Showing 24001 words to 27000 words out of 359620 words

Chapter 9 - Triplets Book 3 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

1957

ina jinka?" "Aunty Afi Ommu ne ta kirani jiya, ta ce na ɗauko mata kuɗin yaya Akil har naira million goma, to dama yau da daddare ya ce zamu je gida, kuma nace mata idan zamu zo gida zan kawo mata, dama zan ɗauka mata 2 million ne a cikin kuɗinsa da yake ajiyewa a bedroom nasa, to amma tsoro nake ji, na rasa ya zanyi, na rasa me mafita, na rasa wajen waye zan nemi shawara, dan Allah ki ceceni, wlh ina tsoron ɗaukar abin da ba nawa ba!!". Ta kai karshen maganar tana hawaye.

A kule Aafia ta ce "Sai dai uban millon 10, ke Umaisha baki da hankali ko? Ta yaya zaki yarda da wannan abin? Kina da hankali kuwa? Ina ilimin naki yake? Ina karatun da kike yi kullun? Haka Allah ya ce ki yi? Allah bai ce ayi wa iyaye biyayya wajen saɓon sa ba, Ki sani naira ɗaya na mijinki, idan kika ci ba tare da ya baki ba, to fa wuta kika ci, to tun wuri ki dawo hayyacinki Kinji na gaya maki, me yasa ba zata tambayi Abbi ba? Idan ma Abbi yaki bata ai yaya Irfan kam ya zama mashi dole ya bata, to wlh kada ki kuskura ko naira ɗaya na yaya Akil ki taɓa ba tare da ya baki ba?".

Tana hawaye ta fara bawa A'AFIA ɗin labarin yadda suka yi da Ommu ɗin da har ta yarda zata ɗauko mata kuɗin, jin hakan yasa jikin Aafia ɗin ya mutuwa, Allah sarki uwa da ƴaƴa kenan, komai lalacewar uwa, in dai tasan ta yadda zata yi magana da yaranta, to tabbas ba makawa zata yi galaba akansu, ta rasa me zata cewa Umaisha ɗin kuma again.

"Aunty Afi kina jina?" Ƴar firgita ta yi jin muryar Umaisha ɗin, Baiwar Allah ta shiga duniyar tunani ne, domin ta gasgata zancen Ommu ɗin, musaman ma da ta ji an ce Abbi ya ce ba zai biya mata ba, ta san halinsa sarai, tabbas zai iya cewa ba zai biya ɗin ba, domin yana da zafin rai da saurin fushi, sai dai kuma yana da saurin sauƙowa, abin da bata sani ba shi ne, Ommu karya ta shirya masu da ciwo, domin tasan da ciwo ne kawai zata yi saurin karyar masu da zuciya.

Tana ƙoƙarin yin magana ta ji Nawid yana ƙoƙarin fitowa daga toilet, cikin sauri ta sallami Umaishar a kan za su yi waya wani lokaci kawai.

Katse kiran ta yi, ta koma ta kwanta tana tunanin mafita, har cikin ranta ta tausayawa Ommun tasu.

Gaban mirror ya tsaya, ya gama shafa mai da perfume nasa, sannan ya juyo ya kalleta, cike da zolaya ya ce "Amarya azo a sanyawa ango kaya". Miƙewa zaune ta yi tana sunkuyar da kanta kasa, da kallo ɗaya ya yi mata ya fahimci akwai abin da ya ɓata mata rai, dan haka sai ya ajiye zancen wasa, cikin natsuwa ya kariso gareta.

A saman bedside drawer ya zauna, cike da kulawa ya riƙo hannunta. "Menene kuma kanwata? Waye ya taɓa ki?" Ƙaƙalo murmushi dole ta yi. "Babu komai yaya Nawid" ta bashi amsa.

"Are you sure?" Ya yi maganar yana ɗan leƙo face nata, ɗagowa ta yi suka haɗa ido, cool murmushi ta sakar masa domin ta tabbatar mashi da babu komai.

"Zaki iya bawa yaya Nawid ɗin ki sumbata a kumatu?" Ya faɗa cikin sigar soyayya. Gyaɗa mashi kai ta yi alamar e, sannan ta ɗaura da cewa in dai zai sanya shi farinciki zata yi mashi.

