban tausayi, bata san lokacin da hawaye suka fara bin kuncinta ba. "Kayi hakuri yaya Irfan ka ji?" Shi ne kawai abin da ta iya furtawa.

"Bakomai Heartbeat ba dai kina nan lafiya ba?" "E ina nan lafiya fatan kai ma kana cikin ƙoƙarin lafiya?". Nisawa ya yi tare da suake ajiyar zuciya "Heartbeat bana cikin ƙoshin lafiya, ji nake yi kamar zuciyata zata fashe ta fito waje a kwana biyun nan da ban jiki ba, please kada ki sake yi mani hakan kin ji ko?". Hawaye take yi sosai, shin me yake shirin faruwa ne, kenan har yanzu Akila bata san soyayyar gaskiya ba, har yanzu ba zata iya tantance wadda take so da gaske da kuma wadda take so dan wani abu ba? To fa akwai gagarumar matsala wlh.

"Heartbeat ya na ji kin yi shiru?" "Kayi hakuri yaya Irfan". "Heartbeat me ya faru kike kuka kuma, subhanallahi dan Allah ki dai'na Kinji? Idan baki dai'na ba zuciyata zata yi mani ciwo". Hannu tasa tana goge hawayen nata. "Kada zuciyarka ta yi ciwo yaya Irfan, wlh na dai'na, ka gani na goge hawayen".

"Good my heartbeat, to yanzu dai gaya mani menene ya sanyaki kuka ƴar kanwar?". Shiru ta ɗan yi kafin ta ce "Kai ne ka sanya ni kuka mana" "Subhanallah ni kuma Heartbeat?" Gyaɗa mashi kai tayi tamkar tana a gabansa. "Ni kuma laifin ne nayi da na sanya matata hawaye? Yau wace iriyar ranan bakin cikice a gareni da na sanya matata kuka da kaina? Duk da ban san laifin da na yi ba, ina rokon da ki yi mani afuwa kin ji matar mijinta?".

Turo


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login