Showing 267001 words to 270000 words out of 359620 words
ya koma ya ɗauka suka cigaba da hira da Areef, zuba mishi idanu Areef ɗin ya yi yana kallon tsantsar soyayyar Rimsha dake kwance a cikin idanun nasa, harara ya watsawa Areef ɗin yana faɗin "Kallon fa?". "Kewarka nake yi mana, ba dole na kalle ka ba, yanzu ka yi mini nisa, anya zan iya jurewa kuwa? Anya nima ba zan ɗauki babyna mu bi jirgin ruwan nan ba? Nasan dai zamu sha soyayya kafin mu iso in da kuke". Magana ya gaya mishi a fakaice, da yake shi ya iya magana a dunkule kuma cikin hikima, tabbas yana zargin Lion ɗin ne, dan a yanayin yanda ya kalli kwayar idanunsa tamkar wanda yake tsaka da kwanciya da mace aka katse shi, sannan ya ce yana son ganin Rimsha an haka shi saɓani da idan ya ce yana son ganinta za'a juya mishi camera ya kalleta, ko lokacin da suka je Abuja idan ya kirasu, da ya ce yana son ganinta za'a juya mishi camera, yau kuma ya tambayi ina take yafi baki goma Lion ɗin yaki kula shi, ya san dai akwai wata a kasa, ga shi kuma ɗan bakin Lion ɗin ya yi kamar an tsotse a cewarsa, ya san ɗan uwansa farin sani, ya san yanda lips nasu yake, so bai taɓa ganin lips nasa a haka ba, ji yanda suka kara ja sosai alamar anyi kiss, shi ne yake gaya mishi magana a takaice..........GASKIYA AREEF ƊAN BAIWA NE KUMA ƊAN SAKA IDO BA KAƊAN BA.
Shiru dai Lion ɗin bai tanka mishi ba, hankalinsa ma baya kan Areef ɗin sam, yana kanta da take faman shiryawa, cikin toilet ta shiga ta sanya kaya, sai ta fito ta tsaya a wajen trolleys ɗin tana shafa Lotions nata daya kwaso mata, so shi ne hankalin Lion ɗin yake kanta, yana kallon duk motsin da take yi, yanzu ta dai'na kukan da take yi ɗin, da ta shiga toilet ma ta wanke face nata fes kafin ta zo ta shafa Lotion ɗin.
Bayan ta kammala ne ta nufi hanyar fita daga ɗakin, taki yarda ta kalli in da yake, wandon jeans baki ta sanya da t-shirt fari tas, kayan sun kamata sosai, da yake curly hairnta yana da tsantsi sosai baya ɗauruwa sai an sanya mishi pil, ita kuma ta duba cikin kayan babu pil ɗin, sai ta saki gashin haka abinta, ta dai gyara shi ya yi kyau.
Tamkar a mafarki ta ji zazzakar muryarsa yana faɗin "Come here". Juyowa ta yi ba musu ta nufi gadon, amma sam taki ɗago idanu ta kalle shi, sai kumbura kumatu take yi, yau an yi mata kiss kuma a cewarta ba muharraminta ba, ba mijinta ba, ba komai ba, abin ya kona mata rai har ya sanyata kuka.
Da hannu ya nuna mata kusa da shi a kan ta zo ta zauna, ba musu ta hau gadon dan tasan bata isa ta yi mishi musu ba, ko tayi ma wahala zata sha kuma babu wani riba, dan ko tana so ko bata so dole ta yi abin da yake so ya kuma ce ta yi. Ɗan karkato da wayar ya yi zuwa saitin face nata, cool murmushi Areef ɗin ya saki yana faɗin "Our Queen ya da ɓata rai haka? Ko baki son yin magana da ni ne?". Jin muryarsa yasa ta ɗago kai tare da sauke nauyayyar ajiyar zuciya ta saki wani ƙayatattacen murmushi tana rufe fuska da hannunta ga idanunta da suka yi ja saboda kuka. Shiru suka zuba mata idanu su dukkansu biyu, Areef yana mamakin me Lion ya yi mata take ta faman kumbura kumatu haka? Ga idanu sun yi ja alamar ta yi kuka, to me ya yi mata? Tun da ya gano dai ba da shi take fushin ba, shi kuma Lion yana kallon irin sihirtaccen kyau da ta kara da take murmushin.
