Showing 348001 words to 351000 words out of 359620 words
auren Anaya ba har sai ya musulunta, ya ɗauka za'a iya bashi ita a haka, shiyasa ma har da ce mata zai zo yaga daddynta........ E lallai akwai chakwakiya.
After some hours. Da misalin karfe 8 na dare, bayan sun yi sallar isha kenan, gabaɗaya kewar mijin nata ya isheta, ga shi tana kunyar barin Brr Naurat ta je wajen shi, shi kuma sam yaki zuwa in da suke, ya kule a cikin bedroom nasa yana aikin latsa laptop nasa, Brady na kwance kusa da shi. Brady na Mark, kwana biyun nan duk a wajen Mark yake kwana, sam yanzu ya rage zuwa wajen Lion ɗin, sai jefi jefi, Mark ya saye shi ta hanyar kunna mishi kallo a waya da sauransu, shi ne ya saye zuciyarsa.
Alex yana tare da Mark a waje suna hirar yanda Mark ya yi rayuwa da kuma mutuwar iyayensa wato causing ɗin Alex ɗin kenan, Mark zai kira Alex uncle dan causin ɗin daddynsa ne.
Cikin harshen turanci Brr Naurat take ta tambayar Rimsha labarin daddynta da sauransu. Sai hira Rimahar take zuba mata na mutanen Nigeria, amma fa hankalinta na wajen tunanin mijinta, duk ta damu, tun da rana bata sake saka shi a idanunta ba.
Sarai Naurat ta lura da tana cikin damuwa, hakan yasa ta yi ƙoƙarin tambayarta me yake damunta. Babu komai ta ce mata, a haka har Mark ya kawo musu abinci. Kin cin abincin ta yi dan tana tunanin zata je su ci da mijinta. Muryar Brr ɗin ce ta katse mata tunani da cewa "Wanene wannan da ya ɗauko ni ɗin?." Shiru ta yi ta rasa me zata ce, ta ce mata mijinta ne ko ta ce mata me?.
Ganin ta yi shiru ne yasa ta ce "Kunyata kike ji ne?." Girgiza kai ta yi alamar a'a. Murmushin Brr ta saki har sai da dimple nata irin na ƴaƴanta Nawazudden da Azharuddeen ya bayana, dama a wajenta su daddyn Rimsha suka ɗauko dimple da gaf teeth. "Rimsha kunyata mana kike ji, ai na san ku mutanen Nigeria sai ku rinƙa cewa wai kuna jin kunyar abu, haka kakanki Dr yake yi wani lokaci, to amma idan har kina jin kunyata haka a kansa, hakan na nufin kuna da wata alaƙa da kusa kenan?."
Shiru ta yi tana murmushi tare da sanya hannu ta rufe fuska. "Rimsha kada ki ce mini aure Nawazudden ya yi miki? A ƴar yarinyar kin nan? Duk da a family'n Dr nasan suna aurar da yara 12 to 13 years ma, amma ai su a kauye suke, ba su ma yi karatu ba, shi kuma Nawazudden me ya haɗa shi da irin wannan al'adar ta kakanin nasa? Ai kinyi yarinya da yawa."
Ita dai bata ce komai ba bayan wannan rufe fuska da ta yi. "Amma kuma gaskiya na yi miki murna na samun miji irin wannan bawan Allah, yana da kirki sosai." (Ni kuwa na ce ke dai kin yi sa'a da kika ga fuskar kirkin nasa, dan haka ki yi fata kada ki haɗu da ainahin true colornsa, idan kika kuskura kika yi ido huɗu da ainahinsa, daga ranar ba zaki ma sake yin maganarsa ba, saboda haushi da zai baki, ya kuma birkita miki tunani.)
