Showing 288001 words to 291000 words out of 359620 words
wai sai ta sauko ma'ana sai sun dawo cikin hayyacinsu sai ta neme shi, kai Areef ba dai iya magana da sa ido ba.
"Kai yaya Areef ɗazun fa na yi maka magana". Miƙa mata wayar Lion ya yi tare da sauketa daga jikinsa ya miƙe ya nufi waje, dan hiran Areef da Rimsha sai su, so yana son ya yi magana da sojojinsa. Shigewa cikin bargo ta yi suka fara zuba hira da Areef ɗin, yana magana yana nufar bedroom nasu dan ya je ya kwaso chains ɗin.
Yana shiga ita kuma Jehan tana fitowa, ta sha wanka fes tamkar ba ita ce ya gama ruwan hawaye ɗazun a ɗakin Aseef wajen Akila ba, ta shirya cikin wani shegen dogon riga mai bala'in kyau launin pink color, ta yafo mayafinsa a kanta, kyau iya kyau ta yi, bata yin make up, saboda su natural beauty ke garesu ita da Rimsha, halittar idanunsu ma tamkar waƴan da suka sa kwalli, lips nasu pink color ne sosai irin na Naurat, gashin gerarsu tamkar an zana, ga dogon hanci har baka, kyakyawan kuma bakin saje kwance musu a gefe da gefen fuskarsu, to me zasu kara a face ɗin nasu? Ai babu, komai normal ne.
Tare mata hanya ya yi yana tambayarta da ta yi wannan uban kyau haka ina zata je, ko sannu bata ce mishi ba, ɗaure fuska sosai ya yi dan kishinsa ta motsa shi ma, ta zauna ya yi irin wannan haɗuwa haka kuma ta ce zata fita yana tambayarta ba zata ba shi amsa ba, to wlh bata isa ba, cikin nuna isa ya ce ina zata je?!.
Jin yanda ya yi maganar babu wasa a lamuransa ne yasa ta ɗago ta kalle shi, wani irin dukan uku uku kirjinta ya yi ganin ya ɗaure fuska sosai, cikin sanyin murya ta ce "Zan je ne daddy ya kaini wajen yin lalle da gyaran jiki". Tana magana tana turo ɗan bakin kamar wanda aka sanya magana dole.
Katse wayar da suke yi da Rimsha ya yi tare da gyara tsayuwarsa a bakin kofar yana kare mata kallo. "Malam ka bani hanya na wuce". Duk in zata yi magana da shi bata taɓa kallon cikin idanunsa ta gaya mishi magana, a'a tana kallon kasa take duk wannan rashin kunya da take yi mishi, bata da kwarin gwiwar iya kallon cikin idanunsa.
"Please kada ki yi lallen kin ji ko? Wlh dukkanmu TRIPLETS ba mu kaunar wannan abin ko kaɗan, idan kika yi zan yi amai sosai, akan hakan kuma ranar Saif ya yi wa sisterta mummunar hukunci, dan ta yi lalle, haka Allah ya yi mu, kyama yake bamu sosai da sosai".
Kallon sama da kasa ta yi mashi kafin ta ce "To ni dama ina ruwana da ku? Ko dai ina da wani relationship da kai ne? Ni dan Allah bani hanya na wuce hai, kada ku so lalle dan Allah" A karshen maganar tata sai ta yi da Hausa yanda ba zai ji ba, ta ce "Ai ko dan na ganka cikin bakin ciki, wlh dole sai na yi lalle, ba dai yau na ji abin da baka so ba? To kana tsaka mai wuya, lalle kullum ba fashi, iskancin banza dana wufi, ba Saif ba zan ga uban da ya isa ya hukuntani a gidan nan dan na yi lalle". Ta kai karshen maganar tana jan tsaki tare da raɓawa gefensa ta nufi hanyar fita daga ɗakin.