Sosai ya ji daɗi tare da ɗan juya mata kumatun nashi yana murmushi, kirginta sai bugawa yake yi, amma haka ta daure, ta matso da bakinta, cikin natsuwa ta bashi hot sumbata a kumatun nasa.

Kusan a tare suka sauƙe nauyayyar ajiyar zuciya, hannayenta ya riƙo "I really love my wife" "I love too yaya Nawid". Miƙewa ya yi ya koma gaban mirror yana faɗin "To za'a zo a sanya mani kayan ne ko ya ya?". Komawa ta yi ta kwanta "Yaya Nawid ni ai ban iya ba". Girgiza kai kawai ya yi tare da wucewa wajen drawer kayansa.

Kayan da yake buƙata ya ɗauka ya wuce toilet, ita kuma ta gyara kwanciyarta tare da kashe wayarta gabaɗaya, a cikin zuciyarta kuwa, ji take yi kamar ta kira Irfan ta gaya mashi abin da Ommu ke buƙata shi ya bata kuɗin, sai dai kuma ta san mawuyacin abu ne Irfan ya bada kuɗin, domin kuwa ya fi Abbi ma yin fushi da Ommu ɗin, ko ganinta baya son yi, kawai dai dan ba yadda zai yi ne, ta zo a matsayin mahaifiyarsa, sai dai hakuri kawai, amma fa tabbas ba zai bata wannan kuɗin ba, shiyasa ma bata tinkare shi ba.

A haka Nawid ya fito ya sameta, ya shirya cikin kananan kaya, kusa da ita ya zo ya kwanta tare da fara janta da hira, tun tana biye mashi kaɗan da kaɗan, har ta ware suka fara zuba hira tare da zubawa juna kalman so da kuma kauna.

To a ɓangaren gidan Lion kuwa.

Rana ta ɗage ta yi sanyi, yamma ta yi, misalin karfe 4 zuwa 5 haka, barcinsa yake yi cikin kwanciyar hankali, daga yanayin kwanciyar da ya yi, zaka fahimci a cikin kwanciyar hankali yake, a hankali hankali yake sauƙe numfashinsa, jikinsa na sanye da pajama launin fari tas, kyakkywar dark black curly hair sa, ya zuba mashi har fuskarsa, bai ɗaure ta bane, hakan yasa ta zubo mashi har kan face nasa, ta rufe mashi fuska sosai, sai sheki gashin nan yake yi, abin mamaki kuma gashin nasa, kusan iri ɗaya dana Rimsha, sai dai nasa bata kai na Rimsha nannaɗuwa kamar indomie ba, ita Rimsha nata ya naɗu sosai.

ɗan motsawa ya fara yi tamkar mai mafarki, a hankali ya cigaba da juyawa tamkar wani ke juya shi, ya ɗan ɗauki tsawon minti biyu a haka kafin ya waro dara daran blue eyes nasa waje, wadda kuma farin cikin idanun suka yi ja sosai, da alama barcin bata ishe shi ba.

Slowly ta sauƙe idanun nasa a saman ɗakin nasa, kafin daga bisani ya dawo da idanun nasa saman gadon nasa. Shiru ya yi na tsawon mintoci kafin nan ya mai da idanun nasa ya lumshe su, a hankali ya motsa kyawawan lips nasa ya furta "Why mummy, why are you always coming in my dream with useless thinks? Why are you disturbing my life?! Do you want me to do something for you, so that you should forget about me? Oh what?". Shiru ya sake yi na tsawon mintoci da a kallah za su iya kai minti 30.

