Showing 138001 words to 141000 words out of 359620 words
ta, ba ƙaramin dariya ta bashi ba, sai uban haɗa zuba take yi baiwar Allah, dawo da kallonsa kan su Lion ya yi, aikin gabansu kawai suke yi tamkar basu san da ita a cikin ɗakin ba, karisowa ya yi yazo ya sanya hannu suka fara yi bibbiyu, sai murmushi yake yi mata, duk ta firgice kamar wadda ta wuni tana tikar aikin wahala.
Bayan sun shin faɗa ƙaramin bed sheet ɗin, sai ya ɗauko mata duvet ɗin ya gyara shi da kyau kafin ya shinfiɗa, dan yasan ba zata iya shin fiɗawa ba, ya yi mata girma, ba ƙaramin kyau gadon nan ya yi ba, ba'a taɓa shinfiɗa wa gadon bed sheet milk color ba sai yau, kullum daga fari sai sky blue mai haske, banbancinsa da farin kaɗan ne, ita ta jera mishi kananan pillows dake zuwa da bed sheet ɗin, su kam ta iya jerasu ba kaɗan ba, ta ɗauki wannan mai design of heart ɗin ta sanya a gaba tsakiyar masu four corner, sai ta ɗauko dogon kuma ta sanya a bayan masu four cornern, mai Heart ɗin dai ya zamana shi ne a gaba, shi kuma Areef wucewa ya yi ya cicciɓo wannan uban bargon, a tsakiyar ɗakin ya tsaya ya maɗe bargon gida huɗu, sannan ya ɗaura saman gadon kusa da pillows ɗin daga ɗan gefe, wani uban tudu bargon ya yi naɗe shi da aka yi, shi ma Areef ɗin da kyar ya naɗe saboda ciwonsa, dan ma ɗazun ya sha magani ya kuma shafa magani a wajen, shi ne ya ji wasau ta ɗan sake shi, ba laifi kuma ciwon tana warkewa sosai ba karya.
Bayan sun kammala ya koma kusa da ƴan uwan nasa dake ta faman aikin gabansu ya zauna, Lion yana fama da laptop shi kuma Aseef waya, tamkar babu su a cikin ɗakin, ita kuma kayan shara da mopping ta ɗauko, yadda kasan ta iya aiki sosai, sai wani zagewa take yi, shara ta fara yi, har ta gama bata ga datti ko ɗaya da ta sharo ba, mamaki ma take yi, wai a hakan kuma kullum sai an share ɗakin har sau uku, ko me suke sharewa oho, mutun ne sai shegen bala'in kyamar datti kamar me, sai zancen zuci take yi har ta fara mopping ɗin, shi ma dai ka tulluka, dan babu wani abin da ta goge, ko'ina tsab yake, amma dan bala'i da shegen son tsabta wai sai an share an yi mishi mopping, kai wannan Saif ɗin akwai kusfa da kakale kakale.
Da ta kammala har zata fita waje, sai kuma ta tuna ai bata sanya musu turare air freshener ba, ta san halinsa sarai yanzu duk kamshin dake karaɗe da ko'ina a cikin ɗakin nan, zai iya cewa bai yi mishi ba sai an kara, wannan ba dan ta gan shi da kafufunsa yana taka kasa ba, da sai ta ce baya taka kasa kuma bai taɓa takawa ba, dan abin nasa ne sai shi ɗin, dama mai yin aiki a karkashinsa ai sai ya shirya ba kaɗan ba, sai ya kai zuciya nesa can kololuwa, kayi kuskure kaɗan kasha bakar wahala, dan ma dai yanzu ba aikin take yi a karkashin sa ba, akwai dalilin na zuwanta ɗakin, ya fi karfin ya tambayi Musharraf abu shi ne yake amfani da ita.
Dressing room ɗin nasa ta koma bayan ta mayar da kayan sharar, turarruka kala kala ta samu, wasu ma da alama bai san ya kamshinsu yake ba, ya dai sa an sayo mashi ya zube su a wajen, kuma kullum air freshener ɗaya yake amfani da shi, dan yafi son kamshin sa, bai taɓa gwada sauran ya ji ya suke ba, tun da wancan ta yi mishi ai shikenan kuma.
