Showing 75001 words to 78000 words out of 359620 words

Chapter 26 - Triplets Book 3 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

1997

ta nufe shi, rungumeta ya yi sosai suna sakin Murmushi a tare. "Nayi kewarki sosai my baby". Ya faɗa kasa kasa.

"Daddy nima nayi kewarka, har ciwo sai da kaina fa ya yi dan baka dawo da wuri ba". Ta yi maganar a shagwaɓe. "Subhanallah ciwo kuma?" Ya tambaya yana ɗago haɓarta, gyaɗa mishi kai ta yi alamar e. "Ayya Sorry ba zan sake tafiya wani waje mai nisa na barki ba, idan zan tafi to kafata kafarki, idan ba haka ba, na fasa zuwa". Murmushi ta sakar mishi tare da kara lafewa a jikinsa, tana jin daɗin wannan damshin ruwan jikin nasa dake taɓata, ya lura da hakan, cikin sauri ya sake ɗago haɓarta suna kallon juna, tabbas idan ya canka daidai ciki gareta, dan ga alamominsa dukka sun bayyana a tattare da ita, wani irin mummunar faɗuwar gaba ya ji lokacin da ya tuna menene silar mutuwar mummyn jelly, Haihuwa, haihuwa ta zo yi Allah ya karɓi kayansa, kwata kwata ma ya mance da zancen kamanni dake tsakaninta da mummy'n Jelly ɗin, shi dai murna ya fara yi ya samu abin da yake so.

Sakinta ya yi tare da nufar gaban mirror, cikin sauri ya shirya tare da yi wa Allah sujudur shukur, sai bin shi da idanu take yi, bayan ya kammala ya zo ya runhumeta sosai a jikinsa yana zuba mata godiya da sambatun me take so ya yi mata, mamaki ne ya kamata, me yake faruwa ne kuma? Ta tambayi kanta.

Zaunar da ita a bakin gado ya yi tare da riƙo hannunta, cike da so da Kauna ya fara magana. "Babyn daddy kina jina ko?" Gyaɗa mishi kai ta yi alamar e "Nine auta a wajen mamana, bayan ni babu wasu, mamana tana sona fiye da tunaninki, amma a haka ta barni tana kuka ta tafi, ba ma wannan ba nake son gaya miki, kinga ni bani da kani kuma Allah bai bani yara da yawa ba, jelly kawai gareni, zan so ki haifa mini yara dozen da zan rinƙa kallah ina jin daɗi, ina rage zafin kewar mamata". Ya yi maganar idanunsa cike tab da kwallah.

Da yake yarinya ce sai bata hango tsantsar ciwo dake cikin rayuwarsa ba, bata hango irin bakin cikin da yake ciki ba, ta ɗauka kawai irin kwallan da ya saba yi ne, bata san wannan kwallah mafi azaba bane a gare shi ba.

