Showing 99001 words to 102000 words out of 359620 words

Chapter 34 - Triplets Book 3 Hausa Novel Complete

10 Dec 2024

2021

da tausayi, me A'isha bata yi muku ba a gidannan?, jikinta fa kuka sayar kuka sami kuɗi, yau an wani gari tana kwance rai a hannun Allah ne zaku ce babu ruwanku da ita? Wlh kukam ko kun tuba Allah ba zai barku ba, domin nasan akwai yara da dama da suka mutu a dalilinku, to ku sani Allah baya yafe hakkin wani, iya laifin tsakaninku da shi kawai yake yafewa, to taya zaku nemo yafiyar waƴan da suka mutu? Wlh ku bakaƙen azzalumai ne, macuta, makirai, kuma kafurai, sheiɗanu kai komai da komai ma, da izinin Allah sai Allah ya kawo karshenku tsinannu, baku babu ganin Annabi, wlh mutuwar walakanci zaku yi, ko kare sai ya fiku mutuwa mai daraja, Allah ya tsine muku albarka, ya kwashewa iyayen da suka aifeku albarka, da haihuwar irinku gara ɓarinku, shegu mugayen iri kawai". Tana magana tana hawaye wani nabin wani, ji take yi wani mahaukacin jiri na ɗibarta, saboda tsantsar ɓacin rai, da alama kuma ta fita a hayyacinta, dan wannan surutai da take yi bata san tana yinsu ba, abin ya yi mata muguwar ciwo, dama kun san halinta, zata iya ɗaukar komai banda cin zalin wani bawa, bata ganin za'ayi rashin adalci ta bari, kuma hakan ne yazama sanadiyar shigarta kaddarori da dama, saboda taimakon Hanan ta yi wa FAROOQ karyar ta yi recorded nasa, daga nan ya turo a kasheta, hakan ya yi sanadiyar zuwanta wannan gida, ta shiga bala'i kala kala a kan taimakon wasu, kun san da hakan!.

Da Iya karfinta na ƙarshe Zinariya ta sa hannu zata kwaci wuyarta, amma ina ta kasa, sabon jini da tsohon jini ba ɗaya ba, duk ta ragwargwaɓe maneji take yi dama, Jehan tazo tana ƙokarin karisa ta.

suna cikin wannan hali sai ga ƴar gwal, ganin abin da yake faruwa yasa ta kariso ciki da gudu ta yi kansu, tana zuwa ta kwashe kafafun Jehan ta zube kasa Zinariya ta bita ta faɗa kanta, dan kuwa taki sakin wuyar tata, Jehan akwai taurin rai da taurin kai ga taurin zuciya over.

Kokawa suka fara yi ƴar gwal na ƙoƙarin kwatar Zinariya, ita kuma Zinariya tana ƙoƙarin baƙontar lahira, Jehan kuwa ta kankameta gam taki saki, kwalbar lemon da Zinariya ke sha kafin Jehan ɗin ta shigo, ƴar gwal ta ɗauko da niyar ta kwalawa Jehan a kai, Jehan kuwa sai da ta daidai ci daidai zata kwala mata, sai ta juya da Zinariyar, kwas kake ji yar gwal ta kwalawa Zinariya a kanta, ga shi da iya karfinta na ƙarshe ta saki kwalbar dan ta fasawa Jehan kai, sai ga shi reshe ta juye da mujiya, nan take kan Zinariyar ya fashe, shi ma kwalbar ya fashe, da alama kuma ya shiga kan Zinariyar, jini ne ya fara zuba kamar wani famfo, a zabure Jehan ta saketa tare da sanya karfin da ya rage mata ta tureta gefe guda ta miƙewa tana tangal tangal kamar zata faɗi, ta nufi waje zata fita, jawota ƴar gwal ta yi da nufin ta daketa, nan take ta fara yi musu hauka hauka, ta nuna musu ta fita a hayyacinta, duk abin da ta samu ɗauka take tana harbin ƴar gwal da shi, hatta laptop ɗin Zinariya na shigar da bayanan kuɗin da aka samu bayan tafiyar hajiya da sauransu Jehan ta ɗauka ta yi wurgi da shi, kan kace me ta fasawa ƴar gwal baki, watsi da komai na cikin office ɗin ta fara yi, a guje ƴar gwal ta watsa waje tana ihun a kawo kara ɗauki mahaukaciya, Jehan ta haukace, da gudu Jehan ɗin ta bi bayanta, suka bar Zinariya kwance rashe rashe a cikin jini, ko motsi bata yi, da alama dai ta mutu ne ko suma.

