Showing 282001 words to 285000 words out of 359620 words
ga su tamkar ka latsa jini ya fita, zuba musu idanu ta yi tana kallonsu babu ko kyaftawa, shi kuma zubawa idanun nata ido ya yi yana kallonsu cike da kaunarsu, a duniya yana bala'in kaunar sleeping ɗin nan nata.
Mark ne ya katse musu kallon da suke yi ta hanyar shigowa bakinsa ɗauke da excuse, kallo ɗaya ya yi musu ya yi saurin kawar da kallonsa tamkar bai gansu ba, saman table ɗin ya ajiye kayan abincin tare da ɗan tsayawa a gefe guda, bawan Allah yana son ya tambayeta ko tana da number wani daga cikin ƴan uwan Anaya dan ya kira ya ji ya lafiyarta tun da number Anaya ɗin bata shiga, sai dai yana bala'in tsoron yi mata magana, bai ma san taya zai fara tambayarta ba, yana tsoron Lion sosai, ita kuma tana da number daddyn Anaya ɗin har da mummunta da yaya Feroz dukka, sai dai bata kawo cewa yana da bukatar ya yi magana da su ba, sai ƴan kame kame yake yi tun da ya shigo ɗakin.
"Is there any problem Mark?". Ya tambaya yana ɗan sauketa daga jikin nasa, kankame shi ta yi taki sauka dan tana son yin magana da shi idan Mark ɗin ya fita, so ta ɗauka ko zai sauketa ne ya fita tare da Mark ɗin, shi ne ta rike shi, kallonta ya yi kafin ya barta a jikin nasa ya mai da kallonsa kan Mark ɗin.
"Sir i want to talk to Madam". Ya faɗa cikin tsoro, daga jin muryarsa kasan a tsananin tsorace ya yi maganar, ba karamar shahada ya yi ba, ya kasa samun sukuni ne, duk abin da yake yi tunanin Anayar ce kawai a cikin ƙwaƙwalwarsa, yana da bukatar ya yi magana da ita idan ba haka ba za'a iya samun matsala, dan har kansa ta fara yi mishi ciwo wuni ɗaya kawai, dama duk wanda ya san turawa yasan basu iya faɗawa soyayya ba, idan suka faɗa fa to komai suna iya sadaukarwa a kan wannan soyayyar tasu, gabaɗaya zuciyarsu suke bawa wanda suke so, suna kula da soyayyar tasu sama da yanda suke kula da kansu, ko dabbobi suke so to fa kular da zasu basu sai ka saki baki kana kallo, dan kula ce ta wuce misali, so su haka soke, shiyasa shi ma Mark ya rasa sukuninsa, ya rasa duk wata jin daɗi wuni yau kawai.
"What do you want to tell her?". Yana magana tamkar yanda yake magana da su da baya, cikin bada umarni da nuna isa tamkar ba shi ne ya gama rarrashin Rimsha yanzu ba, dama fuska kam tamkar kullum haka yake, ko ita Rimshar bai sauya mata face nasa ba, hakan na nufin halittarsa ce Tiger face, babu wasa kuma babu alamar murmushi ma bare dariya.
"Sir i want to ask her about her friend, I want to ask her if she has a number of her own". Sai lokacin ta gane bawan Allah yana so ne ya yi magana da Anaya, ɗago kai ta yi da nufin ta yi mishi magana, wani kallo Lion ɗin ya wurga mata wanda ya sanyata haɗiye maganar ta koma ta kwanta luf a saman kirjin nasa.
Shiru ya yi na tsawo almost 2 mins kafin nan kasa kasa ya ambaci sunanta Meesha, yadda ya yi maganar kasa kasa ko Mark ɗin bai ji me ya ce ba, ita ma dan tana saman kirjinsa ne da ba zata ji ba, na'am ta amsa ba tare da ta ɗago ba "Do you have the number he is looking for?" Jinjina mishi kai ta yi alamar e, ya hanata magana ta hanyar sanya yatsansa ɗaya a cikin bakinta yana wasa da language nata, sam baya son ta yi magana, na'am ɗin da ta ce ma kasa kasa maganar ya fita saboda yatsar nasa dake bakin nata.
