Showing 225001 words to 228000 words out of 359620 words
kuma mallakinka ne, to ka tashi mana my shagwaɓati, ka tashi bari nayi maka tausar ka ji? Uhm uhm". Sai kukan shagwaɓa da ba hawaye take yi mishi, shiru bai motsa ba.
A haka har aka kira sallar mangariba, tana wajen har lokacin kuma kanta a saman kirjinsa, sai zuba mishi shagwaɓa da surutu a hankali kamar mai raɗa take yi, a haka Lion ya shigo ya same su, kallo ɗaya ya yi musu ya kawar da kansa tare da nufar toilet dan ya yi alwala su je masallaci, bata san Lion ya shigo bama, tana can duniyar surutu ga shagwaɓatin nata. "My shagwaɓati ka tashi to na baka abinci a baki, tun fa da safe baka ci komai ba, nima yunwa nake ji mijina, amma ba zan iya cin komai ba sai abin da ka bani da kanka, to ka tashi ka bani a baki dan naci". Duk surutun da take yi Lion yana jinta, ita ce bata san ya shigo ba.
Alwala ya yi yazo ya fice bai bi ta kansu ba, su Abba ma duk sun tafi masallaci, gidan ya rage daga ita Akilar, Aseef, Rimsha, sai kuma Jehan. Har lokacin tana kwance da kanta a saman kirjinsa tana surutu.
Kamar daga sama ta fara jin shasshekar kukansa, dama ya suma ne yana kuka, dan haka sai ya tashi da kuka, a hankali kukan take fita, da kaɗan da kaɗan yana karuwa, ɗago kanta daga kirjin nasa ta yi tana ambatar sunansa, amma bai kulata ba sai famar shasshekar kuka yake yi yana yin wani abu kamar shaƙuwa.
Ta jima tana ambatar sunansa kafin nan ya tsaya da kukan cak, da alama ya ji muryarta ne yasa ya yi wannan shiru yana sauraron. Mayar da kanta saman kirjin nasa ta yi tana faɗin "My shagwaɓati ka dai'na kuka ka buɗe idanunka ka ji? Ai yanzu kam gani nan nazo".
A hankali ya waro dara daran idanuwansa waje, idanun nasa sun yi jawur da su alamar yana cikin ciwo, bata san ya buɗe idanu ba, ta ɗan kifa kai a saman kirjinsa tana surutai abinta, zuba mata idanu ya yi babu ko kyaftawa, ganin abin yake yi tamkar mafarki ne, ɗakin Lion ɗin ya fara bi da kallo dan ya tabbatar da in da yake, a hankali ya sanya hannu ya zame oxygen dake hancinsa, numfashin nasa yanzu ta yi dai'dai.
Hannu ya ɗaura saman kanta dan ya tabbatar ba gizo take yi mishi ba, da sauri ta ɗago jin saukar hannun nasa a kanta, ganin ya buɗe idanu ne yasa ta mike zaune gabaɗaya tana kallon shi, shi ma kallonta yake yi babu ko kyaftawa.
Shigowar Areef ne ya sanya ita ta miƙe ta koma saman bedside drawer ta zauna tare da kawar da kallonta daga kansa zuwa kasa, tana mugun jin kunyar TRIPLETS nasa, su kuma bata san basu san menene ma kunya ba sam, basu san hanyarta ba sam. Shi kuwa har lokacin idanunsa yana kanta, sai kallonta yake yi.
Saman bed ɗin Areef ya hau yana faɗin "Sarkin shagwaɓa sarkin kuka, yanzu ma daga farfaɗowa sai da kayi ko? To yanzu dai ka kara girma ka zama family man sai ka dai'na yi mana wasu tsiyar". Kallon gefen ido ya wurgawa Areef ɗin kafin calmly ya ce "Ni har gobe autan daddy ne, kuma pleasure TRIPLETS, sannan heartbeat ɗin su uncle T, dan haka babu ruwanka da ni". "Au lallai ka warke, to sai ka tashi ka bar mana ɗaki". Kuka ya saka musu yana turo baki.
