Showing 129001 words to 132000 words out of 359620 words

Chapter 44 - Triplets Book 3 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

1996

dake, to a wajen ba sai kin motsa ba zaki mutu, ba zaki sake kallon su mummy ba, dan haka kada ki yarda Mr Emmanuel ya taɓa ki, kinga shi krista ne ma, yana taɓaki kaɗan dodansu na church zai shanye jininki ki mutu, dan haka sai ki kula sosai, kada ki yarda kowa ya taɓaki".

Zaro idanuwan nan ta yi tamkar zasu faɗo kasa, muryarta har rawa yake yi, ta gama tsorata, har wani zufa ta fara haɗawa, hankali a tashe ta ce "Yanzu Rimsha ita ma Fadila zata mutu?" "Kwarai kuwa, nan bada jimawa ba, dan haka kema idan kina son ki mutu to ki yarda wani ya taɓaki". Narai narai ta yi da idanu tamkar zata yi kuka, duk ta rasa me yake yi mata daɗi a duniyar baki ɗaya, yanzu shikenan idan wani ya taɓata zata mutu, Allah ya sota ma ita ba wanda ya taɓa taɓata sai yaya Feroz ɗinsu da daddy, ko Uncle Shitu bai taɓa taɓata ba, yau ta shiga uku ta lalace, duk wannan a zuciya take zantukan nan.

Ganin ta tsoratata sosai ne yasa Rimshar ta fara rarrashinta tare da kara mata karfin gwiwa da shawari ta yadda zata kula da kanta, daga karshe ta ce mata dama idan kana yaro wani ya taɓaka hakan ba zai faru da kai ba, sai ka girma ka fata period ne idan wani ya taɓaka zaka mutu, da yake ta san Anaya ɗin ta fara period, sai ta fito mata ta wannan hanyar, shiru ta yi tana tunanin tabbas last period ɗin da ta yi lokacin mummyn Rimshan sun zo gidansu sun ɗan yi kwana biyu, tabbas da ta gane tana yi ta tsawatar mata a kan kada ta yarda wani namiji ya taɓa ta, tuna hakan yasa ta kara gasgata zance Rimshar, bayan mummyn Rimsha ma, mai aikin gidansu ta yi mata faɗa sosai a kan kada ta kula maza, ita kuma mummynta tana can wajen Aiki, idan ta fita da safe sai karfe 6 na yamma take dawowa, dan haka bata sanin me ma yake wakana a cikin gidan, ranar da Anaya ɗin ma ta fara period ɗin, mummyn nasu bata sani ba, bata nan, mai aikinsu ne ta taimaka ta nuna mata komai, da mummyn ta dawo, iya always da sabbin pant ta bada aka sayo mata, daga haka ba wani bayani da ta kara mata, da alama ita ma mummyn babu ilimin addini sai zallar boko ne a kanta, irin waƴan nan iyaye na Anaya su suka fi yawa a duniyar mu ta yau, dan girman Allah mata mu kula, ƴaƴa hakki ne a kanku da Allah zai tambaye ku ranar gobe kiyama, amma wasu sai su zaɓi abin banza na duniya su yi watsi da tarbiyar ƴaƴansu, idan kuɗi ya bugasu sai su wani ɗebo ƴan aiki, Allah ba ƴan aiki zai tambaya ba, iyaye zai tambaya, ƴarki mace ki jata a jiki ku zama kawaye, duk wata matsalarta ya zama ke zata fara gayawa kafin kowa, kada ki yarda ace ƴarki tana da wata Aminiya da zata rinƙa gayawa sirrinta ba ke ba, ko da sunan wasa kada ki yarda da hakan, dan Allah iyaye a gyara, kada kuɗi da jin daɗin duniya su ruɗeki, akwai mutuwa a tafi a bar duk wani kuɗi da jin daɗin, Allah ya kyauta yasa mu dace ya kuma sa mu gyara, kuna dai ganin mummyn Rimsha baiwar Allah, dalilin tarbiya da ta basu yau ga shi nan anwayi gari al'umma da dama suna amfanuwa da ƴaƴa nata, badan Rimsha ba ya kuke tunanin rayuwar Anaya zai tafi? Ba dan Jehan ba ya kuke tunanin rayuwar Hanan, Maryam, Adiva, zasu kare? Ku duba irin kasadar da Jehan ta ɗauka a kan Maryam, duk dan me? Dan ta kare mata mutuncinta, da mummynsu bata gaya musu mahimmancin shi ba zasu matsa su shiga kasada dan kula da nasu har wanda ba nasu bane? Da ba'a gaya musu amfaninsa ba za su damu da kula da shi har haka ne? Da bata basu tarbiya ba, ya kuke tunanin rayuwarsu zai kasance? Ku duba yadda suka gogi wahalar rayuwa, Rimsha ta sha zullewa maza ga irinsu boda jamiu, duk dan me? Dan an gaya musu mahimmancinsa, so yana da kyau tun yara basu girma sosai ba, da sun ɗan fara hankali, ki zaunar da su, ki nitsar dasu, ki gaya musu amfaninsa, idan ta kama ki haɗa musu da tsoratarwa, duk dan rayuwarsu ne, a raba yara da kawaye, zina ta yi yawa, lesbian, wannan abu yana yi mini ciwo, yana damuna a cikin zuciyata, kaga yarinya ƴar 15 to 16 years ta san lesbian tana kuma yi, innalillahi wa inna ilaihir rajiun, Allahumma ajirni fi musibati, kuma duk abin da yarinya zata yi idan kuka bincika sanadiyar kawayen banza ne, ku duba rayuwar Aafia, dan Allah kirana a gareku iyaye, ku kula da ƴaƴa, ban da kawaye na kara faɗa, a rabasu da kawaye, tun tana karama ki cusa mata tsanar kawaye, idan ta tashi da shi shikenan kin huta, dan Allah a ja yara a jiki, waƴan nan bala'i na yanzu sun yi yawa, saɓon Allah ya yi yawa, Allah yasa mu gyara amin.

