Showing 180001 words to 183000 words out of 359620 words
ci ba?". Ya yi maganar tare da ɗaukar key ɗin motar ya fice daga ɗakin "E ban ci ba, Heartbeat ni fa ba zan iya cin abincin bane, ko na saka a bakina ba zai wuce wuyana ba".
Kitchen ya shiga, da kansa ya ɗebi abinci daga cikin na Lion ya zuba mata a cikin wani dankareren kula mai bala'in kyau, dan yasan dama Lion baya cin ko rabin abincin da ake zubawa a kular tasa, shiyasa ya ɗeba mata, spoon ɗaya ya ɗauko tare da fitowa ya nufi motarsa, da gudun gaske ya tada motar ya fice, a lokacin ita ma Rismha tana ɗakinta kenan tun da baya muka koma.
Sai rarrashinta yake yi a wayar ba tare da ya gaya mata yana zuwa gidansu ba, duk magana idan ya yi sai ruwan hawaye ya kara tsananta a fuskarta, ita kaɗai tasan raɗaɗin azabar da take ji, ba zata iya rabu da shi ba gaskiya. "Heartbeat wai ba zaki dai'na wannan kuka ba har sai kin saka ni yi nima ko?". "Kayi hakuri zan dai'na, amma ko na goge hawayen sai wasu sun zubo ne". "Okey to fito gani a waje". Ya kai karshen maganar tare da yin parking na motarsa a ɗan nesa da gidan nasu.
Zubur ta miƙe daga kwanciyar da take, nan take hawayen nata suka kara tsananta, dirowa kasa ta yi daga saman gadon wayar tana manne a kunnanta, kayan barci ne a jikinta, riga da wando ne masu laushi launin brown color, suna da bala'in kyau ba kaɗan ba, hijabi ta ɗauko zuwa gwiwarta ta sanya a jikinta tare da fitowa ta nufi bedroom ɗin Ammie, har lokacin tana ruwan hawaye, ba ɓoye ɓoye ta sanar da Ammie ga Aseef ya zo zata je wajensa, Allah sarki uwa da ƴa, ita kanta dama ta shiga damuwa matuka a kan halin da ƴar tata ta shiga, dan haka sai ta yar je mata akan ta je suga juna, sai dai kada ta jima dan taga Abba ya kusa dawowa, dan ma ya biya wajen Abbi ne ai da ya jima da dawowa, idan ya dawo ya sameta a waje da Aseef kuma zai yi faɗa sosai, dan ya gaya musu ya yi mata miji, to ta amsa mata da shi, ta juya har lokacin sai ruwan hawaye take yi, binta da kallo Ammien ta yi tana mai matukar tausaya mata, dan tasan wannan aure nata da Irfan babu mai rusa shi, yanzu ma ta barta ta je wajen Aseef ɗin ne dan tana da yakinin idan ta je zata rage damuwa, zata samu ta yi barcin daren yau.
Tun da ya hango fitowarta daga gida shi ma ya fito daga cikin motarsa, jingina da jikin motar ya yi tare da zuba mata idanu yana kallon ta, wani azababben kaunarta ne yake kara ninku mishi a cikin farfajiyar zuciyarsa, har ta kariso gabansa ba tare da ya sani ba, yana can yana tunanin mafita, zazzakar muryarta dake dashe sabida kuka ne ya dawo da shi daga duniyar tunanin da ya faɗa. "Sannu da zuwa ina wuni?" Shi ne abin da ta faɗa.
Ganin har lokacin hawaye na a kan fuskarta ne yasa ya ce "Har yanzu baki dai'na yin kukan ba?" Kasa ta yi da kanta tana faɗin "Heartbeat na gaya maka kukan ne yaki tsayawa wlh, ko na goge hawayen sai ya dawo". Hannunta ya kama tare da jawota ta faɗa saman faffaɗar kirjinsa, tun daga tsakiyar kansu har zuwa tafin kafarsu sai da suka ji wani irin shock, daurewa ya yi tare da ɗago haɓarta ya sanya kyakyawar farar hannunsa yana goge mata hawaye, tuni kukan nata ya tsaya cak, tun da ta faɗa saman kirjinsa ta nemi kukan ta rasa.
