Showing 255001 words to 258000 words out of 359620 words
ce "Ba zan amsa ba, ai kin san laifin da kika yi mini, dan haka ina fushi".
Shiru ta ɗan yi kafin ta ce "To kayi hakuri". Shiru bai amsa ba, sake maimaita mishi good morning ɗin ta yi. "Waye ya ce jiya ki kashe mini waya?" Ya tambaya yana cire glass ɗin face nasa, kara faɗaɗa murmushinta ta yi tana faɗin "To ba kai ne ba kayi mini wani maganar da sai da kasa na kashe wayar baki ɗaya". Zubawa ɗan bakin nata idanu ya yi yana kallon yanda take magana, ita dai Rimsha yau taga ikon Allah, wai dama Mark yana magana haka? Wai dama ya iya magana kenan? Ai ita ta ɗauka daga okey sai no ya iya, sai ga shi yau suna zuba hira da Anaya har da wani wai ya yi fushi dan an kashe mishi waya, innalillahi wa inna ilaihir rajiun, nan take kuma tunanin Lion ya faɗo mata a ranta na yanda ya canza kwana biyun nan, haɗa abin waje guda ta yi wato da canzawar Mark da kuma canzawar Lion, ta haɗesu waje guda tana tunanin tabbas da Mark da Lion ɗin basu da lafiya ne kila, dole da akwai wani abin a kasa.
Tana can tana tunani ita kuma Anaya tana rarrashin masoyin nata, dan fa ya ce shi ya yi fushi gaskiya, a kan me zata kashe mishi waya daren jiya suna tsaka da hira, daga karshe dai sai da ta buɗe motar ta shiga ta zauna ta bashi hakuri da kyau sannan ya hakura tare da miƙa mata hannu suka gaisa, ganin abin nasu azimun ne yasa Rimsha ta yi gaba abinta tana faɗin Anayar ta sameta a cikin class ita bata iya tsayawa.
Cikin zolaya ya ce "Kinga kin kori matar oga ko?". Yar dariya ta yi tana faɗin "Au matar oga ce ma kenan?". Jinjina mata kai ya yi. "Yes matar oga ce, amma fa nina aura mishi ita, shi bai ce yana sonta ba, kawai nina lura da yana sonta ne yasa nake ce mata matar oga". "E lallai ka iya sa ido kam". Ta kai karshen maganar tare da fitowa daga cikin motar ta nufi class nasu tana yi mishi bye bye, ɗaga hannu ya yi shi ma yana yi mata tare da zuba mata idanu har ta kurewa ganinsa ta shiga class nasu.
Ajiyar zuciya ya sauke tare da ciro wayarsa ya fara latsawa kamar dai kullum.
After some hours gidan Lion .
Fitowa daga bedroom nasa ya yi hannunsa rike da wayarsa, yana sanye da pajama ya nufi bedroom ɗin daddy, dai'dai zai shiga Areef ya kariso wajen shi ma zai je wajen daddyn ne, a tare suka shiga.
Kwance a saman bed suka isko daddyn nasu yana kallon kwallo a Tv, shi kuma Aseef yana bedroom nasa shi da AKila, ya ce ta shirya suje ya saya mata kaya kafin Lion ya dawo daga tafiya sai su haɗa musu akwatinsu tun da ta ce mishi mu a al'adar mu anayin lefe, to yanzu dai zasu je sayan kayan da zata rinƙa sakawa ne kafin Lion ya dawo su sami kwanciyar hankali sai a sayi koma me, ta kafe sam ba zasu fita ba ya bari sai ya sami lafiya, ai zata rinƙa sanya kayan Rimsha, shi kuma ya ce no akwai kayan da yake da ra'ayin ta rinƙa sanya mishi ne ba irin na Rimsha ba, shi baya son dogayen riguna, hakan yasa ta lallaɓa ta je ta gayawa Areef dan gaskiya bata son ya fita, seriously bashi da lafiya, Allah ma yasa yana da sauran kwana a gaba ai da hanashi aurenta da akayi ba abin da zai hana shi mutuwa, abin ya taɓa shi ba karya.
