Showing 291001 words to 294000 words out of 359620 words

Chapter 98 - Triplets Book 3 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2001

shafa bayanta a hankali hankali alamar ta yi barci to. Cikin ɗan ƙanƙacin lokaci ta samu natsuwa sosai saboda karfin addu'a, sai sauke ajiyar zuciya take yi tana jan hanci, ta ci kuka ba karya.

Jin ta samu natsuwa ta kara lafewa a jikin nasa tamkar mai jin barci ne yasa ya ɗan rankwafo da kansa a kanta tare da dakatawa daga addu'ar da yake tofa mata. Can kasan maƙoshinsa tamkar mai raɗa ya furta "Meesha". Ɗan ɗago kanta ta yi tana kallon lallausan laɓɓansa, ta kasa kallon cikin kwayar idanunsa, "Are you okey now?". Jinjina mishi kai ta yi tana faɗin "Yes am okey, amma kuma ina jin sanyi sosai yaya Saif". Kallon yanda take aiki tura ɗan bakin nata ya yi. "Meyasa kika cike tsoro har haka ne?".

A shagwaɓe ta ce "Ni fa yaya Saif ba tsoro nake ji ba, da gaske ne naga dodo irin wanda gwaggo take bamu labarin shi a tatsuniya". Sam bai gane in da zancen nata ya dosa ba, wai ana basu labari a tatsuniya, kai Rimsha duniya. Canza topic ɗin maganar ya yi da cewa "Anywhere, yanzu dai a duk lokacin da kika tsorata, ki kasance sunan Allah shi ne abu na farko da zaki fara ambata ba ihu ba, idan kina ihu a duk lokacin da kika tsorata hakan zai bawa shaiɗanun aljanun dake kawaye da ke su iya shiga jikinki har su cutar dake, so be careful". "Tom yaya Saif zan kiyaye". Ya ji daɗin amsar da ta bashi, bata yi ƙoƙarin kare kanta ta hanyar yi mishi musu ko wani abin ba, yasan ita mai addini ce, yasan ta tsorata sosai ne da har ta manta bata furta sunan Allah, amma sam bata yi ƙoƙarin gaya mishi ta tsorata ne yasa ta kiɗime bata yi hakan ba, sai kawai ta amsa mishi da to zata gyara, ya ji mugun daɗi, dayawa daga jikin maza haka suke, sun san komai, amma zasu rufe idanu suyi ta faɗa a kan abin da suka san bake kika yi shi ba, idan baki yi masu musu ba, kika basu hakuri, wlh ba ƙaramin daɗi suke ji ba, zai wuni a cikin zuciyarsa yana sanya miki Albarka, idan kuwa kika yi ƙoƙarin kare kanki dan ki gaya mishi gaskiya, to zaku yi faɗa ne a banza dan ba zai karɓi kuskurensa a wannan lokaci ba, so yana da kyau mata ku lura a kan hakan, ba ko wani lokaci zaku yi musu da su wajen sawa su gane baku da laifi ba, sun san komai, wannan hallitta ce da Allah ya yi musu na ba zasu nuna sun sani ɗin ba, zasu ga kamar idan suka yi hakan zaki renasu ko makamancin haka, ya kamata mata mu waye a kan karatun maza, mu karancesu tsab.

"Why are you always looking at my lips?". Ya tambayeta yana ɗauko wayarsa da ta yi ƴar kara alamar shigowar saƙo. Massage ne da ɓoyayyiyar number, gargaɗi ake yi mishi da babbar murya a kan kada ya yarda ya tonowa kansa abin da zai bin ne kansa da kansa, guntun tsaki ya ja tare da goge saƙon ya ajiye wayar a ransa yana faɗin Wai su kam basu sam shi abin da ba'a so shi yake aikatawa ba ne? To wlh sai ya yi bincike ya gano wasu kungiyar matsafa ne Josephine take ciki, yana da yakinin sune suka turo mishi wannan shirmen banzan da wofin, sun ja ma ya ji yana bala'in kaunar binciken yanzu, kuma sai ya yi idan sun isa kada su bari ya kwana yau, iskancin kawai, har shi za'ayiwa barazana, to wlh sun ma taɓowa kansu ne, sai ya yi abin da basu taɓa zato ba, amma ya ɗan yi mamakin a ina suka samu numbersa, sai dai bai damu ba dan yasan number Nigeria ne, da numbersa na Usa ne wlh wane kaniyarsu su iya turo mishi saƙo kuma har ta shigo, ba zata shiga ba ko sun tura, dan ba kowani shirme yake shiga wayarsa ba.

