Showing 132001 words to 135000 words out of 359620 words
sannu, sai kuka take yi, shi ma Areef ya sha yagushi a fuska ba karya, miƙar da ita Aseef ya yi a kan suje ya saka mata magani, ba musu ta bi shi, shi kuma Areef ya ɗauka mata jakar school nata, suka karisa hayewa saman suka bar Brady kwance a kasa yana mayar da numfashi, ya wahala, ba karamin buga shi da bango Aseef ya yi ba, dan ma ya yi sa'a Areef ba shi da lafiya ai da murɗe wuyarsa zai yi ya mutu, dan yanzu tun da ya fara takurawa Rimsha Areef ɗin baya son shi, ita kuma abin da bata gane ba, idan ta gansu kada ta gudu, in ta gudu sai sun bita, amma da ta gansu zata zura a guje dan tsoro.
Sun zo zasu shiga ɗakin Lion ɗin ta tsaya, kallonta suka yi "Lafiya Rimsha?" Areef ya tambaya, cikin muryar kuka ta ce "Yaya Areef ina tsoron shiga ɗakin yaya Saif ni kam, zan zauna a nan palo kawai". Ɗan lumshe idanunsa ya yi tare da sake warosu a kanta, da hannu ya yi mata nuni da ta shiga ba damuwa, bata son yin musu da babban mutun, dan haka sai ta shiga kawai.
A saman bakin bed nasa Aseef ya zaunar da ita tare da ɗauko A box, saman bedside drawer ya ɗaura A box ɗin kafin ya fara buɗe wa yana duba magani, zama gefenta Areef ya yi, Aseef ne ya yi musu dressing na wajen tare da taimakon Areef ɗin, shi ya nuna mishi maganin da zai yi musu amfani da shi da sauransu.
Rimsha ta sha kuka ba karya, dan maganin yana da zafi, sai rarrashinta suke yi, Aseef ya rakata har ɗaki sannan ya dawo, a ɓangaren Lion kuwa, sam bai ji daɗin saka Brady da ya yi da ya yi faɗa da Areef ba, dan kuwa yasan tsab zai yi wa Areef lahani, amma ba yadda ya iya zuciya ce ta ɗebe shi, ya ji babu daɗi yadda Areef ɗin ya fifita Rimsha da ya sani jiya jiya a kan Brady da suka jima.
(kai gaskiya Lion da sauranka, saboda wakalanci dan baka ɗauki ɗan adam da daraja ba shi ne zaka ce kare ya fi ta, a fifita kare sama da mutun kenan? Innalillahi wa inna ilaihir rajiun, wannan rashin sanin darajar mutun har ina? Gaskiya ya kamata ace Lion ko ba yawa ne ka san darajan mutun.)
A ɓangaren Imran kuwa, lokacin da ya fita, pharmacy ya je ya haɗo mata magunguna ya dawo, har lokacin barcin wahala take yi, kiran Akila ya yi a waya ya tambayeta ina dollyn Jellyn, ta gaya mishi tana nan, ta bawa mai gadi ya zai fi kula da ita, dan wata rana idan tana da class ta tafi school babu mai bawa dollyn abinci, okey ya amsa mata da shi tare da ce mata zai zo ya ɗauka da daddare, tom ta amsa mishi da shi, ruwa mai sanyi ya tsaya a palo ya ɗauko mata tare da komawa cikin bedroom ɗin nasu, gefenta ya zauna jikin nata ya tsananta zafi over, har lokacin sai ajiyar zuciya take sauƙewa, wani irin mugun tausayinta da so da kaunarta ne suke kara ratsa shi, a hankali ya fara ƙoƙarin tashinta dan ta sha magani, yana yi kirjinsa na dukan uku uku dan yasan za'ayi dirama ba karya.
