Showing 237001 words to 240000 words out of 359620 words

Chapter 80 - Triplets Book 3 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2002

waye zata kira kuma.

Ganin babu ne yasa ta fara bincika mishi contact nasa tana ganin sunayen da ya yi saving numbobi mutane, daga uncle T, uncle Herry, Jay, John, General, su Major, Captain Peter da dai sauransu, su ne dai a wayar babu wata suna mai daɗi bayan nasu Aseef, shi ma Imran Prof ya sanya mishi, Josephine kuwa mummy ya sanya mata, amma kuma baya kiranta mummyn a baki, sai dai ya ce mata Josephine, duk da ma da wuya kaji ya yi maganar ta, amma idan zai yi Josephine ɗin yake faɗe a baki, amma ya yi saving num ɗinta da mummy, da alama lokacin da ya musulta ne ma ya sanya numberta a wayarsa har ya sanya mata mummyn, dan kuwa a baya bashi ma da numberta sam, kuma tun da ya musulta bai yi maganarta ba, wata kila yanzu tun da ya musulta zai iya ce mata mummyn kamar yadda ya yi saving numberta, shi ɗin ne baka gane mishi!.

Ta wuce number Areef da ya yi saving da My pleasure, sai dai ta ɗauka number da ta kira da farko ne, sai bata gwada kira ba, yana barci tana yi mishi bincike a contracts nasa. Sai da ta ji wayar ta buga karfe 11 daidai sannan ta ajiye mishi a kusa da shi tare da komawa ɗayar sofar ta takure waje guda danma yau akwai hijabi a jikinta, duk da ba mai girma bane bai kai gwiwowinta ba, amma ya ɗan tare mata sanyi kaɗan, ta takure saboda tsoro, da kyar ta iya samu barci ya yi awon gaba da ita, gabanta sai faɗuwa yake yi.

Can wuraren asuba irin karfe huɗun nan ta farka tare da waro idanunta waje, a hankali ta miƙe zaune tana kallon in da yake kwance, ga mamakinta sai bata ga jacket a jikinsa ba, ɗan waigawa da zata yi, sai taga jacket ɗin a jininta ya rufa mata, shiru ta yi tana tunanin yaushe aka yi hakan kuma? Bata san cikin dare irin karfe 1 nan ta dame shi da rawan sanyi ne ya je ya rufa mata jacket ɗin nasa ba, sai kakkarwa take yi hakwaranta na garuwa waje guda, shi kuma hakan yana hana shi yin barci, dan komai kankantar motsi yana farkar da shi daga barcin nasa, hakan yasa ya farka ya cire jacket ɗin ya sanya mata, shi ne ta samu ta cigaba da barci cikin salama, shi ma ya samu barci mai daɗi cikin salama ba tare da takurarta ba.

Wani irin daɗi ta ji ganin hakan, ɗaukar jacket ɗin ta yi ta manna mishi kiss tare da sanyawa a jikinta tana bin garin da kallo, akwai hasken farin wata, tun farkawarta ta farkar da shi, motsinta ya tashe shi, sai dai bai buɗe idanu ba. Ai dama dole Lion ba zai yi nauyin barci ba, General Of the army fa, ai ba'a barci ya kai wannan mukami ba, tun bai kai mukamin ba suka saba da rashin nauyin barci saboda jiran harin abokan gaba a koda yaushe, lokacin da suke bakin iyaka, a kowani lokaci abokan gaba suna iya farmakansu, hakan yasa basu da nauyin barci, komai kankantar motsi zai tashe su, abin tun daga training suka samo shi, shi yanzu ba wani aiki yake yi bama ya kai mukamin hutu, sai dai aikin da ya ga dama ya saka kansa zai yi, amma rashin nauyin barcin tabi jikinsa, ya zamar masa jiki abin, ko yaya ka motsa kusa da shi sai ya ji, sai dai ya basar ya cigaba da lumshe idanunsa kawai har barcin ta sake ɗaukarsa.

