Showing 210001 words to 213000 words out of 359620 words

Chapter 71 - Triplets Book 3 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

1954

mata fuska shi ne har take ƙoƙarin kawo raini a tsakaninsu? Ya ce kada ta yi abu ta kama ta yi, wlh babu mai karɓarta yau, sai ta gane annabi ya faku, sau tari dama ɗaukar karamar yarinya yake yi mata shiyasa yake kawar da kansa a kan wasu abubuwa da take yi mishi, bai taɓa ɗaukarta a cikakkiyar babbar mace ba, idan ba ku manta ba a baya duk zaman da suka yi da ita a gidan bai taɓa ɗaga idanu ya kalleta ba sai a ƴan kwanakin nan sanadiyar tafiyar da suka yi ne daya kare mata kallo, a nan ne ya fahimci ta fara girma, kuma hakan yana ɗaya daga cikin dalilin da ya sanya yake ƙoƙarin hanata kusantar su Areef kamar da, dan kun sani duk da yake Bature shi mutun ne mai kula da addininsa sosai, yana daraja addininsa, wannan dalili yasa yake taka musu birki ya kuma nuna mata ce yanzu ta girma dole ta dai'na zama a jikinsu Aseef kamar da tun da su ba dutse bane, ko yaya suna jin shauki, shi ne ma yasa ɗazun ya daka musu tsawa dan kada ta koma jikin Areef ɗin ta zauna, ita kuma bata ɗaukar hakan kamar wani abin, dan idan baku manta ba, da farko bata yarda ya rungumeta, amma a hankali ya saba mata da hakan, da ta fahimci ba cutar da ita zai yi ba sai ta saki jiki da shi, bugu da kari kuma taga daddynta ya yarda da shi sosai, shiyasa ta sake musu ta ɗaukesu tamkar yayyunta na jini, ga kuma karin yarinta a kanta.

Wani mahaukacin tsawa ya dakawa Areef ɗin a kan ya matsa mishi a gabansa ko ya yi mishi illah, kin matsawa ya yi yana faɗin "Rimsha ki gudu". Da gudu ta miƙe zata yi waje, ture Areef ɗin gefe ya yi da karfi tare da damko gashin kanta ya janyota baya da karfi, kafin ya hankaɗata ta faɗi kasa, ihun azaba ta sakar mishi, na gashi ta da ya ja, kokarin riƙesa Areef ya yi amma ina ya kasa, dan yau ran maza ya ɓaci over, baya ji kuma baya gani, almakashi ya ɗauko daga cikin drawer da chemical nasa suke, wurga mata ya yi yana faɗin "Ɗauka ki yanke gashin nan gabaki ɗaga ki zubar". Babbar magana, saboda waƴan can sun taɓa gashin sun kamata da gashin ne za ta yanke? Lallai Lion akwai bala'in kishi na wuce misali.

Ta kasa koda motsawa saboda tsananin tsoro da tashin hankali, yanzu gabaɗaya kukanta ma ya dai'na fita, yau taga tashin hankali, bata taɓa tunanin haka Lion yake da zuciya na bala'in fitar hankali ba, lallai ma, kuma a hakan ma saboda ita mace ce yasa bai wani hau ba, dan yasan duka ɗaya kwakkwara idan ya yi mata, ba zata tashi ba, da namiji ne ya yi mishi laifi ai data ga bala'in da ya sha gaban tunaninta.

Ganin haka yasa Areef ya juya ya fice daga cikin ɗakin dan yasa in dai Lion ya hau to duk duniya ba mai iya dannarsa, mafita ɗaya, shi ne su yi mishi allura, amma idan ya ce zai tare shi ma zasu yi faɗa ne, zai yi mishi illar a banza, ga shi dama ba lafiya gare shi ba, ko da yana da lafiya ma Lion ya fi karfinsa, idan suka sami ɓacin rana suka yi faɗa shi yake dakuwa dan karfin ba ɗaya ba, kuma yanzu a halin da Lion yake ciki ba zai ma tuna cewa Areef ɗin yana da wani ciwo ba ya tausaya mishi, idan ya tare mishi gaba tsab zai yi mishi dukan mutuwa, ko sun haɗu sun haɗa karfi da Tga basu iya riƙe shi idan ya fusata, alluran dai ita ce mafita.