"Daddy dama gwaggo Batula ba kanwar ka bace?" Ta faɗa tana rufe mishi idanun dan hawayen dake ciki su zubo ta goge mishi. "Batula kanwata ce amma mamanmu ba ɗaya ba, baki ji nace miki nine auta a wajen mamanmu ba ne? Ba a wajen babanmu na ce ba, wajen mamata, ni ne auta". "Daddy to ina mamanka da babanka, dan Allah ka kaini ina son ganinsu". Shiru ya ɗan yi kafin ya ce "Babana ya rasu, mamata kuma tana a in da bamu isa mun yi gigin tinkarar wajen ba, so kawai ki bar zancen, just kawai ki yi musu addu'a Allah ya jikan baba, mama kuma Allah ya fitar da ita zance ne ko kuma me oho dai, kawai ki yi musu addu'a da ta dace da su, amma itama mama fa bamu da tabbacin tana raye a yanzu ko ta mutu, kawai ki yi musu addu'ar Allah ya jikansu baki ɗaya". Ya kai karshen maganar tare da miƙewa ya shiga toilet dan ya je ya yi kuka sosai ko zai sami saukin abin da yake ji a ransa. Allah sarki sunga rayuwa iya ganin idanunsu, musamman ma shi da yake Auta, an rabashi da mahaifiyarsa tun yana yaro ƙarami, tun bai wuci 2 to 3 years ba, Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun, yafi su Abbi gabaɗaya shiga kuncin rayuwa, ga shi lokacin da ya fara girma ya dawo hannun Abbi, Ommu ta azabtar da rayuwarsa, ya zo ya yi aure da wuri ba dan ya shirya ba, sai dan samun mafita, a auren ma sai da ya fiskanci matsalar dangin matar tasa, shekara ɗaya da aurensa suna tsaka da son juna da matar Allah ya karɓi kayansa a lokacin haihuwa, ya yarda da kaddararsa bawan Allah, ya jure ya cigaba da addu'a, ya riƙi jelly hannu bibbiyu, baban Muneer ya zo ya sake jefa rayuwarsa a cikin kunci, bayan haka jelly ta ɓata, ya sha bakar wahalar da har jinya sai da ya yi, ya sake gane ta, a gabaɗaya rayuwarsa, waje uku ne ya ji daɗi, na farko rayuwar da ya yi ɗan kalilan da daddyn Rimsha, sai rayuwar shekara ɗaya na aurensa da mummyn jelly, sai kuma yanzu da ya sake aure ya auri Ayla, sune iya jin daɗi da ya samu a gabaɗaya rayuwarsa, amma duk da haka bai sare ba, ya dukufa ya koma ga Allah, bai ce wani ne ko wata suka yi mishi wani abin ba, ya yarda jarabawace daga Allah, kuma a wajen Allah kawai yake neman taimako.

Sai da ya yi kuka sosai kafin ya wanke fuskarsa ya fito ya dawo cikin ɗakin, kwance ya sameta a saman gadon har ta yi barci, abin ku da mai ƙaramin ciki, saurin barci.

Kusa da ita ya zo ya zauna tare da shafa kanta ya karanto mata addua'o'i sosai ya tofa mata, sosai yake jin tsantsar kaunarta a cikin zuciyarsa. Ya jima yana kallonta kafin ya haura saman gadon da kyau ya gyara mata kwanciya tare da rufa mata bargo dan garin akwai hadari da iskar ruwan sama.

Alwala ya wuce ya ɗauro a toilet tare da simfiɗa dadduma ya tada sallar la'asar da bai samu ya yi ba.

A ɓangaren gidan Lion kuwa.

Misalin Karfe 8 na dare, zaune suke ita da Akila a ɗakinta suna hira, tana sanye da Abaya mai shegen kyau launin pink color, ita kuma Akila atampha ce ɗin kin doguwar riga a jikinta, Akila ta zuba mata make up tamkar waƴan da zasu je party ko gidan bikin, bata ɗaure kyakkyawar dark black curly hair'nta ba, ta sake shi har gadon bayanta, sai ta yafa mayafin gyalen a kanta, sai tashin kamshi suke zubawa, Akila na ta bata labarin kyawu irin na kakanta Naurat, bata san cewa kakansu ɗaya ba, da yake ita Rimshan ta sani, sai kara tambayarta take yi da waye kakan nasu take kama, kuma dan Allah a ina ta san kakar tasu, nan Akila ta gaya mata a hoto ta santa, Abba yana da hotonta tun tana budurwa har aurensu da Dr Salman da bayan aure duk yana da hotunan, kamar zata yi kuka ta ce "Dan Allah Aunty Akila ki ɗauki hoton a waya ki turomin ko ta WhatsApp ne in ganta kin ji?" To ta amsa mata da shi, har mamaki Akilar take yi na yadda Rimsha ta damu sosai a kan maganar kakar tasu, tambayar kanta take yi sai ka ce Rimsha na da wani alaƙa da kakar tasu.

Suna tsaka da hira Imran ya shigo ya sanar da Rimsha ta je ta kaiwa Saif abinci, cikin sauri ta miƙe tana faɗin "Aunty Akila ina zuwa". Riƙo hannunta Akilar ta yi tana faɗin "A'a Rimsha ki jirani yau muje naga masoyin nan naki". Zata yi magana Imran ya rigata da cewa "A'a Heartbeat ki zauna ki jirata". Ba musu ta amsa da to, da sauri Rimsha ta wuce, sai da ta fita shi ma ya fice daga ɗakin suka bar Akilar ita kaɗai, wayarta ta jawo ta fara latsawa.

