Showing 336001 words to 339000 words out of 359620 words

Chapter 113 - Triplets Book 3 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2037

hankalinsu su yi ta sake duba shi, amma daga baya da suka gane tsagen iya shege ne da zallar madarar shagwaɓa sai kawai su kyale shi, kuma har gobe idan bai da lafiya suka tambaye shi ya ji sauki zai ce musu no, shi bai ji saukin komai, idan ma suka yi sa'a bai haɗa musu da kuka ba. To ita ma Rimsha shi ne take yi mishi yau, wai no, ta tuna mishi Aseef, dayawa daga cikin ɗabi'unta irin na Aseef ɗin ne, shi ne yasa a duk lokacin da yake tare da ita baya kewarsu sosai.

Tuna cewa irin halin Aseef kenan sai ya kyaleta ita da no ɗin nata. Cikin girmamawa bodyguard dake tukasu ya tambaye shi yanzu kuma sai wani hanya zasu bi?. A takaice ya yi mishi bayani, karawa motar gudu ya yi a in da cikin ƙanƙanin lokaci suka isa gidansu Na'urat ɗin.

Shiru bodyguard ɗin ya yi yana mamakin dama gidansu za su kenan? Dama bakinsu ne kenan?. Toh fah!!.

Gida ne mai matuƙar girman gaske, ina da tabbacin yana daga cikin manya manyan gidajen da ake ji da su a kasar, hawa huɗu ne suma gidan nasu tamkar gidan Lion na Washington DC , sai dai gidan Lion ya fi nasu girma nesa ba kusa ba. Wasu jibga jibgan bodyguards fararen Turawa tas da su ne suke shawagi a cikin harabar gidan. Ko'ina ka kai kallonka sai ka ga farin Baturen bodyguard yana kewaye a wajen, dukka bodyguards ɗin suna sanye cikin suit bakake tare da takalma cover baka, hand gloves baki, kowannansu da akwai face mask baki da black glass a face nasu, gabadayansu babu mai fuskar alamar dariya a tattare da su, kunsan mafiya yawan bodyguards dama masu kirar karfi ake zaɓowa, to suma waƴan nan masu jajayen kunnuwa haka suke, ga tsawo ga cika ido.

Gidan ne na tiles da glass, yanzu na kara tabbatarwa da aka ce Naurat tafi Dr Salman kuɗi, irin wannan aljannar duniya, Allah sarki su amarya basu sani ba suka ce wai Naurat dan kuɗin shi ta aure shi, ta biyo shi cin arziki, tana sace mishi kuɗin tana turawa iyayenta, to su zo suga aljannar duniya a nan, idan suka zo wannan gida ai sai su ɓata a ciki su yi wata basu ma san a wani part suke ba.

Ita kam Rimsha ta saki baki ne tana kare kauyancinta......... Ni kuwa na ce dan ma baki je gidan mijinki na Washington DC ba ne, da bazaki yi kauyanci a nan ba, dan nan ba komai bane idan aka danganta shi da nasu.

Ya ɗan jima a cikin motar kafin ya ambaci sunanta, dai'dai lokacin kuma Mark ya buɗe mishi kofar motar. Alex ya sha mamakin ganin cewa gidansu suka zo, to me ya kawo su kenan?. Shi ne tambayar da yake yi wa kansa.

"Let's go Meesha." Ya faɗa tare da nuna mata hanyar fita yana latsa waya. Da sauri ta fito waje, shi kuma Mark a hanzarce ya matsa ya bata hanya. Fitowa shi ma Lion ɗin ya yi a in da yake ta aikin latsa waya, da alama wani abin yake shiryawa, dan fa har gobe ba'a gane ina ya dosa.

Bayan ya kammala latsa wayar ne ya dubi sojojinsa da suka zo, cikin yaren Spanish ya yi musu magana a kan dukkansu shiddan su zauna a waje bari ya zo. Shiru bodyguards ɗin suka yi suna jin wani yaren da basu sani ba. Riko hannunta ya yi tare da cewa Mark su je ko. Ba musu Mark ya rufa mishi baya.