"Au haka ne our pleasure to ya isa our ɗan auta, ba sai ka zuba mini sabon shagwaɓa ba, dan nasan da ka suman nan wani sabon salo kazo da shi". "Wlh bari Lion ya zo sai ya rama mini". "Sai dai ya rame maka ba dai ramawa ba". Kuka ya sake saka musu hakan kuma ya yi daidai da shigowar Lion ɗin.
Karisowa bakin gadon ya yi yana kallon Areef dake faman sauka, damko gashin kansa ya yi calmly ya ce "Me kayi mishi?". A shagwaɓe Aseef ɗin ya ce "My Lion zagina ya yi tayi". Ita dai AKila ta buɗe baki tana kallon kauna irin na TRIPLETS, suna masifar son junansu, ji yadda suke wasa da raha a tsakaninsu gwanin ban sha'awa da burgewa, wani idan zaka kashe shi ma cemaka zai yi Lion kurma ne baya magana, dan basu taɓa ji ya yi ba, amma kana shiga ɗaki ka same shi da TRIPLETS nasa, abin ba'a magana, duk da ba wani biye musu yake yi ba, amma yana magana kaɗan.
"Me zan yi mishi in rama maka?" Ya faɗa yana kara jan gashin Areef ɗin da karfi, "Ni wlh Lion saboda kai zan datse wannan gashi dukka, ka takurawa kaina haka kawai, amma kuma naga alamar my baby tana son gashi ba zai yanke ba". Cewar Areef.
Shi dai Aseef lallaɓawa ya yi da kyar ya miƙe zaune, ya zubawa Akila idanu yana kallonta. "My pleasure ka faɗa mini me zan yi mishi?" Lion ya tambaya ya ƙoƙarin cirewa Areef ɗin wani ɗan abu da ya kallah a jikin gashin nasa. Runtse ido Akila ta yi kasa kasa ta yi mishi alama da ya ce a saki Areef dan yana jin zafin gashinsa da Lion ɗin ya kama, ga shi sai faman cija laɓɓa yake yi alamar zafi.
"My Lion zuwa da safe sai ka bashi punishment mai kyau". Cewar Areef, ya yi maganar yana wurgawa Areef ɗin harara.
"Baby ta ce idona kamar ball, to ga mai idon ball nan tazo ta gani, diba idanunka Aseef kamar kwan lantarki". Cewar Areef da ake riƙe da gashinsa ba'a saki ba amma yana sake neman wani tsokana saboda ya saba tsokanar Aseef ɗin sosai wani lokaci.
Sake shi Lion ɗin ya yi tare da zama a gefen Aseef ɗin yana kare mishi kallo. "How are you feeling now?" Ya tambaya yana dawo da kallonsa kan Areef, hayewa gadon Areef ɗin ya yi tare da sanya hannunsa a saman kan Aseef ɗin dan ya ji zazzaɓin jikin nasa.
Kwanto da kai Aseef ɗin ya yi a kafaɗan Lion ɗin a shagwaɓe ya ce "Heartbeat ta zo na dai'na jin ciwo ai". Kasa ta yi da kanta tana wasa da yatsun hannunta, shi kuma Areef kallonta ya yi kafin ya ce "Kina jina?". Ɗago kai ta yi suka haɗa idanu kafin ta ɗan kawar gefe tana faɗa mishi e tana jinsa.
"Aseef shi ne farincikinmu, shi ne komai namu, muna kaunarsa fiye da yanda muke kaunar kanmu, kinga ya nuna yana sonki sosai, kema nasan kina son shi, to zamu baki amarsa, please ki kula mana da shi sosai, kada ki bari yaji ɓacin rai, kinga muma bamu barin ɓacin rai ya samu waje a zuciyarsa, kullum yana yawan bani labarin irin farincin da kike sanya shi, to dan Allah ki ɗore a haka, dukkanmu haka da kike gani kafin muzo Nigeria babu wanda ya taɓa yarda da mace ta raɓemu, saboda muna ganin ku macuta ne, a kan matan Nigeria muka fara sakewa da mace, saboda duk ƴan Nigeria waƴan da muka yi alaƙa dasu bana banza, mutanen kirki ne, hakan ne kuma yasa muka yarda ba dukka aka taru aka zama ɗaya ba, ko ina akwai na kirki, kada ki yi breaking heart namu! Ki riƙe wannan shaida da muka yi muku, kin so Aseef tun baki san waye shi ba, hakan ma tasa Lion ya ɗaura muku aure, dan mun san soyayyar gaskiya kike yi mishi, so please ku cigaba a haka, idan ya yi miki abin da bai yi miki daɗi ba, ki zo ki same ni ki sanar da ni, shi ma idan kika yi mishi ba dai'dai ba ya zo ya gaya mini, nine alkali a tsakaninku, sannan ki kula mana da kanki sosai kinji ko ƴar autarmu?" Ɗagowa ta yi tana mamakin ya ce mata ƴar autarsu.