Yana tunani yana shafa bayan matar tasa yana jiran ta bashi amsar meyasa take yawan kalle mishi lips. "Allah yaya Saif lips ɗin naka ne suna yi mini kyau". "Serious?" Ya yi maganar yana ɗaga gera ɗaya, tamkar walkiya ta ga ɗaga gerar tasa, dan ta wutsiyar idanunta ta ga hakan, cikin sauri ta ɗago da kallonta zuwa saman face nasa da kyau, dan ta tabbatarwa da kanta da gaske gera ɗaya ya ɗaga irin na Areef ne?.

Tana ɗago idanu ya sake ɗaga mata gera ɗaya ba tare da ya yi magana ba, ba ƙaramin ruwan mamaki ta sha ba, wato shi ma ya iya ɗaga gera guda kenan? Lallaima yaya Saif ɗin nan, wato dai babu abin da bai iya ba shi ma, kawai yi ne ba zai yi ba, amma yanzu ga shi da lokacin yi ɗin ya yi ai yana yi.

Number Sultan ya kira dan ya gaya mishi su fara sauke mishi Alqur'ani mai girma dan zai sake komawa wannan shegen case ɗin na matsafa, a ko da yaushe shiyasa Lion yake nasara a rayuwarsa, ga shi dai shi Bature ne kuma krista ne ya musulunta, amma duk abin da zai yi Allah yake fara sakowa a gabansa kafin komai, Allah kaɗai yake kaiwa kukansa, baya tsoron wani mahaluki a duniyar nan, baya shakkar kowa. Sai dai fa abin mamakin duk da wannan abin da ya faru sun fi jin Josephine ɗin a ransu sama da daddy, sun rasa meyasa suka fi kaunarta.

Bugu ɗaya Sultan ya ɗauka, cikin sanyin murya suka gaisa, sannan ya gaya mishi buƙatarsa, shiru Sultan ɗin ya ɗan yi kafin ya ce mishi "Amma Saif da ka bari sai ka koma tukun nan, akwai haɗari sosai, saboda kaga in da ka nufa yanzu waje ne mai haɗari, sannan tafiya kake yi a cikin ruwa, kasan kuma a cikin ruwan nan babu abin da babu, akwai shaiɗanun aljanu sosai, kuma aiki ne da ya shafi tsafi da shaiɗanun aljanu, ni dai a nawa shawarar zan so ka bari sai ka fita daga cikin ruwan nan, ka koma gida lafiya lou, sai mu ɗaura ko?". Kallon Rimsha dake ta faman kallonsa ya yi yana tunanin wannan ƴar rigimar tasa ma ba zata iya ɗaukar wannan kasada ba, tana jin motsi zata zunduma mishi ihu ta hana shi yin aiki, so Sultan yana da gaskiya, ko dan ma Rimsha zai hakura sai ya koma ɗin, kuma yana ganin girman Sultan sosai, dattijo ne sosai wanda a kallah zai iya kai shekaru 60 zuwa 70, sai mai taimakinsa wato ladan ɗinsa wanda sunansu iri ɗaya da Sultan ɗin, shi ma baban mutun ne, so ba karya Lion yana ganin mutuncin Sultan tun lokacin da ya musulta.

