Showing 66001 words to 69000 words out of 359620 words
an samu shekaru basu yi faɗa ba, a lokacin da suke ƴan 22 to 23 years, kullun na Allah ne sai sun yi faɗa, lokacin shi ma Areef akwai zafin zuciya, Lion bala'in zuciya rashin hakuri, Aseef zuciya, kun san lokacin ciwonsa, to haka zasu yi ta faɗa duk gidan ba mai iya raba su, sai sun jiwa kansu ciwo sun daku iya dakuwa ga junansu, sannan su hakura idan sun gaji, idan suka fara faɗa ko Uncle T tsoron tinkararsu yake yi kada su haɗa da shi, daddy kuwa har kuka yake yi idan sun fara, dan yasan ba shakka sai sun jiwa kansu ciwo, dan dukkansu ba baya ba wajen karfi ga zuciyar bala'i, ɗaya ya ce ba zai hakura ba, idan aka mishi sai ya rama, idan ya rama shima wadda aka rama ya ce ba zai bari ba, babu hakuri ko ɗaga kafa, haka zasu yi ta yi, amma yanzu Alhamdulila sun samu tsawon shekaru a kallah 6 basu yi faɗa ba, kuma duk da wannan faɗa da suke yi fa basu cin abincin idan har ɗaya daga cikinsu baya nan, a tare suke komai, har kwana ɗaki ɗaya suke yi, gado ne uku a cikin ɗakin nasu a lokacin, tun ainahi suna kaunar junansu fiye da tunanin mai tunani, sai dai kunsan dama ana samun faɗa irin haka a tsakanin ƴan uwa, musamman ma twins or Triplets.
STORY💋
"Yauwa Prof menene Aduwa?". Cewar Areef. Shiru ya ɗan yi yana tunanin menene ma wannan aduwar.
Katse mishi tunani ya yi da cewa "To koma menene ka haɗa da aduwa da goribar ka kawo mini da wuri fa" "Tom za'a kawo yau ma zan je kasuwar barci ba za'a rasa ba". Okey ya amsa da shi, daga nan ba su sake yi wa juna magana ba, suna kwanta shiru.
Can after some minutes Areef ya ce "Prof na mance ka ce da sister ta shirya zuwa Monday ta koma school". Ɗan satar kallon Lion dake kwance yana fuskantar gefe da su ya yi, kafin ya ce "Okey amma naji matukar daɗi over wlh". Ya kai karshen maganar tare da shafa kyakkyawar dark black curly hair Lion ɗin.
Juyo da blue eyes nasa ya yi a kansu. Ganin irin murmushin dake a kan fuskar Imran da kuma ɗan uwan nasa yasa ya ji daɗi sosai, yana son ganin Imran cikin farinciki kamar yadda yake son ganin TRIPLETS nasa, har cikin ransa yake jin Kaunar shi, bai taɓa son wani bayan TRIPLETS nasa kamar yadda ya so Imran ba.
Haka suka cigaba da nishaɗi suna hira, duk da bai sanya musu baki ba, yana matikar jin daɗin yadda suke hira da dariya haka.
AFTER SOME DAYS GIDAN HAJIYAR DAƊI 😭.
Tsawon kwanaki uku kenan yau su JEHAN suna rufe a cikin toilet, babu ruwa babu abinci, duk sun fita hayyacinsu, duk kyankyani irin na Jehan jiya sai da ta sha ruwan famfom toilet ɗin dan ta ceci rayuwarta kada ta mutu, sai kuka Adiva take yi, Allah sarki bata saba ba, ga yinwa ga kishin ruwa, sun yi ƙoƙarin buɗe kofar toilet ɗin amma abin ya ci tura, idan baku mance ba ta baya Zinariya suka rufe su, duk sun yi tsuru tsuru da su abin tausayi, sun fita hayyacinsu, tsabar yunwa tasa basu gani sosai, A'isha dai ta yi dana sanin biyewa Jehan, sun buga kofar toilet nan har suka gaji, ko motsin mutane basu ji ba, tamkar basu a duniya, tamkar babu kowa a gidan, Jehan ta yi kokarin buge wurar dake jikin window toilet ɗin dan taga me a wajen, sai taga akwai karafuna ta waje a jikin window, ba halin fita, kuma duk a cikin gidan window yake, ba a waje bane.
