Showing 153001 words to 156000 words out of 359620 words

Chapter 52 - Triplets Book 3 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

1993

kuka ya wuce da ita ciki, yau idan ranta ya yi dubu to ya ɓaci, kuka take yi ba kaɗan ba, a tsakiyar palo ya sauketa tare da komawa waje ya fito da fetur ɗin zuwa wajen engine, zubawa ya yi ya tayar sun yi sa'a ba abin da ya sami engine ɗin.

Bayan ya kunna wuta ya zo ne ya wuce ciki, yadda ya barta haka ya dawo ya sameta, alamar abin ya yi mata mugunciwo sosai, sai kuka take yi, ko kallon in da take bai yi ba ya haura sama abinsa, ya ji daɗi da ya kona mata rai ba tare da ya taɓa lafiyar jikinta ba, zaman dirshan ta yi a wajen tana kuka tana jan Allah ya isanta a cikin zuciyarta,

Fridge na ɗakin daddy ya fara kunnawa kafin ya sake saukowa kasa zuwa wajen mota ya kwaso kayan drinks da suka sawo ya dawo, a cikin fridge ɗin ya zuba su, har lokacin tana zaune a palo tana kuka, tamkar bai san da zaman ta a wajen ba, toilet ya nufa ya yi wanka tare da shiryawa cikin pajama ya fito zuwa balcony dan ya duba mattress ɗin, ya jike sharkaf da ruwa, ɗagawa ya yi ya tsayar a tsaye tare da jingina shi da jikin karafunan wajen, sannan ya nufi bedroom ɗin mum, nata mattress ɗin ya ɗauko zuwa bedroom ɗin dad, da yake girman gadon nasu ɗaya, kunna Ac ya yi sannan ya shinfiɗa bed sheet ya haye ya kwanta tare da ɗauko wayarsa da ya ɗaura a saman bedside drawer tun shigowarsa, da yake wayar tasa wata Prof ce sai bata yi komai ba da ruwan sama ya jiƙasu, ɗan latsa wayar kaɗan ya yi kafin barci ta yi awon gaba da shi, ita kuma sai da ta gama cin kukanta har sai da idanunta suka kumbura, sannan ta miƙe zuwa bedroom nasu ta yi wanka tare da shiryawa cikin wasu shegun riga da wando, jeans ne baki mai bala'in kyau, ya kamata sosai duk da yake na Jehan ce, amma ta ɗan yi kiba shiyasa ya matseta sosai, sai ƴar riga mai karamar hannu fara, hand dryer ta ɗauko tare da junawa ta busar da gashinta, cike da tsoro ta fito ta nufi ɗakin daddyn nata, dan wlh ko za'a kasheta ba zata kwanta ita kaɗai a ɗaki ba, salon wasu karti su shigo, gara mata shi ɗin dai duk da tana jin haushinsa, ga shi baya rufe gidan, sai ya bari a buɗe kayansa, ko alamar tsoro babu a tattare da shi. Da sallama ta shiga cikin ɗakin, sai faman kumbure kumbure take yi, already lokacin ma ya jima da yin barci abinsa, harararsa ta yi tare da kara jan Allah ya isa a cikin zuciyarta kafin ta kwanta saman sofa tana mai jin kuna a cikin ranta, ga bala'in yunwa.

A ɓangaren gidan Hajiyar daɗi kuwa, bayan sun dawo daga super market ɗin, sun sha sayayya ba karya, Jehan sai murna take yi ba kaɗan ba, a hankali Hjy ta turo kofa ta shigo cikin ɗakin nasu, daga ɗan bakin kofa ta tsaya tana faɗin "Jehan". "Na'am mummyn". Ta amsa tana miƙewa zaune, "Ki shirya, ki tsantsara kwalliya mai shegen kyau kina da bako". Cool murmushi ta saki, ita da bata murmushi a baya, "To mummy wani irin kaya zan saka?". Shiru Hajiyar ta ɗan yi kafin ta ce "Baƙon na musamman ne, ɗaya ne daga cikin jigo na wannan gida, kusan zan ce miki shi ya kafa mu da har muka kai izuwa yanzu, ya nuna ra'ayinsa a kanki sosai, dan haka ki saka short zuwa gwiwa, da kuma riga mai karamin hannu ma it's okey". Da fara'ata ta amsa da to tare da miƙewa ta shige toilet, ita kuma Hajiyar ta nufi waje, Maryam Adiva duk suna baje a sama gado sun yi ɗai'ɗai daga su sai guntayen wando zuwa cinya da ƴar riga da bata wuci cibiya ba, sai taunar chewing gum suke yi.