"Yaya Areef where is Jehan?". Kara faɗaɗa murmushin fuskarsa ya yi yana juya mata wayar shi ma, Jehan ɗin tana zaune a bakin gado, fuska a ɗaure kamar kullum, sai turo baki take yi, alamar dai dole Areef ya sanyata zama a wajen ba dan ta so ba.
"Jehan dan Allah ina son yin magana dake ne". Ta yi maganar cikin harshen Hausa dan kada su ji me zata faɗa, jin voice nata yasa Jehan ɗin ta ɗago idanu tana kallon wayar, "Wace magana kuma? Faɗi ina jin ki". Ta bata amsa.
Miƙa mata wayar Lion ɗin ya yi ya miƙe ya fita waje dan ya yi magana da sojojinsa, cikin sanyin murya ta fara magana tamkar zata yi kuka.
"Jehan wlh yaya Saif kiss ya ya mini, kuma ya taɓa mini kirjina ranar, na shiga uku na, ni kuma ban isa in hana shi ba, kuma kin dai san haramun ne ya taɓani ko?" Tana magana tana ruwan hawaye. Saboda iskanci irin na Jehan sai ta ɗaure fuska kamar wata soja tana faɗin "Kin ga Rimsha wlh ban son iskanci, to idan ya yi miki kema ba sai ki yi mishi ba, ai kome ya taɓa miki kema yi mishi kawai zaki yi, wlh ni kada ki sake kawo mini wani zancen banza, waye ma ya ce ki kirani? Lokacin da kike zuwa wajensa a bedroom nasa ku shafe awa huɗu kuna tare duk baki san da haka ba sai yau ko? To ki shafawa kanki ruwan sanyi kawai ki cigaba da yin haramun ɗin". Ta bata amsar tamkar bata san cewa matar aure bace, sam bata nuna mata wani alama da zai nuna hakan ba, idan baku manta ba Areef ya ce kada ta gaya mata in ji daddy, to shi ne bata nuna mata wata alama da zata nuna ita ɗin matarsa ba ce.
Goge hawayen fuskarta ta yi tana ƙoƙarin sauka daga gadon dan a cewarta sam Jehan bata sonta, ba zata kula da matsalar ta ba. Muryar Areef ne ya dakatar da ita a in da yake cewa "Our Queen what is the problem? Ni ya kamata ki gayawa ba Jehan ba, rabu da masifaffa mafaɗaciyar nan, menene ya faru kike kuka?".
Ganin zata iya shiga wuta ne yasa bata da zaɓi dole ta gaya mishi ko zata sami mafita, wani irin daɗi sosai ya ji, a cikin zuciyarsa ya ce dama daga ganin lips na Lion ai ansan kiss ya yi ɗan rainin wayo, zan yi bayani ne, ya kama ƴar mutane yana shanye mata baki bayan ya gama yi wa babanta rashin mutunci, wlh Lion ina tausaya maka. A zahiri kuma cewa ya yi "Rimsha ki kwantar da hankalinki, Lion fa mijinki ne, uncle ya ce kada na gaya miki, amma tun da an zo wannan gaɓar ba zan iya ɓoye miki ba, amma kada ki nunawa uncle na gaya miki, dan baya son ɗaga miki hankali ne yasa ya ce kada a gaya miki, yana tunanin zaki shiga damuwa idan kika sami labari, bai san cewa kina son Lion ba, ni kuma ban gaya mishi ba, saboda bamu samu lokaci ba, yanzu abin da nake so dake ki yi wa mijinki biyayya, ki kula mana da shi sosai kamar yanda na sanki, zan turomiki video in da aka ɗaura auren naki ma a palo ranar, amma ta wayarki zan turo miki, dan bana son Lion yasan na ɗauki video, to dan haka ki kula, asha soyayya lafiya ƴar soyayya, amma ki rinƙa gayawa baby nima ta rinƙa gaya mini kalaman soyayya, idan ba haka ba, muma jirgin ruwa zamu hau".