Bedroom nasa ya koma, alluran ya haɗa na barci mai karfi na 30 mins, ɗaya daga cikin alluransa da ake masa time da yake jinya ne, lokacin da ya dawo bedroom ɗin Rimsha ta kasa motsawa har lokacin, shi kuma yana ƙoƙarin naɗa belt nasa zai zaneta. "Ki yanke gashin nan nace!!"

Tsawa ya daka mata wanda ya sanyata warwarewa, a sukwane ta ɗauki almakashin da nufin ta fara datse gashin nata, hawayenta har sun kafe dan azaba, hannunta ma da kyar ya iya riƙe almakashin saboda kerma da gabaɗaya ilahirin jikinta yake yi.

Shammatarsa Areef ɗin ya yi ya caka mishi alluran a hannu wajen damatsansa tare da zira mishi ruwanta a cikin jikinsa, da yake abune da suka saba yi, sun san yadda suke yi, alluran yana nan ɗan karami da shi, ba zama ka taɓa cewa allura bane, suna amfani da shi wajen kama manyan ƴan ta'addan idan sun shiga yakin sunkuru, da sun yi wa mutun ba zai fi second goma ba zai zube kasa.

A fusace Lion ɗin ya juyo ya damko wuyar Areef ɗin da karfi, sai kuma a hankali idanunsa suka rufe alamar barci, yana ƙoƙarin zubawa kasa, duk da ciwon da yake kirjin Areef ɗin bai hana shi tare ɗan uwan nasa ba ya faɗa saman kirjinsa, wash ya furta da ɗan karfi, dan ya ji zafin ciwon nasa, da kyar ya iya kai Lion ɗin saman bed nasa ya kwantar da shi kusa da Aseef kafin ya zauna a bakin gadon yana sauke nauyayyar ajiyar zuciya.

Miƙa mata hannu ya yi a kan ta bashi almakashin da yake hannunta, ba musu ta rarrafo zuwa gabansa ta miƙa mishi, karɓa ya yi yana sake sauke nauyayyar ajiyar zuciya. "Kawo mini ruwa". Ya faɗa yana ajiye almakashin a gefe, da kyar ta iya miƙewa ta nufi fridge dake cikin ɗakin, ruwa ta ɗauko mishi mai sanyi ta kawo, karɓa ya yi tare da buɗewa ya kafa kai, sai da ya shanye dukka kafin ya cire kansa.

"Me ya haɗaki da Lion?". Ba ɓoye ɓoye ta gaya mishi, bakin ciki tamkar ya tsinka mata mari, a fusace shi ma ya fara magana "Kina hauka ne zaki fita gidan nan da wannan dare haka? Kin san hanyar zuwa prison ɗin ne? Kin san da wa zaki haɗu a hanya? Da ace Lion bai ganki ba me kike tunanin zai faru? Gaskiya kin yi laifi sosai wlh, ya kamata nima na zane ki, idan ma ya hanaki zuwa ba sai ki kirani a waya ki gaya mini ba, idan kina son lallai sai kinga ƴar uwarta ki, ai akwai hanyoyi da dama da zan haɗa ki da ita wanda ba sai lallai ki take maganar da Lion ya gaya miki ba, to ki sani wlh Lion yana iya kin saka baki a case ɗin ƴar uwar taki dalilin laifin nan da kika yi mishi, me yasa kike son ɓata komai da kan ki ne? Meyasa ba zaki gaya mini ba? Kin taɓa gaya mini ga abin da kike so ban samo miki hanyar da zaki same shi bane?". Girgiza kai ta yi tana hawaye tana bashi hakuri, faɗa ya yi mata sosai a kan kada ta sake yin irin wannan gangancin, duniyar yanzu sai a hankali, tsab yarancan zasu lalata mata rayuwa, yanzu ta je ta yi wanka ta kwanta zuwa gobe ko ta wani hali zai haɗata da Jehan ɗin.