"Kina mamaki ne? Ai ke yanzu autarmu ce tun da auta kika aura".
Kwanto da kansa Aseef ya yi a saman cinyar Lion yana faɗin "My Lion yanzu da gaske ka aura mini my heartbeat tawa?" Shafa kyakkyawar face nasa Lion ɗin ya yi kafin ya ce "Je ka yi wanka ka yi sallah sai kazo kaci abinci". Miƙewa ya yi tare da rungumo Lion ɗin yana zuba mishi godiya tare da sumbata a kumatu.
Sumbatarsa shi ma Lion ɗin ya yi suna jin tsantsar farinciki tare da kaunar juna. "Aseef ka je ka yi wanka kazo ka kai matarka wajen parents nata su ganta zasu koma, ni na tsayar da su, na ce sai sunci abinci an kawo musu ita sun gaisa, so ka yi sauri". Cewar Areef, ya yi maganar tare da miƙewa ya nufi waje, miƙewa shi ma Lion ya yi tare da ɗaukar wayarsa ya shiga balcony dan ya yi waya da daddynsa.
Suna fita ya zuba mata ido yana kallon yadda take aikin murza yatsun hannunta. "So kike ki nemi magana dani ko?". Ya faɗa with his full voice babu shagwaɓa a cikinta, ɗago kai ta yi suka zubawa juna idanu, har lokacin tana murza yatsun hannunta. Matsowa ya yi kusa da ita tare da kama hannun nata yana faɗin "Wai ke me yasa kike son neman magana da ni ne? Sai ki yi murje mini yatsuna ko? Bayan kuma kinsan ni yakamata nayi hakan ko?" A wannan karon ya yi maganar a shagwaɓe.
Ɗan turo baki ta yi zata yi magana Rimsha ta shigo cikin ɗakin bakinta ɗauke da sallama, a tare suka amsa mata sallamar, kusa da su ta zo ta tsaya tare da gaishe da Aseef da jiki kafin ta ce "Aunty Akila ya ya Areef ya ce kizo muje ɗakina ki yi wanka ki shirya kafin yaya Aseef ya shirya su Abba suna jiranku".
Sakin hannayen Akilar ya yi tare da riƙo na Rimshar yana faɗin "Me ya kumbura miki idanu our Queen?". Ɗan murmushi ta yi kafin ta ce "Kuka na yi ne da aka ce ka rasu". Ɗan rungumota ya yi yana bata hakuri, da yake shi bai san cewa Lion yana jin kishi idan suka yi hakan ba, shiyasa har yanzu bai dena rungumar tata ba, Areef dai ya dai'na bawan Allah, dan ya karanci ɗan uwan nasa tsab.
"Muje ko our Queen?" Cewar Akikar, ta miƙe dan su tafi ya yi maza ya saki Rimsha ya riƙo hannunta ɗaya yana faɗin "Shi ne zaki tafi babu sumbata bare kiss". Kallon Rimshar Akilar ta yi kafin ta dawo da kallonta kansa, duk ya jefasu cikin kunya shi ko a jikinsa, hankalinsa a kwance ya faɗi maganar.
"Aunty Akila idan kin fito wannan ɗakin, ɗakin da yake kallon wannan ɗin shi ne namu". Cewar Rimsha ta kai karshen maganar tare da juyawa abinta ta fita, dan ba zata iya tsayuwa ba, irin wannan kalamai na Aseef ai sai shi AKila ɗin.