A hankali ya miƙe kuma tare da zama a gefen gadon yana mai tsananta tunani akan cikin daddynsu da mummynsu waye ne mai gaskiya? Me yasa shi kaɗai ne mai yawan mafarkin mum ɗin tasu? Meyasa kuma kullun yake yawan mafarkai marasa kyau ne a kanta? Meyasa take zuwa mashi a siffar da ko wani ɗan adam ba zai so ganin wani nashi a ciki ba? Meyasa take yawan yi mashi ikirarin zata kashe shi a mafarkin? Amma kuma a zahiri tana nuna mutuwar sonsu, tabbas da ya ɗauka shirmen mafarki ne kawai, amma yanzu tsawon shekara 15 yana wannan mafarki bai dai'na ba, babu rana ɗaya da zai kwanta ba tare da ya yi ba, dole wannan Mafarki ta sanya shi cikin ruɗani, menene ainahin makasudin ciwon Michael? Sannan daddy yaki gaya mashi gaskiyar a ina ne gidan magicians (matsafa) da ta kai su, yaki gaya masu in da gidan yake bare su binciki gaskiyar lamarin, ya ce masu ya mance a in da gidan yake, amma abin mamaki shi ne ƴaƴanka har guda uku za'a kai su irin wannan gida dan a salwantar da rayuwarsu, amma har ka iya mancewa da wannan gidan? Abin da mamaki gaskiya, daddy bai yi tsufar da zai yi irin haka ba, dan ma shan wine (giya) ne da ya yi a baya ce ta taɓa mashi lafiyar jikinsa, ba dan haka ba, lafiyayyene sosai, dole dai akwai abin da daddy da mummy suƙe ɓoyewa, wadda ba su son ƴaƴan nasu su sani, Lion bai cika son yana shiga hurumin iyayen nasa ba, kai shi ba iyayensa ba, koma waye baya shiga huruminsa, sai idan abu ya zame mashi dole, amma yanzu a ƴan kwana biyun nan yana ji a jikinsa tabbas dole ya binciko gaskiyar da aka binne tsawon shekaru, bai so hakan ba, domin daga daddyn har mummyn nasu ba wanda yake so a cikinsu, hakan kuma yasa bai shiga wannan faɗa ta su ba, ɗan garama Josephine ɗin ya fi sonta ita a kan daddyn nasu.

Shiru ya yi ƙwaƙwalwarsa na tariyo mashi abubuwa da dama dan gane da iyayen nasu, tabbas yana ji a jikinsa mummynsu na sonsu da gaskiya, kuma tamkar ta fi daddy gaskiya, sannan wannan ciwo da Michael ya yi na tsawon shekaru 30, to tabbas daddy yana da sa hannu, domin kuwa yana yawan ganin Musharraf yana magana da Aseef ɗin a kan ciwo, tabbas ba ciwo ce ta tsakani da Allah ba, akwai wata a kasa, to amma babbar abin tambayar a nan shi ne, meyasa ita kuma Josephine ɗin take zuwa mashi a mafarki tsawon shekaru 15, kullun maganarta a cikin mafarki zata kashe su, ba zata taɓa bari su rayu ba, wani lokaci ta yi ƙoƙarin caka mashi wuƙa har sai an riƙe ta, ba mafarki ce da za'a yasar da ita ba, ba mafarki ce da za'a ce shirme ba ce, tsawon shekaru 15 tabbas akwai wata aya da take son isa masu a cikin wannan mafarkin, to menene? Kuma shi ne kaɗai mai yin wannan mafarki.

Can wata zuciya ta ce mashi to ko dai kai ba ɗan su bane, da sauri ɗayar ɓangaren na zuciyar ta amsa mashi da no ba zai yi wu ba, dole kai ɗansu ne mana, dole kai ne cikon TRIPLETS na MICHAEL and JAMES, idan kai ba ɗansu bane ta ya za'ayi kuyi irin wannan muguwar kamanni haka? Ai zancen kai ba ɗansu bane ma bai ta so ba, ta ko'ina ku ɗauko iyayen naku, daga Josephine ɗin har William ɗin, ta kowani ɓangare kun ɗauko su, so dole sune iyayenku, sai dai kawai ku nemo wata hanya kuma ta daban da zaku nemowa kanku mafita.

Har lokacin shi dai yana ji tamkar ba daddy bane mahaifinsa, domin ko kaɗan baya jin son daddyn nasa, kuma ba shi kaɗai ba dukkansu, duk da wannan uban kammanin dake a kan fuskarsu, amma yana jin tamkar dai shi ubansa daban. TO UBANSA DA BAN KUMA?🤔 A'A KU ƘIRA MANA JOSEPHINE TA ZO TA YI MANA BAYANI, TAYA YA YA ZAMA SHI UBANSA DABAN, KUMA SUKE A TRIPLETS? KO DAI BA TRIPLETS NA GASKE BANE? BABBAR MAGANA WANNAN CAKWAKIYA DA YAWA TAKE.