Idanuwan Jehan sun ƙanƙance sun yi jawur, da akwai dama, da ta yi kuka ita ma, amma ta daure tana rarrashin Adiva, banda sunan Allah babu abinda take kira, ta rasa madafa, sai yanzu zantukan daddynta ke dawo mata a cikin kunnenta, lokacin da yake neman takara, yana yawan gayawa uncle Shitu, idan zaka yi gyara ko kana son dakatar da wata ɓarna a ƙasar nan, to kada ka yarda ko da sunan wasa ka fitar sa nufin ka, dan akwai wasu shegun kuraye da dama da basu son a kawo gyara, su burinsu kawai a ɓata, kansu kawai suka sani, idan zasu ji daɗi to kowa ma ya mutu in yana so, idan ka kuskura ka fitar da nufinka na kawo gyara, to zaka ɓata, kuma ɓata ta har abada, za'a rufe babinka, za'a shafeka tamkar ba'a taɓa yin ka ba, jama'ar dake goya maka baya ma, duk zasu juya maka baya, a kullum jama'a suna amfani da abin da suka ji, ko kuma abin da aka shirya musu karya a kansa suka kalla, ba zasu taɓa yin tunani da kwakwalwarsu ba, da zarar ka shirya musu ƴar karamar karya tsab zasu yarda su hau kai su zauna, sai ka rasa wani irin kwakwalwa ce da mutanen mu, sai ka rasa me yake damunsu, ga gaskiya suna gani sai su take, shi ne babbar matsalar ƴan kasarmu, da suna da zuciyar tsayawa a kan gaskiya, dagiya a kan adalci, cire son zuciya, cin hanci da rashawa, su daina duba ɗan karamin abin da za'a basu, su duba al'ummarsu, su duba cewa wannan ɗan abin da za'a basu zai kare su sake komawa wahala, amma idan suka tsaya tsayin daga a kan ayi adalci, a kawo gyara, a dakatar da ɓarna, to ko basu sami komai ba, adalci ta tabbata zasu ji daɗin rayuwa fiye da tunanin mai tunani, a ƙasar nan ba'a yaki da rashin gaskiya gaba da gaba, idan ka kuskura ka yi gigin yin hakan, to zaka yi danasanin zuwarka duniya, ta karkashin kasa ake yakar tsinannu shegu, ta karkashin kasa ta in da basu zata ba, ta nan zaka yaki duk wasu kuraye marasa adalci masu tauye gaskiya.
Tuna zantikan daddynta yasa ta fara hawaye, yau ne ta tabbatar da abin da daddyn nata yake faɗe, sai dai kayi yaƙin sunkuru da rashin gaskiya, ba dai ka yi gaba da gaba ba.
Ganin tana hawaye yasa Adiva ta dafata tana faɗin "Jehan lafiya kike hawaye haka?". Girgiza kai ta fara yi kafin ta fara magana. "Adiva daddy ya yi gaskiya, yanzu kinga da muna nuna zamu yaki gidan nan ta karfin tsiya, kinga mun kare a cikin toilet, daman daddy ya ce ta karkashin kasa ake yakar rashin adalci, yanzu na gane nufin daddy, hawayen da nake yi kuma saboda daddyna nake yin shi, daddyna ina yake? Yana raye ne ko ya mutu? Bana jin ya mutu Adiva, bana jin hakan a jikina, na fi zaton yana wani wajen yana rayuwa, ya Allah ka kare mini iyayena da ƴan uwana, Rimsha ƴar uwata ɗaya tilo a duniya, ko a ina take yanzu Oho, ita ma ina ji a jikina tana raye, tana wani wajen, Allah sarki, Allah ka kawo mana mafita". Ta kai karshen maganar tana goge hawayen fuskarta.