Da yake bata da lafiya sosai, sai bata wani bi ta kansa ba, ko da ta tashi, kuka kasa kasa kawai ta sa mishi, rarrashinta ya rinƙa yi tare da bata magani, karɓa ta yi ta watsa a baki, shi kuma ya sanya mata ruwa a baki, bayan ta gama ta koma ta kwanta tana kuka kasa kasa, yau dai bakin tsiwa ya mutu murus, kukan ma baya fita sosai. Kusa da ita ya kwanta, sai rarraahinta yake yi, da haka har wani barcin ya ɗauketa, kun san mai zazzaɓi da yin barci minti minti, shiru ya zuba mata idanu yana kallonta yadda take barci tana ajiyar zuciya, zubawa ɗan bakin tsiwar nan idanu ya yi, a hankali furta "Allah yasa daga haka bakin ya yi sanyi".......... To nima dai da Amin na amsa maka dan gaskiya idan bai yi sanyi ba akwai matsala kana ruwa.
A ɓangaren Rimsha kuwa, uniform nata ta cire tare da wucewa toilet dan ta yi wanka, har lokacin hannun nata yana ɗan yi mata zogi kaɗan kaɗan. Bayan ta gama wanka, ta shirya cikin doguwar riga abaya baka ta haye gado, yunwa take ji amma tana tsoron fitowa waje, a wannan hali Areef ya shigo ya same ta, lallaɓata ya yi ta miƙe su je su ci abinci, bata yi mishi musu ba dan yunwa take ji dama, tsoro ne ya hanata fita.
A palon kasa suka isko Aseef saman table yana jiransu, zama suka yi, kamar dai yadda suka zauna da safe, sun sakata a tsakiya, Mark ne ya zo ya yi serving nasu, bata musa ba, ta ci abincin nasu, yau kam ma kusan irin abincin Nigeria ne, shinkafa ce tasu ta can zara zara, sun dafata koriya shar, ta ji nama ba karya, sai wasu daga cikin kayan lambunsu da suke amfani da shi da sauran ingredient nasu, ta ci sosai dan ba karya ta ji yunwa, bayan sun kammala suka miƙe Areef ya ce ta zo su je garden, ba dan ta so ba ta bisu, yanzu tsoron Lion da Brady take yi sosai ba karya.
Zaune suka isko shi yana waya da daddynsu, daddy ya ce yana son ya zo Nigeria, shi kuma ya ce a'a ba yanzu ba, daddy ba zai iya jure rashinsu a kusa da shi ba, amma hakan ya hakura ba dan ya so ba, Brady na kwance a jikinsa, ya sha wahala ne yasa ya lafe a kirjin Lion ɗin tare da lumshe idanu.
Ita da Areef kujera ɗaya suka zauna, shi kuma Aseef kusa da Lion ya je ya zauna yana wani murmushi, yana son gayawa Lion ya je ya nema mishi auren AKila, amma ya fi son ya sami lokaci na musamman ya gaya mishi.
(Jama'a Lion da zuwa neman aure, Wayyo cikina anya kuwa wannan abin zata yuwu?🤣 Ba gara ma Areef ɗin ba, kuma dai ji yadda Lion yake cewa Imran ya kula da waƴan nan halittu🤣 wayaga Lion a wajen Abba ya je neman aure🤣)
💋GIDAN ABBA💋
❤️❤️TRIPLETS❤️❤️
*Duk wace ta karanta mini littafina ba tare da ta biyani hakkina ba Allah ya isa ban yafe ba, sai Allah ya tsayar da mu ranar da bata da abin da zata biyani face ladarta*
E35-36💋
💋GIDAN ABBA💋
Tun da Ammie ta shaki kamshin perfume ɗin Lion sabuwar rayuwa ya shigeta, duk wasu aljanun dake gidan da wasu dodannin sun gudu, rayuwarta ta bayane ya fara dawo mata, Baiwar Allah ashe duk rayuwar da tayi tsawon shekarun nan bata cikin hayyacinta, bata sani ba, yanzu ne ta dawo normal.
Wani daddaɗar kamshi air freshener ne yake tashi tun daga cikin babban palon kasa har zuwa harabar gidan, ko'ina na palon a tsananin gyare yake tsab, sai tashin kamshi ko'ina yake yi, har wani kyalli kayan cikin palon suke yi saboda tsantsar gyara da suka sha, gidan shiru da alama Akila ta tafi school.