Wanka ta yi ta fito ta shirya kamar yadda suka yi da Hjy, sai murmushi su Adiva suke yi suna yaba kyan da ta yi, wayar Adivar ta ɗauka tare da nufar waje, sai sheki gashin kanta yake yi, ya sha gyara sosai a fitar da suka yi ɗazun, ta yi kyau kam ba karya, office ɗin Hjy ta nufa, sai murmushi take yi, ba sallama ta afka ciki, Hjy na zaune a saman dankareren lallausan kujerarta, ga sanyin Ac na bugata, Hamshakiya mandiya, sai wani washe baki take yi taga ruwan kuɗi.

Ganin Jehan ɗin yasa ta kara washe baki tana faɗin "Jehan ga alhajin da yake bukatarki, ya ce ma tafiya zaku yi da shi sai jibi zai dawo da ke". Ba musu ta amsa da okey mummy tare da juyawa ta kai kallonta kansa, wani irin bugu gabanta ya bada, zaro idanun nan nata ta yi tana kallon shi da mamaki, ko mutuwa ta yi ta dawo ba zata manta da wannan fuska tasa ba a rayuwarta, ganin face ɗin nasa kuma yasa ta tuna da wace ce ita, me ya kawota gidan, menene yake faruwa, da ni daku munsan addu'ar da iyayenta suke yi mata ne ya yi sanadiyar dawowarta cikin hayyacinta, amma ita bata sani ba, bata kuma nuna musu ta dawo cikin hayyacinta ɗin ba, sai ta ce to su je ta shirya, magani Hjy ta bata akan idan taje kafin su kwanta da alhajin ta sha dan gudun ɗaukar ciki, ba musu ta karɓa tare da wucewa ta yi gaba tana tunanin yadda zata ɓullowa lamarin, duk sai ta ji wani irin, dressing nan da ta yi sam bata ji daɗin shi ba, amma saboda akwai abin da ta kudurta a ranta, sai ta daure ta shanye, bata nuna kamar kayan sun sanyata bakin ciki ba.

Shi kuma alhajin ya miƙe zai bi bayanta Hjy ta tsayar da shi tana yi mishi magana a kan dan Allah kada ya bari Jahan ta ɗauki ciki, wani irin shu'umin murmushi ya yi, dan shi yasan me ya shirya a kan Jehan ɗin, yasan Nawazudden sosai, akwai ƴar tsama a tsakaninsu, so amfani da Jehan ɗin zai yi ya zuba mata tsafi a ciki ta mutu dan babanta ya yi mishi wani laifi da ta shafe su can, sai dai bai nunawa Hjy hakan ba, ya ce mata ba komai zai kula, da haka suka yi sallama ya bi Jehan suka fita.

Tun da suka ɗauki hanya barin gidan ta kurawa hanyar idanu sai kallo take yi, shi kuma Alhajin bai lura ba yana tuki, da haka har suka fita garin Abuja suka ɗauki hanyar Kaduna. Sai karfe 8 na dare suka shiga garin Kaduna, kai tsaye wani katafaren gidansa dake unguwar su Lion ya nufa da ita, guest house ne, akwai ƴan'sanda biyu dake tsaron gidan, da kuma ƴar aiki guda ɗaya, hakan zai nuna maka babban mutun ne sosai, da alama kuma ya aminta da waƴan da suke cikin gidan ne. Ciki suka shige, tana biye da shi babu musu kamar wata rakumi da akala.