Anaya dai duk ta firgi ce ta tsorata, da kyar Rimsha ta shawo kanta ta yarda zata je office ɗin Mr Emmanuel ɗin, da farko ta ce ta fasa zuwa, ta hakura ta karɓi zero ɗin, sai da ta yi ta bata baki sannan ta miƙe jiki ba kwari duk a mace, tayi ligis ta nufi office ɗin nasa, ita kuma Rimsha ta gyara zama tana jiranta ta dawo su je top shop.

Baki ɗauke da excuse ta shiga office ɗin, yana zaune ya ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya, ganinta yasa ya saki cool murmushi yana faɗin "I knew dama zaki zo, me matsalar?". Saman kujera ta zauna, jikinta sai kerma yake yi, murya a sanyaye ta fara magana "Mr Emmanuel i came to complain about my test results". Kafeta da shegun idanun nan nasa masu kama dana mujiya ya yi, yana kallonta tare da lashe baki kamar wani tsohon maye, idan baku manta ba na gaya muku, bayan halittar dara daran idanu da suka gada har da breast and hips, to ita ma fa Anaya akwai shi, sak Jehan ɗin ne ba maraba, duk lafiyayyen namiji idan ya gansu sai ya kyatsa.

Miƙa mata hannu ya yi akan ta bashi paper ya gani, ba musu ta miƙo mishi hannunta sai rawa yake, karɓa ya yi tare da ajiyewa a gefe, a maimakon ya buɗe ya duba, sai bai duba ba, cike da maitarta ya fara magana da wata shegiyar muryarsa kamar an tada injin niƙa, tamkar wadda ya jima a cikin harkar shaye shaye. "Anaya Azharuddeen Bature, na sani, nasan kinci questions naki dukkan, amma kuma ai ni baki ci nawa rajarabawar bane yasa na baki zero a can".