Haka suka kasance har asuba, sai da ya fara jin kiraye kirayen sallah ne ya miƙe ya nufi cikin gida, da sauri ta bi bayansa, bedroom na kasa ɗaya sabon da ba'a taɓa shiga ba, nan ya shiga dan ya yi wanka da alwala, akwai bedroom a kasa wanda mutun bai taɓa shiga ba, komai na ciki sabo ne, amma yaki zuwa ya kwana a ciki, gara mishi garden, dama kuma already kwanan garden kam ya saba, dan raba dare yake yi a wajen, wani lokaci sai karfe 2 yake shiga cikin gida, kusan za'a ce kawai kwana a ciki yake yi.

Wanka da alwala ya yi tare da fitowa ya nufi bedroom nasa dan ya canza kayan jikinsa zuwa jallabiya, shi ba ruwansa dan su Aseef suna ciki, matsalarsu ce, dan ya ga Aseef ɗin yana son bedroom ɗin nasan ne ma yasa ya bar musu. Sai zuba barcinsu suke yi rungume da juna a cikin bargo, ko kallon in da suke bai yi ba ya wuce dressing room.

Jim kaɗan ya fito sanye da jallabiya fara tas ya fito ya nufi masallaci, a palon kasa ya cikaro da Areef da daddyn Rimsha, ko kallon in da suke suma bai yi ba ya wuce abinsa zuwa masallaci.

Ita kuma bedroom nasu ta koma, Jehan na ta zuba barci, toilet ta nufa, tsarki da alwala ta ɗauro tare da fitowa ta shinfiɗa dadduma bayan ta saka katon hijabi ta tada sallah.

Sai bayan ta idar ne ta tashi Jehan dan ta yi sallah, da kyar ta tashi tana yatsine fuska, ita kuma hawa gado ta yi ta kwanta zuwa karfe 6 ta tashi ta yi shirin zuwa school, Mark ne ya kaita kamar kullum, har ta tafi school ɗin kuma basu haɗu da Lion ba.

Yau jirginsu daddyn Lion ya ɗaga da misalin karfe 10 na safe daga Washington DC zuwa Naija, to sai dai muce Allah ya kawo ku lafiya, sun bar uncle T a gida yana jinya.

Da misalin karfe 10:30 Lion yana zaune a gefen bed nasa, Aseef kuwa Areef ya mayar da shi bedroom nasa, Akila tana tare da mijinta, Areef da daddyn Rimsha suna zaune a palon sama suna hira, ita kuma Jehan tana ɗaki dan bata son fitowa Areef ya takura mata, haushi ma yake bata ɗan rainin wayo a cewarta.

Kiran number Areef Lion ya yi dan ya zo su yi magana, ganin kiran yasa ya miƙe yana faɗin "Uncle ina zuwa ka jirani". Okey ya amsa da shi, duk abin da suke faɗe Lion yana jinsu sarai dan a palon sama suke kusa da bedroom nasa.

Da sallama ɗauke a bakinsa ya shiga bedroom ɗin, kallo ɗaya Lion ɗin ya yi mishi ya kawar da kansa izuwa saman wayarsa, laptop nasa tana garden sun barota a can.

A gefensa Areef ɗin ya zauna yana yi mishi good morning, cikin mutunci da kaunar juna suka gaisa, sai murmushi Areef yake zubawa daddy ya bashi auren Jehan.

"Areef zan yi tafiya zuwa kasar Russia nan da kwana uku, so ka kula da su daddy da kowa, zan tafi da ɗaya daga cikin yaran nan, ko ƙaramar ko babbar, nafi son ma na tafi da babbar dan ita ce mai kama da ubanta, na gaya maka tun yau ne dan iya yau ɗin ne kawai nake da time na zaman magana, akwai sauran abubuwan da zan kammala kafin na tafi, so ina busy". Zaro idanu ya yi yana faɗin "Lion Russia kuma?!". Shiru bai amsa mishi ba.

"Amma dai kasan bamu shiri da kasar Russia ko kaɗan ko? Kana jami'e zaka shiga kasar, to mema zaka je yi a can?".