Tamkar ya san hanyar shiga cikin gidan, haka ya wuce gaba ya je ya buɗe kofar. Kafin ya zo kasar sai da ya sami hoton zanen takardan gidan ya gama kare mata kallo, ya karanci komai sannan ya kama hanya, ba da ka kawai yake aiki ba, ya shirya abubu da dama ba tare da sanin kowa ba, dan haka a shirye tsab ya zo, su daddy ne suke ganin kamar idan ya zo za'a iya samun matsala, amma shi yasan me ya shirya kafin nan ma ya ce zai zo. Ya san ainahin mahaifin Naurat babban soja ne da kasar take alfahari da shi, hakan yasa bodyguards suka yawaita a cikin gidan duk da baya raye ya mutu.

Ita dai Rimsha sai kalle kalle take yi abinta, yau tana gani ikon Allah. Tun da suka sako kafarsu cikin babbar palon gidan ta fara cin karo da masu kama da daddynta da kuma daddyn Anaya, dan Anaya ta tura mata hoton daddynta lokacin suna cikin jirgin ruwa, ba ƙaramin ruɗewa ta yi ba na ganin daddyn Anayar yana kama da daddynta sak, a lokacin ta yi ƙoƙarin kiran number Anayar dan ta gaya mata daddynta yana kama da nata, amma kash number bata shiga, shi ne ta hakura a kan sai ta koma gida sannan ta je gidansu kawai.

Wasu kyawawan matasa ne kamar dai Alex su biyu suna zaune a saman sofa suna hira, gabaɗaya komai na cikin palon blue color ne, tsala tsalan sofa set uku ne a cikin palon, tamkar ba'a duniya mutun yake ba, haka zai ji idan ya shiga irin wannan palon, ya sha komai na kayan alatu.

Bai bi ta kan kowa ba yana shigowa ya saki hannun Rimsha ya haura saman bene tamkar gidansa. Waƴan nan matasa sun sha ruwan mamaki na ganin ya wuce sama kai tsaye bai ce musu ko sannu ba. Sai dai basu ce komai ba duba da suna yi mishi kallon yana kama da ƴan gidan nasu, musamman ma da ya kasance Alex yana da blue eyes irin na kakansu, sai suke kallon yana kama da Alex ɗin, shi kuma Alex kallon mai kama da Aseef Mark yake yi mishi, wannan shi ne cakwakiya!!..... To shi dai Lion da Dr William jacop yake kama, har kwayar idanu da tsawo dukka, Aseef kuma ya fi kama da Josephine, Areef da su uncle T. Amma kuma sai a rinƙa cewa Aseef yana kama da mutane da yawa, to ko dai ita Josephine ɗin tana da ƴan uwan da bamu sani ba ne? Dan ita ce dai Aseef ya biyo a kama, kuma ita ce dai bamu san kowa nata ba. Wannan shi ne cakwakiya ni dai nayi gaba sai kun zo........ Amma kuma fa ana iya samun mutane irin Aseef, wanda idan ka ga face nasu dole zasu yi maka kama da wani wanda ka sani, akwai masu irin wannan baiwa a duniya, sai dai basu da yawa ne, zaka rinƙa ganin face ɗin mutane da dama a tattare da su.

Takurewa waje guda Rimsha ta yi, ta tsorata sosai. Shi kuma akwai dalilin da yasa ya barta a wajen ya haura sama, ya san idan ya haura da ita akwai bala'i, ƙwaƙwalwarta ba zai iya ɗaukar abin da zata gani ba, ba zata iya daurewa ta jure ta rufe baki ta barshi ya aikata abin da zai yi ba, shi ne yasa gara mishi ya barta a cikin palon tun da gidan kakanta ne.

