Showing 357001 words to 359620 words out of 359620 words
daga ruwa? Ko daga jikin bishiya ta fito da zai ce ya aureta ba tare da yardan iyayenta ba? To wlh ba daga jikin bishiya ta fito ba, da iyayenta cike ciff suna raye, ƴar gata ce na wuce misali, dan haka dole ya zo ya nemi izini daga wajen mu, ke Jehan wuce muje ki kaini in da suke, mu zai gwadawa isa, to wlh gidan isa da izza ya zo, ba'a yi wa familyn Dr Salman wannan iskanci a zauna lafiya!!.".
Cikin sanyin murya tare da rarrashi daddyn ya sake cewa "Dan Allah ki tsaya nayi miki bayani dallah dallah yanda zaki fahimta, ba yanda kike tunani ba ne fa, ba haka.....". "Nawazudden wai yaushe muka zama abokan wasa ne da kai?." Shiru ya yi bai sake magana ba, dan yasan halinta sarai da uban iya bala'i, yanzu zasu hau sama jannati su diro, bazata fahimce shi ba, yanda ta fusatannan, dama ita haka take, idan fa ta hau dokin zuciya, to sai dai a daure a bi umarninta kawai.........WANNAN GWAGGON AKWAI RUWAN BALA'I😌
Shi dai Areef bawan Allah da yake baya jin Hausa, sam bai san me ake faɗa ba, bai san cewa zage mishi ɗan uwa suke yi ba, sai binsu da kallo kawai yake yi yana mamakin bala'i masifa irin na ƴan uwan daddyn.
Ita dai Jehan ko a jikinta, sai ma kara shigewa jikin gwaggonta take yi, yo ita ai ko yanzu a je a ɗauko Rimshar, me ya yi mata zafi?......... E kam babu abin da ya yi miki zafi, sai Lion ya zubar miki da hakwara gabaɗaya ne zaki gane ba abin da ya yi miki zafi.
"Jehan ta shi muje gidan". Cewar gwaggon, ta yi maganar tana ƙoƙarin miƙewa. Shi dai Abba da yake yanzu sulhu yake nema da ƴan uwan nasa, sai bai hanata ba, dan yasan ba shiri suke yi da ita ba, zata ma iya gaya mishi magana duk da yake babban yayansu, dan kafin su rabu, ba'ayi rabuwar daɗin rai da ita ba, ya san ya yi musu laifi, kome suka yi mishi suna kan gaskiyarsu, kuma ba zai ga laifinsu ba, dan fa ba'a magana a kan abubuwan da suka wuce, sun yi muni da yawa, musammanma ita gwaggo da take mace, sam bai kamata ya yi mata abin da ya yi mata ba. Allah sarki, shi ma ba laifinsa ba ne......... Nasan kowacecce a cikinku zata so jin wai me ya haɗasu da gwaggo kuma? To kubi komai a sannu, dan idan ba'a sannu kuka bi ba, ba zaku fahimci komai ba, PRINCESS TEEMA zata warware muku komai cikin natsuwa, yanzu dai ku biyoni kawai, dan akwai rina a gaba ba kaɗan kaɗan bama, yanzu komai zai ɗau zafi, saboda yanzu familyn suka haɗu, akwai cakwakiya, yanzu wasan ma ya fara!!.
❤️PRINCESS TEEMA....✍️💋
Daddy yana son ya gaya mata Lion baya nan, amma sam taki sauraronsa, haka ta ce su tashi su kaita gidan, idan ma ba zasu kai ta ba, to su bata key ɗin mota Jehan ta nuna mata hanya ta kai kanta. Cikin mutunci daddy ya ce a'a ba sai ta kai ga haka ba, su je ya kaita.
Mum da Ammie dai faɗar gwaggo ba bakon abu bane a wajensu, ita mum ma ai ta san komai, akwai lokacin da wani malami a makaranta ya zane Jehan dan ta make wata ɗaliba, ai kuwa gwaggo ta figi mota ta je ta sauke mishi ruwan aradu a kai, daga ranar ba malamin da ya sake gigin dukan ƴaƴan Nawazuddeen, idan baku manta ba zamansu a Katsina ma fa anyi irin hakan, Jehan zata ɗauko faɗa, ita kuma ta tare mata, tana da zafin rai ne over.