Da ta gayawa Areef ne sai ya ce Okey to kada ta damu ta kyale shi su gama shiri, dama zai kai Rimsha yin shopping anjuma idan ta dawo daga school Lion ya sanar da shi, to sai su tafi tare, shi ne ta dawo suke shiryawa tare.
Gefen daddyn Areef ya zauna, shi kuma Lion a saman sofa ya zauna yana faɗin "Dad zan yi tafiya gobe, do you want something from me?". Dawo da kallonsa kan shi daddyn ya yi yana girgiza mishi kai alamar baya bukatar komai. "Okey to ba lallai mu sake samun time na zama da kai ba, dan daga nan Abuja zan je, na sanya a shirya mini jirgin ruwa, so ina busy gaskiya, na wuce wata kila da daddare zan shigo idan na dawo da wuri". Ya kai karshen maganar tare da miƙewa tsaye da nufin ya fita.
Jin ya ambaci jirgin ruwa ne yasa daddyn ya ce "Wai Romeo ina ne zaka je?". Kai tsaye ya amsa mishi da Russia. A tsananin razane daddyn ya diro kasa daga saman gadon nasa yana mai maimaita sunan Russia. "No Romeo, kasan me kake faɗa kuwa? Russia fa? Ba zai yiwu ba gaskiya! Ba zaka je ba, bana son ka sake yin maganar ma a nan, koma me zai kai'ka to ka hakura!!". Ya yi maganar yana ɗaure fuska sosai.
Cikin kwanciyar hankali ya ce "Dad already na gama shiri so sai na dawo kawai, amma zuwa ban ga abin da zai hanani ba".
"Romeo na ce maka bana son, bana da bukata, kuma ba zaka je ba!!". "Daddy dama ai ba sonka nake bi ba, ba bukatar ka nake so ba, tafiya ce sai na yi, aiki ne zai kai ni can, so ba umarninka zan bi ba!!".
Cikin tsantsar ɓacin rai ya ce "To zamu gani, idan ka isa ka je mu gani" "Zaka gani dai, tafiya babu fashi, ka sa na kara jin son tafiyar ma da kace baka so, ni duk abinda ba'a so shi nake so!!" Tashin hankali, daddy fa ya sha jinin jikinsa, domin wannan kalma da Lion yake yawan faɗa na duk abin da ba'a so shi kuma shi yake so, to best kalmar daddyn ne lokacin da yake tashen samartaka, ya kware a furta kalmar kamar ba gobe, ya azabtar da mutane da dama ta dalilin wannan kalma, so yanzu abin ya fara damunsa gaskiya, dan kuwa Lion ya fi shi kwarewa a iya furta wannan kalma da kuma aiki da ita, wannan shi ne ɗan na gada ya fi ɗan na koya, abu fa ya fara damun daddy ba karya, wannan shi ne ramakon gayya ta fi ta gayya zafi!!.
Da sauri Areef ya mike ya karisa wajen ɗan uwan nasa yana faɗin "Lion please and please ka fasa wannan tafiyar, tun da daddy ya kafe baya so, kuma kai kanka kasan irin mummunar alaƙar da take a tsakaninmu da kasar Russia, so ka hakura kawai tun da ya nuna baya so, kuma wlh nima bana so, kirjina har dukan uku uku yake yi idan na tuna zaka yi tafiya kuma ga in da zaka je".
Wani irin mahaukacin razanannen tsawa ya dagawa Areef ɗin ransa a ɓace, cikin fushi ya fara magana "Areef ai ni dama abin da ba'a so shi nake aikatawa, ya rage nashi ya yi mini fatan alkhari or not!, Ka gaya mishi tafiya babu fashi, duk abin da zai faru ya faru!!". Ya kai karshen maganar tare da nufar kofar fita, da sauri Areef ɗin ya sha gabansa yana faɗin "Gaskiya babu in da zaka je, dan bamu shirya rasa ka ba!".