Wani katon katako Jehan taci karo da shi a tsakiyar gidan, ɗauka ta yi a fusace ta cigaba da bin ƴar gwal, yau haukace musu tuburan ta yi, a takaice dai da kyar da makyarkyata a ka iya kama Jehan, sai da su tattabara da su zillaziya suka sanya hannu, bayan sun danneta ne, Ƴar gwal na daga laɓe a bayan sauran matan gidan da suka taru, tana loƙo su baki a fashe yana jini, har ya kumbura suntum kamar ruɓaɓɓen alale ta ce "Kada ku sake ta, ku saka sarka ku ɗaureta sosai, wlh mahaukaciya ce, ina ga a mahaukatan ma wannan ta karshe ce, a mahaukatan ma ina ga babu irinta, ku danneta da kyau, ku kula fa kada kuma ta kashe ku". Tana magana tana zare idanu, yau tasha bugu.

Haka su tattabara suka sa karfi suka ɗaure Jehan da kyau, sannan suka ɗauketa zuwa ɗakinsu, daga nan jama'a ko wacce ta koma ɗakinta, ita kuma ƴar gwal da su zanƙaɗaziya suka nufi wajen Zinariya dan suje su kai mata agajin gaggawa. Yau dai anyi ƙaramin yaki a gidar Hajiyar daɗi, matan gidan kowa sai mamakin Jehan yake yi, saboda kowacce tana bala'in mutuwar tsoron su Zinariya kamar me, ba wace ta isa ta ɗaga musu yatsa or murya, yau an wayi gari Jehan ta yi musu hauka hauka ta ragargaji banzaye, ai kunga dole su yi mamaki

GA A'ISHA KWANCE KO TA MUTU KO TANA RAYE OHO😭😭 WANNAN BALAIN DAME YA YI KAMA? ALLAH KA KAWO MANA KARSHEN DUK WASU AZZALUMAI DAKE FAƊIN DUNIYA BAKI ƊAYA, NI DAI NA TAFI GIDAN ABBO, WATA KILA KAFIN NA DAWO KOMAI YA ƊAN LAFA A WANNAN BAKIN GIDAN, KO KAƊAN BAI KAMATA A KIRA WANNAN GIDA DA GIDAN KARUWAI BA, KAMATA YA YI A KIRASHI DA BAKIN GIDA, GIDAN ZALINCI DA AZZALUMAI😭.

GIDAN ABBO💋❤️

Misalin karfe 5 na yamma, aiki take yi a kitchen, yayin da ita kuma Ummi take faman gyaran palo, sanye take da doguwar riga ashe color, ta yi kyau sosai, tana samun kulawar mijinta dana surukuwarta, sai wani kara haske take tana ƙiba, tana aiki tana tunanin mijin nata, kayan miya take gyarawa, ta bawa kofar shigowa baya, sai tunani take yi na ya akayi bai dawo ba har yanzu, ko dai aiki ne ya yi mishi yawa.

Bata idasa tunanin nata ba ta ji an rufe mata idanu ta baya, ko bata juya ba ta san shi ne, domin kuwa Ummi dai ba zata yi mata hakan ba, cool murmushi ta saki, "Yaya Nawid yau fa kayi latti". Ta yi maganar cikin sanyin murya, ƙayatattacen murmushi ya sakar mata tare da kwanto da kansa a saman bayanta yana faɗin "Ke dai bari, ai nasan nayi laifi, shiyasa ma zan fara bada hakuri tun yanzu, nayi kewarki sosai fa".