"To kinga na yanzu na goge miki hawayen dukka, kada ki bari wani ya fito kinji my rigimati?". Gyaɗa mishi kai ta yi alamar ta ji, nisawa ya yi yana tunani, a matsayinsa na namiji, dole shi ya ɓoye tashin hankalinsa da damuwarsa dan ya kwantar mata da hankali, idan ya nuna mata tsantsar bala'in da yake ciki abin zai yi mata yawa, to dole ya danne sosai.
"Me kike wani kallona haka?". Ya yi maganar a shagwaɓe dan ya mantar da ita damuwar da suke ciki, ɗan kwantar da kanta a saman kirjin nasa ta yi tana jan hanci bata ce komai ba, a hankali ya fara shafa bayanta kaɗan kaɗan, jin hakan yasa ta tashi daga jikin nasa cikin sauri tana koran shaiɗan ɗin da yake son ya shiga tsakaninsu, bai damu ba dan ta tashi daga jikin nasa, dama shi burinsa kawai ta yi shiru ta dai'na kuka, to kuma ya yi nasarar tsayar da hawayen nata.
"Zo mu shiga cikin mota kin ji ko?" Da farko taki yarda, sai da taga kamar bai ji daɗin hakan bane yasa ta ce to su je, gidan gaba ya buɗe mata ta shi, bayan ya rufe sai ya zagayo ta mazaunin driver ya shiga, wutar dake kan titin unguwar tana haska har cikin motar ta su, kular abincin ya ɗauko daga gidan baya tare da kawowa tsakaninsu, zuba mishi idanu ta yi tana kallon ikon Allah, buɗe abincin ya yi, wani irin daddaɗar kamshin ne ya daki hancinta, da yake ita kam tana cin ire iren abincin a manyan restaurant da suke sayan abinci, sai bata wani damu ba.
Ɗiba ya fara yi yana kai mata sai tin ɗan bakinta, tun tana nokewa har ta saki jiki tana karɓa, sai zuba mata hira masu daɗi yake yi har ta ci abincin sosai ba tare da ta sani ba, tissue paper ya ɗauko ya goge mata baki tare da rufe kular bayan ya tabbatar ta ƙoshi, ruwa ya sake ɗaukowa a kusa da su ya buɗe ya kai mata sai tin ɗan bakinta, kallon shi ta yi, kashe mata ido ɗaya ya yi kafin ya ce "Wai har yanzu duk da na tura miki hoton mu mu dukka uku kin kallemu, har yanzu ina yi miki kama da su sosai ta yadda baki banbantamu kamar yadda kika ce da farko?".
Jinjina mishi kai ta yi tana faɗin "E wlh ni kullum na kalli hoton sai in kalli kamar mutun ɗaya ne a wajen, ido ne kawai yake banbanta ku, na rasa wlh, sai dai Lion ya fiku cika, kuma kaman ya fiku tsawo ma". Kai mata ruwan bakinta ya yi ta karɓa ta fara sha. "Kin san menene?" Girgiza mishi kai ta yi tana kan shan ruwan. "Da ni da su ko a cikin duhu Rimsha tana iya banbanta mu, mafiya yawan lokuta daddy da ya haifemu idan yana magana a palo da Areef dake cikin bedroom, idan na amsa daga cikin bedroom ɗin a madadin Areef, to wlh baya gane ni na amsa, basu rabe muryata da ta Areef, duk duniya dama Lion ne kawai yake iya rabe muryoyinmu, na sha ruwan mamaki lokacin da Rimsha ta iya rabe muryoyinmu a rana ta farkonta da ganinmu, to haka take banbanta mu ko a cikin duhu, wani lokaci idan na rufe mata fuska ta baya zaki ji ta ambaci sunana, idan na ce waye ya gaya miki Areef ne fa ba Aseef ba, zata kafe lallai dole ni ne ba Areef bane, , shi kan shi Areef ya sha ruwan mamakin banbanta mu da Rimsha take yi a cikin duhu, bare ma masoyinta Lion, bata haɗa shi da kowa ba, karfi da ya ji ta rabamu, ko cikin zolaya idan na ce mata Saif ne bayan na rufe mata ido, zaki ji tana cewa, kai ina GAR ya fi haka, kai in takaice miki kome kika yi wa Rimsha dan ki rikitata a kanmu sai ta rabe miki mu tsab wlh, na rasa wani irin baiwa ke gareta, shi ma Areef ya gwadata har ya gaji ya hakura, su uncle T duk basu rabeni da Areef idan nayi magana, amma ita ina raba mu take yi tsab".
