Showing 327001 words to 330000 words out of 359620 words
a lokacin.
Busar mishi da gashin ta fara yi, tana yi tana cakuɗa hannunta cikin kan nasa. A hankali ya lumshe idanunsa saboda wani irin daɗi da yake ji yana ratse dukkanin ilahirin jikinsa. Ita kanta daɗin taɓa mishi gashin take ji saboda yanda yake da tsananin laushi ga tsantsi kamar me. A hankali ta kai ɗan bakinta ta sumbaci gashi tana sauke ajiyar zuciya. Yana jin duk abin da take yi mishi, jin saukar sumbatar ne yasa ya ɗan waro shanyayyun idanunsa waje. Zuba mata idanu ya yi yana kallon yanda take murmushin tana shafa gashin nasa.
Ƴan mintuna ta ɗauka tana busar mishi dan ya fara yi dama, ita karisawa kawai ta yi. Bayan ta kammala ta shafa mishi mayukansa dake saman mirror a wajen, lokacin da ta je ɗaukar mayukan ne ta fahimci ashe yana kallonta ta cikin mirror. Wani irin kunya ne ya kamata, kenan ya kalli sumbatar gashinsa da ta yi? Ta tambayi kanta. Lokaci guda ta sanya hannu ta rufe face nata tana murmushi. Shi dai har lokacin bai kawar da kallonsa daga kanta ba.
Sai da ta yi kora da kunyarta ya isheta sannan ta shafa mishi mayukan tare da tara gashin nasa waje guda. Da kyar ta iya ɗaurewa saboda bala'in tsantsi, sai da ya sanya hannu ya taimaka mata. Tun da yake a rayuwarsa bai taɓa ganin gashin kansa ta yi mishi tsantsar kyau irin na yau da ta gyara mishi ba. Bai san cewa matar aure tana da baiwa na wuce misali, kome ta taɓa in dai wa mijinta zata yi wa, to fa kyansa na daban ne, zaka ga namiji zai fita waje ya sayi abinci naira dubu ɗaya, amma zai cinye shi kaɗai wani lokaci ma bai koshi ba, amma da zai bawa matarsa wannan dubu ɗayan ya ce ta dafa musu abinci, da izinin Allah sai ta yi wannan abin da wannan dubu ɗayar su ci su koshi har ya yi saura, kaɗan kenan daga cikin ni'imomin da Allah ya yi wa matar aure wanda ba kowa ne ya san da su ba, sunanan bila adadi, idan nace zan tsaya zayyano muku baiwarsu, to sai mu cike littafin TRIPLETS fam bamu kammala ba, zai cinye mana ɗan sauran filinmu, dan haka a takaice matan aure dai Allah ya yi musu baiwa na daban, sai dai dayawa daga cikinsu basu san ta yaya za su yi amfani da baiwar ba, to Allah ya buɗawa kowacce ƙwaƙwalwarta ta iya sarrafa mijinta da kyau ta yanda zasu mori juna, mu dai muna iyaka bakin ƙoƙarin mu wajen ganin mun buɗe muku wasu abubuwa da baku sani ba dan ku gyara gidajenku!!.
Zazzakar muryarta ne ya katse shi da cewa "Noori na iya gyarawa? Ya yi maka kyau?." Ta kai karshen maganar tare da zuro hannayenta ta saman wuyarsa izuwa kirjinsa tana kwanto da kanta a saman kafaɗarsa. Lumshe idanu ya yi tare da sake buɗesu a kanta, ta kwantar da kanta shiru tana jiran amsa.
Hannun nata dake saman kirjinsa ya riko a in da ya jawota ta dawo ta gabansa. Saman cinyarsa ya nuna mata a kan ta zauna ba tare da ya yi magana ba. Ba musu ta zauna tana mai cigaba da murmushi.