Wani mahaukacin damka ya kaiwa Areef ɗin a wuya, rai a matukar ɓace, nan take wasu siraran jijiyoyi suka bayyana mishi a wuyarsa, har wani zufa yake haɗawa, idanuwansa sun yi jajir yau daddy ya nuna mishi isa har da wani cewa to ya tafi ɗin ya gani, kuwa zasu gani iya ganin idanunsu, tafiya dai babu fashi. A kausashe ya ce "Ko ku shirya rasa ni ko akasin haka, sai na tafi, ka bani hanya tun ban yi ball da kai ba!!".
Rai a matukar ɓace shi ma Areef ɗin ya damko wuyar Lion ɗin, sai huci yake yi ya ce "Lion babu in da zaka je wlh!!". Ganin suna ƙoƙarin fara faɗa ne yasa daddyn ya yi saurin zuwa ya shiga tsakaninsu yana ƙoƙarin rabasu, dan kuwa yasan faɗarsu idan ta fara babu kyan gani sam, duk sai sun jiwa kansu ciwo, sai sun yi wa kansu fata fata, babu tausayi suke jibgan junansu tamkar ba jini ne a jikinsu ba, idan suka fara faɗa, zaka rantse da Allah wasu shahararrun abokan gaba ne, mafiya yawan lokuta sai Lion ya gama illata Areef sannan yake hakura, wani lokaci ma sai ya sumar da Areef ɗin sannan ya ɗaukesa juna word room ya fara bashi taimakon gaggawa, haka suke kamar wasu zakuna a dokar dawa idan suna faɗa.
Jan Areef daddy ya yi dan yasan shi ne mai hakurin da zai iya dannarsa kuma ya danne ya hakura, shi kuwa Lion ina ai idan ya zuciya baya ji baya gani, shiyasa daddyn bai yi yunkurin tinkararsa ba. Sakinsa Lion ɗin ya yi tare da nufar waje abinsa, shi kuma Areef daddy ya mayar da shi saman bed tare da ɗauko mishi ruwa mai sanyi daga cikin fridge, karɓar ruwan ya yi tare da buɗewa ya kafa a ɗan bakinsa yana mai jin zafi a zuciyarsa, sam baya son tafiyar ta Lion wlh, amma ya zai yi? Dole ya hakura, dan kome zasu yi wlh sai ya tafi kamar yanda ya faɗa.
Lion kuwa yana barin bedroom ɗin ɗakinsa ya nufa, wanka ya yi tare da shiryawa ya fito shi da Tyrone suka nufi Abuja dan ta Lagos zai fita kasar, shirye shiryen kuma daga Abuja aka farota.
A ɓangaren su Rimsha kuwa, sun rubuta Exams lafiya lou, sai murna suke yi, Anaya ta bawa Rimsha wani haɗaɗɗen yaji da mummyn Rimsha ta kawo musu daga Maiduguri, yaji yana da bala'in daɗi sosai, dama tana kawo musu duk idan zata zo, to wannan karon dai da yake Anaya tana tare da Rimsha sai ta deɓo mata dayawa ta bata, sosai Rimshar ta ji daɗi dan rabonta da cin yaji tun suna Abuja tare da su mummyn nata, idan baku manta ba a gidan Lion ba'a dafa abinci da ya ji, dan basu ci dukkansu, suna yin gym basu isa da cin yaji ba, zai yi musu mummunar illah dan gym ɗin da suke yi ba irin na kananan yara bane.
Sai murnar samun yajin take yi ta karɓa Anayar ta yi mata rakiya har wajen mota, sai bayan ta yi mata bye bye ne ta juyo ga Mark, ya zuba mata idanu yana kallonta, cool murmushi ta sakar mishi tana yi mishi bye bye. Waya ya ɗauko ya fara ɗaukarta hoto tana murmushi wani wajen kuma ta rufe fuska da hannunta, a wani wajen ta turo baki tana faɗa mishi bata so, hotuna dai kala kala ba iya ka ya ɗauketa, ita dai Rimsha wannan abin yana bata mamaki, har ƴar zazzaɓi zazzaɓi ta rinƙa ji na ganin irin sauyin Lion da Mark, gara ma shi Lion ba lokaci guda ya sauya ba, da kaɗan da kaɗan abin ya kama shi, tun zuwansu Abuja da suka dawo, a hankali komai ya sauya mishi, amma har yanzu dai kaso 70 na cikin halinsa na baya yana nan, a hankali hankali dai yana sauyawa, shi kuma Mark lokacin guda ya sauyawa iya Anaya kawai kamar yanda shi ma Lion ɗin iya ita Rimshar ce kawai take ganin ya ɗan canza mata, bayan ita babu wanda ya canzawa, kamar dai yadda yake a baya haka yake a yanzu ga kowa, shi ma Mark hakan yake ga kowa banda Anayarsa, ita kaɗai yake sake mata har su yi magana.