Kallon Lion dake kwance ta yi ta kasa motsawa, ya gane nufinta dan haka sai ya ce "Kije babu wani abu, idan ya tashi zai zama normal, zuciyar zata sauka, amma kada ki kara irin wannan kuskuren, sannan kada ki yarda nan kusa ya sake ganin gashin nan naki, dan wlh kika bari ya gani sai ya yanke shi dukka ya zubar, ki kyale shi sai ya huce na kwana biyu, ai wlh kin ma yi muguwar sa'a, na ma kara fahimtar wani abu a tsakaninku, ba dan haka ba Allah yau da sai dai wata ba ke ba, gateman kuma sai dai mu ce Allah ya jikansa, ki sani kuma idan ya mutu nauyin na kanki dan ke kika yi mishi karya kika sanya ya karya aikinsa, sai ki san yadda zaki yi ki shawo kan Lion ɗin kada ya yi mishi hukunci, dan yanzu Lion sai ya fi jin maganarki sama da tawa, je ki yi wanka ki kwanta sai da safe". Ya kai karshen maganar tare da miƙewa ya nufi waje dan ya je ya yi wanka ya zo ya duba lafiyar Aseef kafin ya kwanta.

Da kyar ta iya miƙewa, zubawa Lion ɗin idanu ta yi yadda yake barci ga fuskarnan a ɗaure tamau tamkar hadari, rai a matukar ɓace, wani irin azababben so da kaunarsa ne yake kara shigarta kamar me, matsowa kusa da shi ta yi, kasa kasa ta fara magana tare da tsugunnawa a kusa da gadon "Kayi hakuri ba zan sake ba, na san nayi laifi sosai, ban ji daɗin ɓata maka rai da nayi ba, amma In Sha Allah ba zan sake ba, ka sani ni koma me ina sonka, kuma ba zan dai'na ba, wannan ita ce kaddarata ni kuma". Ta kai karshen maganar tare da riƙo hannunsa guda ɗaya a cikin nata, ga Aseef kwance a gefensa yana sharara barci.

Zubawa yatsun hannun nasa idanu ta yi tana kare musu kallo, kyau iya kyau, sai sheki farcensa suke yi ga su farare tas kamar madara, hannunsa laushi sosai kamar bai taɓa yin wani aiki ba. Ta ɗan jima tana kallon hannun nasa kafin ta sake shi ta miƙe ta nufi waje.

A gurguje ta yi wanka ta fito ta shirya cikin kayan barcinta masu kyau, dogon wando ne da riga mai dogon hannu, launin pink color, fesa perfume nata ta yi tare da hayewa gado ta kwanta, ba jimawa barci ya yi awon gaba da ita dan ta gaji, ta wahala ba karya.

After 1 day👌

Daddyn Rimsha bai samu damar tashi a jiya ba, sai yau ya taso shi da Tyrone, Tga dai har yanzu yana fama da jinya, ba karya ya wahala a wajen yakar wannan kungiya ta su Areef.

Shiri tsab Aseef ya yi cikin wandon jeans baki da polo t-shirt sky blue, ya yi kyau sosai, ya ɗan sami lafiya da kwarinjiki, kiran Akila ya yi a waya ya ce mata ga shi nan zuwa gidansu, dan ba zai iya hakuri yau kwana uku bai ganta ba, ba zai iya cika kwana na huɗu ba, ga shi gobe ɗaurin aurenta, tsabar kuka da zazzaɓin da take yi, sam muryarta baya fita, su Umaisha duk suna a tare da ita, amma ina ko sannu bata iya ce musu, sai aikin gyara Hjy Batula take yi mata, amma ba uhm bare uhm, yau za'ayi mata kunshi na amare, shi kuma Irfan bai wani damu sai ya rinƙa hira da ita ko ya kirata a waya ba, a cewarsa tun da bata da lafiya gara ya kyaleta kawai, hakan yasa baya damuwa da kiranta yake kyaleta.