Dariya ta kwashe da shi tana faɗin "Kai ai dole Rimsha ta yi muku farin sani kafin ganinku, kasan yadda take kaunar Lion kuwa? Hmm banga laifinta ba dan ta ce muku bata haɗa shi da kowa ba, ai kai ma ban haɗa ka da kowa ba, gaskiya sosai Rimsha akwai kwakwalwa na wuce misali, gata da natsuwa sosai".
Hannayenta ya riƙo bayan ya ajiye robar ruwan, tsareta da idanu ya yi yana faɗin "Wace Rimshar ce mai natsuwa? Sai dai idan wata Rimsha a gidanku, amma mu na gidanmu kamar battery ake saka mata, tana da fitina ga neman rigima wajen Saif, watara Allah sai ya sumar da yarinyar nan ina da tabbaci". Murmushi ta yi tana wasa da ƴan yatsun hannunsa masu bala'in ɗaukar hankali, "Duk abin da kaga Rimsha tana yi wa Lion ni na gaya mata wlh, ni na san cewa yaro mai kiriniya yana da saurin shiga rai, na san idan tana yawan shiga harkarsa tana taɓa mishi abubuwa bai aiketa ba, dole watarana ya ɗago ido ya kalleta, a kwana a tashi dole ya fara sonta, Allah Rimsha ta sha bakar wahala akan soyayyarsa, idan ba shi ta aura ba, wlh aurenta ba zai taɓa zuwa ko'ina ba, tun tana da 9 years a duniya take haukar kallon shi a Tv, ni nasan a yadda yake ɗin nan, ba zai yi saurin ɗaura hannunsa a jikin mace da sunan duka ba, shiyasa na bata wannan shawarar ko kuma in ce maka kullum nake kara bata hakan idan mun yi waya, ta dai'na jin tsoronsa, ta rinƙa taɓa mishi wasu abubuwa nasa ba zai taɓa dukanta ba, amma a nawa ganin da nake masa fa kenan, bacin haka, wlh Rimsha nitsatsiya ce sosai, kuma idan ka lura ai Lion ɗin kawai take yi wa rashin ji ɗin, to ni nake zugata".
Nisawa ya yi yana faɗin "Yes da wuya Lion ya ɗaura hannunsa a jikinta da nufin duka gaskiya, ko ni ai ba zan daki mace ba, to wai me ma zaka daka a jikin mace? Ka je ka sumar ko ka kashe ƴar mutane a banza, mace ai bata da wajen duka a jikinta, shi Lion ma ya ce faɗuwa ce babba ga namiji ya sanya hannunsa a jikin mace da sunan duka, yo Allah na tuba Lion da yake mari manyan zaratan maza su faɗi su suma ina ga Rimsha kuma? Ai idan ya mareta sai mutuwa, gaskiya ma ba zai yiwu ba, duka kam a'a ba zai daketa ba, idan ta cika matsa mishi dai, sai dai ya bata punishment irin su frog jump da sauransu". Ya kai karshen maganar tare da kai hannunta dake cikin nasa saitin ɗan bakinsa ya sumbata.