Cikin sauri ya sha gabanta yana faɗin "Seriously i can't believe it gaskiya, ki ajiye zancen lallen nan dan ba zan yarda ba, in fact baza ma ki fita ba".
"Wai kai uban me muka haɗa da kai ne da kake addabawa rayuwata? Me na tare maka? Meyasa sai ni kaɗai ka takurawa a duk waƴan da suke cikin gidan nan?".
"Because I love you mana, shiyasa nake takura miki, kuma ba zan daina ba har sai ranar da kema kika furta mini kalmar you love me, idan kuma kika ki, to for sure za'a ɗaura auren mu this week, ni wlh na fi karfin ma naje neman aure, sai dai nasa a ɗauko mini yarinya a kawo mini ita, ni kuma na turawa babanta sadaki tare da bawa Sultan umarni akan ya ɗaura auren kawai, amma ke abin da yasa nake binki a hankali, saboda kaunarki nake yi ba so ba, kuma saboda ke ƴar uncle ce, dole nayi abin da zai sanya uncle na farinciki, amma ban da haka wlh nafi karfin neman soyayyar mace!".
"To dama waye ya kiraka a nan? Ba sai ka kara gaba ka nemi wata matar ba, ni dai ma ce bana.....". Ta kasa karisa maganar saboda nauyi da kalmar ta yi mata, a kullum mummynsu tana ja musu kunne a kan su tinkari mutun baki da baki su ce basu son shi, saboda ɗan adam ba abin yarda bane, zuciya bata da kashi, karya ne a duniya ka ce kasan mutum 100, hakan ba zai yiwu ba, ka dai san abin da ya yi niya ka sani dangane da shi, amma mutum shi kaɗai yasan zuciyarsa ya san wanene shi, so kuskure ne babba ka ce da mutum baka son shi a gaban idanunsa, baka san me zai iya aikata maka ba, ko a bayan idanunsa ma bai kamata ka faɗa ba, dan maganar tana iya koma mishi, idan baka son shi sai ka bar abin a ranka kai kaɗai kada ka kuskura ka gayawa wata or wani, Allah kasa mu dace.
"Meyasa baki karisa maganar ba?". Ya tambaya yana matsowa kusa da ita, shiru ta yi bata ba shi amsa ba. "Jehan ni fa wannan faɗar ta ki ma kara saka mini kaunarki yake yi a cikin zuciyata". A duk lokacin da furta kalmar sunan Jehan, har cikin ranta take jin sunan, ya iya kira tamkar a bakinsa aka halicci sunan, idan ya kira har wani sanyi take ji a zuciyarta, sai dai kuma bai cika kiran sunan ba, sai idan zai yi mata magana serious ba wasa ba, shi ne zai ambaci sunan dan ya san idan ya ambata, zata natsu ta bashi hankalinta.
(Bari mu bar waƴan nan ƴan diramar mu je mu leƙa su Meesha mu dawo, kafin nan kila Jehan ta tafi wajen lalle, dan fa ta ce sai ta yi🤣 ana life a TRIPLETS wlh, yau abin nema ya samu, Jehan ta gano abin da Areef baya so, Malam Areef ka shiga uku👊🤣🤣 zamu dawo nan da ƴan mintoci, dalili tasa dole mu bar wajen nasu yanzu.)
Lion yana fita daga cikin bedroom ɗin nasu ya ci karo da Mark dake zaune saman chair dake kusa da bedroom ɗin nasu ya yi shiru, bawan Allah Brady ya kwace mishi waya ya kai wa Rimsha. Ko kallon in da yake Lion ɗin bai yi ba ya wuce wajen sauran sojojin dan ya yi magana da su, ita kuma Rimsha ta kwanta tana ta yi mishi taɓe taɓe a wayar tasa, Brady ya koma saman table yana cinye abincin da ta gudu ta bari, ga wayar Mark a saman table ɗin, ɗan kaniyar kare bai mayar mishi ba, yabar Mark ɗin a cikin tunani.