Hakan ta sa ya ce "Okey uncle i will think about it". Addua'o'i sosai kamar yanda ya saba Sultan ɗin ya yi mishi, shiru ya yi yana sauraron addua'o'i suna ratsa shi tare da sanyaya mishi zuciya, har sai da ya kai karshe sannan ya amsa mishi da Amin uncle......... Ai ko dan addua'o'i da Sultan yake zuba mishi ma dole zuciyarsa ta yi ta sanyi tana rage zafi, dole ya sauƙo, ai addu'ar manyan malamai ba wasa ba. Karin wata haske na abin da baku sani ba, perfume ɗin Lion Sultan yake haɗa mishi ita, shiyasa basu shiri da duk wani shaiɗanin aljani, basu haɗuwa waje guda, to Sultan yake haɗa mishi ita haɗi na musamman, shi ya zaɓi irin kamshin da yake so, sannan Sultan yake tofe mishi ita da addua'o'i masu karfin gaske kafin ya bashi, ainahin turaren daga Dubai yake sayosu ya kawowa Sultan ɗin, idan ya gama haɗa mishi su sai ya kira shi a waya a kan ya aiko a ɗauka mishi, to kun ji tushen perfume ɗin nan, duk wani shaiɗanin aljani ba zai taɓa zama kusa da wannan perfume ɗin ba, ko aljanune a jikinka in dai masu cutarwa ne shaiɗanu da an shaka maka zasu gudu.

Da haka suka yi sallama ya ajiye wayar yana mai dawo da kallonsa a kanta, cikin sauri ta runtse idanu tana murmushi, ba ƙaramin kyau ta yi ba, hannunta ya riko cikin nasa yana kallon ƴan yatsun nata, tunanin maganarta na ɗazun ne ya faɗo mishi a ransa, a in da take cewa yaya Saif lokacin fa da aka yi mini wannan zanen ina yarinya ce, tunani ya yi wato ita yanzu ji take yi ta girma kenan ko? Wai da tana yarinya, kai wannan ƴar rigimar tasa akwai ta da iya magana da son girman, yanzu ma bata wuce a goyata ba wai da tana yarinya yanzu ta girma tab su babba manya.

"Yaya Saif nace maka sanyi fa nake ji?". Ta yi maganar a shagwaɓe sosai, shiru ya ɗan yi kafin ya ce "Har a jikin nawa da kike kwance ma?". Jinjina mishi kai ta yi alamar e tana faɗin "To ai yaya Saif kai ma kayan narci ne a jikinka ba jacket ba, shiyasa nake jin sanyi, da Jacket ne zan shiga ciki ba zan ji sanyi ba". Shiru ya yi bai yi magana ba sai dai ya gyara kwanciyarsa da ita a jikin nasa tare da ja musu bargo zuwa wuyanta shi kuma karjinsa.

Tamkar mai yi mata raɗa ya furta "To sauka mini a jikina". Make kafaɗa ta yi tana faɗin "Ni a'a gaskiya, ina tsoron dodan can Allah, haka kawai na sauka ya kamani, gara mini dai jikin naka duk wuya". Yanda take magana ba ƙaramin gigita shi ta yi ba, zuro hannunsa waje ya yi daga ta cikin bargon ya kashe wutar ɗakin ta hanyar yin amfani da remote dake saman bedside drawer, sannan ya kunna green light dake manne a sama kusa da farin wutar.

"Yaya Saif in tambayeka?". Shiru ya yi bai amsa mata ba, dan sam baya jin yin magana. "Uhm uhm yaya Saif ka amsa mini mana". Yatsarsa manuniya ya sanya mata a cikin ɗan bakin nata yana wasa da harshenta dan ta dai'na damun shi da surutu, tsotsar yatsan nasa ta fara yi tana ɗan cizawa, kwace kayansa ya yi dan kada ta jefa shi cikin wani hali, kukan shagwaɓa ta saka mishi mara dalili.

Shiru ya ɗan yi na ƴan mintocin da ba su wuce 2 ba, kafin nan ya ɗan juya kaɗan da ita a in da ya sauketa daga saman kirjin nasa ya zamana suna fuskantar juna, matso da face nasa daf da tata ya yi yana yi mata wani irin mayen kallon, da yake darene sai idanun nasa suka kara haske, ga kuma hasken green light na ɗakin. Cikin sauri ta runtse idanunta dan ba zata iya gani shi ba.