"To amma Rimsha shi ne kika zauna a nan baki je wajen shi ba?." Tana magana tana cin abincin cikin natsuwa. Baki ɗauke da excuse Alex ya shigo cikin ɗakin. Jin abin da Brr ta ce ne yasa ya ce "Mum a kan me kuke magana ne?." Cikin nuna ko in kula ta bashi labari. Zaro idanu ya yi yana mamakin ƴar Rimshan nan ne aka yi wa aure? Kare mata kallo ya fara yi daga sama har kasa, shi dai bai ga abin da za'a aurar ba, kuma aure ma ga namiji kamar Lion? Wannan ai sai ya kasheta kawai a karon farko, sake baki ya yi yana jinjina al'amarin. Bai san cewa sune suke rena Rimsha ba, suna yi mata kallon yarinya, to su biyota ɗaki suga yanda take sanya Lion ɗin sambatu da kuma sauka daga layi, yo ai kamar yanda namiji baya kaɗan haka ita ma mace bata kaɗan, in dai ta wuce 13 years kuma ta samu tarbiya ai shikenan an gama.
Katse mishi tunani Brr ta yi da cewa ya zo su ci abinci, ita kuma Rimsha ta tashi ta wuce wajen mijin nata. Jiki ba kwari ta miƙe ta fita tana yi musu sai da safe. Shi kuma Alex kusa da mum ɗin tasa ya zo ya zauna saman ɗaya daga cikin kujerun table ɗin. Cikin tsantsar soyayya irin ta uwa da ɗa suka fara cin abincin a tare.
Ita kuma Rimsha baki ɗauke da sallama ta shigo cikin ɗakin nasu. Tamkar babu shi a cikin ɗakin, ko kallon in da take bai yi ba, kamar ma bai san da shigowarta ba.
Toilet ta wuce sai wani ɗari ɗari take yi. A gurguje ta yi wanka tare da fitowa, ta yi mamakin ganin trolleys nasu a cikin bedroom ɗin, bata san cewa shi ya ɗaukosu tun da rana ba, tana can tana surutu da kakanta.
Cikin wasu shegun kayan barci ta shirya, masu matuƙar ɗaukar hankalin, riga ce zuwa iya dai'dai santala santalan cinyoyinta, daga ta saman rigar hannun vest ce gareta, gabaɗaya tudun tula tulanta a waje, bugu da kari rigar ƴar shara shara ce bata da kauri, ainahin zanen shatin tula tulan nata ma a waje, har kan nipples nata shatinsa ya bayyana. Sake gashin kanta ta yi har baya tare da zuba perfume nasa a jikinta.
Sai wani irin sheki santala santalan cinyoyinta suke yi, ta shafesu da Lotion nasa, ita kanta sai sheki take yi. Shi kuwa hankalinsa yana kan laptop nasa, da alama dai wani aiki mai muhimmanci yake yi.
Saman table ta nufa, dan already shi ya ci abincinsa. Zama ta yi tare da zuba abincin ɗan kaɗan. A nutse ta fara ci tana satar kallonsa. Shi ma kayan barci ne launin white color a jikinsa, ya yi matuƙar kyau over, ya saki dark black curly hairnsa, sai ɗan ciza laɓɓansa yake yi a hankali, da alama aikin yana ɗan bashi wahala. Gabar rigar barcin nasa a buɗe ne mai wuyar V, faffaɗar kirjinsa a waje, wannan kyakkyawa kuma kwantatcen bakin gashi nan na kirjin nasa a kwance luf yana wani sheƙi.
Jin azababben kamshin perfume ɗin ya kai mishi karo a hancinsa ne yasa ya ɗan ɗago idanunsa izuwa kanta, dai'dai lokacin ita ma ta ɗago dan ta saci kallon shi. Karaf suka haɗa idanu. Kasa ta yi da nata tana ɗan murmushi, shi kuwa zuba mata idanu ya yi yana kallon ikon Allah, wani irin azababben kyau na wuce misali ta yi.
Duk sai ta ji ta tsargu saboda kallonta da yake yi, wani irin kunya ce ta ji ta lulluɓeta, ƴan kame kame ta fara yi tana wani yin abu kamar mara gaskiya, dama kun san idan mutun ya tsareka da ido yana kallonka, duk sai ka tsargu, to ita ma haka ce.