Cikin wani tampatsetsen bedroom ya shiga da ita, sai kallon hanya take yi, duk in da suka bi ta gani kuma ta haddace, suna shiga ya fara cire kayan jikinsa, ya rage daga shi sai shot kafin ya shiga cikin toilet dan yin haɗe haɗensa na tsafin nasa, tana zaune tana tunanin me mafita, me yakamata ta yi? Can wani idea ya faɗo mata na wani labari da ta taɓa cin karo da shi a Media, wata ta yi wa mijinta, shiru ta yi tana jiran fitowarsa, tsabar ma mugunta ya shirya mata sai bai ce ta yi wanka ba, sauri sauri kawai yake yi ya aiwatar da abin da yake so, saman gado ya hau tare da cire shot nasa yana faɗin ta zo mana, tsirara haihuwar uwasa ya yi a gabanta, yau shi ne karo na biyu da ta ga wannan tashin hankali, amma ta daure ta danne bata nuna mishi zata tirje ba, cikin dakiyar zuciya ta ce "Ina son shan ruwa mai sanyi da fruits kafin mu yi komai, kai baka ga hanyar da muka sha bane? Ai ina jin yunwa".

Ɗan kwaɓe fuska ya yi kafin ya ɗauko waya ya kira mai aiki a kan ta kawo mata, "Yauwa Alhaji bana son a yanka mini fruits ɗin dan ina da kyankyani sosai, ni zan yanka da kai'na dan bana son datti". Dariya ya yi yana faɗin "Ai dama baki yi kalar datti ba". Murmushi dole ita ma ta yi tana mai duba time a wayar Adiva dake hannunta, shi kam ko a jikinsa, dan yasan sai Hjy ta saye imaninsu ta yadda basu yi wa mutun musu kafin ta fara ɗaurasu a network, Jehan kuma akwai basira, ta fahimci hakan ne shiyasa ma bata nuna musu ita ta fita daga tarkonsu ba, tana ciki ba zata yi musu musu ba ta nuna.

Ba kunya ba tsoron Allah mutumin nan yana kwance tsirara har mai aikin nan nasa ta kawo mishi abin da ya bukata, da alama shi da mai aikin ma suna sheke ayarsu tun da bai rufe jikinsa ba har ta shigo. Saman bedside drawer ta ɗaura tray ɗin tare da yi wa Jehan sannu ta juya ta fita, fruits ne irinsu Apple ayaba lemu da sauransu, sai wata ƴar madaidaiciyar wuƙa mai kaifin bala'i tare da robar ruwa mai sanyi da glass cup kwara ɗaya a saman tray ɗin.

Natowa Jehan ɗin ta yi tare da fara ɗaukar ruwa ta yi bismillahi ta buɗe robar ta sha, dai'dai lokacin kuma a ka kira shi a waya, da yake wayar tana kusa da shi sai ya ɗaukota yana faɗin "Bari ma na sanyata a airplane mode dan kada a takura mana da kiraye kiraye muna tsaka da jin daɗin mu, mutane basu san lokacin da ya dace su kira mutun ba, su dai idan bukatarsu ya taso shikenan........" Bai kai karshen maganar ba ya ji wani bakin azaba ya ziyarcesa, da iya karfinta ta sanya wukar da aka kawo mata dan yanka fruits ta yanke mishi gabansa wato bananarsa, daga tushensa ta yanke ba ma sama sama ba.

Tana yankewa ta yi wurgi da wukar tare da ɗaukar wayarta ta fisge nashi dake hannunsa ma ta haɗa dukka biyu ta nufi waje da uban hudu,. Ihu ya kurma tare yunkurawa, amma ya kasa tashi, nan take jini ya fara gangarowa, ihu ya cigaba da waje muryar nan tasa yana kurmawa.