A haka Lion ya shigo ya samesu, sam bata san da Bradyn a cikin ɗakin ba, a tunaninta ya bi Lion, cikin harshen Spanish ya ce da Bradyn ya ɗauki wayar Mark ya mayar mishi da kayansa, haushi ya ɗan yi alamar amsawa kenan kafin ya ɗauki wayar da sauri ya nufi waje.
Shi kuma Lion saman bed ɗin ya hau tare da sanya hannu ya karɓi wayarsa, hotonsa take ta faman kallo abinta, hannu tasa ta rufe idanunta tana murmushi, ta ji kunya ya kamata tana kallon hotonsa a karo na biyu kenan yau kawai. Yatsa ɗaya ya sanya mata a ciki dimple nata da suka lotsa yana kallon ɗan bakinta da take zuba murmushi, ga fararen hakwaranta da suke tas tamkar audiga, kamar bata taɓa cin wani abin ba saboda haskensu.
Shiru suka yi almost 5 mins a haka kafin ta ɗan zame hannun nata a hankali ta buɗe idanunta ta saci kallon shi, karaf suka haɗa idanu, da sauri ta mayar da hannayenta dukka biyu a saman face ɗin nata tana cigaba da murmushi, hannu ɗaya ya kai ya zame hannun nata yana faɗin ta buɗe idanu.
Turo baki ta yi tana faɗin "Yaya Saif Allah kunyarka nake ji, ni ba zan iya buɗe idanuna na kalli cikin naka ba". Sunan kunyar ma yau ya fara jinta, dan haka sai ya ɗaura hannunsa a saman lallausan kumatunta tare da rankwafowa kanta yana faɗin "Open your eyes i said". Tamkar zata yi kuka ta waro idanun nata waje tana turo baki kamar biro, yaya Saif ɗin nan nata ya cika takurawa mutun, a cewarta.
Zubawa laɓɓansa idanu ta yi tana kallon yanda suka yi ja sosai, shi kuma ya zuba nata idanu ido yana kallon kwayar idanunta, kiran sallar da wayarsa ta fara yi ne yasa ya ɗan kawar da kallonsa izuwa kan wayar tasa, lokacin sallah ya yi, mikewa ya yi dan baya wasa da lokacin sallah sam, kome yake yi da lokaci ya yi zai ajiye dan gabatar da sallah, shi yasa akoda yaushe yake yin nasara a kan makiyansa, saboda baya jinkiri wajen gaishe da ubangijinsa, shiyasa ubangiji ma baya jinkiri wajen biya mishi bukatunsa, wannan faɗi ne na Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama, matukar zaka yi aikin Alkhari da bautar Allah a kan lokaci, to shi ma ubangiji zai zama mai amsa maka buƙatunka a kan lokaci, sallah ba abin wasa bane ƴan uwa, shi ne aiki na farko da ake fara bincika a ranar tashin kiyama, idan ta yi kyau, to fa ana sa ran ka tsira, idan bata yi kyau ba, kofar azabarka ce ta buɗe, Allah ka bamu ikon yin sallah a kan lokaci.
After some hours, bayan sun yi sallar isha, Mark ya kawo musu abinci, kin ci ta yi, shi kuma ya ci ya ƙoshi dan bai san cewa fushi take yi ba, da ya ce ta zo taci abincin, sai ta ce mishi ta ƙoshi, dan haka sai ya ci kayansa kuma ita ta yi serving ɗin shi.
Bayan ya kammala ta haɗa kayan abincin zata fitar da su ya ce ta barsu a wajen Mark ya zo ya ɗauka, kuka ta saka mishi tana turo baki, idanu ya zuba mata yana kallon ikon god, sai da ya ga da gaske take kukan nata ga hawaye wani na bin wani ne yasa ya ce "Lafiya dai ko?". Kara sautin kukan nata ta yi tana cigaba da turo baki.