"Ni kam ba zan iya misilta irin adadin kewarka da nayi ba, tun ɗazun tunaninka nake yi, amma me ya sa ka jima har haka? Bayan kuma kace mini karfe 4 zaka dawo". Zame hannayen nasa daga saman idanunta ya yi tare da mayar da hannu ɗaya saman shafaffen cikinta yana ɗan shafawa, ɗauke wuta ta yi na wucin gadi tare da ajiye kayan niyar dake hannunta ta juyo da sauri.

Tana juyowa ya jawota jikinsa ya rungume, a tare suka sauke nauyayyar ajiyar zuciya na kewar juna, "Me ka sayo mini a hanya?" Ta yi maganar kasa kasa, "Kayan daɗi na sayo Miki, amma sai dare zan baki, yanzu dai yunwa nake ji, da kuma gajiya, zaki yi mini tausa ko?" Ya kai karshen maganar yana ɗan raba jikinsu, "Ni ban iya tausa ba ai". "Shima zan koya miki kamar yadda na koya miki kiss, yanzu dai a bani kiss na barka da dawo kafin a kawo mini abinci".

"Yaya Nawid ka bari mana kaga fa Ummi tana Palo, kowani lokaci daga yanzu zata iya shigowa cikin kitchen ɗin nan, idan ta ganmu fa?" Jan dogon hancinta ya yi, "Waye ya ce miki Ummi zata shigo? Ai tana ganina na shigo Kitchen ɗin, sai da muka gaisa ta yi mini sannu da dawowa, kuma tasan idan na shigo sai na taɓa ki, Kinga kuwa ba zata shigo ba dan ita zata ji kunya, kin san Katsina da kunya, amma ni bani da shi". Dariya ta kwashe da shi, wai shi bashi da shi, innalillahi wa inna ilaihir rajiun, ta faɗa a cikin ranta.

"Ni ki daina dariyar nan ki bani hot kiss bari na je nayi wanka". "Rufe idanunka to" ta yi maganar tare da tsagaita dariyar da take yi.

Ba musu ya datse idanun nasa tare da matso mata da bakinsa, ɗan ɗaga kafanta kaɗan tayi, ta yadda zata kamo shi tsawo, cikin natsuwa ta kai bakinta sai tin nashi ta fara kissing na kayanta, kamar jira yake yi ya jawota jikinsa tare da fara matsa mata breast ɗinta ta saman rigar nata, kankame shi ta yi ta zura hannayenta dukka biyu a bayansa, cikin sauri ya juyar da kiss ɗin ya dawo shi yake kissing nata ba ita take kissing nashi ba, sosai yake matse mata breast nata yana wani sakin numfashi da sauri da sauri.

Sun ɗan jima a haka, sai da ya fara fita a hayyacinsa tukunnan ta kwace kanta tare da juyawa ta koma kan aikin da take yi, duk abin da suke yi Ummi na gyaran palo tana jinsu, dan palon ba nisa da Kitchen ɗin, idan da sabo ta saba da tsiyarsu, wani lokaci ma a gabanta idan ya shigo Kitchen ɗin yake sumbatar Aafia a kumatu, sai dai ta kawar da kanta kamar bata gansu ba, bata son su matsa kusa da ita ne, da farko Nawid ya ce zasu koma gidansa, ita taki yarda, ta ce a'a su zauna kusa da ita, Baiwar Allah kuma bata takura musu, komai suke so suyi, sai ma kara musu kwarin gwiwa da take yi a kullum.

Da kyar ya iya barin kitchen ɗin ya nufi bedroom nasu, a palo ya wuce Ummi bai ce mata komai ba ita ma bata ce mishi komai ba, yana shiga ɗaki ya ajiye jakarsa tare da nufar toilet dan yin wanka, ita kuma sauri sauri ta karisa wanke kayan miyar ta fara haɗa mishi abinci dan ta kai mishi...........

❤️❤️TRIPLETS❤️❤️



E25-26


Da kyar ya iya barin kitchen ɗin ya nufi bedroom nasu, a palo ya wuce Ummi bai ce mata komai ba, ita ma bata ce mishi komai ba, yana shiga ɗaki ya ajiye jakarsa tare da nufar toilet dan yin wanka, ita kuma sauri sauri ta karisa wanke kayan miyar ta fara haɗa mishi abinci dan ta kai mishi.