Dubawa ta fara yi, dan ita bata ma san da wanne yake amfani ba, ɗaya baya ɗaya ta rinƙa ɗauka tana buɗewa ta ji kamshin ya yake, dukkansu suna da bala'in daɗi, har da mai kamshin mangoro a cikinsu, nitsuwa ta yi ta zaɓa mishi dai'dai da ra'ayinta, wadda ya kwanta mata a rai ta kuma ji daɗin kamshinsa ba kaɗan ba, cikin zumuɗi ta ɗauke shi ta fito cikin ɗaki, lungu da saƙo ta fara bi tana fesawa.
Kusan a tare dukkansu TRIPLETS ɗin suka ɗago kansu jin daddaɗar kamshin da ya daki kofofin hancinsu, Aseef, Areef kallonta suke yi, shi kuma Lion kallon air freshener hannunta yake yi, kamshin ya kayatar da su ba kaɗan ba, har wani lumshe idanu Lion ya yi.
Tsab ta gama fesa musu tare da mayarwa, ta fito zata nufi waje, Areef ya kirata a kan tazo ta zauna su yi hira, okey ta amsa mishi da shi tare da dawowa ta zauna kusa da shi, cikin zolaya ya ce "Sister yau kin canzawa ɗakin mu kalar kamshinsa". Zata yi magana Brady ya shigo yana wani haushi, da ga gani wani abin ya je ya aikata, a guje ya nufi jikin Lion, hayewa ya yi tare da sauke bindinsa a saman laptop ɗin da yake aiki, ɗan matsar da laptop ɗin gefe ya yi tare da rungume Brady ɗin da kyau, kasa kasa ya ce mishi ina ya je tun ɗazun, haushi ya yi tamkar mai bada amsar in da ya je ɗin, baki ta saki tana kallon ikon Allah, Lion baya magana amma kuma har da tambayar Brady ina ya je tun ɗazun, ba karamin burgeta kuma suka yi ba, hakan ya tabbatar mata da ba son wasa Lion yake yi wa karen nan nasa ba.
Ƴar kara laptop nasa ta yi alamar shigowar saƙo, a tare gabaɗayansu suka kai kallonsu kan laptop ɗin, a zafafe ta miƙe tsaye tana ambatar sunan mummynta, dan kuwa hoton mummynta ne ya bayyana a kan screen ɗin laptop ɗin, da alama browsing yake yi Brady ya shigo, bata gama buɗuwa ba ya kawar da laptop ɗin ya rungumi Brady ɗin, shi ne yanzu ta buɗe yasa laptop ɗin kara alamar ya gama.
Binta da kallo dukkansu suka yi banda Lion, dan shi tamkar bai san da ita a wajen ba, shi ma Brady har da wani juyowa da sauri yana kallonta dan tsabar gulma, "Is she your mum?". Cewar Areef, gyaɗa mishi kai ta yi alamar e, hannu ya kai ya ɗauko laptop ɗin tare da matso mata da shi gabanta da kyau dan ta gani, tabbas mummynta ne, sanye take da lace milk color, ta sha kyau sosai, tana zaune a cikin palonsu na gidansu dake Abuja, ko a ina ya samo hoton oho mishi, ga shi dai a gidansu na Abuja ne nan, kai Lion kamar wani aljani haka yake.
Miƙa musu hannu Lion ya yi akan su ba shi laptop na shi, ba musu suka miƙa mishi, can kasa kasa ya yi wa Brady magana a kan ya sauƙa mishi a jiki bari ya cigaba da aikin da yake yi, kin sauƙa ya yi tamkar bai ji ba, fita harkarsa ya yi ya cigaba da aikinsa, dan ba shi da lokacin biye mishi, haka suka zauna, ita da Areef suna hira kasa kasa, Lion yana aiki, Aseef yana latsa waya har aka kira sallar mangariba. Kusan a tare su ukun suka miƙe, ita kuma bata tashi ba, tana jiransu su fita tukunnan, dan kada ta yi ta karo da su. Har cikin ransa Lion ya ji daɗin ganin yadda gadonsa ya yi tsantsar kyau da bed sheet milk color, sai dai bai nuna a filli ba, toilet ya wuce ya ɗauro alwala ya fito, tsalle Brady ya fara yi a kan lallai sai ya bishi, bai musa ba ya ɗauke shi, da mamaki su Areef suke kallon shi ta ya za'ayi ya tafi da kare masallaci? Sai dai basu yi mishi magana ba.