Kasa kasa kamar mai raɗa ya ce "I really love my heartbeat, kece bugun numfashina, idan bake to babu ni". Buɗe tafin hannunta ta yi tare da ɗaura nasa hannun a saman natan, yazama kamar sun tafa da juna kenan, cikin shagwaɓa ta ce "Promise me that ba zaka taɓa barina ba duk wuya duk daɗi". Matso da fuskarsa daf da tata ya yi "I promised you that ko me wuya ko me daɗi ni naki ne, a kanki zan tsaya ba ja baya". Cool murmushi ta saki har sai da gaf teeth nata suka bayyana
Heartbeat ya ambaci sunanta a tsananin sanyaye, ita ma a sanyaye ta amsa mishi, "Fito da harshenki dukka waje bari na gani". Ba musu ta fito da ita, tana da tsawo sosai harshen nata, nauyayyar ajiyar zuciya ya sauƙe kafin ya ce tom ta mayar, mayarwa ta yi tana tambayarsa menene yasa ya ce ta fitar, jan dogon hancinta ya yi yana faɗin "Sai gaba zan gaya miki dalili". Make kafaɗa ta yi a kan lallai bata yarda ba sai ya gaya mata ita dai, kara matsowa kusa da ita sosai ya yi har suna iya jiyo sautin numfashin juna, "Ba kin ce na dai'na irin maganar sai mun yi aure ba?". Jinjina mishi kai ta yi alamar e, "To kin gani ki bari sai mun yi aure sannan zan gaya miki dalili".
Turo baki ta yi taso jin meyasa ya kalle mata harshe, amma ba komai ai, yanzu ma da ya ce sai sun yi aure tun da ta ce ya dai'na irin wannan magana, ta fahimci ina ya dosa, sai dai bata san me na'amar hakan ba, ta dai fahimci duk zancene da ya shafi ma'aurata.
"My shagwaɓati zan koma gida kada Abba na ya dawo ya sameni a waje, zai yi faɗa sosai, Ammie ta ce kada na jima". Har cikin ransa sai da ya ji wani raɗaɗin zafi, amma haka ya danne tare da gaya mata kalamai masu daɗi dan kada ta shiga gida ta shiga cikin damuwa koma ta yi kuka, sai da ya tabbatar ya sanya ta farinciki sosai har da dariya kafin ya ce to suje ya taka mata zuwa bakin gate. A tare suka fito suka nufi gidan, sai hira yake zuba mata, burinsa ta mance da komai ta yi barcin cikin farinciki.
Sai da suka je bakin gate ne ya ɗan jawota jikinsa ya rungume, dan su a kasarsu hakan ma sallama ce, ɗan shafa lallausan kumatunsa tayi kafin ta raba jikinsu ta wuce zuwa cikin gida, binta da kallo ya yi har sai da ta shiga palo sannan ya bawa mai gadi dama ya rude gate ɗin, ya juya zuciyarsa cike tab da bakin ciki, shi kaɗai yasan me yake ji.
Cikin mota ya koma ya zauna tare da kifa kansa da jikin steering motar yana jin zuciyarsa na tafasa kamar zata kone, yanzu ko hawayen ma ya nema ya rasa, saboda bala'in ta kai mishi bala'i. Ya jima a haka kafin ya kunna motar zuwa gida, yana kan hanya ta kira shi a waya dan ta ji ko ya isa lafiya, kin ɗauka ya yi har sai da ya koma sannan ya kirata suka cigaba da hira suna farantawa juna rai tare da kara nitsawa cikin kogin soyayyar juna. Shi kuma Areef yana can yana ta bincikensa, ya tasa hoton Jehan da ya ɗauko daga laptop ɗin Lion yana kare mata kallo, shi dai wlh ta shiga ransa ba kaɗan ba, musamman idan ya kalli idanun nan nata masu kama dana daddynta, suna matukar burgesa, abin da baku sani ba gabaɗaya TRIPLETS Allah ya jarrabesu da bala'in kaunar manya manyan idanu, suna ɗaukar hankalinsu sosai, bare ma idan idanun suka kasance farare tas abin ba'a magana, ga family'n Dr Salman kuwa gabaɗayansu ba baya ba wajen manya manyan dara daran idanu, shi ne yasa Lion yake bala'in son idanun Rimsha, sun kasance manya manyan farare tas, ga su sleeping eyes, ai dole ma ya so su, dan abin nasu a jini yake.