Zame mayafin abayar dake kanta ya yi a in da ya ajiye shi a gefe guda saman mirror, da yake ya fita tsawo sosai sai ya zamana da ta zauna a cinyar nasa yana iya kallon tsakiyar kanta sosai. Hand dryer ya ɗauko tare da sake kunnata ya fara busar mata da gashi. Wani irin haɗaɗɗen murmushi ta saki lokacin da ta ji abin da yake yi mata. Duniya kenan, yau GAR ne yake busar mata da gashin kanta? Allah mai iko mai yin yanda ya so da bayinsa, yau dai gata a saman cikyar mutumin da take mahaukacin kauna tun tana yarinya, bugu da kari yanzu ya zama mallakinta, mijinta ne shi ɗin, ga tsantsar kulawa da yake bata, sam bata damuwa da tsantsar kishinta da yake yi, domin Areef ya gaya mata sai ana son abu ne ake kishinsa, to ta kwantar da hankalinta, idan Lion baya sonta ko kallon hanyar da take ma ba zai yi ba, so ne yaja yake kishin, kuma ta godewa Allah ma da ya bata namiji mai kishinta har haka, hakan na nufin shi ɗin mai tsantsar kula ne, zai bata kulawa fiye da tunanin mai tunani, duk wani motsi idan ta yi sai ya so jin menene yake damunta, ko dan kada wani ya raɓeta zai zamana kullum yana son ta kasance kusa da shi, haka zalika zai bata soyayya mai tsayawa a rai ta yanda bazama ta ga wani soyayyar a Tv ko a wani waje bama har ya burgeta, duk wani abin da ya san zata kallah a waje ya burgeta, to fa zai yi ƙoƙarin ya ga ya yi mata shi fiye da yanda ake yi a wajen dan kishin kada na wajen ya burgeta, kaɗan kenan daga cikin baiwa da falalar samun namiji mai kishi, ko takalmar sakawanki ba zai bari wani ya gani ba dan kishi.
Meesha, ya ambaci sunanta a hankali, ya kuma yi maganar dai'dai lokacin da yake kashe hand dryer yana tara mata gashin nata dan ya ɗaure. "Na'am Noori." "Tashi muje kici abinci sai mu wuce an gama shirya komai mu ake jira."
"Noori na koshi mu tafi kawai." "No zaki ci, because ba zan bari kici abincin gidansu kakanki ba idan munje, the are not Muslim, so zai iya kasancewa suna cin something da ba dai'dai ba a musulce." Zaro idanu waje ta yi tare da juyowa gare shi tana faɗin "Noori dama wajen kakana muka zo?".
Jinjina mata kai kawai ya yi ba tare da ya yi magana ba, sake juyawa ta yi tana fuskantar mirror tare da sakin wani ƙayatatcen murmushi. "Noori yanzu zan ga kakana wanda ta haifi daddyna? Tana gidan nasu ne? Da.....". Bata kai karshen maganar ba idanunta suka sauka cikin nasa ta cikin mirror. Cikin sauri ta runtse nata tana murmushi, bata san cewa ya tsareta da kallo ba.
Ɗan kwanto da kansa a saman kafaɗarta ya yi tare da daidaita fuskokinsu waje guda. Calmly ya furta "Open your eyes." A hankali tamkar mai tsoron wani abin ta ɗan waro idanun nata waje. Kai tsaye sai saman fuskokinsu ta cikin mirror. Nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke tana kallon yanda suka yi wani azababben kyau, haɗin ya yi matuƙar dacewa, chocolate color and white color, abin ba'a magana.
"Are you interested?." Ya faɗa a hankali kamar mai raɗa, kuma ya yi maganar yana ɗaga mata gera ɗaya. Jinjina mishi kai ta yi alamar e, ɗaura hannunsa a saman shafaffen cikinta ya yi yana ɗan shafawa a hankali. Cike da tsokana ta sanya hannu ta shafo kyakkyawan sajensa zuwa wuyansa suna kallon juna ta cikin mirror. Yau dai ta daure tana kallon face nasa, amma ba cikin kwayar idanunsa ba.
"Noori." Ta ambaci sunansa. Tsareta da idanu ya yi ba tare da ya amsa ba. "Noori ina ka samo abaya?." Shiru ya ɗan yi na ƴan mintoci kafin ya ɗan juyo da kansa hakan tasa ɗan bakinsa ya kasance a saitin kunnenta. Raɗa ya fara yi mata a kunnen nata a hankali. Kyakkyawan murmushi ta sakar mishi tare da juyowa ta rungume shi da kyau.