Cool murmushi ta saki tana ɓoye fuska na rashin kunya, wai ita a dole ta ji kunya, guntun tsaki Jehan ta ja zata mike ta bar wajen, cikin sauri ya rikota yana faɗin "Sister zan kiraki ta wayarki anjuma". Ya kai karshen maganar tare da katse kiran.
Wani irin daɗi na wuce misali ta tsinci kanta a ciki, mikewa ta yi ta diro kasa daga saman gadon ta nufi waje, tana ƙoƙarin fita shi kuma yana shigowa, karo suka yi ta ɗan yi baya kaɗan dan ta bashi hanya ya wuce, tsayuwa ya yi yana kare mata kallo, ta yi kyau sosai da ita, wayarsa ta miƙo mishi sai murmushi take yi baki yaki rufuwa tana wani sunkuyar da kai kasa, mamaki yake yi na abin da ya sanya murmushi haka kamar ba ita ce mai zuba kuka yanzu ba, tuna cewa da Areef ta yi waya, yasan fin murmushi ma zata yi in dai Areef ne, karɓar wayar ya yi yana faɗin ta zo ta zuba mishi abincin, okey ta amsa mishi da shi tare da juyawa ta koma cikin bedroom ɗin.
Ya fa sha ruwan mamakin ganin yanda take ta uban murmushi kamar ba lafiya ba, abincin ta zuba mishi tare da tura mishi a gabansa, cike da murna ta miƙe da nufin ta fita, calmly ya ce ta zo ta zauna taci abincin mana, ba ɗazun ta ce tana jin yunwa ba? Ina ai murnar sanin shi mijinta ne yasa ta ƙoshi ma, sam ta nemi yunwa ta rasa, ya gudu, ta ƙoshi ta bashi amsa tare da ficewa waje dan ya kalli a ina suke.
Ba ƙaramin razana ta yi ba ganin irin tabkeken tekun da suke ciki, ihu ta kurma dan ta razana ba kaɗan ba, ta yi ihun kuma tana runtse idanu tare da ɗaura hannu ta toshe kunnuwanta. Da sauri sojoji biyu suka yi kanta dan a tunaninsu wani abin ne, shi kuwa Lion kai ya ɗaga yana kallon Tv dake manne a cikin ɗakin wanda yake haɗe da camera da zaka iya kallon waje, da farko sam bai yi niyyar tashi ba, amma ganin sojojinsa sun nufeta yasa ya mike ya bar abincin ya nufi wajen.
Dai'dai lokacin da ya fito su ma sojojin suka iso wajen, ganin shi yasa suka yi baya dama basu yi tunanin yana kusa bane yasa dole suka nufeta dan su tabbatar da tana lafiya ba wata matsala, a cikin ruwa suke so ko wani lokaci ana iya samun matsa, wata kila wani abin ta gani shiyasa ma suka yi yunkurin kawo mata taimakon gaggawa.
Wani irin mugun kallo ya watsa mata wanda ya sanyata haɗa malaman jikinta tare da wucewa sumui sumui ta koma cikin ɗakin nasu, bin bayanta ya yi ya wuce saman bed ya kwanta, cike da tsoro ta ce "Yaya Saif abincin fa? Naga baka ci ko rabi ba". Shiru ya yi bai tanka mata ba, bata san cewa in dai ya fara cin abin baya tashi ba, idan kuma ya tashi to fa ya hakura da abincin kenan sai dai kuma wani lokacin.