Tsotsar yatsan nasa ta fara yi kamar sweet tana ɗan ciza mishi, tamkar wanda aka watsawa ruwan kankara haka yake ji a jikinsa, duk ta saukar mishi da kasala, dan fa ba karya yana da azababben sha'awa, kawai dan dama bai san da hakan ba ne, bai taɓa kwatantawa ba, yanzu kuma da gabaɗaya komai nasa ta buɗe da ta taɓa shi kaɗan komai yake motsa mishi, sai dai baya ɗaukar hakan a matsayin wani abin azo a gani ma, dan idan zaka kashe shi bai san me yake tsakaninsa da Rimsha ba, shi dai kawai tana burgesa, batun kiss kuma wannan abu ne da kun riga da kun sani su fa kiss a wajensu ba wata tsiya ba ce, ko ba masoya ba suna yi, so ko ba son yarinya kake yi ba su suna iya kissing nata, amma fa shi ya fara yardan wa kansa tabbas akwai wani abin a tsakaninsu, idan zuciyarsa ta ce mishi so ne, sai ya ce a'a shi bayan TRIPLETS nasa ba zai so kowa ba, kawai abota ce or tausayi a tsakaninsu, haka a koda yaushe yake ƙoƙarin tursasawa zuciyarsa da ta yarda da hakan............Tab akwai aiki kenan, ka gama kissed na yarinya ka ce abota ko tausayi, zaka yi bayani da yarenku na Spanish ne or turancin da kuka fi iya wa ne wlh, mu dai je zuwa ba dai yanzu kana iya jin feeling ba? Zaka ga abota.🤣🤣
Ɗauko wayarta daga saman bedside drawer in da ya ajiye ɗazun da Brady ya kawo mishi ya yi, miƙawa Mark ɗin ya yi yana faɗin ya je ya duba number, cike da murna har yana sauke nauyayyar ajiyar zuciya ya zo ya karɓa tare da nufa waje.
Mark ɗin yana fita Lion ɗin ya zame hannunsa daga bakinta dan ba ƙaramin ɗaga mishi hankali take yi ba da irin ɗan ciza ƴatsar nasa da take yi. Ɗago kanta ta yi tana faɗin "Yaya Saif meyasa Mark zai rinƙa shigowa ɗakin nan kai tsaye?". Shiru ya yi dan shi ma sam bai ji daɗin hakan ba, bai so Mark ɗin ya shigo ya samesu a haka ba, ga shi ba wani kayan kirki ne a jikinta ba, amma da yake sun saba da hakan ne yasa bai ce da Mark ɗin ya fita ba, ya saba ɗakinsa ne shi kaɗai, kuma Mark ɗin yana shigowa duk lokacin da ya buƙacesa ba tare da wani shamaki ba, shiyasa yanzu ma ya shigo ba wata shamaki abin sabo ne.
"Yaya Saif ni kam bana son ya rinƙa shigowa, ya tsaya a waje zan rinƙa zuwa na karɓi abincin ko kuma zan je kitchen ɗin na rinƙa ɗauka da kai......". Bata kai karshen maganar ba ya wurga mata wani shegen harara da dara daran idanun nan nasa, hakan yasa ta shanye maganar. "Ki je ki karɓo a hannunsa?". Ya maimaita maganar yana mai cigaba da wurga mata kallo mai kama da harara.
Ba ƙaramin razana ta yi ba, nan take ta sha jinin jikinta, tunani take yi wai yaushe yaya Saif ɗin nan nata zai yi koda murmushi ne a rayuwarsa? Wlh face nasa a ɗaure kullum ɗin nan yana razanata ba kaɗan ba, daurewa kawai take yi dan tasan ba zai taɓa lafiyar jikinta ba. Girgiza mishi kai ta yi tana mai datse idanunta gam.