Jin ihunsa yasa ƴan'sandan dake bakin gate suka nufo ciki da gudu, ita ma mai aikin da gudu ta nufo ɗakin, laɓewa bayan wani ɗaki Jehan ɗin ta yi, tana ganin ƴar'sandan suka wuce zuwa ɗakin nasa, bayan sun wuce ne ta fito a guje gabaɗaya jikinta kermar tsoro yake yi, gudun cetar rai zata yi, fitowar da ta yi kuma ashe mai aiki ta ganta, da gudu ta kira ƴan'sandan tana gaya musu gata can gata can, kafin su zo ma tuni ta isa bakin gate, sai dai gate ɗin a rufe yake da kwaɗo, tsabar bala'in tashin hankali da take ciki, bata san lokacin da ta kama gate ɗin ta haye ta dira waje ba, gabaɗaya wayoyin saman ginin sun ji mata ciwo, amma bala'in da take ciki yafi wannan, tasan idan suka kamata a cikin wannan gida to sai dai gawarta ya fita, ta san wadda ta yi wa wannan aika aikan ba ƙaramin mutun bane, ƴaƴan Farooq ne uwa ɗaya Uba ɗaya, idan baku manta Farooq wanda ya yi kokarin lalata rayuwar Hanan a Katsina na ba, to yayansa ne wannan alhajin..........Dama idan bala'i ta yi balai zaka yi abin da ba ka taɓa zaton zaka yi shi ba, yanzu dai bala'i tasa Jehan haura saman gate, dama haka ne, in kaga bala'i ba abin da ba zaka iya yi ba, san da zaka yi ma, ba zaka sani ba, sai daga baya bayan ka samu natsuwa zaka yi ta mamakin ya akayi kayi abu kaza? Allah dai ya raba mu da bala'i.

A guje ƴan'sandan suka buɗe gate ɗin suka rufa mata baya, a haukace ta hau saman hanya tana gudu ga kanta babu ɗan kwali, saura kaɗan wata danƙareriyar mota ta takata, har ta ɗan bugeta ta faɗi kasa ma, da alama ta ɗan ji ciwo, dan ma dai Allah yasa driver motar ɗan hannu ne, ya iya tuki sosai, shiyasa ya yi nasarar taka birki a cikin wannan yanayi, ganin ta faɗi kasa ne yasa matukin motar ya fito da sauri ya nufo ta, dan ya ganta karamar yarinya ce, ba wata babbar mata bace. Zaro dara daran brawn eyes nasa ya yi yana faɗin "Areef kazo ka kallah ta ɗan ji ciwo fa, ka zo ka dubata, kuma ka ga wasu ne suke binta".

Yana zaune a gaban mota, shi dai burinsa azo a kai shi wajen heartbeat yau ya ganta su gaisa, amma Aseef zai ɓata musu lokaci, tun da bata ji ciwo ba sosai ba Allah ya tsare basu bugeta sosai ba, ba sai ya wuce su tafi ba, me na wani kiran shi ya zo ya ganta. Dama sun ce da Akila suna zuwa ne, yau za su je su gaisa da Ammie, ita kuma Akila ta gaisa da Areef, shi ne suka shirya tsab za su je.

Ganin sai kiransa Aseef ɗin yake yi ne yasa shi fitowa yana jan tsaki, Aseef ya ɓata mishi rai, dai'dai lokacin kuma ƴan'sandan suka iso wajen, da yake unguwar na manya ne, kun san babu jama'a, kowa yana cikin gida..........


Yaya makomar wannan lamari zai kasance? Anya alhajin nan zai rayu kuwa? Shin Jehan ta kyauta kuwa? Aseef, Areef zasu taimaka mata kuwa? Alhajin zai kyaleta kuwa? Ga kuma kaninsa Farooq dama yana nemanta, Jehan ta tara maki ta ko'ina, Ya makomarsu Adiva? Shin Lion zai kama wadda ya je nema kuwa? To bari dai na barku haka sai mun haɗu on Monday idan mai dukka ya kaimu

❤️❤️TRIPLETS❤️❤️


*Duk wace ta karanta mini littafina ba tare da ta biyani hakkina ba Allah ya isa ban yafe ba, sai Allah ya tsayar da mu ranar da bata da abin da zata biyani face ladarta*




E41-42💋


Ganin sai kiransa Aseef ɗin yake yi ne yasa shi fitowa yana jan tsaki, Aseef ya ɓata mishi rai, dai'dai lokacin kuma ƴan'sandan suka iso wajen, da yake unguwar na manya ne, kun san babu jama'a, kowa yana cikin gida, kallo ɗaya ya yi mata ya kawar da kansa yana faɗin "Me yasa kake ta kirana ne wai?". Ita kuma buguwar da ta yi nan ne yasa ta ke ganin jiri jiri bata wani jin me suke faɗe sosai.