Haka suka ɗunguma zuwa gidan Lion gabaɗayansu, har da Ammie da bata fita, yau ta bi su, dan bala'in faɗar gwaggo abin kallo ne, kuma dole ne ma su rakata, dan kada ta je ita kaɗai Lion ya kasheta babu mai kwatanta. (Hasbunallahu wani'imal wakil😂 gwaggo duniya mai zaman kanta😂😂)
Suna shiga palon sama a gidan Lion ɗin suka isko bala'in da ya wuce karfin tunaninsu.
Gabaɗaya waƴan da suke gidan suna palon saman. Daddysu Lion, Uncle Herry, Jay, da kuma John, sune a palon. Ga Lion da ya diro yanzu ya shake TGA kamar zai kashe shi, babu Rimsha a wajen, tana bedroom ɗin Lion ɗin, dan ba zata iya ganin wannan bala'in ba, shi ne ta gudu abinta.
Nasan zaku so jin me ya haɗa Lion da TGA faɗa, to ku saurara. Idan baku manta ba kwana biyu da suka wuce, Lion yana yawan bincike a laptop nasa, to ba komai yake bincika ba fa ce case ɗin mum da daddynsu, abin da ya haɗasu faɗa. Abin da yasa yake binciken dan yaga sun kusa isa Nigeria ne, shi ne yasa ya fara. To da ɓangaren mum ɗin nasu ya fara bincikawa, a nan ne ya cikaro da kullum weekend sai TGA ya je wajenta, abin ya yi mugun ɗaure mishi kai, shi dai ya san a baya ko mai kama da ita TGA baya son gani, shi ne ma yake cewa a kasheta idan ta zo gidan, to kenan me yake yawan zuwa yi a wajenta? Me yake kai shi?. Ga shi kuma babu camera a cikin gidan nata, a iya bakin gate kawai Lion ɗin ya sanya camerar, to bai san me suka yi a cikin gidan ba idan TGA ɗin ya je. Shi ne yasa tun kafin ya iso Nigeria ya kira TGA ɗin a waya a kan duk in da yake ya tabbatar kafin ya shigo yana gida, dan yana son ganin shi cikin gaggawa.
So a takaice dai suna shigowa a palon sama ya isko TGA ɗin, shi ne ya tsaya ya tambaye shi me yake zuwa yi wajen Josephine? Wajen matar da ya fi tsana a duniya sama da kowa!. Kin faɗa mishi TGA ɗin ya yi, a in da ya fara yi mishi kame kame, to shi ne ya shake shi, ko ya gaya mishi gaskiya ko kuma ya kashe shi, faɗar da suke yi kenan.
Su daddyn Rimsha suna shigowa Imran da Aseef suka biyo bayansu, kusan a tare suka shigo gidan. Ita kuma Naurat tana zaune a saman sofa gefe guda tana kallonsu, ta kasa magana. Alex da Mark suna waje filin sauran sojojinsa.
Ita kuwa gwaggo ko a jikinta, tamkar bata san ana faɗa a palon ba, ba abin da ya dameta da su, ita dai abin da ta zo yi kawai zata yi. Cikin fushi ta ce "Ku nuna mini wani isasshe ne mijin Rimshar?". Nan take kallo ya koma kanta. Sam ba wanda ya lura da Naurat dake wajen, gida ya kacame da hayaniya.
A wani irin mahaukacin tsananin razane gwaggo ta furta "Dr William!!". A yanayin yanda ta kira sunansa da karfi harta Lion ɗin sai da ya juyo da kallonsa kanta.
Ɗan zaro idanu daddynsu Lion ɗin ya yi yana kallonta, zuba musu idanu kowa na palon ya yi yana kallonsu. "Wace ce ke?". Shi tambayar da daddyn Lion ɗin ya yi mata.