"Tashi ki je ki ci abinci". Jin ya faɗi hakan ne yasa ta waro idanun nata tare da yunkurawa zata tashi, har zata miƙe sai ta tuna zancen Akila, komawa ta yi ta manna mishi haɗaɗɗiyar sumbata a saman lallausan kumatunsa tana sakin cool murmushi tare da runtse idanunta, nan take dimples nata suka lotsa. Sosai ta kara tafiya da imaninsa, tamkar zai sake jawota jikin nasa, sai kuma ya fasa dan yana son ta ci abinci.
Kiƙewa ta yi zuwa wajen trolleynta ta ɗauko yajin da Anaya ta bata dan ta saka shi cikin kayan da suka yi sayya shi kuma Lion ya haɗo da shi ya zuba cikin trolleyn. Bayan ta ɗauka saman table ta wuce ta zauna dan ta fara cin abincin.
Kiran Areef Video call ne ya shigo wayar tasa, ganin kiran yasa ya ji dama ya sake kashe wayar dan barci yake son ya yi, amma ba zai iya kin ɗaukar kiran TRIPLETS nasa ba a ko wani hali yake ciki, sannan da ya ga kiranma sai da zuciyarsa ta harba tamkar ɗaya daga cikinsu yana cikin tashin hankali da damuwa, hakan ce tasa ya ɗauka da wuri dan ya ji menene.
Yana ɗauka a matuƙar ruɗe Areef ya fara magana. "Lion ka kawo agajin gaggawa, matar Aseef tana gaf da mutuwa, poison ta ci, gabaɗaya sun haɗu a palo da su daddy suna cin abinci kawai ta zube kasa kumfa na fita daga bakinta, i think masu girkin ne suka sanya poison ɗin, yanzu dai na yi iya kan bakin ƙoƙarina wajen ganin na ceci rayuwarta, amma tamkar ana kara poisonin ɗin ta ne, abin sai karuwa yake yi tamkar kara cin gubar take yi, abin ya ɗaure mini kai ya kuma sha gaban tunanina, please ka kawo mana agajin gaggawa na wata hanya da zamu ceceta kada ta mutu".
Shiru ya ɗan yi na ƴan mintocin da ba su wuce biyu ba, sai azalzala mishi Areef yake yi da ya yi magana, amma shi kuma ya yi shiru yana ɗan tunani, can kuma sai ya ce "How comes za'ace matar Aseef ta ci poison? Taya za'ayi ace kowa a gidan ya ci abincin lafiya lou sai ita ce kawai ta ci poison a ciki? Wannan ba laifin masu yin girki ba ne, laifin daga cikin masu cin abincin yake tun da kowa a gidan ya ci abincin lafiya lou! Amma ba tare da Aseef ta ci abincin bane?". A ruɗe Areef ɗin ya amsa mishi da "Wlh i don't know, ina ga kamar tare suka ci abincin, ni bana gidan kirana Aseef ɗin ya yi a waya a kan na yi sauri nazo na ceci rayuwarta kada ta mutu, so ban san ya abin ya kasance ba". "Shi Aseef ɗin kuma yana nan lafiya?" "Yes yana nan lafiya, shi fa ya kirani a waya da kansa!".
Mayar da kallonsa kan Rimsha dake ta faman haɗa spoons waje guda ya yi, ɗan zuba mata idanu ya yi yana kallon yadda take zuba yaji a gabanta tana tsince namar dake cikin abincin tana tarawa a gefe guda alamar bata son ci, dawo da kallonsa saman face nata ya yi, yana kallon yanda take murnar cin yajin da take yi, nan take kwakwalwarsa ya ayyana mishi Akila ce zaune a wannan waje ba Rimsha ba, tunani ya fara yi na yadda akayi ta ci guba ita kaɗai a gidan, yanda Rimsha ta zuba wannan yaji a gabanta zai zamana haka aka zuba guba a gaban Akilar lokacin da suke cin abinci, to waye ya yi hakan? Ta ya za'ayi gabaɗaya family'n suna saman table ɗin cin abincin a tare har a zuba mata guba a gabanta babu wanda ya gani? Wannan abu ne mai wuyar ganewa mai kuma ɗaure kai.