A cikin wannan kwana uku da suka yi a rufe, sallah ma a zaune suke yin shi a cikin toilet ɗin, ita Jehan azumi take ɗauka a gabaɗaya kwana ukun, shiyasa abin ya yi mata sauki, su A'isha kuwa, ruwan toilet ɗin suke wuni sha ba abinci, cikinsu ya yi ta ciwo kamar zasu mutu, haka zasu wuni suna hawaye, da daddare kuwa, Adiva da Maryam cikin baf ɗin wanka suke shagewa su kwanta, ita kuwa Jehan a zaune take kwana, idan barci ya kwasheta har faɗuwa take yi wani lokacin, Aisha kuwa, a kasa mai gabaɗaya take kwanciya dan suna wanke toilet ɗin, Bayin Allah nan abin tausayi, duk wanda ya gansu sai ya matsa musu kwallah, har wani shegiyar rama suke yi.
Su kuwa su Zinariya, suna can suna harkokin gabansu, sun kawo sabbin ƴan mata da wasu sabbin matan aure ƴan hannu, kuɗi nata kara shigowa kamar ba gobe, sun bar bayin Allah a cikin toilet, tamkar ba rayuka suka rufe a ciki ba, Allah dai ya yi mana maganinsu ya toni asirin tsinannu shegu. In Sha Allah sai sun girbi abin da suka shuka, zasu ɗanɗani ƙuɗarsu kuwa.
WANNAN KENAN A GIDAN HAJIYAR DAƊI BARI MU LEƘA GIDAN LION DAN JIN YA AKE CIKI.
AFTER SOME DAYS.
Yau ma dai tsala wanka suka yi, suka shirya cikin kananan kaya, a yau ne kuma Imran ya tafi karɓo musu ɗin kinsu dake wajen tela, yana fita ba jimawa suka shirya cikin wando jeans ash color mai shegen kyau, ta ɗan kamasu daga ta sama, ta kasar kuma ta buɗe, riga kuma top ce pink color, sun yi kyau sosai kamar ka sace su ka gudu da su, Rimsha zata ɗaure gashin kanta Akila ta hanata, wai ta sake shi kamar ba Indiya, kuma kun san yadda gashin nata yake, sak gashin kakanta Na'urat, abin ba'a cewa komai sai dai Masha Allah.
Haka ta biyewa Akila ta saki gashin har gadon baya, perfume ɗin Akila suka sanya a jikinsu, Rimsha ta fito kamar baturiya sai dai hasken fatar ne kawai da bata da shi kamar nasu, ita kuma Akila da yake gashin ta bai kai na Rimsha tsawo ba, sai ta ɗaure shi tare da sanya ɗan ƙaramin handkerchief ta ɗara a gaban goshinta, tsakiyar kanta a waje.
Da farko Rimsha ta ce ba zata fita babu ɗan kwali ba, daga ƙarshe kuma da Akilar ta yi ta zugata, sai ta yarda suka nufi waje a hakan.
Babu kowa a palon sama, dan haka sai suka sauƙa kasa, nan ma babu kowa, waje gabaɗaya suka nufa, ita kuma Jelly tana can tana barci abinta.
Garden ɗin gidan suka nufa, sai satar kallon sojojin da Lion ya karo Akila take yi, ita kuma Rimsha tsoronsu ma take ji, fuskokinsu kamar wasu shanaye a ɗaure, ita kuma Akila kyau take kalla, taga fararen turawa, ga tsawo ga murɗewar jiki, shiyasa take ta faman satar kallonsu. A ƴan kwana biyun nan dukka Imran ne yake yin aikin Rimsha na gyara ɗakin Lion da na su Mark, dan har ga Allah Rimsha bata iya gyaran ɗaki ba, bata san yadda ake yi ba, bare ma gyaran gado, sam bata iya ba, a hankali hankali dai tana koya.
Babu kowa a garden ɗin, zama suka yi, Rimsha ta ce bari ta ɗauko masu ice cream su sha, dan su ji daɗin hira, to Akila ta amsa mata da shi, miƙewa ta yi ta koma cikin gida, ita kuma Akila ta zauna shiru sai kalle kalle take yi, garden ɗin ya haɗu iya haɗawa ba karya. Daga karshe ta ɗauko wayarta ta fara latsawa.
