Showing 183001 words to 186000 words out of 359620 words
kallonsa zuwa kan Aseef, da ya dukar da kansa kasa kamar mai tunanin wani abin, ga kuma waya a hannunsa kamar mai latsawa, sai dai ga dukkan alamu ba wayar ma yake kallo ba, ya shiga duniyar tunani ne.
Zuba mishi idanu sosai ya yi yana kare mishi kallo, har yanzu akwai ragowar shatin yatsun ɗan'sandan nan da ya mare shi a fuskarsa, wajen ya yi ja. "Who slapped you?". Ya faɗa yana ɗaure fuska sosai, dama ga fuskar ba'a magana, tamkar hadari kullum, ƴar firgita ya yi tare da fara latsa wayarsa daka hannunsa, shi ya mance ma da marin nasa da akayi, yanzu bala'in da yake ciki tafi karfin mari.
"Wani ɗan'sanda ne ya mare shi". Cewar Areef, "A kan me?!" Ya faɗa a tsawace, sai lokacin ya ɗago kansa tare da kai kallonsa kan fuskar ɗan uwan nasa.
Ɓacin rai iya ɓacin rai Lion ya ji, akan me wani zai ɗaura hannunsa a saman kyakkyawar fuskar heartbeat nasu,? To koma waye uban shi sai ya karɓi hukunci wlh, dan bayan shi ba wanda ya taɓa ɗora hannu a saman wannan kyakkyawa kuma lallausar kumatun, shi ma sau ɗaya ya taɓa marin shi, kuma da dalilin, so dan haka bai ga dalilin da wani mahaluki zai ɗaura hannunsa a jikin TRIPLETS nasa ba kuma ya kyale shi, ba'ayi wannan mutumin ba a duniya a cewarsa.
Nan take Areef ya gaya mishi duk yadda aka yi, abin ya fara damunsa yanzu, wato kenan a kan Jehan wani ya mare shi? Wai shi ya rasa gane me matsalar TRIPLETS nasa da jinin Nawazudden ne, shi gaskiya yanzu sun fara ɓata mishi rai, ya fara jin ya tsani Nawazudden ɗin ma, akan me dalilinsa ƴan uwansa mafi soyuwa a garesa zasu rinƙa shiga haɗari, gaskiya shi ba zai yarda da hakan ba, dole ya taka musu birki kuma ya ɗauki mata, sai dai fa abin da bai sani ba shi ne, ya makaro, dan shi kan shi soyayyar Nawazudden ɗin tana cikin zuciyarsa, shi ne bai sani ba dan bai san menene ma soyayyar ba, amma tabbas shi ma yana kaunar Nawazudden da family'nsa, dama idan baku manta ba, da Rimsha da babanta muguwar shiga ran bala'i ke garesu, idan ka zauna da su to dole sai sun shiga ranka ta yadda zaka kaunace su ba tare ma da ka sani ba, to shi ɗin ma hakan ce, yana bala'in Kaunar Nawazudden ɗin, shi ne bai gane ba, kuma cire son Nawazudden a ransa ba abu bane mai yiwuwa a saukake yadda yake faɗe a baki, su kuma su Aseef sun riga da sun yi nisa, ba zasu iya dai'na son uncle nasu ba, ya zamo wani ɓari na jikinsu. TO FA BABBAR MAGANA SHI KUMA LION KISHIN BALA'I KE GARE SHI NA FITAR HANKALI, YANZU YA FARA KISHIN TSAKANIN ƳAN UWANSA DA DADDYN RIMSHA NE KO YAYA? DAN WANNAN DAI ALAMAR KISHI CE.
Shiru suka yi gabaɗayansu ba wanda ya sake yin magana, after some minutes Areef ya miƙe yana faɗin "Zan je prison tare da Mark ina dawowa". Zaro idanu Aseef ya yi yana faɗin "Prison kuma? Me zaka je yi a can". Nufar waje ya yi yana faɗin "Ƴar uncle zan je gani". Zai miƙe ya bishi Lion ya riƙo hannunsa tare da juyowa suna fuskantar juna.
"What is wrong with you?" Ya faɗa a sanyaye yana kuma tsare shi da blue eyes nasa.