"Where is she?" Ya tambaya yana mai sake jinjina al'amarin a ransa tare da dawo da kallonsa kan wayar. "Tana bedroom ɗin Aseef ɗin". "Okey take da camera to her place let me see her". Okey ya amsa mishi da shi tare da ɗaukar wayar da sauri ya nufi bedroom ɗin na Aseef.
Gabaɗaya ƴan gidan suna cikin bedroom ɗin, harta daddyn Rimsha da Jehan, hankalin kowa ya yi mummunar tashi, musamman ma daddyn Lion ya shiga tashin hankali sosai bare ma da ya ga yanda Aseef ya haukace musu suna neman rasa shi gabaɗaya, ga kuma Akilar tana ta faman ta shake wuyarta tamkar ba zata rayu ba, kowa dake cikin ɗakin sai da ya yi mata hawaye, harta uncle Herry da su Jay, dama shi kam John already yana sonta, dan haka ya sha kuka ba kaɗan ba, ita ma Jehan sai da ta zubarwa da Akilar kwallah sosai yau, Aseef kam ba'a magana, dan haukace musu gabaɗaya ya yi, sai da daddyn Rimsha ya rungume shi sosai ya hana shi taɓata, amma yaki yana ta ƙoƙarin kwace kansa, John ya zo ya haɗu suka rike shi sosai, sai kuka yake yi musu yana faɗin, shi ma dan Allah a bashi poison ɗin yasa su kwanta tare da Heartbeat nasa, idan ma mutuwa ne sai su mutu tare, wlh idan ta mutu shi ba zai iya rayuwa ba, dan girman Allah a agaza shi ma a bashi gubarnan, da farko ma cewa ya yi sam sai ya yi mata kiss sun raba gubar tare, da kyar Areef ya janyesa daga wajen nata ya miƙa shi wa daddyn Rimsha, bawan Allah duk ya birkice ya fita a hayyacinsa, Akila ke ciwo amma ya fita shiga tashin hankali, har wani jiri yake ji kirjinsa na harbawa da karfi karfi, yanzu duk jikinsa ya mutu kamar wani gawa haka ya kwanta a jikin daddyn Rimsha, hawayen da yake fita daga idanunsa ne zai tabbatar maka da bai mutu ba yana da rai.
Daddyn Lion a matsayinsa na babban likita ma ya kasa shawo kan matsalar Akilar, mummunar guba aka bata, wanda ba zai kashe ta a lokaci guda ba sai ya gama nakasata ya wahalar da ita tare da kashe duk wasu kwayoyin halittarta, sannan ya kasheta,
Saman gadon Areef ya haye da wayar tare da juyawa Lion camerar dan ya ganta da kyau, shiru ya zuba mata idanu yana kallonta, sai fama take yi abin gwanin ban tausayi, idanuwanta tamkar zasu fito waje saboda zarosu da take yi, bakinta, hancinta duk suna fitar da jini mai kauri tamkar ba jini ba, tsabar kaurin jinin ma har wani pink pink ya yi, alamar gubar ta fara azabtar da ita, ta fara ratsa jininta da kyau............... WAYE KUKE TUNANIN YA BAWA AKILA GUBA A CIKIN WANNAN FAMILY'N⁉️
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥
KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔
ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne.
KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA,
INFECTION KILLER,
COLACCA,
SAI KAYAN GYARA PAGE.
KACA KACA.
YALLAGWADA.
JIGIDA.
RUWA RUWA.
BANI BANI.
WOMEN JELL BATA BATA.
DAFIN KAXA.
TANTABARA.
XABUWA.
CICCIƁI.
AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER
09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH,
BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI.