Sai da suka fito palon kasa ya ce da Brady ɗin ya zauna yana zuwa, da kyar ya yarda ya zauna, su kuma suka nufi masallaci, suna fita ita ma ta miƙe ta fice zuwa nata ɗakin. A palon sama ta haɗu da Imran, "Yauwa Rimsha wajen ki zan je dama, zan je gida ni da Jelly, da naso mu tafi da ke, amma Areef ya ce a'a, dan haka ki kula da kanki sosai sai mun dawo". Okey ta amsa mishi da shi tare da yi mishi addu'ar Allah ya kaisu lafiya ya kuma dawo da su lafiya, Amin ya amsa da shi, ta wuce bedroom nata shi kuma ya juya ya koma kasa, har lokacin Jelly tana zazzaɓi, idan ta sha magani ya sauƙa, anjima kaɗan kuma ya sake dawowa, amma dole haka zai ɗauketa ba dan ya so ba, sai dan ya je ya amsa kiran iyayensa.
A ɓangaren su Lion kuwa, bayan sun yi sallar mangariba da issha, tsayuwa Lion ya yi a waje ɗan nesa da gidan nasu yana waya da Tga a kan idan ya sami sauƙi ya taho mishi da daddyn Rimsha nan Nigeria, shi kuma Aseef cikin gida ya je ya ɗauko mota ya fita, Areef kuma ya koma cikin gidan dan suje su ci abinci da Rimsha, ya ga kwana biyun nan tana barci da wuri, dan sabida school.
Yana shigowa gida Brady ya fara yi mishi haushin ina Lion, buɗe mishi gate ya yi tare da yi mishi nuni da hanyar in da Lion ɗin yake, da yake ya san su kamshi suke bi, tsab zai iya gano Lion ɗin, sai bai damu ba ya sake shi, da gudu ya fice abinsa, shi kuma Areef ya koma wajen Rimsha.
Yana zuwa ya haye jikin Lion ɗin yana wani kuka kasa kasa, shafa lallausan gashin jikinsa Lion ɗin ya fara yi yana cigaba da wayarsa, fita shi ma yake son ya yi, shiyasa bai koma cikin gidan ba, kuma ba da motar gida yake son fita ba, ya sanya a kawo mishi sabuwar mota, akwai abin da zai je dubawa ne da ya shafi aikinsa, sai dai fa da Rimsha yake son fitar, dan ita ce ta san abin da yake nema ɗin wadda bai bayyana shi ba, ko ina zasu je,? Shi ya barwa kansa sani.
Kamar daga sama ya ji an fisge wayar nasa, gently ya ɗago idanu, tuni ɓarawon ya watsa a guje abinsa, su biyu ne matasa, irin gayun nan ne masu yawo wando kugu a sake, da alama kuma suna ɗan taɓa shaye shaye, wani irin mahaukacin dirowa kasa Brady ya yi yana wani girgiza ya rufa musu baya, shi kam Lion gyara tsayuwarsa ya yi yana mamaki tare da tunanin wannan rayuwa, wai ace matasa yara masu jini a jika ba zasu je su nemi aikin yi ba sai su zauna sata?, Zuciya duk ta mutu, gaskiya wannan abin yana ƙona mishi rai, ya tsani ya ga mai matatciyar zuciya, ya fi son yaga kowa ya zama jarumi, ya tsayawa kansa har ma da wasu.