Girgiza kai ya fara yi yana faɗin "Nothing". Shiru ya yi bai sake magana ba, dan dama baya tambayarsu abu ya sake maimaitawa, shi kuma Aseef ɗin ƙoƙarin ƙaƙalo murmushi dole ya yi dan ya tabbatarwa da ɗan uwan nasa ba komai, ya san cewa idan har Lion ɗin yasan cewa a kan mace ya shiga wannan damuwa har haka, to fa shi da auren Heartbeat har abada, dan wlh Lion sai ya wargaza komai, zai ce dama ai yasan mata balai ce, daga haka kuma sun jawa Rimsha, abubuwa dai zasu kwaɓe sosai, shiyasa ya gwammaci ya ɓuye damuwarsa shi kaɗai, ko Areef ba zai gayawa ba, dan yasan dukka bakinsu ɗaya ne, idan Areef ya ji, to tamkar a kunnen Lion ne, dan sai ya gaya mishi, haka suke gabaɗayansu, ko shi Areef ya gayawa magana ya ce kada ya gayawa kowa, to fa sai ya gayawa Lion, wuyarta dai a faɗa mishi ɗin ne, ana faɗa zai labartawa Lion ɗin, shi ma Lion ɗin wani lokaci yana gayawa Areef ɗin magana idan ta shafesu or daddy, a takaice dai dukkansu bakinsu ɗaya ne, so mafi alkhari a gareka idan baka son ɗaya daga cikinsu yasan da magana, to ka ɓoye kayanka a cikinka, dan soyayyar da yake tsakanin TRIPLETS ya wuci wasa, sun wuci tunanin mai tunani.
A palon sama Areef ya ci karo da Rimsha tana riƙe da Jacket ɗin Lion da ya rufa mata daren jiya, "Good morning my lovely brother". Ta faɗa tana ɗan murmushi, "Morning our Queen ina zaki je?" "Zan mayarwa da yaya Saif rigarsa ce". Shiru ya ɗan yi yana kallon rigar kafin ya ce "Okey je ki dawo ina jiranki a wajen mota ki zo mu je wajen sister a prison". Cike da murna ta amsa mishi da to, da sauri ta wuce zuwa cikin ɗakin, shi kuma ya wuce zuwa kasa.
💋PRISONERS💋
Ɗakin da suka kai Jehan ɗaki ne mai ɗauke da mata guda uku da ita huɗu, biyu daga cikin matan, manya ne masu ɗan shekaru wanda a kallah zasu kai 28 haka, ɗayar kuma matashiya ce. Da yake bata san su ba, sai tana ɗari ɗari da su, saman gadon da ya kasance mallakinta ta zauna a bakin tana tunanin yadda zata yi da gidar Hjyr daɗi, ita ba halin da take ciki bane ma ya dameta, su Adiva dake gidan Hjyr daɗi sune a gabanta, da kuma yadda zata yi ta rusa gidan, a cewarta bata bukatar taimakon kowa, dan bata yarda da kowa ba, su kansu hukuma bata yarda da su ba, a cewarta ɓata gari sun yi yawa a ciki, dan haka sai ta natsu ta samu aboki na kirki wadda ta san ba na banza bane daga cikin hukuma kafin ta bashi hujojin da take da su, yanzu bukatarta ta fita daga cikin prison ɗin nan ne, idan ta fita, zata fara bincike a kan hukuma dan nemawa kan tafita, kafin nan kuma sai ta tabbatar da ta tsaya da kafafunta ta yadda zata ci uban Hjyr daɗi babu surki, ta tsani matar tamkar ta sanya wuƙa ta cinke mata maƙogoron wuya kowa ya huta.