Ya ɗan ɗauki lokaci kafin ya amsa mishi da "Kakansu zan ɗauko, ƴar Russia ce ai, so tana wajen iyayenta sun kamata sun rufeta a ɗaki dole dole sai ta zama kafura kafin su saketa tayi rayuwa kamar ko". Shiru Areef ya yi yana tunanin wannan bala'i da Lion yake neman jefa kansa, ya sani basu ko ga maciji da kasar Russia, ƙasar America da Russia sam basu shiri ko kaɗan, babu mutunci a tsakaninsu, sannan ya ce zai shiga cikin kasar ya ɗauko ƴar cikin kasar, dama ga shi family'nta a kule suke da Family'n Dr Salman, ya je su sauke haushin a kansa, dan cewa ma zasu yi ko shima ɗin family'n Dr Salman ɗin ne, tun daga nesa su harbe shi da bindiga ko su yi mishi wani abin, lallai kam akwai ƙura, amma kuma yana da kyau a ɗauko Na'urat ɗin dan kada su sanyata ta yi ridda, sai dai fa daddy ba zai taɓa yarda ayi wannan tafiya ba, barema idan ya ji akan abin da ake rikici ƴan uwan Naurat sun hasala sun fusata an musuluntar musu da ƴar uwa, idan baku manta ba ya tsani musulmai, ya ji labarin sun kamata sun rufe tsawon shekaru taki yarda ta zama krista, haushi kamar su rataye kansu ne Lion ya ce zai shiga har cikin gidansu ya ɗaukota, anya kuwa hakan zai yiwu? Akwai babban haɗari gaskiya, da wuya ma gwamnatin kasar ta barshi ya shiga cikin kasar, ina bama zai yiwu ba.

"Kai sarkin tunani, ta ruwa zan shiga kasar, kuma na gaya maka zan tafi da yarinya ɗaya dan mu sami jituwa tsakanina da matar, so ka kula sosai". Da yake yasan Lion idan ya yi magana baya canzawa sai ya ce "Allah ya bada sa'a ya kare mana kai, amma fa Lion to sai dai ka tafi da Rimsha ba dai Jehan ba, ni ba zan iya yin kwana ɗaya ban ga baby ba". "Dama da farko da ita naso tafiya, amma tsoronta ya yi yawa shiyasa nace zan tafi da babbar".

Tsuke fuska ya yi yana faɗin "Wlh hakuri zaka yi ka tafi da ita ɗin dai, baby kam babu in da zata je gaskiya, idan ba kana son wlh nabi bayanku ba in ka tafi da ita". Shiru ya ɗan yi kafin ya ce "Bari na sanya Mark ya shirya sojoji biyar da shi Mark ɗin shida kenan, sun isa dan kula da jirgin ruwan da zamu tafi da shi".

Nan take wani tunani ya faɗowa Areef, to in dai haka ne ta jirgin tuwa zasu bi ai ya sami hanyar da zai sanya Lion ya yi aure cikin sauki, amma bari ya gwada duk da yasan da wuya ya amince.

Nisawa ya yi tare da fara magana a tsantsar nitse kamar wani malami mai yin wa'azi. "Lion in dai haka ne to bai kamata ka tafi da Rimsha a haka ba, kasan dai ba ta yadda za'ayi ta zauna a cikin sojoji ko? Dole a kusa da kai zata zauna, duk da akwai wasu ɗakuna a cikin jirgin, amma a kusa da kai zata zauna dan tsaron lafiyarta da kuma kula da ita, ba zai yiwu ka barta a wani ɗaki daban kai kana wani daban ba, dole a ɗakinka zata zauna, kuma kasanta dama da bala'in tsoro sosai, baza ta taɓa yarda a cikin waƴan nan tabka tabkan takun da zaku keta cikin jirgin ruwa yana tafiya ta yarda ta kwanta a ɗaki ita kaɗai ba, zata yi ta ganin kamar mutuwa zata yi ko zata nitse cikin ruwa, kasan tafiya a cikin ruwa fa sai wanda ya daure, ruwa yana da giggiwar ɗibar mutun kamar jiri idan yana da yawa, so zata tsorata sosai, idan kuma a ɗakinka zata zauna kaga a matsayinta na mace ba muharramarka ba haramun ne a addini, so yanzu kawai a ɗaura muku aure yadda zata zauna a ɗakin naka ba tare da wani tsinuwar mala'iku ya sauka a kanku ba, idan kun dawo daga tafiya zaka iya sakinta tun da kun gama aikin".