Ɗan zaro idanu ta yi tana tambayarsa wani jarabawa kuma bayan wadda ya rubuta musu suka yi, ko dai ya yi wani bata sani bane? Da yake babu Allah a zuciyar bare ayi zancen kunya, sai ya fito kwaro kwaro ya gaya mata irin abin da yake da buƙata su yi kafin ya bata result mai kyau, a razane ta ce mishi ba zai yi wu ba, kai tsaye shi kuma ya ce mata to ba zata taɓa cin test na shi ba, kullum idan ta yi zero zata samu, idan dai har bata bashi kanta ba, to wlh ta shirya karɓar zero kullum, idan kuma ta shirya bashi kanta ko yanzu ne, to ta shiga toilet na shi dake cikin office ɗin zai zo ya sameta, tsabar rashin kunya har da ce mata ya yi ba zata jima ba, ba zai fi minti 20 ba anyi an gama, kuma kada ta damu ba wanda zai gane, dan ba zai yi mata yadda wani zai gane ba, da gudu ta miƙe ta yi waje dan ma kada ya ce zai taɓata, sai dukan uku uku kirjinta yake yi, har wani sara mata kanta yake yi, yanzu me zata cewa daddy da mummynta akan wannan test ɗin?.

Amma fa yadda Anaya ta yarda da boko ta ke kuma so, da Rimsha bata yi mata hakan ba, da tabbas dan ta ci test nata zata yarda mishi da abin da yake nema, dan dai kunga, da farko da Rimshar ta gaya mata, ba ta ɗauki abin a wani matsala ba, Allah dai ya sota da rahma ya kuma tsareta a yau kam, sai dai bamu san me gaba zata haifar ba.

Kuka ne mai karfi ya kubce mata, a ɗari ta shiga class ɗin nasu, Rimsha na ganinta ta miƙe a razane tana ambatar sunanta tare da tambayarta lafiya, zuwa ta yi ya rungumeta tana kuka ba tare da ta yi magana ba, jijjigata Rimsha ta fara yi tana ambatar sunanta, "Anaya lafiya kuwa? Ki yi mini magana mana, dan girman Allah ki gaya mini kada ki saka na suma, kin ɗaga mini hankali sosai, wani abin ya yi miki ne?".

Cikin kuka ta gaya mata duk abin da ya faru daga A har Z ta feɗe mata biri har wutsiya, daga karshe ta ɗaura da cewa ita test nata ne ma ya dame ta, yanzu Mr Emmanuel ya ce ba zai sake bata result mai kyau ba, ta shiga uku ya zata yi.

Goge mata hawayen nata ta fara yi tana rarrashinta tare da bata hakuri akan kada ta damu dan ya bata zero, ta barshi da Allah, zai saka mata, idan ta je gida ta kwana sallah ta kai kukanta ga Allah, zai yi mata maganin shi, da kyar ta samu ta rarrasheta ta yi shiru, a yau dai basu fita break ba har a ka dawo class, duk sun yi jugum jugum da su, abin gwanin ban tausayi, Rimsha abin ya shiga jininta sosai, ta san ita ma da wuya idan ba zero zai yi ta bata ba, yau duk wani karatu da aka yi musu, bai wani shiga kansu ba, har lokacin tashi ya yi, Rimsha aka fara zuwa ɗauka, tana ganin motarsu ta ce da Anaya ta zo su gaisa da ƴan uwanta, da murna Anayan ta bita suka je, sai dai ga mamakinsu sai suka ga Mark ne kawai ya zo, ta so ta tambaye shi inasu yaya Areef, amma ba sai na gaya muku ba, kun san halinsa sarai, bata ga fuskar tambaya ba, ko kallon in da take ma bai yi ba, Anaya tana ce mishi good afternoon sir, amma ina ko kallonsu bai yi ba bare su saka ran zai amsa musu.