Ɗan dafe kansa ya yi, shi dai bai san yaushe Rimsha ta dawo irin Aseef ba, yarinya sai shagwaɓa kamar ba gobe, amma dai tana burge shi over idan tana yi, har wani sanyi yake ji a cikin zuciyarsa.
Ɗaukarta ya yi cancak suka nufi saman bed yana tambayarta menene ya sameta. "Yaya Saif to ba kai ne ba?". Tsareta ya yi da idanu ba tare da ya sake yin magana ba. "Na ce maka ni bana son Mark ya rinƙa kawo mana abinci, zan je in rinƙa ɗaukowa, amma shi ne ka bari yanzu ma ya shigo mana da abincin, kuma ka ce ya zo ya kwashe kayan abinci, shiyasa na yi fushi kuma ba zan ci abincin ba". A tsananin shagwaɓe ta yi maganar, yanda ta yi maganar kuma dole shi ne ya amsa mata da okey ba dan ya so ba, saboda ta saukar mishi da kasala, ta sanya shi shiga cikin yanayi, ta rikita mishi kwakwalwa da shagwaɓar tata, uwa uba da ta kai karshen maganar sai da ta sanya ɗan bakinta a saman kumatunsa ta ɗan ciza dan ta huce haushi, hakan da ta yi ba ƙaramin kara birkita mishi lissafin ƙwaƙwalwa ta yi ba.
Saman bed ɗin ya sauketa tare da nufar toilet yana faɗin, to ta je ta ci abinci, Mark ba zai sake shigowa ba, shi zai ɗauko abincin da kansa tun da haka take so. Sosai ta ji daɗi, shi dai Lion akwai tsananin kishi, ba zai iya barinta ta fita ta keta cikin sojojin nan ta shiga kitchen wajen Mark ta ɗauki abinci ba, gara mishi Mark ɗin ya kawo mishi abincin kofar bedroom nasu shi ya fita ya karɓar, e lallai Rimsha ta ciri tuta ko a iya haka, dalilinta ne yau zai rinƙa karɓo musu abinci da kansa?!! Abin da mamaki, kishi dai yau ta yi amfani.
Wanka ya yi ya shirya cikin kayan barci ya zo ya kwanta tare da jawo wayarsa yana tunanin me zai hana ya fara bincike a kan Josephine yanzu tun da baya aikin komai?. Ita kuma abincin ta ci ta gama, sannan ta wuce toilet ta yi wanka tare da yin shirin barci sannan ta hau saman sofa ta kwanta sai zuba kamshi take yi, ga kayan barcin nata ma wasu irin kaya ne wanda suke ƴan sharara sharara marasa nauyi, riga ce mai ƙaramar hannu kamar na vest, sai dogon wando har kasa.
Har ta kwnata ta sake miƙewa ta feshe musu cikin bedroom ɗin nasu da air freshener mai bala'in daɗin kamshi wanda Lion ya ɗauko musu, bayan ta kammala ta zo ta kwanta a saman sofa, shi kuma Brady yana wajen Mark, dama shi yawonsa yake tafiya sai lokacin da ya ga dama yake shigowa, yau kam ma da gangan Mark ɗin ya rike shi su yi hira tare, dan yau ba'a gida suke ba, babu su Tyrone, ba abokan hira, shi ne ya rike Bradyn dan ya rage mishi kewa.
Yana ƙoƙarin miƙewa ya ɗauko laptop nasa dan ya fara bincikar tsakanin daddynsa da Josephine wai waye ne mai gaskiya a cikinsu? Wannan abin ya fara damun shi sosai gaskiya, yana da bukatar sanin gaskiya a yanzu kam. Bai kai ga miƙewa ba Malika ta fito a siffar dodo ta tsorata Rimshar, tana tsaka da tunanin Lion ɗinta kawai taga abu ya fito kamar wani shaiɗani ga kawo ɗaya a tsakiyar kai, idanu kamar zasu zazzago waje, wani mahaukacin ihu ta kurma tare da mikewa a guje ta nufi saman gadon, ta san dai duk wani bala'in da ya ta so Lion ɗinta ne kawai zai iya tare mata, shiyasa shi kaɗai take nufa idan wani abin ya taso.