Guntun tsaki ya ja tare da ɗaukar wayarsa ya fara latsawa dan Areef bashi da hankali ya lura, aure kuma shi? Abu kamar hauka ko wasan yara, haba ai shi bashi da lokacin yin aure, bashi ma da lokacin mace, gani yake yi Areef ya samu matsala ne a kwakwalwarsa, so bai kamata ma ya bashi amsar wannan shirme da hauka ba.

Shi kuwa Areef dan ya karawa abin armashi da kara haɓakata dan ya tabbatar da zancensa har da mikewa ya nufi waje yana faɗin "Bari na fara yin magana da uncle zan dawo mu karisa maganar mu".

Ko kallon in da yake bai yi ba, dan bama da Rimshar zai tafi ba, da Jehan ɗin zai tafi dan tafi dakiya da rashin tsoro, Rimsha tana ganin wani bala'in ai rungume shi zata yi ta hana shi cetansu da kuma cetanta, ta ja a ci galaba a kansu, yasan kuma ba ƙaramin yaki za'ayi ba kafin ya shiga kasar Russia, akwai cakwakiya, ya yi alkawarin kuma sai ya kammala case ɗin Nawazudden tas zai koma kasarsu, yana son haɗa shi da kowa da kowa nasa su koma kamar da ne. Wannan aiki idan ba General Of Army ba waye zai iya shi? Su kansu su daddyn basu san in da mahaifiyarsu take ba, amma har ya nemota zai je ɗauko ta, zai shiga gagarumin haɗari saboda su, gaskiya daddyn Rimsha ya ciri tuta, Lion ya yi mishi abubuwa da yawa, sai dai shi kuma daddyn yana kullace da Lion ɗin na abin da ya faru a tsakaninsu, bawan Allah bai san gagarumin taimakon da Lion ɗin ya yi mishi bane, da ya sani ba zai kulkace shi ba.

Zama Areef ya yi kusa da daddy yana faɗin "Uncle ina so ne ka bawa Lion auren Rimsha zasu yi tafiya, idan suka dawo zai saketa, kaga bai dace su yi tafiya a haka ba suna matsayin da sukenan, Rimsha ta girma ai".

Areef ya tabbaka babban kuskure a maganarsa da ya ce a bawa Lion auren Rimsha zasu yi tafiya ne, idan ya dawo zai saketa, sai kace wata kayan wanki ko kayan gwanjo, wani uba ne zai yarda da hakan? Ƴar cikinsa fa, Rimsha 14 years a mayar da ita bazawara ne kenan ko yaya? Haba maganar ta yi muni over, ai wlh koda ba zai saketa bama daddy ba zai bashi aurenta ba bare kuma har da wani cewa idan suka dawo zai saketa kamar wata kaza, maganar ta konawa daddy rai over, shi kuma Areef bai yi mishi bayanin Lion da wuya ya saketa ɗin ba, tarko Areef ɗin ya kafa mishi dan ya kamu da sonta ai, shi kawai ya faɗi maganar ne dan yana tunanin daddyn yasan komai da yake wakana, bai san cewa tun da ya zo ai bai samu zama dasu Rimshar ba bare ya fahimci akwai kusanci tsakaninta da Lion ɗin.

Rai a matukar ɓace shi ma daddyn ya tabbaka babban kuskure wanda ya dawo yana danasani mara amfani, dan kuwa cikin fushi ya ce "Wlh Allah ya sauwaka na bawa Saif auren ƴata, koda ma yana sonta ba zan bashi ita ba bare kuma baya sonta, tafiya zasu yi idan ya dawo ya sake ta, ita ɗin an gaya maka kayan wanki ce? Ko kaza ce? Wlh ba zan bashi ba, ko namutu sai na bada wasiha kada a bashi ƴata".