Lokacin da kai abincin ya fito daga wanka yana tsaye a gaban mirror, ta cikin mirror ya zuba mata idanu yana kallonta, in da ta saba ajiye musu abinci, a nan ta je ta ajiye, zata fice daga ɗakin ya ambaci sunanta kasa kasa, juyowa ta yi tana kallon shi.

"Baki fitar mini da kayan sakawa bafa," cikin zolaya ya yi maganar, ba musu ta dawo wajen drawer kayan nasa, kananan kaya ta fitar mishi, tana ƙoƙarin juyawa ta nufe shi, sai ji ta yi ta buge shi, da sauri ta ɗago kai, bai bari ta kalli face nasa ba, ya yi saurin jawota jikinsa, "Wai ni sister yaushe ne zaki barni nayi wasa dake son raina ne?" Ya yi maganar kamar mai yin raɗa.

Shiru ta yi bata amsa shi ba, sai wani ɓoye fuska a kirjinsa take yi, bayanta ya fara shafawa a hankali yana sauke numfashi, shiru ta kwanta a jikinsa bata motsaba har sai da ya saketa dan kan shi, yana sakinta fa miƙa mishi kayan nasa, karɓa ya yi ya nufi toilet, ita kuma kitchen ta koma.

A palo ta haɗu da Ummi, zata wuce kitchen ta dakatar da ita ta hanyar cewa "A'a Aafia ki bar girkin zan je in karisa, ki je ki kula da mijinki tun da ya dawo". Kasa ta yi da kai, a dole ta ji kunya, sumui sumui ta juya ta koma, dama ita ma tana son zama ta kula da kayanta, dan kawai kada Ummi ta ce ta bar mata girki daga kai abinci ne yasa ta fito, badan haka ba, ta fiso mijinta ya ci abinci a gabanta, dan ta san adadin komai da yake buƙata, ma'ana tasan adadin cinsa da sauransu, dama kuma yana da kyau ku san adadin abincin da mijinku yake ci, dan kada ki rinƙa labta mishi abin da ba zai iya cinyewa ba, ki zuba mishi abin da ya fi karfin cikinsa, ko kuma wadda ta yi mishi kaɗan, sai ya zo yana a kara mishi ko daɗin ji babu, wai a kara.

Lokacin da ta dawo ɗakin shi ma ya fito daga toilet ɗin shirye cikin kayan data fitar mishi ɗin, ya yi kyau sosai, ya fito a cikakken saurayinsa, duba time ya yi 5:30, in da ya saba zama ya je ya zauna, cikin natsuwa ta karisa in da yake, abincin ta fata zuba musu, bayan ta gama ne suka fara ci a tare, cike da so da kaunar juna, da kuma kula da juna, sai zuba mata hira mai shegen daɗi yake yi, ita kuma sai bin shi da murmushi take yi har suka kammala.

Miƙewa ta yi ta tattare kayan abincin ta nufi waje, Ummi tana kitchen tana faman zuba soyayyar nama a cikin miyar da Aafia ɗin ke haɗawa. "Ummi bari na karɓa miki". Ta faɗa bayan ta ajiye kayan abincin.

"A'a Aafia ai kin yi abinci, miyar kuma bari na karisa, ke dai jeki ki kula da mijinki, Allah ya yi muku albarka, ya dawwamar min da rayuwarku a cikin tsantsar farinciki". Amin ta amsa da shi tare da yi wa Ummin godiya ta juya ta koma ɗakinsu.

Kwance ta isko shi saman doguwar kujeran, ya ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya, ya zuba wa Tv dake manne a jikin bango idanu. Daidai saitin kansa ta zo ta sanya hannu ta ɗan ɗaga kannasa ta zauna tare da ɗaura kan nasa a saman cinyarta, juyo da kallonsa a kanta ya yi suna fuskantar juna. "Sister kinsan duk wani abu da nake so, Allah ya yi miki albarka, kina sanya ni farinciki sosai da sosai, ba abin da zan ce sai dai nayi ta yi miki addu'ar fatan alkhari".