Yatsa ya sanya mata a cikin dimple nata yana jin tsananin farinciki a tattare da shi. Sumbata ta kai mishi a wuyarsa ita ma tana cikin tsananin farinciki. Maganar da ya gaya mata a kunne ya yi matuƙar sanyata farinciki fiye da tunanin mai tunani.
(Ko me ya gaya mata?🤔 Amma muje dai zuwa zata fito fili ne ma muji.)
Hannunsa ɗaya ya ɗaura a saman bayanta a in da ya ɗago haɓarta suna fuskantar juna. Sai sakin murmushi take yi. "Why kike son yin smiling har haka?." Ɗan turo baki ta yi, a wannan karon bata runtse idanunta ba, sai ma ɗaga su sama da ta yi tana jujjuya su. A shagwaɓe ta ce "To Noori murmushin nawa baya yi maka kyau ne na dai'na yi?."
Shiru ya ɗan zuba mata idanu kafin ya bata amsa da cewa "Yana yi mini kyau over to over." "To Noori kai ma dan Allah ka yi murmushin ko sau ɗaya ne mana, ban taɓa ganin ko da sunan wasa kayi murmushin ba, tun da nake karama ina kallonka a Tv, fuskarka a ɗaure tamau na santa, har kuma izuwa yau a ɗauren take, ina son in gani ko da sau ɗaya ne kayi murmushin."
Ya ɗan ɗauki lokaci yana kallonta kafin ya amsa mata da "I don't know how to do it, that is the reason why ban taɓa yi ba, even my pleasure yana son nayi, amma i don't know how to do." Shiru ta yi tana ɗan tunani yanda ya furta my pleasure wato Aseef, ashe dama ya iya kiran sunan soyayya, wato shi TRIPLETS nasa kawai ya iya sakawa wannan suna kenan?. Bata san ita ma sunan da yake kiranta ɗin suna ne na musamma ba, shi kaɗai yasan dalilin da yasa ya sanya mata wannan suna haka.
"Noori in koya maka yanda ake yi zaka yi mini?." Girgiza mata kai ya yi yana faɗin no. "To why baka son na koya maka?." Ta tambaya kamar zata yi kuka. Shiru ya ɗan yi kafin ya amsa da "Because bazata yi mini kyau ba, smile is for women only, ba zan iya yi ba ko da kin koya mini." "To Noori idan ina son kayi fa?."
Ɗan jan kumatunta ya yi yana faɗin "Zaki haɗa har da nawa sai ki rinƙa yi, it's okey ko?." Turo baki tayi tana tunani, kila ita kuma haka ne kaddararta, kila har ta mutu ta koma ga Allah ba zata taɓa ganin murmushi mijin nan nata ba, wato ma ita ce zata yi nashi murmushin? To fuskarsu ɗaya ne? Allah yaya Saif ɗin nan ya iya abu shi ma. Duk wannan zantuka a cikin zuciyarta take yin su.
Miƙewa ya yi tare da ita a jikinsa. Hannu tasa ta saƙalo wuyarsa tana kara lafewa a kirjinsa. Yana fitowa sojojin nasa suka sake juya musu baya cikin girmamawa. Tsananin tsoron ganin Rimsha suke yi, dan Mark ya ja musu kunne a kan kallonta, ya gaya musu kanwar oga ce, shi dai bai san cewa matar oga ce ma bakiɗaya ba, dan bai san da batun auren ba, ya dai san ogansa fa ya kamu da sonta, gudun kada ya yi ɓaran ɓarama ne yasa ya ce wa sojojin kanwar oga ne kawai. Sun sha ruwan mamakin jin hakan, amma basu da zaɓin da ya wuce su yi shiru, dan basu isa su tambayi Mark ɗin a kan yaushe oga kuma ya samu kanwa ba? Tun da su dai sun san TRIPLETS su kaɗai Josephine ta haifa, kuma ya za'ayi kanwar ogar ma ta kasance bakar fata kuma ƴar Nigeria? Amma da yake su dai umarni kawai suke bi sai suka yarda a kan kanwar oga ne, shi ne yasa suke mugun bata girma. Kun dai san suma ba yara ba ne, tsab sun fahimci soyayya ce mai zafi tsakanin ogan nasu da ƴar yarinyar nan, hakan tasa suke kara respecting nata fiye da tunanin mai tunani.