Ɗaya daga cikin matan dake cikin ɗakin ne ta katse mata tunani da cewa "Yarinya sannunki da zuwa gidan holewa da shagali tare da sharholi, amma gaki ƴar karamar yarinya har haka laifin me kika yi da ya cancanci a kawo ki nan?". Ɗaya daga cikinsu ne ta sake katseta da cewa "To ya wuci kisa ne, kin san fa yaran yanzu duk ƴan ta'adda ne, bar ganinta yarinya hmmm wannan daga ganin idanunta a bushen nan ba karamar ɓarna zata yi ba a duniya". Ita dai shiru bata tanka musu ba, miƙewa matar da ta fara maganar ta yi ta dawo kusa da ita ta zauna tana faɗin "Ki saki jikinki, nan gidan jin daɗi ne ai, ki zama jan wuya dan ki zama zakarar gwajin dafi a gidan nan, a nan ba'a yin shiru shiru, wlh idan kika yi shiru shiru azabtuwa zaki yi, ki buɗe baki ki yi magana, yanzu dai gaya mini laifin me kika aikata da har aka kawo ki nan?".
(Niko na ce baki san da waye kike magana ba gaskiya, jehan ai ba shiru shiru ba ce, kawai bakunta ce, amma daga baya zaku san wace ce ita ai)
Juyowa Jehan ɗin ta yi ta dafa matar tana faɗin "To ke laifin me kika yi da har aka kawo gidan yarin?".
Babu alamar shakka ko tsoro, nadama bare kuma sarewa a tattare da matar, idanunta a tsaitsaye, a bushe garau, ta ce "Kishiyata mana na zubawa shinkafar ɓera taci ita da ƴaƴanta biyu suka mutu, ni kuma aka wucu dani nan, ni wlh wannan gidan ma ya fi mini daɗin zama, amma wai fa kashe ni za'ayi, kawai zaman ɗan lokaci nake yi a nan, kuma da kike ganina a cikin ɗakin nan, nine mai ƙaramin laifi, wancan kuma ban san me ta yi ba, mun tambayeta sai ta ce babu komai, to babu komai za'a kawota nan ne?".
Ai kuwa Jehan bata san time da ta sake ta ba, baya kaɗan ta ja tana kare mata kallo, jibi yadda ta furta ta yi kisan tamkar wadda ta kashe kaji ko tattabaru, ba mutane ba, anya wasu suna son samun rahmar Ubangiji ko yaya take kuwa? Kai gaskiya wasu dai sun rantse dole dole sai sun tabbata a wutar jahannama, a haka kuma wai ita ce mai karamin laifi da suke ikirari a cikin waƴan da suke a ɗakin before Jehan ɗin, wannan bala'i da me ta yi kama?.
Kallon banza Asiya wadda ta yi magana ɗazun ta wurgawa Jehan ɗin kafin ta ce "Me kika wani ja baya dan kinji abin da Raliya ta ce? Ai ke karamar ƴar iska ce, mu kam ai jiga jigai ne, dan haka ma ki daina tsoro na gaya maki, a duniyar yanzu kada ki ji tsoron kowa nake gaya miki, ki zama jaruma kamar dai mu?". Da alama wannan Asiyar ƴar wiwi ce, ƴar hauce ba kaɗan ba, tana abu kamar wata jikar kauraye.
Shiru Jehan ta yi tana tunanin in dai zata zauna a nan, to ya zama dole ta fito da halinta na baya, domin ta lura gabaɗaya ƴan gidan nan tantiran ƴan iska ne, to dole ta koma ainahin jinin Nawazudden ɗinta dan su ci uban juna, daga zuwanta yau taga bala'in da ya sha gaban tunaninta, ji bi yadda suke faɗar laifukansu da bakinsu sanka sanka, lallai duniya abin tsoro ce, ba dole mu rinƙa shiga masifu kala kala ba.
Matsowa kusa da ita ɗayar da bata yi magana ba take shiru shiru mai suna Ameera ta yi tana faɗin "Ni ban san sunanki ba, amma dai koma ya sunanki ina son ki sani wlh ban aikata wani laifi ba aka kawo ni nan, zaluntata aka yi, kawai fin karfi a ka nuna mini".
Juyowa Jehan ɗin ta yi suna fuskantar juna da Ameera ɗin, yarinya yar matashiya da ba zata wuci 21 years ba, zuba mata idanu Jehan ɗin ta yi, da alama yarinyar tana da ilimi kuma ta yi karatu.