Kamar kullum Kitchen ta wuce ta ɗauko abincin, da sallama ta shiga ɗakin nasa, yana zaune saman bed nasa, jikinsa na sanye da wandon jeans baki da T-shirt fara tas, high neck t-shirt ne mai dogon hannu, ya ɗaure dark black curly hair'n nan nasa a bayan wuya, da alama yau yana cikin bakinciki, dan fusataccen fuskar nan tasa har wani kyalli take yi, saboda bala'in ɗaureta da ya yi, bata kalli in da yake ba, dan tana tsoron kada su haɗa ido ko ta kalli cikin idonsa ya tsorata ta.

In da ta saba ajiye mishi abincin ta je ta ajiye, tana zama bai fi da minti biyar ba sai ga shi ya miƙe ya iso in da take, a in da ya saba zama ya zauna tare da lanƙwashe kyawawan fararen kafafunsa.

Abincin ta fara zuba mishi, while shi kuma ya zubawa yatsun hannunsa idanu yana kallon,

A hankali ya juyo da kallonsa a kanta da nufin ya kalli abin da take zuba mashi a cikin plate ɗin, dan yau ba komai zai ci ba, akwai abin da baya sha'awar ci yau, yana ɗago dara daran blue eyes nasa kai tsaye suka sauƙa a saman kirjinta wadda kuma anyi sa'a wuyar abayar tata ta gangaro kasa kaɗan, hakan ya yi sanadiyar bayyanar sunansa dake a waje, sai dai sunan bai fito sosai ba, sakamakon ba sosai wuyar rigar tata ta yi kasa ba, iya sunan GRA ne kaɗai ya bayyana, saura ba su fito ba, dawo da kallonsa ya yi a kan fuskarta wadda shi ne kallonta na farko da ya fara yi a rayuwar zaman da suka yi, sun ɗan jima a tare amma bai taɓa ganin face nata ba sai yau, wannan kallon da ya yi mata kuma tayi daidai da ɗagowar kanta domin ta saci kallonsa ko me yake yi.

Ido cikin ido suka kalli juna yau, wani irin bugu da karfi kirjinta ya yi, yau ta kalli cikin tsakiyar kwayar idanunsa, a sukwane ta yi kasa da kanta yayin da shi kuma ya sanya hannunsa ya zame mayafin dake a kanta tare da riƙo rip ɗin gaban rigar tata domin ya zuge kasa ta yadda zai samu damar ganin abin da ta rubuta a kirjin nata da kyau.

A razane ta miƙe da nufin ta gudu ta bar ɗakin, cikin zafin nama ya riƙo hannunta tare da fisgota da karfi, ai kuwa yana fisgota sai saman kirjinsa ta faɗa, ko kaɗan bai ji komai ba tamkar wani dutse, ita kuwa suma ne kawai bata yi ba, amma har wani fitsari take ji ya zo mata da wani uban gudu tamkar zai zuba mata a pant nata, duk ta kiɗime ta fita hayyacinta, bata san time da ta saki wani marayan kuka ba wadda daga ji kasan cewa kukan tsoro ne ainun.

Shi bai wani damu dan tana jikinsa ba, abin da yake gabansa kawai yake yi, abin da ya yi niya kenan wato ganin me ta rubuta a wajen domin zuciyarsa na gaya mashi sunan sane da gaske kamar yadda ya gani.

Hannu ya kai ya damki zip ɗin rigar nata da nufin ya zuge, cikin sauri ta kai hannu bibbiyu ta kankame gaban rigar tata, ta hana shi zugewa, tana yi tana matsalar kwallah bibbiyu.