Fitar Rimsha ke da wuya, sai ga Areef sanye yake da Army trouser, da kuma farar T-shirt, ya yi kyau sosai, yau da alama yana ji da tsiya, domin kuwa ya yi kitso guda bibbiyu ta gefe da gefen kunnuwansa, kuma ba ƙaramin kyau suka yi mishi ba, sauran gashin nasa kuma, ya tara a tsakiyar kansa ya ɗaure, hannunsa na riƙe da wani cup mai shegen kyau, sai tiririn hayaki ne ke fita daga cikin cup ɗin, da alama coffee ne a ciki, kafafunsa na sanye cikin home sleepers masu shegen laushi launin ash color, ɗayar hannunsa na riƙe da wayarsa yana latsawa, da alama kuma wani saƙon yake turawa.
Kwata kwata bai san da mutun a cikin garden ɗin ba, sai ya shiga da sallah kasa kasa ta yadda babu wanda zai iya ji, ita dai kanta na kan wayarta tana karanta saƙon ɓoyayyen masoyinta.
Bai lura da ita ba, wucewa ya yi zai zauna, kwatsam ta ɗago kai dan jin ɗan motsi da ta yi, shi ma kuma a lokacin ne ya lura da ita, a razane ta.........
❤️❤️TRIPLETS❤️❤️
E17-18
Bai lura da ita ba, wucewa ya yi zai zauna, kwatsam ta ɗago kai dan jin ɗan motsi da ta yi, shi ma kuma a lokacin ne ya lura da ita, a razane ta miƙe tsaye tana kallon shi, kirjinta sai dukan uku uku yake yi, shi kuma cool murmushi ya saki kafin ya zauna a in da yake son zama tare da ajiye cup ɗin hannunsa. "Why are you standing?" Ya faɗa cikin sanyin murya, ya yi maganar kuma yana ƙoƙarin fara latsa wayarsa.
A hankali ta koma ta zauna tana kare mishi kallo, tabbas wannan shi ne a hoton da ɓoyayyen masoyi ya tura mata, sai dai hoton tun yana ɗan 22 years kenan? Ta tambayi kanta da kanta, duk da bata kalli fuskarsa sosai ba a hoton, tabbas soyayyar da take yi mishi ta gaskiya ce, tabbas ko a ina zata iya gane shi, tabbas ma shi ne, TO FA BABBAR MAGANA.
"Prof sister right?" Ya faɗa yana mai dawo da kallonsa a kanta, da kyar ta ɗaga mashi kai alamar e, mamaki take yi yadda ya nuna kamar bai gane ta ba, kenan yana tunanin ita ba zata iya gane shi bane dan ya tura mata hotonsa yana ɗan 22 years ko yaya yake nufi? Ta sake tambayar kanta da kanta, tambayar kuma da bata da amsarsa.
"Heartbeat right?" Ya sake tambayarta, kara zaro idanunta waje sosai kamar zasu firfito su faɗi kasa ta yi, domin sai yanzu ma ta ji wannan zazzakar murya tasa, kuma wlh yadda ya kira Heartbeat ɗin nan, haka yake kiranta a waya, tabbas shi ne, daddaɗar muryarsa ne, kyau nasa ne, komai da komai na sa ne, ta kasa magana, sai kare mishi kallo take yi, yanzu tambaya biyu ya yi mata bata amsa ba.
Ganin tana ta kallon shi ne yasa ya kashe mata ido ɗaya tare da ɗaga mata gera ɗaya yana faɗin "Nayi maki kyau ne?" Duk maganar da yake yi cikin harshen turanci yake yi, babu hausa ko ɗigo a bakinsa, watakila yana tunanin bata gane shi bane yasa bai yi hausa ba, ko kuma dai ya abin yake ne? Na kasa ganewa.
"Heartbeat ki yi magana mana? Why ki ke ta kallona haka? Shin na yi wani laifi ne, ko dai kina so na ne?". Ya kai karshen maganar cikin zolaya.
Miƙewa ta yi da sauri dan ta gudu da nufin ta bar wajen, in dai shi ne ɓoyayyen masoyi to bata son shin, domin dama idan baku mance ba, ta ce bata son maza masu yin gym, kuma shi Areef tamkar Lion yake, yana yin gym sosai da sosai.