Kasa cigaba da cin abincin ta yi a in da ta miƙe kawai ta nufe shi tana wani sunnar da kai kasa tare da ɓoye fuska na rashin kunya. Time da zata sanya kayan bata yi tunanin cewa zata ji kunya idan ya gani ba, sai yanzu ne take wani sunnar da kai na rashin kunya.
Tana zuwa ta faɗa saman faffaɗar kirjinsa tana cigana da ɓoye fuska. Haushi Brady ya fara daka mata na a kan me zata kwanta mishi a jikin Lion ɗinsa. Tamkar bata ji yanayi ba, sai ma kara saƙalo wuyarsa da ta yi tana wani ɗan turo baki tare da yi mishi yauki da yanga.
Cikin dabara ya kawar da laptop ɗin daga gabansa zuwa saman bedside drawer, hannu bibbiyu yasa ya rungumota da kyau yana sauke nauyayyar ajiyar zuciya. Ba karya ya yi kewarta sosai, kawai wannan aikin ne ta sha kansa da ta sanya bai je ya ɗaukota ba, ita ma ta yi kewar shi sosai, dan haka yana rungumeta ta sauke nauyayyar ajiyar zuciya.
"Noori Allah nayi kewarka sosai yau." Ta yi maganar tamkar zata saka mishi kuka. Ɗan ɗago haɓarta ya yi suna fuskantar juna. "To ba gani yanzu kin zo gare ni ba?." Jinjina mishi kai ta yi tana mai kara rungumo shi sosai. Haɗe fuskokinsu waje guda ya yi yana kara kare mata kallo. "Noori meyasa kake yawan son kallona?." Ta tambaye shi a shagwaɓe. Dirowa kasa Brady ya yi ya wuce zuwa wajen Mark abinsa, dan ya lura Lion fa ba tashi yake yi ba.
Ya ɗan ɗauki lokaci kafin ya bata amsa da cewa "Because you are mine." Zaro idanu waje ta yi, bata taɓa tunanin zai ce ita mallakinsa ba ne, kai Lion da abin mamaki yake, baka taɓa game mishi, idan ya yi wani abin sai kaga kamar ba shi ba.
Ganin ta zaro idanu ne yasa ya ɗaura lips nasa a saman tata tare da fara kissing nata a nutse. Tamkar jira take yi ita ma ta fara mayar mishi da martani. Kankame juna sosai suka yi. A hankali ya fara romancing nata, daga karshe sai ya kwanta tare da ita a jikin nasa a in da ya ja musu bargo suka kule a ciki, a nan ne ya fara romancing nata da zafa zafa.
Tun tana ƙoƙarin taya shi har ta kasa dan ya kureta, tuni ya rabata da kayan jikinta ya shiga murzarta da kyau da kyau, sai dai fa yanayi yana taka tsantsan dan tsaro, bai zurfafa da yawa ba. A haka ƴar lallaɓawar ma sai da ta yi mishi kuka, yana birkita mata tunani ne sosai. Kuka ta rinƙa yi mishi shi kuma yana zuba mata sambatu.
Sai da ya ɗan ji sauki sauki a jikinsa, sannan ya rabu da ita tare da kwanciya gefe ya jawota jikinsa, kashe wutar ɗakin ya yi da kuma kara musu gudun Ac. Kankame shi ta yi tare da lafewa shiru tana shakar daddaɗar kamshinsa har barci ya yi awon gaba da ita. Shi ma ba jimawa barci ta ɗauke shi. ASUBA TA GARI.
AFTER SOME DAY'S💋
❤️PRINCESS TEEMA💋......✍️
AREEF AND JEHAN.
Yau ta kama Monday, kuma a yau ne game nasu ya zo ƙarshe. Tun safe da misalin karfe 7 ya shirya ya bar gidan, ba komai yasa ya bar gidan ba sai dan ya yi maganinta kuma ya tantance tana son shi ne ko bata son shi. Tana can cikin bedroom nata tana zuba barcin da ta saba, dan ita wani lokaci ma sai 11 na safe take tashi daga barci, sam bata san tsiyar da gogan nata ya shirya mata ba.