Gently ya ce "Remove your hands". Jin sexy voice nasa mai haukatar da tunani mai sauraro saboda daɗi, ba karamin haukata ta ya yi ba, bata ma san time da ta zame hannayen nata ba, sai dai ji ta yi ya zuge zip ɗin kasa har zuwa shafaffen cikinta, datse idanunta ta yi da kyau, wani irin azababben kunyarsa ne ya kamata, yau wani ya kallan mata tula-tulanta, kuma gata a kwance a jikinsa, abin haushi ma namiji ba mace ƴar uwarta ba, kuma namijin ma ba muharraminta ba, babu abin da ya haɗa su, innalillahi wa inna ilaihir rajiun, shi ne kawai abin da ta iya furtawa a cikin zuciyarta.

Shi kuwa bai wani damu ba, hasalima bai kai idanunsa kan tula tulan nata ba, abin da yake bukatar gani shi kawai ya zubawa idanu yana karantawa tare da jan kyakkyawar farar vest ɗin jikinta kasa dan ya gani da kyau.

Tsab ya karance kafin ya dawo da kallonsa a kan kyakkyawar face nata da ya sha make up sosai yau, ta datse idanu gam tamkar zata fasa su, saboda matse su da ta yi, gabaɗaya ilahirin jikinta karma yake yi, kuma tabbas ya lura da hakan...............
❤️❤️TRIPLETS❤️❤️



E19-20



Tsab ya karance kafin ya dawo da kallonsa a kan kyakkyawar face nata da ya sha make up sosai yau, ta datse idanu gam tamkar zata fasa su, saboda matse su da ta yi, gabaɗaya ilahirin jikinta karma yake yi, kuma tabbas ya lura da hakan, daidai lokacin kuma Areef ya shigo cikin ɗakin bakinsa ɗauke da sallama irin ta addinin Musulunci, bai lura da ita a jikin ɗan uwan nasa ba sakamakon sun bawa kofar shigowa baya.

Jin sallamar Areef yasa ya saki vest ɗin nata tare da sakinta, daidai lokacin shi kuma Areef ya kariso wajen, ya sha ruwan mamakin ganinta a jikin Lion ɗin, bai yi tunanin wani abin Lion ɗin ya duba a jikin nata ba, bai ma lura da zip ɗin rigarta a zuge kasa ba, da yake kunsan akwai vest, hakan yasa bai gane ba, amma dai kansa ya ƙulle, ya san dai dole akwai abin da ya kawo ta jikin Lion ɗin, to menene wannan?.

Zama ya yi kusa da ɗan uwan nasa har lokacin bai kau da idanunsa daga kansu ba, ita kuma idanunta a datse har lokacin, shi kuma Lion tun shigowar Areef yake kallon face nata yana nazarin wani abin, yes tabbas akwai abin da yake nazari dan gane da face ɗin nan nata, tabbas ya taɓa kallon mai irin wannan fuska sak a tare da Josephine, to wace ce? Ya tambayi kansa.

"Stand up from my body!" Shi ne abin da ya furta a nutse. Jikinta sai kerma yake yi ta miƙe daga jikin nasa ta sauƙa kasa, har ga Allah ganin sunansa yasa gabaɗaya ya ji wani iri, jikinsa ya yi sanyi, amma yana da bukatar ya tabbatar da tun yaushe aka yi wannan zane dan ya lura kamar ba na yanzu bane, idan zanen ya jima kenan hakan yana nufin dan Allah aka yi shi, idan kuma bai jima ba, akwai dalilin yin ta.

Cike da tsoro da fargaba idanunta a rufe bata lura da Areef ba, ta nufi hanyar fita daga ɗakin, har lokacin jikinta na karma, da kyar take iya taka kafafunta ta riƙe kanta dan kada ta zube kasa.

"Come here". Ya furta tare da dawo da kallonsa a kan Areef. Da kyar ta iya juyowa ta nufo shi tana mai kallon kasa, ta ki yarda ta ɗago kanta bare ma su yi ido huɗu.

In da ta saba zama, a nan ta koma ta zauna. "What is your Name?" Ya tambaya yana ɗauko wayarsa. Gabaɗaya ta nemi natsuwarta ta rasa, ta rasa ina zata sanya ranta ta ji daɗi, ta rasa me yake yi mata daɗi, da kyar murya na rawa ta bashi amsa da "My name is Rimsha". Shi dai Areef sai mamaki yake yi, wai me ya haɗa su ne? Ya kasa ganewa fa, a fitar da shi daga duhu.