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥
TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️
👊FATEEMA ZAHRA MUSA (PRINCESS TEEMA OR STAR LADY)✊
*Domin samun karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 0816 139 0581*
73
Zuba musu idanu gabaɗayansu Lion ya yi yana karantar face ɗin kowa, dukkansu babu wanda alamar rashin gaskiya yake a tattare da shi, wani irin azababben tari da Akilar ta fara yi ne ya sanya Lion ɗin dawo da kallonsa a kanta, gabaɗaya hankalin kowa ya dawo kanta, dukkansu sun yi shiru suna sauraron su ji me Lion zai ce kuma, shi dai daddy ya yi iya yinsa a matsayinsa na likita shiru, shi ma Areef ya jarraba, amma poison ɗin ma karuwa yake yi sosai.
Almost 2 mins Lion yana kare mata kallo kafin calmly ya ce "Areef kwance mata chain ɗin nan da yake wuyarta ka saka mini shi a cikin ruwa". Miƙawa daddyn Rimsha wayar tasa ya yi a kan ya rike mishi da kyau ta yanda Lion ɗin zai ji daɗin ganin abin da suke yi, matsowa kusa da ita sosai ya yi tare da sanya hannunsa ya ɗan ɗago kanta yana furta Bismillahirrahmanin a cikin zuciyarsa, gabaɗaya sun zaro idanu suna ganin ikon Allah. "John help me with water inside bowl". Cewar Areef ɗin, ya yi maganar yana cire mata chain ɗin.
A sukwane John ya nufi hanyar fita, dakatar da shi Lion ya yi tare da cewa Aseef ya tashi ya kawo ruwan ba John ba, da mamaki su daddyn Rimsha suke kallonsa, me Lion yake shirin aikatawa kenan? Menene yake faruwa? Tambayoyin da suke yi wa kansu kenan.
Shi ma Areef ya ɗan yi mamaki, amma sanin halin ɗan uwan nasa yasa bai wani damu ba, yasan komai sai da dalilin Lion yake yin shi, kuma tun da ya ji haka to fa akwai matsala kenan.
Kallon daddyn Rimsha Areef ɗin ya yi tun bai yi magana ba daddyn ya fara ƙoƙarin tashin Aseef ɗin a kan ya tashi ya kawo ruwa, kasa tashi ya yi dan gabakiɗaya ilahirin jikinsa ya mutu, sai kerma kamar mai zazzaɓi jikin nasa yake yi, ko motsi ba zai iya yi ba, shi kaɗai yasan me yake ji bawan Allah, tabbas idan Akila ta mutu Aseef zai bita, domin kuwa son da yake yi mata ya wuce gaban misali.
"Lion Aseef fa ba zai iya kiƙewa ba". Areef ya faɗa yana ƙoƙarin sauka daga gadon hannunsa rike da chain ɗin da ya kwance daga wuyar tata. Shiru Lion ɗin ya ɗan yi na tsawon 3 mins kafin ya ce "Okey keep the chain behind this your uncle, then ka je ka ɗebo ruwan because da kai da Aseef all abu ɗaya ne". Okey ya amsa mishi da shi tare da ajiye chain ɗin a bayan daddyn Rimsha saman bedside drawer kenan, da yake daddyn yana ta gaban bedside drawer ne saman sofar dake kusa da gadon.
Ruwa ya je ya ɗebo a bowl tare da dawowa cikin ɗakin, kafin ya dawo Lion ya ce da daddynsa ya fara treating na Akilar yanzu za su iya shawo kan matsalar, ana cire mata chain ɗin ta sume a wajen har lokacin kuma bakinta na fitar da kumfa mai haɗe da jini, ba ɓata lokaci daddy ya fara ƙoƙarin ceto rayuwarta, shi kuma Areef ya zo ya sanya chain ɗin a cikin ruwan da ya kawo, kafin ya sanya sai da ya furta Bismillahirrahmanin rahim a cikin ziciyarsa sannan ya saka chain ɗin, da wuya Areef ya yi