Da yake da safe ne gabaɗaya ahalin gidan suna nan basu fita wajen aiki ba, kowannansu yana dakinsa, hakan kuma ya yi mishi dai'dai yanda yake so, dan so yake ya yi musu tsatsauran hukunci ko da kaɗan ne, saboda sun bashi haushi, kuma ya ɗauko Na'urat a gaban kowa ya tafi da ita, sai yaga karshen iskancin nasu, duk sai ya koya musu hankali a cewarsa.

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥

*KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔
ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*.

*KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA,
INFECTION KILLER,
COLACCA,
SAI KAYAN GYARA PAGE.
KACA KACA.
YALLAGWADA.
JIGIDA.
RUWA RUWA.
BANI BANI.
WOMEN JELL BATA BATA.
DAFIN KAXA.
TANTABARA.
XABUWA.
CICCIƁI.
AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER
09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH,
BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*.


❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥


https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S


❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥



*Dedicated to Sadiya. Ubangiji Allah subhanahu wata'ala ya baki haihuwa, ya baki ƴaƴa kyawawan gaske masu albarka, Allah ya baki waƴan da zaki ce yi su yi bari su bari, Allah ya sa wannan jinkirin rashin haihuwar ta zama miki alkhari.*


TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️

❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA💋)


*Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 0816 139 0581*





E81

After some minutes da ba su wuce 40 ba, sai ga shi ya sauko kasa. A in da ya barta a nan ya dawo ya sameta. Cikin harshen Spanish ya ce da Mark ya ɗaure mishi matasa biyun nan dake zaune a saman sofa...... Bai kai karshen maganar ba idanuwansa suka sauka a kan Alex dake bayan Mark ɗin yana tsaye. Ɗan zaro idanu ya yi yana kallon shi. Shi kansa da kallon farko ya ɗauka Aseef ne, sai da ya kalle shi da kyau ya fahimci ba Aseef ɗin ba ne, amma ba karya sun yi kama na wuce misali. Kawar da kansa ya yi tare da miƙa mata hannu, da sauri ta taho ta faɗa jikinsa.

Na san za ku so jin me ya je ya yi a sama, to ku saurara, binsu ya yi ɗaki ɗaki ya yi musu ɗaurin goro tare da ɗaure musu baki kamar an aikosa, kamar wasu kaji haka ya yi musu, harta tsofaffin wato yayyun Naurat ɗin bai bari ba, cikin dabara da salon iya aiki ya yi musu hakan ba tare da ya sami wata matsala ta sun yi mishi ihu ko makamancinsa ba, yakin sunkuru ya yi musu. To shi ne abin da ya je ya yi a saman ya dawo, yasan idan suka tafi da Rimsha tsab zata yi ihu ta tona mishi asiri, shiyasa ya bar Brady a mota. Idan taga ya toshewa mutun baki kuka zata fara yi, shi ne yasa ya barta a kasa tare da Mark, ya san waye Mark, haka kawai Allah ya sanya mishi kaunar Mark ɗin a cikin zuciyarsa, baya yarda da kowa, amma Mark yana da kusanci da zuciyarsa sosai, yana jinsa sosai a ransa.

Massage ya yi wa sojojinsa a kan su shigo dan su fito mishi da kowa dake cikin ɗakunan da ya bi ya ɗauresu kamar kajin nan, ya san idan ba haka ya yi musu ba, to wlh ba za'a sami fahimta a tsakaninsu ba, za su iya kira mishi sojoji su tada yaki a tsakaninsu, shi dai baya barin ko ta kwana, idan aka kawo mishi wargi to fa zai yi ba dai'dai, kuma kakansa His excellency ya ce ya bi komai a hankali har ya shiga ya fito, babu wata hukuma da zata tare shi dan ya shirya musu makarkashiya, dama kuma kunsan kasar America gwana ce wajen shirya shiryen sheyen abubuwa, to shi ne yasa ma kuka ga ya shigo kasar lafiya lou, kuma shi ne yasa ya ɗauresu dan ya yi komai a tsanake.