Ganin zata gudu ne yasa ya yi saurin miƙewa ya riƙo hannunta yana kare mata kallo. "Heartbeat what is the problem? Why ina yi maki magana you refuse to amsa me, and then kina ta kallona, daga karshe ki tashi zaki gudu, menene matsalar, ko dai kin fasa so na ɗin ne?" Ya faɗa yana ɗaga mata gera ɗaya alamar zolaya.
Ƙoƙarin kwace kanta take yi dan ta gudu, da karfi ya jawota jikinsa har sai da ta buge shi a ciwonsa, wash ya ɗan furta da karfi.
Zuba mashi ido ta yi tana kare mashi kallo, ya riƙera sosai, sai kare mata kallo from Head to toe shi ma yake yi, wani tunani ne ya faɗo mata, tun da bai nuna ya santa ba, ita ma ta biye mashi a haka taga karshen me zai yi, ba dai ya ce ranar Wednesday zai zo gida ba, to ai gobe ne Wednesday, ta biye a je a bai santa ba, zata ga ranar Wednesday idan ya zo gida kuma me zai sake ce mata, dan dai ita ta san wlh shi ne wannan, ko kaffara ba zata yi ba, kallon ƙurillah ta yi wa hotonsa, wannan brawn hair ɗin nasa, sannan ga muryarsa, yadda ya kirata da Heartbeat yanzu, tamkar yadda yake faɗa ne a waya, ga shi yanzu ya ce ko ta dai'na son shi ne, akwai hujjoji da dama da suke tabbatar mata da tabbas ko rantsuwa ta yi ba zata yi kaffara ba shi ɗin ne.
Yin wannan tunani yasa kasa kasa ta ce "To sake ni na gaya maka". Da hausa ta yi maganar, amma kuma tamkar ya ji me ta ce, sai ya sake ta tare da komawa ya zauna a saman sofar, domin sosai yaji zafin buge mashi ciwon nan da tayi.
Komawa itama ta yi ta zauna a saman nata sofar in da ta tashi. Zuba mata waƴan nan shegun rikitattun dara daran ash eyes ɗin nasa ya yi, duk yasa ta tsargu, sai wasu ƴan kame kame take yi, mamaki ne ya rufe shi, wai ita heartbeat me matsalar ta ne? Ya tambayi kansa.
Ita kuma Rimsha tana barin wajen da nufi ta je ta kawo masu ice cream, a palo ta haɗu da Imran ya dawo daga karɓo musu kaya, zai fita ita kuma ta shigo palon kenan, sai ya ce ta je ta kaiwa Saif abincin rana, mamaki tayi sosai akan meyasa daga jiya zuwa yau Lion yake cin abicni akan lokaci, kuma yake barci a kan lokaci, Meyasa? Abin da bata sani ba shi ne, dama tarin tulin aiki da rashin kwanciyar hankali yasa baya samun damar cin abinci, amma yanzu Alhamdulila da mumnynsa da ɗan uwansa sun tsira daga wajen waƴan nan tsinannun matsafan, babu wata aiki da ta rage mashi fa ce aikin daddynta daya fara last week, yanzu ya samu kwanciyar hankali sosai, domin shi ƴan iskan Nigeria bai ɗaukesu a wata tsiya ba, gani case ɗin daddynta yake yi kamar cin kaza ne, dama yakin da su TAG za su je ne yasa bai mai da hankali a kan aikin daddyn nata ba, ya tattara hankalinsa a kan nasarar su TAG ɗin, yanzu kuma tun jiya bai sake duba case ɗin ba, yana ɗan busy na tura gawarwakin sojojin da a ka kashe zuwa ga iyalansu da sauran abin da ya dace a matsayinsa na babba, to a takaice dai yanzu ya sami kwanciyar hankali yana da damar cin abinci sosai da kuma samun barci akan lokaci. To kun ji abin da yasa tun da Rimsha ta bar garden bata dawo ba.
Shiru suka zauna a garden ɗin, tunani kala kala ne cike fal a cikin ranta, shi kuma ya tsareta da idanu sai kallonta yake yi kamar zai cinyeta ɗanye, tamkar mai son yin wata magana, amma kuma bai ce komai ba.
Ganin ta yi kasa da kai ta yi shiru ne yasa ya ɗauko cup ɗin coffee ɗinsa yana faɗin "Zo na baki coffee