Yana ƙoƙarin miƙewa ta haye jikinsa tana ihu, shi kuma bawan Allah bai ga komai ba, dan Malika wa iya Rimshar kawai ya fitowa, da yake tasan ba zasu ji ta ba, sai ta yi dariya tana faɗin "Ƴar kaniya kawai, zaki wani zo ki kwanta a saman sofa ki bar mana angon mu shi kaɗai a saman gado, wato baki ji nasihar Akila ba kenan? Mu samu da kyar mun tayaki yaki a kan soyayyar taki ne har kika samu nasara shi ne kike kokarin watsa mana kasa a idanu ki ruguje komai ta hanyar yin nesa da shi ko? To mu zuba da ni da ke ƴar nema". Ta kai karshen maganar tare da kwashewa da dariya sannan ta ɓace ɓat kamar wata walkiya.
Ita kuwa Rimsha ta kankame shi sosai tamkar zata koma cikin jikinsa, sai ihu take kurmawa kamar ba lafiya ba, su kansu sojojin Lion ɗin sai da suka yi mamakin irin ihun da take yi, yarinya kamar kanta akwai motsi, basu san cewa Malika ce ke yi mata tsiya wani lokacin ba, ta razanata tasa ana yi mata kallon mahaukaciya ko tana da matsala a kwakwalwa.
Ganin yanda jikinta yake kerma sosai ga kuma kuka da take yi ne yasa ya ɗago kai dan ya ga ko dai Brady ne ya tsoratata, bawan Allah shi bai ga komai ba, ɗago haɓarta ya yi dan ya rarrasheta ta yi shiru ta gaya mishi menene, amma ina ta ki yin shiru, dan fa ba karya ta tsorata iya tsorata, irin wannan halitta da daddare haka ya fito maka ba tare da ka shriya ba, dole kwakwalwa ta juye.
Sai ambatar sunanta Meesha yake yi, amma ina sam bata jin shi, sai ihu sosai take yi, hakan yasa ya haɗe bakinsa da nata dan ya sata ta yi shiru, kara kankame shi ta yi tana jan numfashi da kyar da kyar. Sai da ya tabbatar da ta sami natsuwa ta yi shiru sannan ya saketa yana mai ɗago haɓarta, ta runtse idanu gam hawaye na zuba daga idanun nata.
"Meesha why are you crying?" Cikin kuka murya a dashe ta fara magana da kyar da kyar "Yaya Saif dodo na gani fa". Sake ɗago idanu ya yi yana bin ɗakin da kallo, ganin ba komai ne yasa ya fara tofa mata addua'o'i kawai, dan a tunaninsa tsorata ta yi, dama ya san ta da shegen tsoro, ga shi kuma ta ga a cikin ruwa suke, kila ta fara barci ne ta yi mafarkin sun nitse cikin ruwa, shi ne ta farka take yi mishi ihu wai dodo ta gani, ko a ina taga dodon ƴar rigima kawai, haka yake ta tunani a ransa.
Yana tofa mata addu'a yana shafa bayanta a hankali hankali alamar ta yi barci to.
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥
KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔
ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne.
KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA,
INFECTION KILLER,
COLACCA,
SAI KAYAN GYARA PAGE.
KACA KACA.
YALLAGWADA.
JIGIDA.
RUWA RUWA.
BANI BANI.
WOMEN JELL BATA BATA.
DAFIN KAXA.
TANTABARA.
XABUWA.
CICCIƁI.
AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER
09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH,
BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI.
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥
TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️
👊FATEEMA ZAHRA MUSA (PRINCESS TEEMA OR STAR LADY)✊
*Domin samun karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 0816 139 0581*
74
Yana tofa mata addu'a yana