Ɗaukarta cancak ya yi suka koma saman. Bai zame da ita ko'ina ba sai ɗaki na karshe a sama bakiɗaya. Da akwai key a jikin kofar, dan haka sai ya murɗa ya buɗe.

Bakinsa ɗauke da sallama suka shiga ciki. Jin sallama yau a gidan GENERAL TRUMP ne yasa a hanzarce ta ɗago kanta. Tana daga zaune saman bed ta kifa kai da gwiwowinta, da alama tana cikin tsananin damuwa.

Dattijuwa ce, amma da yake jikin Turawa baya saurin nuna tsufa, suna da jiki mai kyau, sai tsufanta bai wani bayyana ba, idan ka ganta zaka ce 35 years gareta, gata kuma da ƙaramin jiki mai shegen kyau. Kyakkyawar gaske ce, fara tas tamkar ka taɓa jini ya zuba, ga dark black curly hair har bayanta a kwance. Ashe ita Rimsha ta ɗauko a gashi.

Tsawon shekaru 33 tana kulle a cikin wannan ɗaki, ko waje bata leƙawa, babban yayansu wanda Lion ya fara ɗaurewa yanzu shi ne ya rufeta a cikin ɗakin, suna azabtar da ita a kan lallai sai ta dawo kafura ta fita daga addinin Musulunci, ita kuma ta ce sai dai su kasheta, amma wlh ba zata yi ridda ta zama krista ba, ta rigada ta musulta kenan, bata ga wanda ya isa ya mai da ita krista ba, shi ne suka rufeta, abin ci ne kawai yake sanyawa suke buɗeta. Duk kudin nan nasu dan bakin mugunta sau ɗaya suke bata abinci a rana, ruwa ma ɗan kaɗan suke bata, ta azabtu matika na tsawon waɗan nan shekaru, amma duk da haka bata ji kamar ma zata iya fita daga cikin addinin musulunci ba, sun hanata hijabi dan kada ta yi sallah, amma a hakan sai ta yafa wani abin ta yi, dai'dai da rana ɗaya lokacin sallah bai taɓa wuce ta ba.

Daga karshe dai suka hakura suka barta a cikin ɗakin rufe kawai suna bata abinci sau ɗaya. Naurat ta sha bakar wahala sosai a rayuwarta, tasha na Amarya a Nigeria, ta kuma sha na ƴan uwanta a nan, ita da ta taso ƴar gata sosai, saboda su uku ne kawai mata a cikin yaran GENERAL TRUMP goma sha uku, goman dukka zaratan maza ne, su uku ne mata, da ita da kannenta mata biyu wanda su basu zaune a Russia ma, tun asali a America suka yi karatu, so suna can da zama basu dawo nan ba har yanzu, ita kaɗai mace ta rayuwa da daddynta, ya yi mata gata fiye da tunanin mai tunani kafin ya mutu ƴan uwanta maza su cigaba da kula da ita, haɗurwarta da Dr Salman a shopping ya fara canza komai, shi ne kuma mafarin wahalarta har zuwa yanzu.

Karisowa cikin ɗakin ya yi tare da sauke Rimsha kasa. A gefen bed ɗin nata kusa da ita ya zauna, haka kawai Allah ya sanya mishi kaunar dattijuwan nan har cikin ransa, musamman idan ya tuna irin gwagwarmayar da ta sha a kan cewa ba zata bar addinin musulunci ba, sai ya ji ya kara kaunarta over. Cikin harshen turanci ya fara yi mata magana a nutse.

Ya gaya mata ɗaukarta ya zo yi su koma Nigeria. Kin yarda da shi ta yi, duba da shi ma Bature ne, kafewa ta yi a kan cewa ita bata san Nigeria ba kuma bata da wata alaƙa da Nigeria. Baiwar Allah muryarta ma da kyar yake fitowa saboda jimawa da ta yi bata magana da kowa.