Aseef da Akila ma sai zuba barcinsu suke yi. Wannan gida dai kun sani ba sai na sake faɗa ba, gida ne na yara jiki dukka madara iyaye jiki dukka madara, ba ƴaƴan malam shehu ba ne, sai su yi ta zuba barcinsu son ransu, sai time da suka ga dama suke tashi, ba wanda zai tashesu daga barci, idan yunwa ta tasheka ma to sojoji masu yin girki dai sun gama aikinsu, bayin Allan tun karfe 7 suke gama komai su jere a saman table, amma mutanen gidan nan ne su zo su ci ya zama tashin hankali, wasu ma sai 12 suke cin abincin, irinsu daddyn Rimsha kenan, ita kuwa Jehan duk time ɗin da ta tashi barcin take ci. Haka suma Aseef da Akila, duk time da suka tashi suke ci. Shi kuwa daddynsu Lion, wani lokaci ma ba cin abincin safen yake yi ba, sai dai su sha green tea shi da uncle Herry. Mutane ne dai gasu nan kala kala, iri irin ra'ayi sun iya, kowa da kalar tasa, ba zaka taɓa sanin ina ma suka dosa ba, kowa kawai abin da ya zo mishi cikin ƙwaƙwalwarsa yake aikatawa. Shi John ma ai dama sai ya sha giya ya bugu da daddare tukun nan yake yin barci, shiyasa idan ya fara barcin safe baya tashi da wuri, wani lokaci sai karfe 2 ko 3 na rana, sai lokacin da giyar ta sake shi, ga shi baya yi mata shan wasa. Shi kuwa Jay ɗan ba ruwana, matarsa yake kira a waya su yi ta zuba soyayya har dare ya tsala, wani lokaci ma sai asuba ya gabato yake hakura su yi barci, shiyasa shi ma baya tashi da wuri, sai ya kai 10 or 11, kai a takaice ma duk gidan ba mai tashi barci kasa da karfe 8 sai masu aiki, sojoji, sai kuma Lion da shi dama bai damu da yin barcin safe ba. Lokacin da Rimsha take zuwa school ne tana tashi da wuri.
Yanzu ma duk sai zuba barcinsu suke yi, shi uncle T tun ranar da ya zo, ya saka kafa ya bar gidan bai kara dawowa ba, ya tafi yawonsa, sai Allah kaɗai ya san mishi in da ya tafi.
Da misalin karfe 11 dai'dai ta farka daga barci. Ko da ta farka ta jima a kwance har 11:30, sannan ne ta lallaɓa a hankali ta sauko kasan bed ɗin, ta nufi toilet. Wanka ta yi tare da dawowa ta shirya cikin wandon jeans baki da t-shirt maroon. Ta yi kyau sosai, dama ita bata son manyan kaya, kuma dama bata saba sakawa ba idan baku manta rayuwarsu a baya ba.
Fitowa ta yi ta nufi bedroom ɗin daddynta, a duk tunaninta zata sami Areef a wajen, dan yau da kewarsa da kuma tunaninsa tare da begen son ganinsa ta tashi. Amma ko da ta shiga baya nan, daddyn nata kawai ta samu kwance a saman bed yana latsa wayarsa, sai murmushi yake yi. Chatting suke yi da Rimsha, amma sam bata gaya mishi sun ɗauko Na'urat ba, dan Lion ya ce kada ta gayawa kowa, hakan yasa bata faɗa ba. Sai zubawa daddyn nata shagwaɓa take yi a kan tana kewarsa, shi kuwa ya ce mata ba wani nan, ba tana tare da GAR ba? Yasan ba wani kewarsu da take yi, kawai wayancewa take son ta yi mishi dan ya ce mata yana kewarta.
Voice ta yi mishi a in da take zuba mishi kukan shagwaɓa a kan lallai ita wlh tana kewar shi over. Guntun tsaki Jehan ta ja tana ji kamar ta damƙo Rimshar nan ta bata a jikinta, saboda a cewarta duka Rimsha take so, wani kayan takaice har da kuka a cikin voice ɗin. Shi dai daddy da yake ya san matsalar baby Jehan ɗin tasa, sai ya miƙe zaune tare da ajiye wayar a gefe yana ce mata sarkin rigima an tashi?.