Saman table chair a cikin bedroom nasu ya sauƙeta, zama ya yi a gefenta saman ɗayan kujerar. Abincin ta fara zuba musu cikin natsuwa. Mikewa ya yi ya ɗauko wayarsa a in da ya turawa driver jirgin nasu sako da su dakata tun da tun ɗazun jirgin yake yi musu alamar sun iso madakata. Dama sojojinsa a tsananin tsorace suke na ganin sun fara haura iyaka kuma Lion ɗin yana sane. Amma bai ce a dakatar da jirgin ba, ba su san yana can yana zuba soyayyarsa bane yasa ya mance ma da sun isa madakatarsu, ga shi ƙasar da suka zo dama sai a hankali, to ace kuma tun daga farkon shiga kasa sun fara karya musu doka? Ai abin ba zai yi musu kyau ba, amma saboda isa irin na Lion sai da ya gama shan love nasa tas sannan na ce su dakata. Bayin Allan suna ganin rayuwa, basu isa su yi komai ba sai da izininsa Allah sarki.
In da ya tashi ya dawo ya zauna, ta gama zuba abinci, spoon ya ɗauka ya ɗebo da nufin ya kai bakinsa. Kuka ta saka mishi tana kumbura kumatu irin na shagwaɓa. Fasa kai abincin bakinsa ya yi a in da ya juyo ya tsareta da ido. Gabaɗaya ta zama ƴar rigima yarinyar nan, ya faɗa a ransa.
Ganin bai yi magana ba ne yasa ta tsananta kukan nata tana mai turo baki. "Meesha what happened? Why are crying?."
"To Noori ba kai ne ba, a gida fa idan kuna cin abinci da su yaya Aseef, sai ka bawa yaya Aseef first spoon naka cikin soyayya da kaunar juna, yanzu kuma ba yaya Aseef shi ne ni ba zaka bani first spoon ɗin naka ba ko? Yanzu fa ni ce yaya Aseef naka tun da baya nan?." Tana magana tana hawaye kamar da gaske.
Ɗago hannunsa ya yi a in da ya duba time a jikin diamond watch nasu na TRIPLETS. Jawota jikinsa ya yi yana ɗan bubbuga bayanta alamar rarrashi, bai yi magana ba sai dai ya ɗan matso mata da spoon ɗin alamar to ta karɓi first spoon ɗin nasa.
Cool murmushi ta saki ga wasu guntun hawaye na iya shege a kumatunta. Kaɗan ta karɓi abincin ta bar mishi sauran a spoon ɗin tana faɗin "To kai kuma ka ci wannan." Girgiza kai kawai ya yi tare da kai spoon ɗin bakinsa ya cinye. Lokaci na tafiya ita kuma ta zauna tana zuba mishi shagwaɓa tana kara cinye musu lokacin. Hakan yasa kawai ya fara bata abincin a baki dan su yi sauri, ya lura idan ba haka ya yi mata ba tabbas ba zasu bar cikin jirgin nan da wuri ba.
Sai da ya tabbatar ta ƙoshi tap sannan ya kyaleta tare da miƙewa ya ce su je. Kuka ta saka mishi a kan shi ya bai ci abincin ba, rarrashinta ya fara yi tare da ɗaukarta cak ya ɗauki Maltina ɗaya suka nufi waje. Sai zuba mishi shagwaɓa take yi a kan ita dai sai ya ci abinci gaskiya, shi kenan zai zauna da yunwa ko yaya?. Sam bai kulata ba, ya kyaleta tamkar bai san tana yi ba.