Da hannu ya yi wa Rimsha alama a kan ta zo, da sauri ta kariso kusa da shi ta zauna. Dama kamar yasan Na'urat zata yi mishi gardama, shi ne yasa ya taho da Rimsha, idan baku manta ba da Jehan ya so zuwa ma, dan ita ce mai kama da daddynta, a wani ɓangare kuma yana son zuwa da Rimsha dan launin fatarta irin nasu family'n Dr Salman, yanda Na'urat ta sha wahalar nan baya jin kamar zai yi mata dole a rayuwarta, shi ne yasa yake binta a hankali.

Cikin sanyin murya ya sake gaya mata da gaske shi ba cutar da ita zai yi ba, tafiya da ita ya zo ya yi dan ya mayar da ita cikin ƴaƴanta, hakan ce ma tasa ya zo mata da jikanta ƴar Nawazudden ɗinta dan ta shaida, ya san cewa ko zata manta kowa, to ba zata manta Nawazudden ba, dan shi ne ɗa mafi soyuwa a gareta. Ai kuwa duk kin yarda da ta yi da shi, jin ya ambaci sunan daddyn Rimsha sai da ta ɗago sosai tana kare musu kallo, sai dai fa ita a yanayin yanda take kallon face ɗin Lion da ƴan uwanta na nan yake yi mata kama, amma ganin Rimsha yasa ta ji ta yarda da su, duk da cewa Rimsha bata wani kama da daddyn nata, sai dai kama ta jini, da mum take kama.

Kara yi mata bayani ya yi a nutse dallah dallah yanda zata fahimta, yanda kuma rikicin tsufa ba zai sanya ta kasa ganewa ba. A takaice dai ya yi babban sa'a ta yarda da shi dalilin Rimsha, dan haka sai ta amince zata bishi. Ya ji matuƙar daɗi sosai, shi da kansa ya taimaka mata ta miƙe tare da saukowa kasan bed ɗin. Sai murna Rimsha take yi yau ta ga kakanta mai tsananin kama da daddynta.

Riko hannunta Naurat ɗin ta yi tana ji tamkar hannun Nawazudden ta rike, tana bala'in kaunar daddyn Rimsha da daddyn Anaya, tafi sonsu sama da kowa a cikin ƴaƴan nata.

A hankali suka fito palo, nan ya iske kowa na gidan, gabaɗayansu sojojin sun fito da su sun zube su a palon. Sun yi mugun bashi haushi ne na izayar da suka rinƙa yiwa ƴar tahalikan nan na tsawon shekaru, ya so ne ma ya yanke wa kowannesu koda kunne ɗaiɗai ne, amma kuma yana sauri, dan haka sai ya kyale su kawai.

Har ya kai bakin kofar palon rike da hannun Naurat ɗin ita kuma tana rike da hannun Rimsha. A hankali ya juyo ya ce da Mark ya kwance Alex da shi zasu tafi.

Cikin girmamawa Mark ya ce yana neman alfarma Lion ya yi hakuri ya sanya a kwancesu, dan saboda uncles nasa ne, ƴan uwan daddynsa ne, dukka ya sansu ta cikin hoto, yana da hoton kowannansu, Alex ɗin ne kawai dama suke waya da shi, kuma Mark ɗin ne ya nemo number Alex ɗin dalilin wannan zuwa da za su yi.

Shiru Lion ɗin ya yi yana mamakin, Allah mai iko, yau dai ga Mark a cikin family'nsa, Mark ɗin ma jikan gidan ne kamar dai su Rimshan.

Jinjina mishi kai ya yi yana faɗin, ya barsu idan sun tafi za'a kwancesu, dan sun ɓata mishi rai fa. Haka ba dan ya so ba ya kyalesu, ya kwance iya Alex ɗin kawai sojojin suka sanya shi a gaba suka bar palon.

Wani karfin hali sai wajen Lion, ya shigo


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login