Wani irin shewa da dariyar takaice ta yi kafin ta ce "Dr William ni kake cewa waye ni ko? Ko da yake hakan ba baƙon abu bane a wajen ka, kuma dama ai bani da wata alaƙa da kai a yanzu, dan haka yanzu bama wannan ba, ina ƴaƴana suke bakin azzalumi? Ko suma baka sansu ba?". Zaro idanu ya yi sosai yana kallonta kafin ya sake cewa. Wai wacece ita? Kuma wani ƴaƴa take magana a kansu?.
Wani irin kallon banza ta watsa mishi tana faɗin "Nan kasarmu ka zo! Ko da yake baka san cewa ni ƴar Nigeria ba ce ko? To yau ka sani, nan a kasarmu kake! Dan haka ka shiga hankalinka da kyau! Ka gaya mini ina *TRIPLETS* na? Ko ka gaya mini in da suke, ko kuma kayi danasanin sanina a rayuwarka! Wlh wannan karon sai ka bani ƴaƴana, azzalumi, jinin shaiɗan kawai! Can kasarku ce, shi ne yasa na barka, amma nan kasar mu ce, zaka ga yanda ake tijara sanka sanka!! Zaka san da ƴar Nigeria kake yi!!". Tashin hankali!!.
Duk waƴannan maganganun da ta yi, ta yi shi ne cikin harshen turanci, dan tasan William dai baya jin Hausa.
Jin wannan bala'in da ƙwaƙwalwa take ƙoƙarin kasa ɗauka ne yasa Lion ya saki TGA tare da juyowa da kyau yana kallon daddyn nasa da gwaggo. Aseef kuwa tambayar kansa yake yi to wasu TRIPLETS ake magana a kansu kenan?. (Ni ko na ce ku mana🤣 akwai wasu TRIPLETS bayan ku ne?😌😒)
A fusace Areef ya dakawa gwaggon tsawa yana mai gaya mata ta shiga hankalinta, ya isheta zagin daddynsu da take yi. Sai a lokacin ta ɗago kai tana kalli Areef ɗin, wani irin bugu kirjinta ya yi, shi kansa Areef ɗin sai da ya ji matuƙar bugu a kirjinsa na haɗa idanu da ita da ya yi.
"Daddynku? Hmmm daddynku ko kuma bakin shaiɗan mai wutsiya? Dr William ai ba mutun bane, shaiɗan ne a suffar mutun, ni ƴaƴana kawai zai bani yau, bani da wata alaƙa da shi kuma!!".
Aseef ne ya katseta da cewa "Wasu ƴaƴa naki kuma? Mu daddynmu bayan mu bashi da wasu ƴaƴan, iya mu TRIPLETS ne kawai ƴaƴansa". Zaro idanu ta yi tana faɗin "Au cemin zaka yi kune ƴaƴan nawa, ba shakka ga shi kuwa ka yi kama da Abban Imran, hasken kawai zaka gwada mishi".
Areef duk da zuciyarsa na dukan uku uku a kanta, bai hana shi tinkararta dan ya sharara mata mari ko da guda ɗaya bane, wai ko zata dawo cikin hayyacinta. Dan su a mahaukaciya suka ɗauketa. Yau dai family sun ga bala'in da ya sha gaban tunaninsu. Ita dai Naurat tana zaune tana binsu da kallo, a matsayinta na Brr tana karantar kowa dake wajen, tana son gane mai gaskiya, kuma Allah da ikonsa, da yake hayaniya ya yi yawa, ba su lura da Naurat ɗin a wajen ba.
Da gaske gaske Areef ya nufota tare da ɗaga hannu zai mareta. Tsawa Lion ya daka mishi a kan kada ya kuskura. Cak ya tsaya yana kallon Lion ɗin. Gabaɗaya palon kallo ya koma kan Lion ɗin, da gudu ita ma Rimsha ta fito daga bedroom ɗin nasu ta zo ta tsaya a bakin kofa tana kallon wannan bala'in da ya sha gaban tunaninta.