Miƙewa ta yi tana wani tangal tangal kamar zata faɗi, ta gaji over, ga uban gudu da ta sha, baiwar Allah ga dirar da ta yi ta saman gate kafarta na ciwo, bugu da kari duk ta kukkuje jikinta da wayar dake saman gate ɗin, ta ji ciwo,. A sugwane Aseef ya ce "Areef wlh she is resembling uncle face, they look alike, i think sister Rimsha ce, daughter uncle ce ita ma, kalli face nata ka gani". Hararar shi Areef ɗin ya yi yana faɗin "Zaka wuce mu tafi ne ko kana gaya mini she look like Uncle,? Wai ka manta nan kasarsu uncle ne? To dole akwai masu kama da shi over, so please let's go ina son mu dawo na kira Lion dan nayi magana da my Rimsha, ina missing nata over, tun safe bamu yi magana ba fa".

Katse su ƴan'sandan da suka iso yanzu suka yi da cewa "Ke wuce mu tafi". Maganar da suka yi kuma yasa Areef da Aseef ɗin gabaɗaya juyo da kallonsu a kansu, da kallo ɗaya Areef ya yi musu ya fahimci marasa gaskiya ne, shi ma Aseef a nasa tunanin ya san dole wani abin zasu yi mata, duba kuma da irin shigar da yake jikinta, wata kila fyaɗe suka yi kokarin yi mata ta ki yarda, shi ne ta gudu suka bita, a tunanin Aseef kenan, shi kam Areef kai tsaye yasan basu da gaskiya.

Kokarin kamata suka yi Aseef ya ce ba zai yi wu ba, wlh babu wanda ya isa ya kamata, dan ta yi mishi kama da uncle Hosain sosai, ko da ba ƴar uwarsa bace, to dole zai taimaka mata saboda albarkacin kamar da fuskarta ta yi da shi, dan haka sai ya tsaya tsayin daka a kan lallai ba zasu tafi da ita ba.

Jingina da jikin motar Areef ya koma ya yi, tare da goya hannayensa a saman faffaɗar kirjinsa yana kallon karfi hali irin na Aseef, shi ya dage a dole lallai sai ya tafi da ita, yarinyar da bai san ta ba, kawai daga ganin wasu sun bi yo ta a cikin daren nan ya wani tsaya shi dole sai ya taimaketa, ga shi ba shi da karfin ko na ɗaga kwalin sweet, su kuma ƴan'sandan da suka biyota sun ce lallai sai sun tafi da ita, domin kuwa ta aikata laifin da dole su kasheta.

Wani dogon tsaki Areef ɗin ya ja Aseef yana ɓata mashi lokaci, ya ƙosa ya koma gida ya kalli ya Rimsha ta wuni yau su yi video call, yana kewarta sosai da sosai.

Yana tsaka da tunani bai ankara ba sai jin wani kara na sauƙar mari mai sauti ya yi.

Cikin sauri ya ɗago kai tare da kai kallonsa kansu Aseef ɗin, ɗaya daga cikin ƴan'sandan ne ya wanke Aseef da wani mahaukacin mari, da sauri Aseef ɗin ya dafe kuncinsa da hannunsa, idanunsa sun yi jajawur domin ba karya ya maru sosai. Kan ka ce me ɗayan ya sake kwashe kafafunsa a in da ya zube kasa a waje, nan fa suka yi yunkurin yi mashi ɗan iskan duka domin su tafi da ita.

Wani irin mugun bakin ɓacin rai Areef ya ji wadda tasa bai ma san lokacin da ya raba jikinsa da jikin motar ba ya yi kansu a zafafe.

Cikin zafin nama ya hau jibgansu tare da watsi da su kamar an aikosa, nan take ya koma ainahin waye shi, wato ya koma jam'in C.I.A cikakkun jarumai masu bada rayukansu akan al'ummarsu, kafin ma su shiga aikin sai sun sanya hannu


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login