Ganin bai kulata bane yasa ta tattare kayan abincin tas ta haɗesu waje guda, tana son kwanciya Brady na banci a saman sofa, ita kuma tana tsoron hawa gadon nasa, wayarta ta ɗauka tare da shinfiɗa dadduma a kasa ta zauna ta fara kiran number Akila dan su yi waya, lokacin da kiran ya shigo wayar Akilar, sai shagwaɓa Aseef yake zuba mata a kan shi gaskiya tare zasu yi wanka, idan ba haka ba ba zai ci abinci ba, sai biye mishi take yi ita ma tana zuba mishi shagwaɓa, har mantawa suke yi da duniyar da suke ciki idan suna tare suna zuba shagwaɓar nan tasu, ji suke yi tamkar su cinye juna dan so da kauna.
Da farko ya ce bazata ɗauki kiran ba har sai ta amsa mishi da zasu yi wanka tare, zai yi mata ta yi mishi, yana kwance saman bed daga shi sai short da singlet, ita kuma kayansa ne pajama a jikinta, taki sanya wanda ya saya mata a shopping, dan ta ce wlh ba zata iya saka su ba, duk kayan bana mutunci a ciki, daga ƴar pant mai haɗe da bra sai pant mai igiyoyi, ta ce bazata iya sakawa ba, shi kuma ya ce ya fahimci sai ya yi disvirgin nata zasu shirya, hakuri ta rinƙa bashi kafin ya hakura ya kyaleta ɗazun kenan, sai da ma ta haɗa mishi da kukan gaske, sannan ne ya ce ya hakura ya barta sai Lion ya dawo.
Ganin kiran Rimsha ne yasa ya barta ta ɗauka, da farko ya hanata, cikin zumuɗi ta ɗauka tare da sanya wayar a hand-free dan tasan mijin nata ba hausa yake ji ba.
"Aunty Akila ina wuni". Da fara'a ta amsa da lafiya tare da tambayarta ya angonta, da mamaki ta ce "Aunty Akila kenan kema kin sani?" Jinjina mata kai ta yi tana faɗin "E mana na sani, Heartbeat ya gaya mini, shi ma kuma Yaya Areef ne ya gaya mishi. Ɓoye fuska ta yi kamar tana gaban Akilar tana wani murmushi. "Kai Aunty Akila shi ne ni baki gaya mini bako?" "Ke ban son tsiya ta ina zan gaya miki ɗin? Ke da a gidan nan lokacin da kike nan ba mai ganinki, da kin dawo daga school kin wuce wajen mijin naki, to Allah dai yasa kina kula mana da yayan namu sosai, ba ki zauna ki na yi mishi shirme ba, kin san fa shi yana da wuyar sha'ani kuma ba shi da shi in ji heartbeat".
Shiru ta ɗan yi kafin ta ce "Aunty Akila ni ai yau ne ma yaya Areef ya gaya mini". "Kai dama ɓoye miki suka yi zasu cuci yayana a banza ko? Lallaima waye da ɗanyen aikin nan kuma?". Kai tsaye ta bata amsa da daddy ne ya ce a ɓoye mata, jin cewa bappanta ne yasa ta waske da cewa.