Turo baki ta yi tana ce mishi "Good morning dad." "Morning my daughter how are you doing?." Shiru ta ɗan yi kafin ta ce "Daddy i wanted to eat something, am feeling hungry." Ta kai karshen maganar tare da miƙewa ta nufo palo. Kasa ta nufa dan a can table na kasan ake jere abinci. Zuba kalar wanda take so ta je ta yi, ga abincin kala kala sama da kala goma jere cike a saman table ɗin, zaɓa ta yi wanda ya yi dai'dai da ra'ayinta, sannan ta ɗeba tare da haɗo duk wasu abin da zata buƙata ta koma saman.
Bedroom ɗin daddy ta koma, saman lallausan carpet na kusa da bed ɗin ta zauna tare da zube abincin a kasan, har lokacin bata cire tsammani Areef zai shigo cikin ɗakin ba, sai dai kuma har ta ci abincin ta kammala sam bai shigo ba.
Hira suka yi ta zubawa da daddy bayan ta kammala har zuwa azahar, a nan ne suka yi sallama ta koma bedroom nata dan ta yi sallah. Shi ma daddy ya miƙe ya shiga toilet.
Bayan ta idar da sallah ne sai ta fara tunanin to yau ina Areef ya je? Kuma ga daddynta a gida bai fita ba bare ace sun fita tare, to shi ina ya je?. Haka dai abu ya fara tsamari har zuwa la'asar bata gan shi ba, ta kuma kasa tambayar daddynta ina yake, ta kasa cin abincin rana, ta shiga damuwa sosai da sosai na wuce misali.
Hayewa saman bed nata ta yi da yamma kenan bayan ta yi sallar la'asar. Duk ta damu fiye da tunanin mai tunani, kwanciya shiru ta yi tana tunanin abubuwan da suka rinƙa faruwa a tsakaninta da shi, bata san time da ruwan hawaye ya fara bin kuncinta ba, ta kasa goge hawayen, haka ta barshi ya cigaba da zuba, idan ta rufe idanu face nasa kawai take gani yana murmushi, tana jin yunwa amma ta kasa iya cin abinci.
Wasa wasa har ta yi sallar isha bai dawo gidan ba, abin ya isheta har ta fito zuwa bedroom nasa dan ta duba shi. Ko da ta je babu shi babu alamarsa. Bedroom nata ta koma, yau ta kasa zuwa su yi hira da daddynta ma.
Tana zuwa ta haye saman bed nata ta hau kuka, yunwa kamar zai kasheta amma sam ko kallon in da abincin yake ma ta kasa, ga shi bata da phone numbersa. Hawaye ne wani na bin wani a saman kuncinta tana daga kwancen, Allah sarki wlh har faɗawa ta yi na wuni ɗaya, har ta ɗan rame, idanunta sun kara fitowa sosai, kun san idan mutun ya rame idanunsa suna kara girma, to ita ma hakan ce ta kasance da ita.
Har karfe 10 na dare bai dawo ba, ita kuma bata dai'na ruwan hawaye ba, ga uban yunwa, sai dai idan ta gaji da kwanciya ta juya ta nan, idan ta sake gajiya ta juyo, duk ta jike lallausan pillownta da hawaye. Duk wannan halin da ta shiga daddynta yana sane da ita, amma sam bai kulata ba, saboda shi da kansa ya ji daɗin abin da Areef ɗin ya yi mata, yanzu ai zata san cewa yana da matsayi a cikin zuciyarta.
Tana tsaka da kukanta hawaye wani na bin wani, ta luluƙa duniyar tunaninsa. Tamkar daga sama ta ji ana goge mata hawaye, sam bata ji shigowar mutun ba. A hanzarce ta waro idanunta sosai tare da miƙewa zaune. 4 eyes suka yi da shi yana zaune saman bedside drawer, hannunsa na rike da handkerchief fari kal mai bala'in laushi kamar audiga.
"Jehan meyasame ki kike kuka?." Kai Areef ɗan duniya ne number