Sai da ya ɗauketa hoto iya son ransa kafin ya ɗan matso da face nasa ta glass ɗin motar yana magana kasa kasa, sam dukkansu basu ji me ya faɗa ba, dan haka sai Anayar ta matso kusa da shi sosai tare da ɗan rankwafowa kansa tana tambayarsa me ya ce, da yake su basu san me kunya ba a rayuwarsu, sai ya sumbaceta a kumatu yana faɗin abin da ya ce kenan ta zo ya sumbaceta su yi bye bye, sam Rimsha bata ga abin da ya yi ba, dan tana ciki, kuma ta mayar da hankalinta kan students dake safa da marwa a wajen, ita kuma Anaya rufe fuska ta yi tana murmushi ta bar wajen da sauri, komawa cikin motar da kyau ya yi tare da kunnata ya ja suka bar waje zuciyarsa cike da tunaninta.
After some minutes, bayan ta yi wanka ta ci abinci ne ta ɗauko sim card nata ta nufi bedroom ɗin Lion, bakinta ɗauke da sallama ta shiga, baya nan yana Abuja basu dawo ba, dressing room nasa ta shiga ta ɗauko wata danƙareriyar waya mai bala'in tsada, wayar ta yi mata kyau over, kunnata ta yi sai taga hotonsa ne a saman screen ta fuskar wayar, yana zaune a bakin pool nasu na Washington DC, daga shi sai kayan shan iska, farare tas masu bala'in kyau, kafarsa na sanye da wasu takalma masu bala'in kyau irin home sleepers ɗin nan, ya ɗaure gashin kansa ya bar wannan guntu na gaban goshin, idanunsa akwai glass blue color, ya yi kyau over. Ba karamar daɗi ta ji ba, sumbatar wayar ta yi tana murmushi, kai kallonta saman wayar ta yi sai taga akwai sim card a cikinta, shiru ta ɗan yi tana tunanin to sim ɗin waye? Ta cire ta sanya nata ne ko kuma dai ta barshi a ciki kamar yanda ta gani?.
Ganin babu mai bata amsa ne yasa ta fito daga cikin room ɗin zuwa cikin ɗakin tare da zama a gefen gadonsa, tunani ta fara yi wai shin ina yake ne ma? Ina ya tafi? Ganin shi ma babu mai bata amsa ne yasa ta miƙe ta fita zuwa wajen Areef dan su tafi shopping bayan ta sanya sim card ɗin nata.
A ɗakin daddynta ta isko Areef ɗin, ya tasa Jehan a gaba sai tsokanar yake yi daddy nayi musu dariya, saman gadon ita ma ta haye tana faɗin "Yaya Areef mu tafi". Kallon kayan jikinta ya yi kafin ya ce "Jeki saka wannan abin da kuke sakawa har kasan nan, irin wanda kika saka da safe, ki rufe jikinki kaf". Okey ta amsa mishi tare da cewa "Daddy yaya Saif ya ce na koma ɗakinsa da zama, ya ce ko palo bai yarda na fita ba, yanzu ma shi ne ya ce yaya Areef ya kai ni shopping". Ta yi maganar tamkar zata yi kuka.