Zazzaƙar sexy voice na Lion ɗin ne ya daki dodan kunne kowa da yake cikin palon, cikin sanyin murya ya ce "Wannan mata tana da gaskiya, dole tasan daddy, idan bata san shi ba ya akayi ta kira sunansa kai tsaye? Ya akayi ta san yana da TRIPLETS har take ikirarin ƴaƴanta ne?". Cikin sauri Areef ya ce "Lion ka san me kake faɗa kuwa? Kenan kana nufin wannan mata tana da gaskiya ita ce ta haifemu? To idan haka kake tunani what about Josephine? Ya za'ayi ace ba Josephine ba ce mum ɗin mu? Kada ka manta da ita Aseef ya yi kama sosai, tana kama da mu, shi ma kamar karya ce?". TASHIN SENSE, WANNAN SHI NE TASHIN HANKALI MADARARTA
Shiru Lion ɗin ya ɗan yi na ƴan mintuna kafin ya ce "Ban yarda ita ta haife mu ba, amma dole ta san daddy, kuma dole suna da alaƙa, dan haka daddyn ne zai gaya mana gaskiya!!". Nan take kallo ya koma kan daddyn suna jiran amsa. A nutse ya ce musu "Ni ban san wannan matar ba, bayan Josephine ni bani da wata mata". Tashin hankali!!.
Dawo da kallon shi kan gwaggo Lion ɗin ya yi yana ƙoƙarin sake yin magana ta riga shi da cewa "Wa ce Josephine ɗin? Ba dai Josephine da na sani ba?". A takaice daddyn ya ce mata ai Josephine dai guda ɗaya ne shi ma ya sani a rayuwarsa.
Dariyar takaici wanda aka ce yafi kuka ciwo gwaggon ta yi mai isar ta kafin ta ce "Dr William baka tsoron Allah sam sam a rayuwarka, zafa ka mutu watarana, to bari ku ji, da Josephine Jacob Roshan da William Jacob Roshan, da Herry Jacob Roshan, sai Tyson Jacob Roshan, bari ku ji uwarsu ɗaya ubansu ɗaya, dama ai dole ku yi kama da Josephine, dan kanwar uban ku ce!! Bakin mugu azzalumi kawai"........ TO FA JOSEPHINE DA WILLIAM UWARSU ƊAYA UBANSU ƊAYA KUMA? TA YAYA HAKAN ZAI KASANCE? WANNAN WANI IRIN CAKWAKIYA CE? SHIN A INA MA GWAGGO TA SAN DR WILLIAM? YA AKAYI JOSEPHINE TA ZAMA UWAR TRIPLETS? MEYASA DR WILLIAM ƊIN YA TSANE JOSEPHINE ƊIN? TO YA AKAYI TGA YAKE ZUWA WAJEN JOSEPHINE BAYA KUMA YA TSANETA? YA AKAYI JOSEPHINE DA DR WILLIAM SUKA YI ZAMAN AURE TARE DA SOYAYYA IDAN AN CE UWARSU ƊAYA UBANSU ƊAYA? AI BABU AURE A TSAKANIN WAƳAN DA SUKA FITO CIKI ƊAYA, DUK DA WASU TURAWAN RAYUWARSU KAMAR TA DABBOBI SUKE YI, AMMA AI SU MASU ILIMI NE SOSAI, KUMA YANZU AI AN WAYE OVER, TO IDAN MA HAKA NE SU UNCLE HERRY BASU SANI BENE DA SUKA BAR JOSEPHINE ƊIN TA YI ZAMAN AURE DA DR WILLIAM? IDAN HAR DA GASKE GWAGGO CE UWAR TRIPLETS TO MEYASA TA RABU DA SU? A INA KUMA TA RABU DA SU? ME YA KAITA KASARSU? KO DAI ZUWA NIGERIA DR WILLIAM ƊIN YA YI?. TANA TA IKIRARIN CEWA WILLIAM JACOB BAKIN AZZALUMI NE, A INA TA SAN SHI DA HAR TA SAN SHI AZZALUMI NE? GWAGGO TA TAƁA AURE NE KO DAI TRIPLETS ƊIN SHEGU NE? DAN DAI KUN SAN BABU AURE A TSAKANIN KARUFI NAMIJI DA MUSULMA MACE!! WAYE NE MA YA ƊAURA MUSU AUREN DA HAR SU ABBA BASU SANI BA? TO TA YA AKAYI SUKA SAMI TRIPLETS? GA SHI DAI TA CE DR WILLIAM ƊIN NE UBANSU, DA BAKINTA TA FAƊI HAKAN, TO A YAUSHE TA HAIFI ƳAƳA HAR UKU SU DADDYN RIMSHA BASU SANI BA? BA ZAI YI WU ACE DADDYN RIMSHA BAI SAN TANA DA ƳAƳA BA, YA AKAYI SU LION ƊIN BASU SAN CEWA JOSEPHINE KANWAR UBANSU BANE?. WILLIAM JACOB KRISTA, AISHA DR SALMAN SULTAN WATO GWAGGO MUSULMA, KUMA ACE SUNE IYAYEN TRIPLETS? ANYA KUWA HAKAN ZAI YI WU? KAI ƘWAƘWALWA MA FA BA ZATA ƊAUKI WANNAN CAKWAKIYA BA. GASKIYA AKWAI RINA A KABA BA KAƊAN BA, KAI AI BA MA IYA RINA BA, AKWAI RINONI A KABOBI MARASA ADADI!!!.