Ɗan zunguran Rimshar ta yi kasa kasa ta ce "Rimsha a ina kuma kika samo Bature? Ko dai ɗan uwan ki ne? Dama kuna da ƴan uwa turawa ne?". Da yake bata taɓa bata labarin TRIPLETS ba, ita tana da siriri sosai, iya hirar school kawai take yarda su yi ban da na gida, wani lokaci har faɗa Anaya ɗin take yi mata ta ce wato ba zata bata labarin ƴan uwanta bako, sai dai ta yi murmushi ta ce zata bata mana, da haka suke rabuwa. Yanzu ma murmushi ta yi tare da shigewa cikin motar tana faɗin "Idan nazo gobe zan gaya miki, amma dai ba ɗan uwana bane, soja ne mai yi wa su yaya Areef girki". Ɗan sake leƙo shi Anaya ɗin ta yi, har ga Allah ya yi mugun shiga ranta, ta ji tana bala'in son shi, shi kuwa Rimsha na shiga ya kunna motar ya wuce suka bar Anaya tsaye tana ɗaga musu hannu.

Suna fita school ɗin uncle Shitu na danno hancin kan nasa motar, ya zo ɗaukar Anaya, Rimsha hankalinta na kan jakarta tana ɗan duba takardunta, bata gan shi ba, sun yi saɓani.

Uban gudu sosai Mark yake shararawa a kan titin nan, suna mantawa nan a Nigeria suke, ba Washington DC ba ne, Allah ya tsare suka isa gida lafiya lou, yana kashe motar a parking space ta riga shi fitowa ta nufi cikin gida, binta da kallo gateman ya yi, babu kowa a palon kasa, kai tsaye sama ta nufa.

Tana saka kafarta a saman benen shi ma yana sako kafarsa Brady na makale a bayan shi, dan bashi da wajen zama sai ya ɗane bayan Lion ɗin, ya iya tsiya sosai karen nan, baya taɓa yarda ya tafi da kafafunsa in dai ba dole ba, tun yana ɗan jariri Lion ya saba da goya shi a baya, shiyasa da ya girma ma yaki dena hayewa, ko Lion ya ce ya sauƙa ya tafi da kafa sai yaki kamar wani yaro, duk wata tsiya karen nan ya iya shi sanka sanka, da alama garden zasu je, yana ganinta ya diro kasa daga bayan Lion ɗin, kunsan karnika da shegen son shinshina mutun su ji ko daga ina ya fito, kun san su kamshi suke bi.

Ganin ya diro kasa yasa ta fara ja da baya da baya, ko sannu Lion bai ce mishi ba, bata ankara ba sai ji ta yi ta buge mutun ta baya, da sauri ta juya dan ganin waye ne.

Areef ne daga shi sai singlet da three quarter, yau garin ana zafi, rana ta take, kallon Lion dake ta tafiyarsa ko kallon in da suke bai yi ba ya yi, shi kuma Brady duk da Areef ya zo bai dena nufota ba, zuba mishi ido Areef ya yi sai da ya kariso wajen yana ƙoƙarin fara shinshinarta, wani wawan mari Areef ɗin ya kai mishi a kumatunsa, da karfi ya daka haushin da ya sanya Lion da ya yi gaba juyowa dan ya ga me ya same shi.

Kara mishi wani marin Areef ɗin ya yi, cikin harshen turanci ya tambaye shi me Rimsha ta yi mishi da yake takura mata a gidan nan? Ta shiga harkarsa ne? Ko kuma ta taɓa kula shi ne? Sit ya natsu tamkar yaro da aka nitsar ake yi wa faɗa da nasiha mai ratsa jiki, kun san fa suma dabbobi suna jin magana sosai,. Abin ya ɓatawa Lion rai, dan me akan wata Rimsha za'a marin masa Bradynsa, dan haka cikin harshen turanci ya ce da Brady "B fight for your ride!". Yana kai karshen maganar ya fice daga palon abinsa.