"Yaushe kika yi wannan zanen? Kuma me yasa kika yi ta?". Yana maganar yana tura saƙo a watarsa zuwa ga Aseef. Cike da tsoro da fargaba, bata san lokacin da ta ce mishi last week ta yi ba, ta rikice ta manta ko yaushe nema ta yi zanen.

Jin ta ambaci last week yasa ya ce ta ɗauko mishi chemical da ya zubawa mata a lallen hannunta ranar bari ya zuba ya goge zanen, wani irin mahaukacin razana ta yi tare da sakin kuka mai sauti, ita kaɗai tasan azabar dake tattare da wannan shegiyar chemical ɗin, shi dai Areef ya zubawa sarautar Allah idanu kawai yana kare musu kallo, tun da an rasa me fidda shi daga duhu.

Ɗago dara daran blue eyes nasa ya yi tare da sauƙesu a kanta, nan take ta natsu sit tare da haɗiye kukan nata, ta nemi kukan ta rasa, tuni ya gudu, wargi ma ai waje ya samu, ba tare da ya yi magana ba ya mai da kallonsa izuwa saman drawer da chemical ɗin yake ciki, ta gane nufinsa, wato ba zai maimai ta maganarsa ba kenan.

Jiki ba kwari ta miƙe ta nufi wajen drawer, shi kuma Areef ya sanya hannu bibbiyu ya tallaɓo kumatunsa ta yadda zai ji daɗin mai dasu Tv'nsa kawai, tun da an rasa mai fidda shi duhu.

Ɗauko chemical ɗin ta yi tazo ta miƙa mishi tare da zube gwiwowinta a kasa, karɓa ya yi tare da buɗewa, gently ya ce ta cire rigar tata sannan ta sanya hannu ta tare chemical ɗin ta zuba a kirjin nata da kanta, shi kuma zai zuba mata a hannun, kuka take yi baiwar Allah, hawayen nan wani na bin wani, kara tsananta kermar jikinta ya yi, idanunta tamkar zasu firfito su faɗo kasa, hannayen nata sun kasa tsayawa wajen jan vest ɗin nata zuwa kasa, tsantsar kerma da jikinta yake yi ne, yasa komai nata ya kasa tsayawa waje guda, duk wata zuciya mai imani idan ta ga halin da take a ciki sai ta matsa mata kwallah, amma shi kuma Lion tamkar wani mai zuciyar dutse, ko kaɗan bai ji tausayinta ba.

"Lion wai me yake faruwa ne?". Cewar Areef ya yi maganar yana kamo hannunta dake ta faman kerma ta ɗaura a saman kirjinta ta kasa jan vest ɗin nata kasa, shiru Lion bai tanka mishi ba, riƙota da kyau Areef ɗin ya yi tare da jawota ta dawo kusa da shi, har lokacin kuma kallon ɗan uwan nasa yake yi, ya kasa kawar da kansa yana jiran amsa.

"Sister me yake faruwa? Me ya haɗaki da Lion?". Kasa magana ta yi, kuka yaci karfinta Baiwar Allah, hawayen nata ya fara goge mata yana mai kara jawota jikinsa.

Daga ita har shi sai da suka yi wani mahaukacin razana jin tsawar da Lion ɗin ya daka musu akan ta bashi hannunta ya zuba mata chemical ɗin nan ta zuba a kirjinta, tsabar razana bata san lokacin da ta kankame Areef da hannayenta dukkan biyu ba, ganin ta fita a hayyacinta sosai ne yasa Areef ɗin ya rungumota sosai a jikinsa yana ɗan bubbuga bayanta.

"Saif me yake faruwa ne? Me ta yi maka?". A karo na biyu ma shiru ya yi bai tanka ba, miƙewa da ita a jikinsa Areef ɗin ya yi, bayan sun miƙe tsaye sai ya saɓata a kafaɗarsa dan ya lura ba zata iya tafiya ba, kuma ya lura muddin bai fitar da ita daga ɗakin nan ba tana iya mutuwa saboda tsabar razana.

Bai ce da su komai ba har suka fice daga ɗakin, ya yi hakan ne kuma


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login