"To shikenan hakan ma bappa ya yi dai'dai, yanzu dai ba kin sani ba? Sai ki ɗaura ɗamarar kula mana da yaya sosai, ki tabbatar kina sanya shi farinciki, kada ki yarda ki bari ya shiga damuwa, kullum ki rinƙa kasancewa kusa da shi, dama ke ba mai son manyan kaya ba ne, so ki rinƙa zuba mishi wankar irin su short zuwa cinyar nan da sauransu, ki tashin kansa, kin san zuciyar sojoji sai kin yi da gaske, dan a bushe zuciyar take sosai, zaki sha wahala kafin ki zuba mata ruwa ta yi laushi, bar ganin misali ace yana sonki, wlh kika yi mishi ba dai'dai ba tsab zai manta da soyayya ya yi ball da ke, so kada ki yi la'akari da cewa dan yana sonki zaki yi mishi wasu abubuwa da zasu ɓata mishi rai, ko ki ce zaki gwada shi, irinsu ba'a gwadasu wlh, idan kika yi kuskuren yin haka kuwa idan baki yi sa'a ba kina iya rasa wani abu na daga halittar ki, sai dai daga baya su dawo suna danasani mara amfani ke sun rigada zuciya ta ɗebesu sun cutar dake, to kamar yanda na sanki da natsuwa, kowani namiji yana son mace mai natsuwa ba mai rawan kai ba, kin fini sanin waye shi, ki sami kamar kwana uku kina yawan zama kusa da shi dan ki karanci abubuwan da ya fi so, da kin karanta shikenan ina mai tabbatar miki yaya Saif ba zai yi miki wahalar Juyowa gabaɗaya gareki ba, ko wani namiji da abin da ya fi so a tattare da mace, iya abin da na sani dai shi ne babu namijin da baya son mace mai shagwaɓa, wannan shagwaɓar shi yake banbanta mace da na miji, ko ya nuna miki a zahiri baya so, wlh a cikin zuciyarsa daɗi yake ji idan kinayi, zaki ga wasu mazan idan kina yin shagwaɓa zasu nuna kamar basu so basu damu ba, wlh suna jin daɗi sosai, akwai wasu kuma matan ne sam basu iya shagwaɓar ba, wata zaki ga sai yana cikin ɓacin rai ta zo tana wani turo mishi baki ita a dole zata yi mishi shagwaɓa, irin haka idan aka samu ɓacin rana sai ki ga ya tsinka mata mari dan ransa a ɓace yake, so komai yana da lokacin da zaki yi wa namiji, yanzu dai ki karanto mana yaya Saif tsab sai musan ta yanda zamu yi maganinsa, babban shawarar da zan baki a nan dai shi ne, kada ki yarda yana saman gado kina saman kujera, mallakinki ne mijinki ne, ato yana sama kina sama, idan da damama ki shige jikin kayanki kina masa wasa, a lokacin zaki iya zuba mishi shagwaɓa son ranki dan yana kwance ne ba abin da yake yi sai tunaninki or tunanin duniya, dan haka ki mantar da shi a wani duniya yake da salon shagwaɓarki, kinga yanzu ku biyu ne, ki rinƙa rikita mishi kwakwalwa da wanka na shegun kaya masu watsa mishi tunaninsa, kin san dai ba sai na gaya miki ba bai taɓa yin soyayya ba, so yanzu fa ko da kin rumgume shi ba zai ce miki komai ba, ba zai wani damu ba koda kin kwanta a jikinsa, ba zai ce miki ki tashi ba, ba kuma zai ɓata rai ba, ba duka ba zagi, haka zalika babu harara, so kawai wani lokaci idan yana tsaye ki haye bayansa ki kwanta, zaki ga sai dai ma ya sanya hannu ya rikoki da kyau, amma fa ki rinƙa fahimtar sai idan baya cikin ɓacin rai zaki yi mishi hakan, bari na gaya miki idan yana cikin ɓacin rai yanda zaki rarrashe kayanki cikin sauki ya sauko ba tare da ya sani ba, ya manta komai ya afka duniyar da kika ja shi ciki, idan yana cikin ɓacin rai ki........." Kwace wayar Aseef ya yi yana mamakin irin surutun da take zubawa babu ko hutawa, ga shi baya jin me take faɗa tun da ba Hausa yake ji ba, sai magana kawai yake ganin tana yi kamar calbi ya tsinke.
Kuka ta saka mishi tana faɗin "Kai My shagwaɓati ni ka bani wayata bamu gama ba". Da yake bai katse kiran ba Rimsha tana jinsu duk irin shagwaɓar da Akilar take zubawa. "Ni gaskiya ba zan baki ba, ki huta da maganar haka ya isa mana, tukun nan ma me kike gayawa Mrs Lion ɗin?" Turo baki ta yi tare da yin ƙoƙarin sauka daga gadon, jawota jikinsa ya yi yana faɗin "Haba my sarkin rigima to ina zaki je baki bani kiss ba? Ni fa Allah kuka zan yi miki idan kina yi mini rowar kayana".
"Ni my heartbeat ka sakeni mun ɓata, ina tsaka da bawa kanwata lecture ne zaka hanani, so kake ta sha wuya wajen