*❤️PRINCESS TEEMA......✍️💋 A KODA YAUSHE NI ƊIN TA DABAN CE, SHIYASA KOMAI NAWA YAKE NA DABAN NE😍😌😂 TRIPLETS GIDAN SURPRISE DA CAZA ƘWAƘWALWA TARE DA ABIN MAMAKI, NA YAU KUMA KUN JI TA YANDA YA ZO🤔🧐😌 TO KU GYARA ZAMA SOSAI DAN MU JI KOMAI A TARE*
*DOMIN SAMUN DAMAR KARANTA WANNAN KAYATATCEN KUMA SHAHRARREN LITTAFIN NAWA MAI SUNA TRIPLETS, HANZARTA KI YI MINI MAGANA TA WANNAN NUMBER 0816 139 0581, DAN KADA AYI TAFIYAR PRINCESS TEEMA BABU KE, AKWAI LABARAI MASU TASHIN ƘWAƘWALWA DA SUKA SHA GABAN TUNANINKI, NISHAƊANTARWA, ILMANTAR, FAƊAKARWA TARE DA WA'AZANTARWA, DUK SAI PRINCESS TEEMA.💋 KADA KI YARDA ACE KINA KARATUN LITTATTAFAN HAUSA KUMA BAKI TARE DA PRINCESS TEEMA💋 LABARAINA SUN SHA BANBAN DA SALON LABARAN DA KUKA SANI, KUMA SHAIDA NE KO MY READERS?❤️🧐 TO MU JE ZUWA, BAYAN TRIPLETS AKWAI MAI ZAFI GASKE, MAI TAFASA DA ZAI SHA GABAN TUNANINKU, ZAI TAFI DA ZUCIYOYINKU BA NA WASA BA.❤️ TRUST ME MY PEOPLE'S, TAFIYATA BA ZAKI JI KUNYA BA, BA ZAKI TAƁA DANASANI BA, BANA BAWA READERS KUNYA, GA DAƊIN LABARI HAR BAYAN KUNNE😍😂 IDAN KINA KARATUN LITTAFINA HAR WANI BARCI BARCI ZAKI JI SABODA DAƊI😂🧐 GA UPDATE A KAN LOKACIN⏲️😍🧐 GA UBAN YAWAN READ MORE❤️💋 KO WANI PAGE KUMA SAI KIN KARU DA ABUBUWA DA DAMA MASU AMFANI KUMA KI NISHAƊANTU,❤️💋 KO YA KUKA CE READERS?.*
*TAMMAT BI HAMDILLAH, NAN NA KAWO KARSHEN BOOK 3, SAI MUN HAƊU A BOOK 4. NA SO LITTAFIN YA TSAYA MINI A BOOK 3, AMMA KASAN CEWAR DOGON LABARI NE YASA HAR MUKA TAFI BOOK 4, IN SHA ALLAH SHI NE NA KARSHE.*
SIGN BY PRINCESS TEEMA....✍️💋❤️❤️
SSG Palace Gujungu