"Heartbeat ka sanya Rimsha jin kunya ta gudu". Janyota ya yi ta faɗa saman jikinsa yana faɗin "Ke dai kika sanyata ta gudu ni babu ruwana, yanzu dai a bani sumbata". Kallon balcony ɗin ta yi in da Lion yake kenan, sumbatar lallausan kumatunta ya yi kafin ya ce "Shi fa Lion babu ruwan sa da mu, dan haka ki ma dai'na kula shi, ko shekara zaki yi a cikin ɗakinsa wlh ba lallai ya ɗago idanu ya kalle ki ba, dan haka ni a bani sumbata ki dai'na wahalar mini da kanki".
"To rufe idanunka". Ba musu ya rufe ruff, a kumatu ta manna mishi haɗaɗɗiyar sumbata tare da miƙewa daga jikin nasa ta nufi waje da sauri dan kada ma ya ce zai yi mata wani abin da ya fi sumbata ga su Abba na jiransu.
Ƙayatattacen murmushi ya saki yana binta da kallo har ta fita, nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya miƙe da nufin ya shiga toilet ɗin, wani irin jiri ne ta ɗebesa ya faɗa saman bed ɗin, dafe kansa ya yi dan wani irin sara mishi da ta yi, shiru ya ɗan kwanta na ƴan mintoci da basu wuce biyar ba kafin ya sake ƙoƙarin miƙewa, still akwai jiri sosai a tattare da shi, hakura ya yi da miƙewa ya zauna yana mayar da numfashi.
After some minutes ya kira Lion akan ya zo ya taimaka mishi ya shiga toilet jiri sosai yake ji, cikin natsuwa ya shigo cikin ɗakin.
Ya miƙe bari ya gani ya ce mishi, mikewa da zai yi ya sake yunkurin faɗuwa saboda jirin, tare shi ya yi yana kare mishi kallo, wato dai bai dawo normal ba har yanzu, sai sun bashi treatment na musamman, dama ai irin wannan yankar kauna da aka yi musu dole suyi rashin lafiya.
Tallafa mishi ya yi zuwa toilet ɗin, da kansa ya haɗa mishi komai da komai, daga karshe ma sai ya ce bari ya yi mishi wankan kawai, da yake shi ma Aseef ɗin sarkin shagwaɓa ne sai ya ce Okey, can kuma kome Lion ɗin ya tuna, sai ya ce no ya fasa yi mishi ya yi kawai da kansa, turo baki ya yi yana faɗin shi fa ba zai iya ba, jikinsa duk ciwo yake yi mishi, ko sabulun wanka ba zai iya rikewa ba, ba zai iya zuba su shampoos a gashinsa ba, kai mikewa ma ba zai iya yi ba, Lion ɗin ya yi mishi wankar kawai, sam bai kula shi ba ya fice daga toilet ɗin ya barshi, dan Aseef sai Allah.
Da yaga da gaske Lion ba zai yi mishi wanka ba sai ya lallaɓa ya yi, a wannan karon ba shagwaɓa ba ne, da gaske yana fama da bala'in jiri ne da ko miƙewa ba zai iya yi ba, shi ne yasa ya yarda ayi mishi wankar, amma da yaki yi mishi haka ya lallaɓa ya yi wa kansa, da dafa bango ya isa wajen kyawawan fararen towels dake gere a ma'ajiyarsu ya ɗauko ɗaya ya ɗaura a kugunsa, bawan Allah da kyar ya fito daga cikin toilet ɗin, Areef kawai ya samu a cikin ɗakin.
Yana ganin ɗan uwan nasa nata faman dafa bango ya miƙe da sauri ya kariso gare shi yana tambayar ko lafiya, kukan shagwaɓa ya saka mishi yana faɗin "Bana iya tafiya ne, idan na sake bangon zan faɗi saboda jiri". Cikin zolaya ya ce "Zaka sha allurai kenan". "Kai fa Areef mugu ne wlh, to ba sai ku yi ta yi mini alluran ba, kada ku bari sai kunga na mutu". Rungumo shi ya yi yana faɗin "Haba our heartbeat, kasan fa lafiyarka shi ne kwanciyar hankali a gare mu, alluran dole ce zata sanya ayi ai". Ko sannu bai sake cewa ba, ya cigaba da turo baki.