Haɗe fuskokinsu ya yi waje guda yana mai lumshe idanunsa shi ma, a hankali ya fitar da harshensa izuwa saman lallausan laɓɓanta na kasa yana ɗan tattaɓa lips ɗin nata, wani irin yanayi ta shiga, buɗe ɗan bakin nata ta yi da nufin ta kama harshen nasa, janyewa baya ya yi yaki bata, idanunta a datse gam ta turo mishi ɗan bakin alamar shagwaɓa, bata ji daɗi ba da yaki bata.

Sake zuro harshen nasa ya yi zuwa saman lips ɗin nata, a hankali yake ɗan wasa da harshen a saman lips ɗin ba tare da ya kai cikin bakinta ba, sake kokarin kama harshen nasa ta yi, ina nan ma janyewa baya ya yi bai bari ta kama ba, kukan shagwaɓa ta saka mishi tana ɗan bubbuga kirjinsa, sam bai kulata ba a karo na uku ma ya sake zuro harshen nasa zuwa saman lips ɗinta, a wannan karon ta ci alwashin sai ta kama harshen, ƙoƙarin kamawa ta yi yana ɗan janyewa kaɗan kaɗan yana janta da wayo har ta matso kusa da shi sosai, a in da ya ɗaga kai daga rankwafowa da ya yi a kanta, ya zamana yana miƙe.

Kuka ta saka mishi tana kokarin barin jikin nasa, rikota ya yi tare da zura harshen nasa cikin ɗan bakin nata yana tsotsar lips nata na kasa, nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke tare da cizan harshen nasa dan ta huce takaicin wasa da hankalin da ya yi mata, bai san time da ya furta wash ba jin yanda ta cije shi, zame harshen nasa ya yi tare da kara mannata sosai da jikinsa yana shafa bayanta, har cikin ransa yake jin irin sokinsa da breast nata suke yi a kirjinsa, a da ya rainasu sosai, yanzu kuwa ga shi suna tsokale mishi zuciya, musamman ma idan ya matseta sosai a jikin nasa, shi kaɗai yasan me yake ji, dama kun sani ita ba saka breziya take yi ba, to yau ko vest ɗin ma bata saka ba dan kayan barci ne a jikinta.

Hannu ya ɗaura a saman mazaunanta da suke matuƙar ɗaukar hankalinsa, kowa ya san matan Turawa basu da mazaunan mai girma sosai, sai dai shape da hips, amma basu da halittar mazaunan, akwai ɗaiɗaiku da suke da shi, amma ba su da yawa, hakan yasa nata suke matuƙar ɗaukar hankalinsa, dan ita fa tana da su sosai, a cike suke ga shape kamar me, musamman idan ta sanya kayan da suka ɗan kamata suka fito da su sosai, suna burg shi over, a duk halittar jikinta sun fi burg shi, shiyasa yake yawan taɓasu, ga soft skin nata da bala'in laushi tamkar fatar jariri, shi kaɗai yasan abin da yake ji a duk lokacin da yake taɓa skin nata, ko da hannunta ne kuwa.

Shafasu ya rinƙa yi a hankali hankali har ya zura hannunsa ciki ta yanda zai sami damar shafasu da kyau, waro idanunta waje ta yi jin ya zura hannunsa ta baya a cikin wandon barcin nata, idanunsa a lumshe yana bata wani irin hot kiss cikin natsuwa mai mantar da masoyi a wani duniya yake ciki, komai nasa cikin natsuwa da kwanciyar hankali yake yi, zame hannun nasa daga mazaunanta ya yi tare da haurowa zuwa saman bayanta har izuwa gashin kanta, suman kwance ta yi mishi ta kasa wani kataɓus, ko ɗan kissing na shi da take yi ma yanzu ta dakata tana bin shi da kallo.

Kamar daga sama taga yasa ɗayar hannunsa ya rufe mata idanu yana zame ɗan bakin nasa daga tata, cool murmushi ta saki, wato dai bai rufe idanunsa sosai ba yana kallon duk irin kallon da take yi mishi, Allah yaya Saif ɗin nan ma sam baka gane mishi, ta faɗa a cikin zuciyarta.