A ɓangaren ita kuma Rimsha, zaune take a palon kasa, har lokacin shigar ɗazun ce a jikinta, abinci take ci cikin natsu, yaya Imran ya saho mata abinci, Mark mugu ya hanata yin girki, wai abincin kasarsu na da wari, ɗan banza ya zo ya zauna mana a kasarmu amma dan iskanci wai abincin mu na da wari.

Cikin kwanciyar hankali take taunar abincinta. Sanye cikin fararen kaya masu shegen kyau Malika ta bayyana a gefenta, wani irin haɗaɗɗen murmushi ta saki. "Malika ina kika shiga kwana biyu?" Dogon numfashi ta ja tare da sauƙewa a hankali.

"Rimsha ke dai bari, ba zaki gane bane, ina can ana ta faman faɗa a kasarmu, kinsan sarkinmu kwanaki bashi da lafiya, to Allah ya yi mashi rasuwa, shi ne fa ake ta faɗa akan waye zai hau mulki, shiyasa kwana biyu na ɓuya, yanzu ma na ɗan leƙo mu gaisa ne kawai, ba jimawa zan yi ba, zan koma saboda har yanzu bamu samu zaman lafiya ba, duk da cewa Yarima Haruna ya karɓi Mulkin, to amma ƴan uwansa sunki yarda, wannna ya ce shi ne zai riƙi mulki, wannan ma ya ce shi ne, aikin kenan, har yanzu hayaniyar da ake yi kenan.

Ita dai Rimsha almara take ɗaukar abin, ji wai harda wani sarkinsu ya mutu ana yaki, to ko a gidan uwar wa suke yakin Oho? Ko dai a saman iska suke yakin ne? Sai tambayar kanta take yi, saboda yarinta irin tata.

Ganin haka yasa Malika ta kawar mata da wannan tunani "Ina angonmu Rimsha?."

Wani cool murmushi ta saki, an sosa mata in da yake yi mata kaikayi, sosai Malika ta ji daɗin ganin wannan murmushi nata, dama kuma abain da take nema kenan. "Malika dan Allah ina son in tambaye ki". Tsareta da idanu Malika ta yi ba tare da ta yi magana ba.

"Malika dan Allah ko kin san ta ya ya aka yi Ayla ta baro Daular Mutuwa? Abin ya tsaya mani a raina, dana tambayeta a waya kuma, ta ce mini ta manta, to dan Allah idan kin sani ki gaya mini".

Shiru ta ɗan yi na tsawon lokaci kafin ta fara magana a nutse "E Ayla ta baro Daular Mutuwa ne da taimakon wani daga cikin Daular Mutuwar, sun sha faɗa sosai kafin ya samu ya fito da ita, bayan ya fito da ita kuma, akwai wani ruwan tsafi da ya bata, ni ban san faɗar da suka yi a ciki ba, na dai ga lokacin da ya fito da ita, ya bata ruwan tsafin domin ta sha, tana sha kuma ta zube a wajen sumammiya, bata sake farkawa sai bayan kwana ɗaya, a in da kuma ta farka a kusa da wannan kauye da kuka haɗu, shi kuma wadda ya bata ruwan tsafi ya kuma fito da ita, yana ganin ta suma ya juya ya koma cikin Daular Mutuwa, to kin ji abin da ya faru kenan, abin da yasa kuma ki ka ji cikin Ayla na kumbura a lokacin, wannan ruwa da ya bata ta sha ne, shi ne yasa hakan ta faru kafin ya saketa".

Rimsha zata sake magana sai ga Mark ya fito daga cikin Kitchen, karo na farko yau da ya sauƙe idanuwansa a kanta, baya iya ganin Malika, ita kaɗai ce a wajen a idanunsa, ba karamin mamaki ya sha ba ganin irin kyanta, sosai ya kare mata kallo daga sama har kasa, ga idanun nasa dara dara, sai dai suna cikin bakin glass, hakan yasa bata gane yana kallonta ba.

"What is your name?" Shi ne abin da ya tambayeta da wata fasasshiyar muryarsa a wajen, mamaki ne ya kamata, dama wannan mai fuskar ɓaunan yana magana? Ai ita ta zaci ma kurma ne wlh.