Jin Aseef zai zo yasa ta tashi da kyar ta shiga bedroom ɗin Ammie dan ta sanar da ita, bata yin komai sai da yardan mahaifiyar tata, Aunty, Hjy Batula, Ammie ta samu a cikin ɗakin, sannu ta yi musu kafin ta ce "Ammie ina son yin magana dake". Okey ta amsa tare da miƙewa ta zo ta riƙo hannunta suka nufi waje, har wani jiri baiwar Allah take gani.

Bedroom ɗin Abba ta shiga da ita, da yake baya nan suna can shi da Abbi suna nasu shirye shiryen, kun san yadda bikin turawa, da uba da ƴaƴan duk haɗewa suke yi sai ka rasa gane ina iyayen suke ina yaran, to wannan ma haka ne, dan Abba da Abbi dai duk ɗabi'ar tana tare da da su, dan sune manya sun girma sosai a kasar Russia kafin su dawo Naija, so ɗabi'ar ta fi zama a jikinsu sosai.

"Akila lafiya?" Ammie ta tambaya, da kyar ta iya gaya mata Aseef ne ya kirata a kan yana zuwa, shiru Ammie ta ɗan yi kafin ta ce "To Akila ba zan hanaki zuwa wajensa ba, amma dai ki san ta in da zaki bi ki fita kada a ganki, kin ga jama'a suna cike, kada ki ja mana magana, kuma ki ce da Aseef ɗin ya tsayar da motarsa a can nesa da gidan nan, wlh duk lokacin da na yi sallah ina rokan miki mafita, Aseef dai shi ne idan na tuna zaki aura hankali yake kwanciya ba Irfan ba, shiyasa bana hanaki kula shi, dan ina ji a jikina kamar da shi za'a ɗaura auren nan gobe ba Irfan ba, amma Allah shi ne masanin gaibu, ba zan taɓa son a baki abin da baki so ba, ki je ki gan shi, amma kada ki jima, ki kuma kwantar mishi da hankali sosai, dan yadda na ganshi kwana huɗu da suka wuce sai da nayi mishi kwallah". Allah sarki babu mai fahimtarka sama da Mahaifiyarka a duniyar nan, uwa ta wuce wasa, babu mai son abin da zaka so sama da mahaifiya, ita ke sadaukar da farincikinta dan ƴaƴanta, uwa baban jigoce ga rayuwar ɗan adam, Allah ka jikan iyayenmu da suka rigamu gidan gaskiya, waƴan da suke raye Allah ka kara musu lafiya, ka kuma bamu ikon yi musu biyayya mu bisu sau da kafa.

Rungume Ammie nata ta yi tana ruwan hawaye, ita kaɗai tasan me take ji a ziciyarta, wlh tasan idan aka ce yau an ɗaura aurenta da wanin Aseef shikenan tata tazo karshe.

Ɗan raba jikinsu Ammie ta yi tana faɗin "Kije kada su Halima su yi tunanin wani abin muke faɗa da bamu yi magana a idanunsu ba, ki kula dai kada ki bari Abbanki or wani ya ganki, idan kika bari hakan ta faru kin san sauran, komai sai ya lalace miki, zaki haɗu da fushin mahaifinki sosai". Okey ta amsa da shi tare da juyawa ta fice da sauri, bedroom na Akil ta nufa, kayan Umaisha ta sanya, dama na gaya muku a baya idan baku manta ba, da Umaisha da Akila da Rimsha yanayin jikinsu kusan ɗaya, shape nasu ɗaya, dan haka kayan Umaisha sai ya zauna ɗam a jikinta tamkar nata ne dama bana Umaisha ɗin ba, ɗinkin riga da skit ne, kayan sun fita sosai.

Bedroom nata ta koma ta ɗauko bayafinta, dan Umaisha bata da mayafi, sai zumbula zumbulan hijabai har kasa, ita kuma ba zata iya saka hijabi ba gaskiya a cewarta, cikin dabara ta ɗauki mayafin bata bari su Umaisha ɗin sun ga me ta ɗauka ba, sai murna suke yi yau ta ji sauki har ta sanya kaya masu kyau, sai fara'a Umaisha take yi, Jelly kam tana kwance shiru kamar wata malamar islamiya, da alama dai malaikun natsuwa ne suka yi mata addu'a.