Baki ɗauke da sallama Abba ya shigo cikin palon, ko kaɗan babu alamar mamaki a kan fuskarsa, domin kuwa shi ma yanzu ya dawo cikin hayyacinsa, abin da yasa kuma bai yi mamakin gyara palon da aka yi ba, saboda already yasan Ammie ba kazamiya ba ce, mace ce mai bala'in tsabta na amutu, akwaita da son gyara, ga bala'in son kamshi, shiru shiru bata son hayaniya, sai dai fa idan ka taɓota, zaka gane annabi ya faku, bata da fara'a sosai, amma ba laifi tana ɗan murmushi, yanzu gabaɗayansu ita da Abba sun dawo cikin hayyacinsu sanadiyyar turaren Lion........NASAN KOWA A ƘAGE YAKE DA YA JI TARIHIN AMMIE, TO KU GYARA ZAMA IN SHA ALLAH TARIHINTA NA NAN TAFE NAN BA DA JIMAWA BA, NIMA NA ƘAGU NAJI MENENE MATSALARTA? ME TAYIWA WAƳAN NAN SHAIƊANUN ALJANUN SUKE AZABTAR DA ITA HAR HAKA, GA DUKKAN ALAMU DAI SUN NUNA MUTUNIYAR KIRKI CE A RAYUWARTA TA BAYA, TO MENENE YASA HAKAN YAKE FARUWA DA ITA? KU KASANCE DA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA DAN JIN YADDA KOMAI YA WAKANA.
Sama ya nufa yana mai shaƙan kamshin air freshener mai bala'in daɗi da yake fitowa daga cikin bedrooms nasu, a ƙage yake da ya shiga cikin ɗakin nasu, ɗakin Ammien ya fara nufa, baki ɗauke da sallama ya shiga, tana zaune saman dadduma ta idar da sallar azahar tana addu'a, ko'ina a cikin ɗakin nan a gyare yake tsab, ga azababben daddaɗar kamshi da kuma sanyin Ac mai ratsa zuciya yana tashi.
Sai wani lumshe idanu yake yi ya kariso cikin ɗaki, da sauri ta miƙe tare da nufo shi tana yi mishi sannu da dawowa cikin harshen turanci, da yauwa ya amsa mata tare da rungumota, ta sha kwalliya da wata danƙareriyar doguwar riga mai bala'in kyau da tsada, bata yi wani make up sosai ba, dan ba wani son make up ɗin take yi ba, iya ka powder ta murza da kwalli, ta ɗaura gyalen rigar a kanta kafin ta sanya hijabi, dukkansu bayin Allah sun shiga sabuwar rayuwa, da alama ma sun mance da rayuwar da suka yi a baya, idan kuma basu mance ba, to akwai wani abu a kasa, amma lokaci ne zai nuna mana komai, dan abin da mamaki yadda Abba bai yi mamakin sauyawarta ba, duk da eh yasan haka take a baya, amma basu nuna wata alamu da zata nuna cewa sun san sun yi rayuwa cikin kazanta da wahala ba, ko da yake dama idan dodannin ma suka zo suka zanesu, mantar da su komai suke yi, koma dai me lokaci zai nuna mana menene yake faruwa? Menene gaskiyar lamari?.
Sannu da zuwa ta yi mishi, shi kuma cike da nuna so da kulawa ya tambayeta ina su Imran, AKil, AKila, basu dawo bane?, Da mamaki cikin harshen turanci ta ce "Su Imran ban san in da suke ba, Akila kuma ta tafi school, amma ka kira mini Imran ɗin a waya, ya zo maza, ko ina suka shige Oho". Sai da ta yi maganar ya tuna Akil ya gaya mishi zai koma Madina sati mai zuwa, ya sha'afa da zancen baki ɗaya sai da ta yi maganarsu yanzu.