Brady kuwa haukata su ya yi, ko ban faɗa ba na san kunsan Brady mugu ne mafaɗaci, wannan wandon nasu da suke tafiya ƙugu a sake sai da ya zamo zuwa kafafunsu, dan kuwa duk da sun yasar da wayar Brady ɗin ya ɗauka, yaki barin binsu, sai haukata su yake yi ga wayar Lion ɗin a bakinsa ya riƙe gam, duk ya ruɗa jama'ar da suka biyo hanyar, ga shi bashi da tsoro ko kaɗan, baka isa ka razana shi ya gudu ba, sai dai ya kara haukata kai mai razana shi ɗin........
❤️❤️TRIPLETS❤️❤️
*Duk wace ta karanta mini littafina ba tare da ta biyani hakkina ba Allah ya isa ban yafe ba, sai Allah ya tsayar da mu ranar da bata da abin da zata biyani face ladarta*
Dedicated to A'isha Baita Jiddah💋
E37-38💋
A takaice dai sai dai Brady ya haukatasu, har sai da suka bar layin baki ɗaya, ɗaya daga cikinsu ma har cikin kwata sai da ya faɗa, ga wando na faɗuwa, abin gwanin ban tausayi gwanin ban dariya, basu san cewa Brady ɗin ba zai cijesu ba, saboda akwai waya a bakin nasa, kawai bala'i ne irin nasa yasa ya wahalar da su ya ki kyalesu har sai da ya tabbatar da numfashi ma da kyar suke iya fitar da shi, sannan ya kyalesu ya dawo wajen Lion.
Tsaye ya isko Lion ɗin a wajen bai ko motsa ba, tsalle ya yi ya haye jikinsa tare da miƙo mishi wayar, karɓar wayar ya yi yana yi mishi faɗa akan meyasa ya hau mishi jiki bayan ƙafarsa akwai datti, tsabar iya shege irin na shi sai ya wani riko Lion ɗin a wuya yana wani mimmiƙewa, shafa jikinsa ya fara yi tare da nufar gida, bai yi niyar komawa cikin gida ba, hasalima ɓuyanwa Brady ɗin ya yi dan ya tafi in da yake son zuwa, ya so ne kawai a kawo mishi mota Areef ya haɗo mishi trolleynsa, ya fito mishi da Rimsha su tafi, amma Brady ya ɓata mishi jiki dole ya koma ya sake yin wanka ya kuma yi mishi wayo ya gudu.
Babu kowa a palon kasa da sama, cikin bedroom nasa ya wuce, daddaɗar kamshin air freshener ne ta daki hancinsa, shaƙa ya yi tare da lumshe idanuwansa ya sake buɗewa, abin da ya faru shi ne, bayan ta yi sallar issha ta sake dawowa ta gyara mishi ɗakin tare da kawar mishi da laptop nasa zuwa saman bedside drawer, ta gyare wajen sofar sannan ta kara mishi air freshener mai shegen daɗin kamshi irin na ɗazun, ba ƙaramin daɗi ya ji ba.
Toilet ya wuce da Brady ɗin, wanka ya yi tare da wankewa Bradyn kafa da sauransu, bayan sun fito dressing room nasa ya nufa, shiryawa cikin pajama milk color ya yi, ya ɗaura jacket mai ɗan girma a kai tare da ɗaukar wata ƴar karamar kyakkyawar trolley ya zuba kaya kala shidda a ciki, kala biyu ne cikakkun tsadaddun kaya jeans and T-shirt, kala biyu kuma three quarters ne masu bala'in kyau da tsada da T-shirt nasu, sai pajama guda ɗaya da kuma kayan barci guda uku da ya zuba daga baya, diamond watch nasa na TRIPLETS ya ɗauko tare da perfume nasa guda ɗaya, sai karamar kyakkyawar farar towel, shots and singles, da saukan kayan buƙata nasa, dukka ya shirya cikin trolleyn, bayan ya kammala ya sanya wani haɗaɗɗen cover shoe mai bala'in tsada kalar pajamar jikinsa wato fara, ya yi kyau ba karya, sai tashin fitinannen daddaɗar kamshin perfume nasa yake yi, ya ɗaure kyakkyawar dark black curly hair sa a bayan wuya, ya ɗauki pistol gun, daga karshe ya sanya face mask a face nasa.