Jinjina mata kai daddyn ya yi yana faɗin "Duk abin da ya ce miki to kibi umarninsa kin ji ko my daughter?". Gyaɗa mishi kai ta yi zuciyarta cike fal da mamaki. "Allah ya yi miki albarka my siha". Amin ta amsa da shi, duk jikinta a mace, Areef ya lura da hakan, dan haka sai ya yi ƙoƙarin sanyata farinciki, da haka ya ce da Jehan ta shirya suje shopping ɗin, kai tsaye ta ce bazata je ba, bai tilastata ba, ya rabu da ita suka tafi shi da Rimsha sai Aseef da AKila, sun bar daddynsu daddyn Rimsha dasu uncle Herry a gida.
Sun sha sayayya ba kaɗan ba, duk kuma abin da suka saya Lion ne ya biya kuɗin, dan a ɗakinsa Areef ya ɗebo musu kuɗin, Aseef kayan shanawa dana barci kawai ya ɗebawa Heartbeat nasa, ita ma Rimsha ta ɗauki kananan kaya sosai, sai kuma jallabiyoyi da perfume, sai hijabai guda biyu da kuma kayan Indian ta da zata sanya gobe, daga karshe ta ɗauki vest dozen ɗaya farare tas.
Shi kuma Areef ya sayawa Jehan kaya da yawa, ciki kuma har da breziya da su pants, dan yasan size nata gabaɗaya, idan baku manta ba da tana prison ya saya mata pants, kuma ba wani bane ya gaya mishi size nata, da idanunsa ya auna kawai, ganinta yasa ya gane girman komai, da haka sai ya saya mata komai dai'dai ma'auninsa. Sun sha sayayya ba karya sannan suka dawo gida.
Har ɗaki Areef ya kaiwa Jehan ɗin kayan, ita kuma Rimsha ta wuce bedroom ɗin Lion da gabaɗaya kayanta da suka sayo, a dressing room nasa ta shirya komai, Aseef da Akila suka wuce bedroom nasu. Bayan ta kammala komai ta ci abinci ta yi wanka ne ta haye saman sofa ta yi kwanciyarta dan ta yi barci, ba jimawa barci ya yi awon gaba da ita.
A ɓangaren Jehan kuwa, sun sha dirama da Areef, data ga kayan da ya saya mata ne ma yasa ta kara yarda wlh shi ɗan iska ne da gaske, ji ta yi ta kara tsanarsa, idan ba iskanci ba me na saya mata su breziya? Shi kuma dai yasan matarsa ce tun da daddy ya bashi aurenta, kuma har sadakinta ya biya, ba ɓata lokaci ya bawa daddyn bakudan kuɗaɗe daloli daya kwaso a wajen Lion, shi kansa bai san nawa bane, kawai ya zubewa daddy a matsayin sune sadakinta, shiyasa baya shayin ya yi mata duk abin da ya yi niya.
Da misalin karfe 8 na dare, sosai Rimsha ta shiga damuwa ganin Lion yau sam bata gan shi a gidan ba, ta rasa waye kuma zata tambaya, ta yi barcin ta har ta tashi ta yi wanka, ta je kitchen ta ɗauko mishi abincinsa ta zo ta yi sallar mangariba da issha, amma shiru bai dawo ba, kunna wayarta ta yi tana duba time, shiga cikin wayar ta yi tana dubawa, da alama wayarsa ce da ya taɓa amfani da ita, dan akwai hotonansa dayawa a ciki, sai dai kuma wayar ta yi kama da sabuwa ce sosai, bayan hotonsa babu wani abin da yake cikin wayar.
Shiru ta yi tana tunanin ina kuma ya shiga, ga shi bata san numbersa ba bare ta kira shi, komawa ta yi ta kishingiɗa a saman sofa tana tunanin mafita.
Can kasan maƙoshinsa ya yi sallama tare da shigowa cikin ɗakin, tamkar ta watsa a guje ta yi mishi oyoyo haka take ji, ba karamin daɗin ganinsa ta ji ba. Sannu da dawowa ta yi mishi, sam bai amsa ba kuma bai bi ta kanta ba, da alama ransa a ɓace ya dawo, toilet ya nufa, shiru ta yi tana tunanin yanda face nasa, ta razana ba kaɗan ba, dan da alama a kusa zuciyarsa take