A ɓangaren Rimsha da Lion kuwa, barci gabaɗayansu suka koma, iska mai daɗi yana kaɗa shi, ita kuma sanyi iskar ya yi mata, a hankali yayyafin ruwan sama ya fara sauka a kansu, wajen akwai runfa ta yadda ruwa ba zai shiga ba, to amma ruwan da iska sosai yake tafe yasa iskar yake kaɗo ruwan har ciki yake taɓa su.
A hankali ya waro dara daran blue eyes nasa tare da sauko da kansa kaɗan, karaf sai saman kyakkyawar fuskarta ya sauƙesu, sai zuba barci take yi kamar ba gobe, lumshe idanun nasa ya yi tare da sake buɗe su a kan face ɗin tata, shiru ya yi yana tariyo makusantar Josephine da ya sani ko zai ga mai irin wannan face ɗin, shi dai yasan tabbas ya taɓa ganin matar tare da Josephine to wace ce? A hankali ya kwantar mata da kanta a saman sofa tare da miƙewa ya nufi wajen fridge dake wajen, ruwa mai sanyi ya ɗauko, dawowa ya yi ya zauna a saman wata sofa daban, nan take ruwan sama ta kece kamar da bakin kwarya, shan ruwan tas ya yi tare da ajiye robar ruwar ya kishingiɗa a saman sofar tare da fito da wayarsa ya fara latsawa, a haka har suka kai asuba, ga ruwan sama yaki tsayawa, yana son komawa cikin gida ya ɗauro alwala zuwa masallaci, amma ina ruwa kamar da bakin kwarya yake zuba.
Da yake ita ma jikinta ya saba tashi da asuba, sai ga shi ta farka, tare da miƙewa zaune, wani azababben sanyi ne ya bugeta lokacin guda, cikin sauri ta takure jikinta waje guda, baiwar Allah ta yi barci mai nauyi bata ma san ana ruwan sama ba, jin zuban ruwa yasa ta fara waije waije dan nemo ina yake, can saman sofa ta ganshi a kwance yana latsa waya, ware jacket ɗin nasa ta yi tare da sanyawa a jikinta ta takure waje guda tana rawan sanyi, jacket ɗin ya yi mata yawa sosai. Shiru shiru har aka yi sallar asuba, shi kuwa yana kwance abinsa daga shi sai T-shirt polo da jeans sky blue, amma baya jin wani sanyi, ita ce dai ta takure kanta, dama kuma kun san yanayi ba ɗaya ba, shi ya saba da sanyi mai kankara, dole ba zai ji komai ba a wannan sanyi tamu ta nan.
Karar sautin garuwar hakwaranta yasa shi ɗago idanunsa izuwa kanta, mamaki yake yi wai ita wannan wace iriyar mutun ce? Yanzu sanyin me ake yi a nan da har zata rinƙa bari har haka? Kai anya ba wani cuta yake damunta ba kuwa?. Ayya shi bai san mu a wajenmu wannan sanyi ne sosai mai ratsa kashi ba. Cigaba da latsa wayarsa ya yi bai sake bi ta kanta ba har gari ta fara haske, sannan ne ruwan saman ya tsagaita, lokacin karfe 5:44, miƙewa ya yi ya wuce izuwa cikin gida, da sauri ta miƙe ta bi bayansa, a tare suka shige, kai tsaye ya nufi bedroom nasa ita ma ta nufi nata.
Sallah dukkansu biyu suka yi dan lokaci ya kure, haka zalika kusan a tare suka shiga wanka, dan a tare suka dawo cikin gidan, bayan ya yi wanka ya fito, shiryawa ya yi cikin pajama launin white color, saman bakin bed nasa ya zauna yana ƙoƙarin kiran number Areef sai gasu sun shigo a tare kamar abin haɗin baki.
Saman sofa suka zauna, cikin sanyin murya da nuna kula da juna suka ɗaga mishi gaisuwa, shiru ya yi bai amsa ba, can kuma sai ya ɗago da