"Meeeesha". Ya ambaci sunanta cikin wata iriyar murya da bai taɓa yin magana da ita ba, bai taɓa sanin ma yana da ita ba, a tsananin sanyaye muryar ta fita, ya kira sunan kuma da salo a cikin voice ɗin nasa, duk da cewa dama kullum a wani irin salo yake kiran sunan, sai ya ja sunan cikin natsuwa da jan hankali yake ambata, amma fa na yau daban ne, ita kanta sai da ta ji tamkar ba shi ba ne ya kirata, yanayin jan sunan da ya yi ma yau har da kara mata wasali, ga kuma zazzakar sexy voice ɗin nasa a tsananin nutse da kwance tamkar mai jan numfashi ne ya amsaci sunan, bugu da kari ga barci da tsananin sha'awa a tattare da muryar tasa, sai hakan ya bada wata kala mai tafiya da imanin masoya.

"Na'am yaya Saif". Ta amsa mishi ita kuma a tsananin shagwaɓe tana shafa lallausan sajensa, wani irin daɗi yake ji na shafa sajen nasa da take yi. "Kwanta ki yi barci dare ya yi". Ya faɗa tare da manna mata haɗaɗɗiyar sumbata a lallausan kumatunta, ita ma sumbatar ta manna mishi a kumatun nasa tana ɗan murmushi.

Shafa bayanta a cigaba da yi har barci ya yi awon gaba da ita, shi kuwa bai yi barci ba har karfe biyu na dare, a hankali ya ɗan yunkuro tare da raba jikinsa da nata, cikin natsuwa ya kwantar da ita a gefe tare da miƙewa zaune ya zuro kyawawan fararen kafafunsa kasan gadon kafin ya miƙe gabaɗaya ya nufi toilet.

Wanka ya yi tare da ɗauro alwala ya fito, Sallah ya fara yi yana karatun Alqur'ani mai girma har aka kira sallar asuba a wayarsa, bayan ya yi sallar rakatainil fajir ne ya yi asuba sannan ya yi askar kafin ya mike ya nufi bed ɗin ya kwanta tare da tashinta a kan ta je ta yi sallah, miƙewa ta yi duk jikinta yana yi mata ciwo, wanka ita ma ta yi tare da ɗauro alwala ta zo ta yi sallah.

Bayan ta idar ta yi askar kafin ta miƙe ta nufi bed ɗin ita ma, already ya yi barci abinsa, dan bai samu dama ya yi na dare ba, kusa da shi ta zo ya kwanta tana ɗan satar kallonsa har barci ya yi awon gaba da ita.

A ɓangaren su Jehan kuwa, ɗaure fuska sosai Areef ya yi cikin nuna isa ya ce "To zo ki wuce ki je ko yi lallen in gani". Jin yanda ya yi magana ne yasa ta ɗago idanu tana kallonsa, babu ko alamar wasa a tattare da shi, nan take ta sha jinin jikinta, shiru ta yi tana tunanin to ko dai ya ji abin da ta ce da hausa ne? Bata san shi ɗin ɗan baiwa ne yana da kwakwalwa sosai ba, yana iya karantar yanayin da mutun ya yi magana a ciki sai ya gane me mutun yake son faɗa ko da baya jin yare, ko da bai gane duka ba yana cankar wasu ɗaiɗai, idan mutun yana cikin ɓacin rai ne ya yi magana, so zai iya cankar a kan me ya yi maganar, kuma bugu da kari zamansa a tare da su yau da gobe tasa yana jin wasu kalmomi masu sauki daga cikin Hausa waƴan da ake yawa ambata irinsu zo, tafi, ba zanzo ba, bana so, ina so, zan ci, ba zan ci ba, da sauran kalmomi da ita Jehan ɗin ita da Rimsha da daddy suke yawan amfani da su, so yasan wannan, ko da ta ce sai ta yi lalle, ya ji me ta ce, ya san ma'anar sai na yi, shiyasa ya ce mata to ta zo ta wuce ta je ta yi lallen ya gani.

"Jehan am i your mate? Da har ni zan ce miki


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login