Sai da suka fito wajen ne ya sauketa tare da riko hannunta, dan yasanta da shegen tsoro, ko a wajen saukarsu ma zata iya bashi matsala. Haka kuwa aka yi, shegen tsoronta yasa ta kasa sauka daga jirgin, dan tana ganin kamar ruwan dake bakin tekun ma yana da zurfi. Girgiza kai ya yi tare da ɗaukarta ya saɓa a saman kafaɗa. Sai da suka sauka ya sauketa yana tunani wai shi kam anya ba horon sojoji zai fara bawa yarinyar nan ba kuwa? Yarinya sai hangen tsoro kamar farar kura.
Gaisawa da jami'an bakin ruwa su Mark suka yi. Tsayuwa Mark ya yi yana magana da su, shi kuwa Lion wucewarsa ya yi abinsa rike da hannunta suka nufi wata hanya. Tambayarsu Password da sauransu Jami'an suka fara yi. Sam Mark bai nuna musu kamar suma jami'ai ba ne, kawai ya fitar da password ɗin ya miƙa musu da sauran abubuwan da suka buƙata. Bin Lion da kallon suka yi suna mamakin yanayin jikinsa, ya yi musu kama da GAR na kasar America, basu san cewa shi ɗin ba ne. A takaice dai suka kammala komai da Mark ya zo ya sami su Lion suka wuce zuwa wani waje dake can gefe da tekun.
Tamkar gida wajen yake. Basu kai ga karisawa wajen ba ma jibga jibgan motoci har shidda suka nufosu. Mamaki Rimsha take yi na motocin waye kuma waƴan nan, gabaɗaya motocin bakake ne sai kyalli suke yi tamkar sabbi. Dakatawa suka yi da tafiya har sai da motocin suka iso garesu suka yi parking.
Buɗe mishi gidan baya na motar tsakiya Mark ya yi yana mai sara mishi. Hannunta ya saki kafin ya nuna mata cikin motar dan ta shiga. Cikin sauri ta shige ta zauna kafin shi ma ya shiga. Kara sara mishi Mark ɗin ya yi tare da rufe kofar motar sannan ya juyo ya nufi motar dake kusa da nasu amma ta baya.
Yana ƙoƙarin buɗe kofar motar ne wani kyakkyawan matashin Bature fari kal da shi mai kirar karfi ya fito daga cikin motar. Kyakkyawan gaske ne, Allah mai halitta kamanninsa ɗaya sak da Aseef, kamar an tsaga kara. Shi kansa Mark sai da ya ɗan yi jim yana ganin wannan matashi, ya yi kama da Aseef sosai da sosai. Shiru ya ɗan yi yana karewa matashin kallo. Sai daga baya ya fahimci wannan ya fi Aseef shekaru, kuma shi idanunsa Sapphire blue ne, while na Lion kuma Sky blue, sapphire blue ta fi shiga kala sosai. Duk da cewa Turawa kusan kamanninsu ɗaya dama, amma dai wannan ya yi kama over da Aseef, harta gashin kansu brown color iri ɗaya, idanun ne kawai banbanci sai shekaru da ya fisu.
Ɗan rungumo shi matashin ya yi yana faɗin "Michael Trump?." Jinjina mishi kai Mark ya yi alamar e haka ne shi ne Michael Trump. Cike da fara'a ya ce "My name is Alex Trump, nice to meet you my brother." Shiru Mark ya ɗan yi yana jujjuya sunan iyayen nasu, ya ji sunan iri ɗaya ne, dukkansu Trump, Trump kamar abin haɗin baki. Abin da bai sani ba shi ne sunan kakansu ne Trump ɗin hakan tasa aka yawai ta masu irin wannan sunan a family'n, dayawa daga cikin uncles nasa sun yi wa kakan nasu takwara, shi ne yasa shi ma Alex ɗin sunan babansa ya zama Trump.
Jin motar da Lion yake ciki sun danna musu horn ne yasa Mark ya ce su shiga ciki sa karisa magana a hanya, sake rungumo shi Alex ɗin ya yi kafin su shige ciki. A tare motocin suka tashi zuwa cikin gari. Sai tambayarsa Alex yake yi a kan ina zasu je ne? Me kuma suka zo yi a kasarsu?. Shiru ya yi bai bashi amsa ba, dan idan baku manta ba shi ma fa Mark kamar gunki yake wajen