To ya amsa mata da shi tare da ciro waya ya kira number Imran ɗin, bugu ɗaya ya ɗaga, cikin girmamawa ya gaishe da Abban nasa, da fara'a sosai a kan fuskarsa ya amsa tare da ce mishi "Ina kake ne Imran?" "Abba ina gidan Saif ne lafiya?" Nisawa ya yi kafin ya ce "Tom ka zo Ammie ku na buƙatar ganinka yanzu". Shiru ya ɗan yi kafin ya ce "Abba jelly ce bata da lafiya, babu ta yadda za'ayi na tafi na barta". "Me ya sameta?" Ya faɗa yana ɗan zaro idanu, ita ma Ammien zaro idanu waje ta yi tana kallonsa tana jiran ta ji me ya faru.
Ƴan kame kame ya fara yi musu, daga nan Abban ya fahimci menene matsalar, dan haka sai ya ce zuwa yamma idan ta sami lafiya ya taho da ita, da mamaki ya ce "Abba Ammie ba zai zama matsala da ita ba?" "E babu komai ka taho da ita". Okey ya amsa da shi, katse kiran Abban ya yi tare da juyowa yana kallonta yadda ta tsare shi da ido tana jiran ta ji menene yake faru, Ammie ba karya kyakkyawa ce idan baku manta ba, gata fara tas mai ɗan ƙaramin jiki, idan ka ganta, ba zaka bata bata shekarun nan nata ba, ba zata taɓa cewa ita ta haifi Imran, Akil ba, amma za'a iya cewa ita ta haifi AKila, nan ma ba kowa ne zai yarda ba, dan ba karya ta mori jiki mai kyau.
"Me yake faruwa Abban Imran?". Still dai cikin harshen turanci ta yi maganar, to fa akwai ayar tambaya a nan, kenan bata jin hausa ne ko kuma yaya ne? Ko dai dama ba su yin magana da hausa ne before ta fara ciwo? To Allah masani mu dai je zuwa, koma menene munanan zamu ji komai daga biri har wutsiya.
"Ɗan ki fa ya angwance ne, idan an sami baby sai ki shirya zama kaka". Ya faɗa yana mai sakinta ya nufi toilet, da sauri ta sake shan gabansa tana faɗin "Ban gane ya angwance ba? Yaushe ya yi aure kuma?". Ɗan shafa kan ta ya yi cikin zoyala ya ce "Au a bayanan da na yi miki jiya ban gaya miki sun yi aure ba ko?". Da sauri ta gyaɗa mishi ka alamar e "To da Imran da Akil duk sun yi aure". "Kai, kai, kai a lallai tom waye suka aura ban sani ba?" Kai tsaye ya gaya mata su waye ne matan nasu, fuskarta ɗauke da fara'a ta ce "Tom ka kirasu duk su kawo mini matan nasu nan yau ɗin nan ba sai gobe ba, su kawo mini surukaina mu zauna". Jinjina mata kai ya yi babu ko ɗigon alamar mamaki a face nasa, da alama dai jiya sun yi zama da ita ne, tun da kunji ya ce a bayanan da ya yi mata bai gaya mata su Imran sun yi aure bako? Hakan na nufin jiya ya mata bayanin wasu abubuwa shiyasa baya mamaki.
Toilet ya shiga ita kuma ta wuce ta fitar mishi da kayan sakawa tare da zama saman gefen bed tana jiransa ya fito.
A ɓangaren gidan Lion kuwa.
Da misalin karfe 4 na yamma, suna zaune a garden suna hira, Aseef, Areef, Rimsha, dukkansu fuskokinsu ɗauke da murmushin, da gani kasan suna jin daɗin kasancewa a tare, sun nutsa cikin hiran da suke yi ne Areef ya ce da Rimsha "Our Queen jeki ki ɗauki abincin Lion ki kai mishi ɗakinsa kin ji?". Zaro wannan fararen dara daran sleeping eyes ɗin nata ta yi, ba ita kaɗai ba har da Aseef, shi ma ya sha ruwan mamaki har sai da ya zaro idanu waje.