Ai kuwa tamkar alluran soja ya yi wa Brady ɗin, nan take ya daka haushi tare da yin tsalle ya haye jikin Areef ɗin ya fara kai mishi yagushi a fuska, ba ji ba gani yake yagushin shi, ƙoƙarin kama hannun nasa Areef ya yi, amma ina yaki yarda ya bada damar yin hakan, daga jikin Areef ɗin ya sake daka tsalle zuwa jikin Rimsha dake tsaye a wajen, ita ma yagushi ya fara kai mata ta ko'ina, yana yi yana daka uban haushi kamar ba gobe, da ganga kuma Lion ya ce mishi hakan, dan yasan Areef ba zai iya kama shi ta sauƙi ba, horon sojoji gare shi, ya horu ba karya, idan baku manta ba na gaya muku mafaɗaci ne na a mutu, kama shi ba abune mai sauki ba, yana da wayo over, dama shi Lion ɗin ne ya ce mishi ya rinƙa jin maganar TRIPLETS nasa, shiyasa yake raga musu, yanzu kuma tun da an ce ya kwaci ƴancinsa ai shikenan.

Sai ihu Rimsha take yi ta zube kasa tana birgima, ganin zai yi mata illah sosai ne yasa Areef ɗin nufarsa a zafafe, ransa a matukar ɓace ya yi ƙoƙarin kama shi, da yake yasan idan ya kama shi ba zai yi mishi da daɗi ba, sai da ya bari ya iso yana ƙoƙarin damko shi, sai ya daka wani uban tsalle ya haye saman kan Areef ɗin ya rufe mishi idanu da gashin jikinsa, kokawa suka fara yi ba kaɗan ba, a tsatsan ɓacin rai Areef ya yi wurgi da shi, ya bugu da jikin bango ya faɗi kasa, wani mahaukacin haushi ya sake dakawa tare da miƙewa ya yi wani girgiza, a guje ya sake mufarsu, Areef bawan Allah ba zai iya faɗa da shi bane saboda ciwon dake kirjinsa, bai gama warkewa ba, shiyasa ma Bradyn ya bashi wahala, baya iya ɗaga hannunsa sosai dan a gefen kafaɗa ne ciwon take, kuma Lion yana sane da hakan ya ce Bradyn ya kwatan wa kansa ƴanci, yasan a yanzu haka Brady zai ji musu ciwo sosai, da dai Areef yana da lafiya ne, da wane kaniyar Brady ya iya taɓasu ma, tuni zai yi wurgi da ɗan banza ko ya murɗe mishi wuya ya mutu kowa ma ya huta da masifarsa.

Yana nufosu da gudu Aseef da ya fito tun ɗazun ya zuba musu idanu ya sha gabansa, shi kuma Areef bama ta su yake yi ba, ya duƙa yana rarrashin Rimsha da Brady ya yagushiwa hannu, fuskarta ya so yagusa da waƴan nan shegun faratun nasa masu tsini, shi ne ta sanya hannunta ta tare face ɗin nata yagushin ya sauƙa a hannun nata, sai jini yake yi, shi ne Areef ya tsugunna yana bata hakuri tare da riƙo hannun nata yana dubawa.

Shi kuma Brady, faɗa suka fara yi da Aseef gadan gadan, sai wani ƙoƙarin yagushin Aseef yake yi, ai kuwa Aseef ya yi wurgi da ɗan banza, da gudu ya sake tashi ta nufo shi, a karo na biyu kuwa, maƙogoronsa Aseef ɗin ya damko, da karfi ya shaƙesa tare da zare mishi ido, cikin harshen turanci dai ya ce mishi "Au ka manta ni na sayo ku kenan? Da ni zaka yi faɗa? Ko Areef da ka jiwa ciwo dan bashi da lafiya ne mara kunyar banza, idan baka rabu da mu ka bar palon nan ba Allah sai na murɗe maka wuya ka mutu mun jefar da banza". Haushi ya daga mishi da karfi, mari shi kuma ya kifa mishi a fuska tare da damko hannayensa dukka biyu ya sake yin wurgi da shi a jikin bango, a wannan karon dai a hankali ya yi haushin, alamar ya jigata kuma ya wahala, ko kallon in da yake Aseef ɗin bai yi ba ya nufi su Areef dake ta faman yi wa Rimsha sannu.

Kusa da ita shi ma ya zo ya tsugunna tare da kamo hannun nata yana mata


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login