"To me yasa aka kawo ki nan?" Miƙewa ta yi ta dawo saman gadon Jehan ɗin tana faɗin "Wani yaron amshakin mai kuɗi ne ya yi wa wata yarinya fyaɗe, shi ne iyayen yarinyar suka kai kara court, dana ji labari a matsayina na ƴar jarida mai son tallafawa kasar, sai na nemi zantawa da yarinyar, ni gaskiya ƴar talakawa ce, da kyar da suɗin goshi iyayena suka iya biya mini kuɗi nayi karatu, iya diploma na tsaya a karatu na, Allah ya sa dai ina da rabo na sami aiki, to kamar dai yadda kika sani ne a duniyar yanzu mai kuɗi shi ne mutun, talaka kuma bawa ne, haka aka tauyewa yarinyar nan hakkinta, aka rufe case ɗin da wasu kananan shaidu wai dama yarinyar bin maza take yi, shi yaron lokacin da abin ya faru ma baya kasar, kawai dai talauci ne ya yi wa iyayenta yawa yasa suka yi wa yaro wannan sharri dan su sami kuɗi, iyayen yaro suka saye alkali ya basu gaskiya, har da ɗaurawa iyayen yarinya diya da zasu biya wai dan sun ɓata wa yaro suna, ni kuma dana ga haka sai na yi ƙoƙarin zantawa da yarinyar, na samu hujoji daga wajenta shi ne nayi ƙoƙarin bankaɗo gaskiya, daga haka ne fa suka ɗaura mini sharrin ina dillancin kwayoyi, ni ban san taya akayi kwayoyin maye suka shiga jakata har gidan mu ba, ina dawowa daga wajen aiki ƴan'sanda suka kamani wai sun sami information a kan ina dillancin manya manyan kayan maye, daga haka court ta yanke mini hukuncin ɗaurin rai da rai a nan gidan, dan ba kananan kayan maye aka samu a jakata ba, ban san hawa ba ban san sauƙa ba, sai dai na ganni a nan, yanzu sai Allah kaɗai ya san ya iyaye na suke, yau watana uku kenan a nan, kanina ne kawai ya taɓa zuwa sau ɗaya farkon rufeni da aka yi, ya ce mini baba yana asibiti, tun daga ranar ni ban sake ganin kowa nawa ba". Ta kai karshen maganar tana sharar kwallah dake zubo mata, ita kam Jehan ta rasa ya zata yi da waƴan nan abubuwa, can gidan Hjyr daɗi ga Maryam da take son ta kama ubanta ta yi mishi ɗan yen hukunci, nan kuma ga Ameera, wannan bala'i da me ya yi kama ne wai?
Dariya Asiya ta kwashe da shi har da shewa tana tafa hannu, ita ma dai Raliya dariya ta kwashe da shi tana faɗin "Yo idan ban da abin ɗan talaka da neman saka kai cikin masifa, ina ke ina nemo wasu hujjoji dan ki tona mishi asiri fisabillilahi? To ai shikenan yanzu ga shi ai kin kare a wannan gida ɗaurin rai da rai, dama wannan abin ne kike ɓoyewa kika ki gaya mana laifinki? Wlh na zaci ma kan wani kika fille ko kin kwakwale idanun wani jaririn ne? Ashe ke salihar baiwa ce ma ban sani ba, to ai ga shi yanzu zaki kare gabaɗaya kuruciyarki har tsufa zuwa mutuwa a nan, kuba ƴan shisshigi ba? Ɗan talaka da bai iya samun karamar dama ko ya take ba, to yanzu ai sai ki baza shaidar kowa ya gani". Ta kai karshen maganar tare da sake tuntsurewa da dariya.
A walaƙance Jehan ta kalleta ta watsar kafin ta ce "Ke dai anyi dabba jahila wlh, an gaya miki shi talaka ba mutun bane? To idan baki sani ba ki sani, wani talaka da yake yawo a cikin bola sai ki tarar ya fi shugaban kasa samun matsayi a wajen ubangiji, ki zama mai yin fariya da aikata aikin Allah ba saɓon Allah ba, ki bugi kirji ki ce kina da kusanci da Ubangijinki ta gefen sallah, azumi, Zakka, sadaka, da sauransu, ba ki daki kirji kina cewa kin fi wani abu kaza na duniya ba, Allah da ya baki ba wani abin kika yi mishi ya baki ba, haka suma waƴan da bai bawa din ba, ba wani abin suka yi mishi ya hana su ba, bai manta da kowa ba, yana sane da dukka bayinsa, so ki zama mai fariya da kin fi kowa aikata aikin Allah ba kin fi wata or wani samin wani abu na duniya ba, banza ballagaza kawai, wadda bata san ciwon kanta ba". Ta kai karshen maganar rai a matukar ɓace.