Jawo trolley ya yi zuwa cikin ɗakin, lokacin Brady ya fice waje, ba ƙaramin daɗi ya ji ba ganin Brady baya ɗakin, dan ba tafiya da shi zai yi ba, massage ya yi wa Mark a kan ya ɗaure mishi Brady ɗin kada ya ga tafiyarsu, sannan ya yi wa Areef massage a kan ya turo mishi Rimsha ta same shi a waje gate baki ɗaya, ya wuce ya ɗauki laptop nasa ya sanya a cikin trolleyn ta gefe, yana gamawa ya nufi waje abinsa.
Babu kowa a palon sama da kasan baki ɗaya, waje ya nufa kai tsaye, gabaɗaya sojojin dake gidan suka fara sara mishi, har suna rige rigen karɓar trolley dake hannunsa, hannu ya ɗaga musu alamar baya buƙata, buɗe mishi gate gateman ɗin ya yi, cikin taku mai nuna isa da izza ya nufi waje,. Ɗan nesa da gidan ya tsaya yana latsa wayarsa, alamar massage yake rubutawa.
Sanye take da kananan kaya dai kamar kullum, akwaita da son kananan kaya dan su ta taso tana sakawa, lokacin da daddynta, mummynta suke nan, shi ne kayansu ko da yaushe, shiyasa bata iya jurar saka wasu kaya sai su, wandon jeans ne pink color, sai riga fari, wandon akwai kyalli sosai a jikinsa, shi kuma rigar high neck t-shirt ne, ga rigar ya kamata sosai, da yake ita ba saka breziya take yi ba, sai gabaɗaya shatin tula tulan ya bayyana, dan ma ta sanya vest a ciki, bata saka bra sai vest, kanta na ɗaure da pink ɗin ɗankwali, gyalen abayar tane ta ɗaura a kan nata, ta yi kyau sosai, sai zuba kamshi ita ma take yi, a tsorace ta fito wajen, kafin ta fito sai da gateman ya tsayar da ita, a kan ba zata fita ba, sai da ta gaya mishi Lion ne yake kiranta yana waje, sannan ya bata hanya dan yasan yanzu Lion ɗin ya fita.
Ganin shi a ɗan nesa da gidan ga trolley a kusa da shi ba karamin mamaki ya bata ba, ɗan kunna hasken screen ɗin wayarta ta yi dan ta duba time, 8:20 cikin natsuwa ta karisa in da yake tsaye ɗin, cikin girmamawa ta ce mishi "Gani nan yaya Saif". Ko sannu bai ce mata ba, sai latsa waya yake yi, bai kuma kalli in da take ba, shiru ta tsaya a gefensa tana addu'ar Allah yasa lafiya. Tsayuwar minti goma suka yi a wajen sai ga wata danƙareriyar bakar mota kirar jeeb mai bakar glass ta paka a gabansu, sai kyalli motar take yi tamkar yanzu a ka fito da ita daga laidarta.
Wani jibgegen Baturen soja ne ya fito daga cikin motar, gabansa ya kariso cikin girmamawa ya miƙa mishi key ɗin motar yana risinar da kansa kasa, karɓa ya yi tare da ɗaga wa sojan hannu alamar ya je kawai, cikin sauri ya bar wajen ya nufi cikin gida, shi kuma Lion ɗin gidan baya na motar ya buɗe ya sanya trolleynsa kafin ya buɗe mazaunin driver ya shiga, ita dai tana tsaye tana ganin ikon Allah, bayan ya shiga ya kunna motar ne ya danna mata horn alamar ta shigo, da yake ita ma renon ice cream da madara ce ta gane nufinsa, sai ta buɗe gidan baya zata shiga, gently ya ce "Ni driver ki ne?".
Da sauri ta girgiza mishi kai tare da rufe kofar ta dawo gaba ta shiga, tana shiga ya bawa motar wuta suka ɗauki hanyar barin cikin Kaduna, da yake ita bata san ta ina ake shigowa Kadunar or fita ba, sai bata san fita zasu yi ba, ta ɗauka wani waje zasu je a cikin gari kawai su dawo, ga shi shi ya ɗauki trolley da kaya, ita kuma daga ita sai na jikinta da waya a