RIMSHA ta bashi amsar, kokarin kiran sunan ya yi a cikin zuciyarsa, amma ya kasa, a maimakon Rimsha, sai ya ce Rishma, ganin sunan ba zata maimaitun mashi bane yasa ya ce ya ta je ta ɗauki abincin oga ya gama haɗawa.

Okey ta amsa mashi da shi, ta miƙe cikin natsuwa, yau dai bai tafi ba, ya tsaya binta da kallo, ƴar karama da ita sai shegen kyau kamar ita ta yi kanta, Malika dai ta zuba idanu tana ganin ikon Allah, tare kuma da dariyar mugunta, kome take yi wa dariya oho, ita kaɗai ta barwa kanta sani.

Yana tsaye a wajen har ta fito ɗauke da abincin, zata yi wa Malika magana, cikin sauri ta ɗaga mata hannu alamar ta je kawai, idan ta yi magana Mark zai ce ta haukace, tun da shi baya kallon Malika ɗin.

Sama ta wuce, shi kuma ya wuce ya koma cikin Kitchen ɗin, dan ya ɗauko abincin Areef, yau kawai ya ji yana son tayata aiki ne, shiyasa zai kaiwa Areef nasa abinci. TO FA YANA SON TAYATA AIKI KUMA? SHI DA BAYA KO MAGANA? HMMMM.

A bakin kofarsa ta tsaya kamar kullum, kasa kasa ta yi sallama a nutse, kamar dai kullun shiru, a hankali ta zuro kafafunta cikin daɗin. Daddaɗar kamshin perfume nasa ne ya fara kai mata karo a kofofin hancinta. Shaƙa ta yi ta lumshe idanu, har wani nishaɗi take ji.

Babu kowa a cikin daɗin, yau dai taƙi ɗago idanu gudun kada ta ga wani abin mai razanarwa, har sai da ta ajiye mashi abincin nasa a in da ta sa ba ajiye mashi, sannan ta fara ƴan waige waigen ko zata ga ta ina yake.

Ganin babu kowa ne yasa ta yi zamanta a wajen tana cigaba da kallon ɗakin, sai dai ta ɗan yi kasa da kanta.

Jin kamshin perfume ɗin nasa ya karu a ɗakin ne yasa ta ɗago kanta, ya fito daga dressing room nasa, ya bata baya yana kallon fusataccen fuskarsa a jikin mirror, da alama akwai abin da yake yi, jikinsa na sanye da jallabiya fara tas, kai.... shi dai yana bala'in son farin color a rayuwarsa.

Sai satar kallonsa ta kasan ido take yi, duk da bata ga face nashi ba, bata ganshi ta gaba ba, tabbas tasan ya yi wa kayan kyau over, da alama ya rage tsawon gashin kansa, domin yau da ya ɗauke ta, jelar bata da tsawo sosai, ba kamar ko da yaushe ba.

Sai bayan ya gama abin da yake yi ne, ya dawo kusa da ita a in da ya saba zama ya zauna, cikin sauri ta fara zuba mashi abincin, can cikin ƙwaƙwalwarta zazzakar sexy voice nasa ya daki dodin kunnenta har cikin ƙwaƙwalwarta.

"Give me my photo". Shi ne abin da ya faɗa mata, yau ta tattara natsuwarta sosai, bata son ta cigaba da yi mashi laifi, a bayanan da Imran ya yi mata ta fahimci cewa yes tabbas yana yi wa Imran kara sosai da har take yi mashi irin waɗan nan laifuka ya kyaketa, kuma tana cin albarkacin har da daddynta da yake matukar taimakon ASEEF.

Cikin natsuwa ta amsa mashi da okey, sannan ta miƙe ta ɗauko mashi wayar, sai dai jikinta sai kerma yake yi, lokacin da ta zo miƙa mashi wayar hannunta sai kerma yake yi, kallo ɗaya ya yi wa hannun nata ya karɓi wayarsa ya fara aikin latsawa, tun da ya fahimci tana mutsuwar bala'i tsoronsa, sai ya ji a ransa bai kamata ya yi mata magana da karfi ba, zata iya mutuwa idan hakan ta faru, dama kuma magana da karfi ba halinsa bane.

Abincin ta zuba ta tura mashi, sai daɗi take ji, yau bata yi mashi laifi ba, ita kaɗai sai murmushi take


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login