"Yaya Areef abincin yaya Saif kuma?" Ta yi maganar tamkar zata sa kuka, shafa kan ta ya yi cike da kulawa ya ce "E sister abincin shi, kada ki damu ba zai hanaki zuwa school ba, na rana da dare kawai zaki rinƙa kai mishi, da safe Mark zai kai ki school, yau Aseef yana barci, ni kuma ba zan iya tuki bane yasa Mark ya je ya ɗauko ki, shi kuma Prof matarsa bata da lafiya, shi ne nace ya zauna kusa da ita, to daga yanzu Mark ne zai rinƙa kai ki school, tashi ki je ki kai mishi abincin da wuri, tun ɗazun kinga ya yi mini massage". Tom ta amsa mishi da shi tare da miƙewa jiki ba kwari ta nufi cikin gidan, kamar dai kullum kananan kaya ne a jikinta, wando jeans baki da t-shirt maroon, ta ɗaura wani ɗan ƙaramin gyale baki na doguwar rigarta a kanta.
Bayan tafiyarta Aseef ya dubi Areef ya ce "Areef what is going on ne? Me yasa zata kaiwa Lion abinci?". Wayarsa ya ɗauko ya fara latsawa yana faɗin "Bincike mana, bincike a kan face ɗin nan nata Lion ɗin yake yi, ai dama na gaya maka zai buƙa ce ta a kusa da shi, sai dai ba zai ce mata ga abin da yake yi bane, kuma ka bita yanzu ka gani, ka san me nake tunani?" .
Girgiza kai ya yi alamar a'a "Idan ta je ɗakin, zai rinƙa yawan ganin face nata dan aikinsa, da aikin babanta, ina mishi mummunar addu'a da ya faɗa tarko, wlh duk wadda ya kalli sister sai ya ji yana sonta, shi ma kuma zai sota In Sha Allah, mu zuba ido mu gani, ina tunanin ma ni kam nan ba da jimawa ba hakan zata faru, dan zaka kalla zai ɗan saki jiki da ita, sannan kuma zai so ta rinƙa zama kusa da shi, abin da yasa kuma zai so zamantaa kusa da shi, kasan halinsa, yafi karfin ya nemi alfarma or ya tambayi wani mutun wani abu, to akwai tambayoyin da ya kamata ya yi mata, amma ba zai yi ba saboda idan ya yi hakan kamar ya nemi alfarma a wajenta ne, zai yi amfani ne da zaman da take yi kusa da shi ya binciko amsoshin tambayoyinsa da kansa".
Shiru Aseef dai ya ɗan yi kafin ya ce "Ni ma fa ina son in sami special time, lokacin da yake cikin farinciki na gaya mishi batun aure na, ya je ya nema mini aure heartbeat". A sukawane ya juyo da ash eyes nasa zuwa kan Aseef ɗin, cikin sauri ya ce "Amma Aseef yau ka sha wine (giya) ko?" "Wine kuma?" Ya faɗa yana zaro idanu.
"E mana wine, yo idan ba wadda ya sha wine ba, waye zai ce Lion ya je ya nema mishi aure, hmmm wlh na rantse ba zan yi kaffara ba, idan kayi ganganci yi mishi magana ma ba zai kula kaba, idan kuma ka matsa ya kula ka ya je, to fa ka sani da kai da Heartbeat har abada, dan kuwa izza da isa zai je ya nunawa iyayenta, ko ma ya ce a ɗauko mishi iyayen nata a kawo su har nan, idan hakan ta faru kuma Heartbeat ɗin taka zata dai'na sonka, dan su a nan kasar basu yarda a raina iyayensu, suna bin umarnin iyayensu sosai, ba zata taɓa yarda tana ji tana gani Lion ya sanya a ɗauko iyayenta kamar wasu yaransa a kawo su gidan nan ba, kuma ta yarda ta cigaba da zama da kai ba, na dai gaya maka, gwara ka canza hanya dan Lion kam ba zai je neman alfarman a baka aure ba, yanzu fa na gama gaya maka, wasu tambayoyi yake son yi wa Rimsha, amma saboda yafi karfin neman wani abu wajen wani, shi ne gara ta rinƙa zama kusa da shi tana kai mishi abinci daga motsinta da yanayinta har ya fahinci abubuwan da yake so, na buɗe laptop nasa jiya, na rasa a ina ya samo hotunan kusan gabaɗaya family'n uncle Hossain, har da mahaifin Prof naga hotonsa a can, ina ga fa babban al'amari ne kuma babban case ne ba kaɗan ba, dan