A fusace Raliyar ta damko wuyar rigarta tana faɗin "Bani da mutunci, wlh yanzun nan sai na saɓa miki kamanin, ke har kin isa ki ɗaga mini murya a cikin ɗakin nan dan ubanki?". Buge hannun nata jenan ɗin ta yi, a walakance ta ce "Ke ma kika ce baki da mutunci bare kuma ni, to da kike kallona hakan nan, sam ban san menene mutunci ba, na fiki zama mara kunya, dan haka ina mai baki shawara wlh tun wuri ki kama kanki babu ruwanki da ni, bana shiga harkar kowa, amma idan mutu ya shiga tawa, to fa ya sani duk girmansa bana shayin na bi ta kan mutun na take banza!!".
A harzuƙe Raliyar ta miƙe tare da sake riƙo mata wuyar riga ta ɗaga hannu da nufin marinta, cak Jehan ɗin ta riƙe hannun nata tare da miƙewa ita ma tana faɗin "Wlh idan kika yi gigin marina bazaki sake marin wata ba a duniyar nan, an gaya miki ni irin kishiryaki da kika kashe ne? To ni ba haka nake ba, ni kaɗai na gayyya ce mai zaman kanta, idan kina so ki jawa kanki bala'in da gabaɗaya zuria'arku ba zasu iya ɗauka ba kuma to Bismillah zaki iya sanya hannunki a jikina".
Abinku da prison, Asiya tana makale saman gadonta tana zuga Raliya a kan kada ta yarda wannan ƴar yarinya ta ɗaga mata murya, ita taki yarda ta sauƙo ta shiga faɗar dan tana tsoron idan gandurobobin sun ji ana faɗa suka zo, su haɗa da ita su yi mata hukunci, shi ne taki saukowa ta shiga, tana daga sama tana kara hura wutar abin.
Miƙewa Ameera ta yi tana rokonsu a kan dan Allah su bari, ita kuwa Raliya har cikin ranta ta tsorata da jin kalaman Jehan, tana ganin kamar Jehan ɗin ta taki wani tsiyar ne, dama kunsan irin wannan idan baka san mutun ba irin haka ta kasance a tsakaninku, to zaka rinƙa ganin kamar ya taki wani abin ne, tsoron da ta ji ne yasa da Ameera ta basu hakuri, sai ta hakura ta saki Jehan ɗin ta koma saman gadonta ta kwanta, ita ma Jehan komawa saman nata gadon ta yi ta zauna tana tunanin yadda zata ɓullowa waƴan nan abubuwa da suka sha kanta.
Gefenta Ameera ta zauna tana tambayarta a kan me ta aikata da har aka kawo ta nan, ba musu ta gaya mata ga abin da ta yi, daga Raliya har Asiya sai da suka ce eh!! Da karfi, wato ta yanke gabansa gabaɗaya, Jehan da iya shege har da iya gaya musu gabaɗaya ta cire bata rage ba, dafe kirji Ameera ta yi tana jinjina mata irin wannan aiki, ita da take da 21 years a duniya ma yaushe zata iya kallon namiji babba zindir ba kaya bare har ta kama ta yanke, innalillahi wa inna ilaihir rajiun, ai gani da ido ma kawai babbar bala'i ce, duk wata mace a ranar da ta fara kalla sai ta shiga tsoro bare ita Jehan da take ƙaramar yarinya, kuma abin mamaki idan tana magana hankalinta a matukar kwance, tamkar ba ita ta aikata ba, to yau dai sun ji labarin da ya goge musu hadda, daga haka ɗakin ya yi tsin kowa da abin da yake tunani a cikin ransa.
A ɓangaren Rimsha kuwa,