Saman mirror chair ya zaunar da shi tare da fara shafa mishi Lotions na Lion masu daɗin kamshi kyau da kuma tsada, a wannan hali Lion ɗin ya shigo hannunsa rike da farar jallabiya ya same su, miƙawa Areef jallabiyar fara kal da ita ya yi yana faɗin ya sanyawa Aseef ita, a bedroom ɗin Aseef ɗin ya je ya ɗauko mishi, karɓa ya yi ashe da short da singlet a jiki, sai suka faɗi kasa dan a tunaninsa jallabiya ce kawai ya karɓa.
Ɗauka ya yi tare da shirya ɗan uwan nasa ya shunfiɗa mishi dadduma tare da taimaka mishi zuwa saman daddumar ya zaunar da shi, dole a zaune zai yi sallah dan ba zai iya tsayuwa ba, jiri zata kayar da shi, shi kuma Lion balcony ya koma ya zauna ya cigaba da abin da yake yi.
A can Palo kuma sai hira su Abba suke yi, yanzu sun saki jiki da daddyn Rimsha, dan ya nuna musu babu komai, komai ya wuce, za su tafi gida Areef ya ce sam sai sun tsaya, haka ba dan sun so ba suka tsaya suka ci abinci, da yake su sun saba cin irin abincin a Russia, san basu wani ji komai ba, Mark ne ya yi serving nasu, da farko sun ki yarda su ci abinci, sai da daddyn Rimsha ya saka baki, hakan tasa suka hakura suka ci, shi dai Irfan bai ce komai ba, ya yi shiru, dan shi dama ba shi da yawan magana, daga um sai umum, har cikin ransa ya ji zafin rasa AKila, amma bai nunawa iyaye nasa ba, da suka bashi hakuri ma bai ce komai ba, bawan Allah ya danne sosai, amma fa har azzaɓi yake ji mai zafi, sai dai bai bari sun gane bane.
Bayan Aseef ya gama idar da salla ne Areef ya taimaka mishi zuwa palo wajen su Abba dan ya gaisa da surukan nasa, ita ma Akila ta yi wanka ta yi sallah yanzu tana shiri, kayan Rimsha ta sanya, da yake Abaya ce sai suka ɗan yi mata daidai, ita dai Jehan tana kwance saman bed ko sannu bata ce da Akilar ba, ita ma Akilar da yake tana sauri bata kula ta ba, a tunaninta ma barci Jehan ɗin take yi.
A can palo kuwa, da fara'a suka tarbi Aseef dan sun ga yadda daddyn Rimsha yake kaunarsa, so ko dan ɗan uwansu Hosain dole zasu so Aseef, cikin mutunci suka gaisa, sai murmushi daddyn Rimsha yake yi, yau Aseef ya sami AKila.
Da zuwansa palon bai fi da 5mins ba Rimsha ta fito tare da AKila, ita kam Jehan tana ɗaki, ta ce ba zata zo ba dan suna cika mata kunne da surutu, so gara mata ta yi ta kwanciyarta a cikin ɗakin.
Tun da ta shigo Aseef ya tsareta da idanu yana kallonta, ta yi kyau sosai abinta, kusa da Abba ta je ta zauna, ita kuma Rimsha ta juya ta koma sama dan ta je ta gyarawa Lion ɗakinsa. Bakinta ɗauke da sallama ta shiga cikin ɗakin, yana balcony yana zaune, amma kuma zucuyarsa yana son ganinta, dan yau basu da kwanciyar hankali basu haɗu ba sam.
Gyaran bed ta fara yi mishi kafin ta share ɗakin duk da ba datti, ta yi mopping da kyau, ita ma tana kewarsa, tana begen ganin kyakkyawar fuskarsa, sai dai bata san yana cikin ɗakin ba, ta yi tunanin ya fita ne, dan haka data gama gyaran sai ta haye saman sofa ta kwanta tana mai da numfashi, ta gaji sosai ɗan wannan aiki da ta yi.
Ta ɗauki a kallah 10 mins kwance a wajen tana hutawa,