Bata wani kula su ba ta nufi waje tana faɗa musu tana zuwa, bedroom ɗin Akil ɗin ta sake komawa ta ɗauko face mask ta sanya a face nata tare da fesa perfume nasa, akwai mutane sosai a palo, haka ta zo ta wucesu, wasu sun gane ita ce wasu kuma basu gane ba.

A harabar gidan ma akwai jama'a amma haka ta ketasu ta wuce zuwa waje, da yake a harabar gidan sai hidima da aikace aikace suke yi, sai basu lura da ita ba, su kuma su Irfan su part ɗin Imran, waje ta nufa, ta yi tafi mai ɗan nisa kaɗan, amma tana iya hango gidan nasu, sannan ta tsaya tare da kiran shi a waya a kan ga in da zai sameta kada ya je kofar gida, okey ya amsa mata.

Bata fi minti 10 da tsayuwa ba sai ga shi nan ya danno hancin motarsa, a hankali yake tuka motar, hakan zai sa ka gane yana cikin tsantsar mawuyacin yanayi. Cikin sauri ta buɗe kofar motar ta shiga gidan gaba dan kada wani ma ya ganta, ko yaya Akil ya ganta, Alhamdulila glass ɗin motar ma baka ce, ta kuma yi sa'a ba wanda ya ganta ɗin, ruwa ya ɗauko a roba ya miƙa mata dan ya ga tana haki kamar wadda ta yi gudu, karɓa ta yi tare da cire face mask ɗin face nata, ta kafa ruwan a bakinta, ta sha mai ɗan yawa kafin ta cire ta mayar ta rufe tare da miƙa mishi, karɓa ya yi ya ajiye.

Zuba mata idanu ya yi na ƴan mintoci kafin nan ya ce "Heartbeat kin ga yadda kika rame kuwa? Ba zan iya juran hakan ba gaskiya". Ɗago dara daran idanunta na gadon nan ta yi, da ta rame ma sai idanun nata suka kara fitowa dara dara da su over, zuba mishi ido sosai ta yi, shi ma ya rame sosai, na shi ramar ma ya fi nata, duk yana harkitse.

"My shagwaɓati hakuri zamu yi, mu fawwalawa Allah komai, In Sha Allah idan mu rabon juna ne Allah zai kawo mana mafita, matar mutun ai kabarinsa ne". Nisawa ya yi kafin nan ya riƙo hannayenta tare da matsowa kusa da ita, zuba mata ido sosai ya yi while ita kuma tana kallon kasa.

A nutse cikin sanyin murya ya fara magana "Yanzu da gaske Heartbeat Abba ba zai canza magana ba? Da gaske Abba ba zai bani ke ba? Please ki ce mashi zan yi duk abin da yake so, dan Allah kada ya rabani dake, wlh zan iya mutuwa idan hakan ta faru, please my heartbeat ki ji tausayina, ni ban san menene soyayya ba sai a kanki, ban taɓa yin soyayya ba sai a kanki, tun rana ta farko da prof ya tura mini hotonki nayi bala'in kamuwa da kuanarki, wlh zuciyata ba zata iya jure rashinki ba, ba zan iya ba, ki tausayawa rayuwata, wlh nafi kowa sonki, na fi shi ma Irfan ɗin sonki, please my heartbeat ki rarrashi Abba, kome yake so nayi mashi in dai bai saɓawa Allah ba, to zan yi mashi dan ya bani ke, kin ji ko?". Ya kai karshen maganar yana zubar da kwallah.

Hawaye ne suka fara gangaromata daga eyes nata zuwa face nata, ta kasa ɗago kai ta kalle shi, tabbas bata san me yake cikin zuciyarsa ba, amma dai tana da yakinin idan bai same ta ɗin ba, kamar yadda ya faɗa, mutuwa zai yi, ta tabbatar da yana yi mata wani irin mahaukacin so, kuma ita ma a nata ɓangaren tabbas idan ba shi ɗin ta aura ba, zuciyarta zata ita bugawa, shi ne zuciyarta ta aminta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login