Dama kuma duk wani uba na kirki zai ji zafin magana irin haka idan akayi ta a kan ƴarsa, sai dai daddyn a in da ya yi kuskure yasan halin Lion ɗin, amma yana bari zuciya ta ɗebesa tasa ya yi abin da zai na danasani daga baya, ya san cewa idan Lion ya ce abu to ba yadda ya iya da shi sai hakuri, amma haka wani lokaci idan ya hau dokin zuciya idanunsa suka rufewa ya faɗi kalamai masu zafi.

To a wannan rana ma tarihi ce ta maimaita kanta, domin kuwa Lion ya ji duk abin da suka faɗa, hakan ta sanya shi ya fito cikin kunan rai ya yi wasu maganganu masu zafi ga daddyn. "Ba zan auri ƴar ka ba saboda baka so ko? To wai kai baka san ni duk abin da ba'a so shi nake yi ba ne? Bani da ra'ayin yin aure a rayuwata, amma a yau yanzu ba sai anjuma ba za'a ɗaura aurena da ƴarka, sannan ka sani zan yi tafiya da ita kamar yadda Areef ya faɗa, da ba da ita zan tafi ba, amma yanzu da kayi magana da ita zan tafi, sannan kuma kai ne waliyin da zaka karɓi wannan auren kuma ka bayar ko kana so ko baka so! Daga karshe kuma sai ka fara azumin kaffara na rantsuwar da kayi ba zan aureta ba!!". Tashin hankali, danasani daddy ya farayi na maganganun da ya yi, domin kuwa ya sani auren Rimsha da Lion yau babu fashi kamar yadda Lion ɗin ya faɗa, shikenan yanzu ya ɓatawa ƴarsa rayuwa da kansa da kalamansa? Magana kalilan ta sanya ya cuci yarsa, yana shirin ko ace ya jefata cikin wahala? La ilahi ya lilliahi.

Shi kam Areef sam bai so abin ya zo musu a karo na biyu ma da haka ba, ya so ne su fahimci juna, bai san meyasa sam daddyn Rimsha da Lion basu shiri ba, basu haɗuwa inuwa ɗaya, daddy zuciya da saurin hawa, idan ya hau kuma baya iya controlling kansa, sannan bugu da kari shima yana da izza, shi kuma Lion duk balai idan ka ɗaga mishi murya tofa sai ya sanya kayi laushi, bare kuma daddy da yake faɗan maganganu masu zafi akan Lion ɗin, ai dole bazasu shirya ba, dole kullum idan suka haɗu sai ta kwaɓe musu, idan bai yi sa'a bama ya jawa Rimsha bala'i kenan, dan da wuya idan Lion ba zai azabtar da ita ba, dan daddynta ya ji kunan rai sosai, sai dai kuma ta wani ɓangaren Areef ɗin ya ji daɗi da Lion ɗin ya amince zai aureta, babban abin jin daɗi na gaba kuma, Lion idan ya yi niyar yin abu fa to baya fasawa, saboda kayi niya ka sake fasawa ma shi yana ganin ai kaskanci ne da nuna faɗuwa, ka zubar da girmanka, dan haka wannan hatsaniya data faru a tsakaninsu bai sa ya ce zai fasa ɗauko Naurat da haɗa daddyn da family'nsa ba, laifin wani baya shafan wani, idan ya ɗauko Na'urat ba iya daddy kawai ya yi wa ba harda surukansa wato su Abbi.

Makudan daloli wato dollars ya ɗebo daga ɗakinsa wanda shi kansa bai san adadin yawansu ba, yazo ya zubewa daddyn a kan shi ne sadakin Rimsha, wayarsa ya ɗauko ya kira Sultan limamin masallacinsa na Washington DC, ya sanya wayar a hand-free, Sultan ya zama mishi waliyi, daddy dole ba dan ya so ba ya bada auren Rimsha Sultan ya karɓa aka ɗaura aure take a wajen a Washington DC wato cikin Masallacin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login