Hannu tasa tana shafa face nasa, cikin sanyin murya ta ce "Yaya Nawid farincikin da kake sanya ni yafi wadda nake sanya ka, fata na dai Allah ya kare min kai a duk in da kake, Allah yasa kada wata mace taga kyanka sai muni, ya zamana ni kaɗai zan ga kayana" "Eyee wato ma dai addu'a kike yi na kashe mini kasuwa ko? To ban yarda ba, haka kawai? Ni bana so, ina laifin ki ce mata kyawawa zuƙa zuƙa kamar ke haka, guda uku su makale suce sai ni, ai kinga......." Bai kai karshen maganar ba ta rufe mishi baki da hannunta, a kule ta ce "Haka ma zaka ce?" Girgiza mata kai ya yi alamar a'a, tun da ba halin yin magana, ta rufe mishi baki.

Miƙewa ta yi tare da kwantar mishi da kansa a saman sofa ta nufi gado ta kwanta, irin ta yi fushin nan, da sauri ya miƙe ya bi bayanta yana ambatar sunanta, kin kulashi ta yi, ta yi kwanciyar ruf da ciki, tare da kwantar da kanta a saman pillow.

Saman bayanta ya haye ya kwanta tare da kwanto da kansa a saman kafaɗarta, murya a sanyaye ya fara magana "Haba my sweetheart, me yasa zaki ɓata ranki bayan kinsan wasa nake yi miki, nifa ke kaɗai kin ishe ni, bana son wata, please tashi kiyi mini tausa kin ji ko? Na tuba ba zan kara ba".

Ɗan ɗago kanta ta yi, da sauri ya sauƙa a kan nata, pillow ta ɗauka ta fara bugun shi da shi, tana kumbura kumatu, sai dariya yake yi gwanin ban sha'awa, shammatarta ya yi ya haɗeta ita da pillow gabaɗaya ya rungume yana dariya, shigewa jikinsa da kyau ta yi tana murmushi,. "Eyyee ranar nace kishi kike yi, kin ce ba haka ba, to yau kuma menene? Ko dai shi ma wannan ba kishi bane?" "A'a yaya Nawid, ba kishi bane, ni bana kishi ai, na gaya maka kula da kai ne, wai ka manta amanarka a ka bani ne?". Hancinta ya ja zai yi magana aka fara kiraye kirayen sallar mangariba, shiru ya yi yana salatin annabi yayin da ita ma take yi, sai bayan an idar da kiran sallah ne suka yi addu'a da ya kamata.

Sauƙowa kasa ya yi daga saman gadon ya nufi toilet dan ya ɗauro alwala, ita ma sauƙowa ta yi ta fiddo mishi da jallabiya, bayan ya fito, ya ɗauki jallabiyar ya koma toilet ɗin, jim kaɗan ya fito sanye da ita ya nufi masallaci, amma kafin ya tafi sai da ya manna mata hot sumbata a kumatu, ita ma ta mishi reply, sannan ya wuce zuwa masallacin, ita kuma ta haye gado ta kwanta dan yau bata sallah.

A ɓangaren gidan Abbi kuwa.

DADDYN JELLY & AYLA.

Wasa wasa laulayi ya kankama, kwata kwata bata cin wani abincin kirki, cikin nata mai mugun zaɓar abinci ne, ga uban laulayi, cikin ƴan kwanakin da basu fi biyar da bayyanar cikin ba, har ta yi wani uban rama, kullun sai kwanciya a kasa tana bin sanyin tiles, ba wan da bai tausaya mata ba, shi kam daddy ma ba'a magana, kullum yana tare da ita, da ta yi motsi zai tambaye ta ko wani abin take so, ya dai'na fita ko nan da cikin gida wajen su Abbi, babban abincin da ta fi ci a yanzu shi ne yalo, dan haka daddy ya jibge mata su dayawa a cikin fridge, da yaga sun kusa karewa, zai sayo wasu, yana ji da cikin nan nasa, yana ririta kayansa, dama ko ban faɗa ba kum sani, kunsan Ayla raguwa ce number ɗaya, yanzu ma ragwancin take zuba mishi ba karya, haka zai yi ta biye mata, dama da lafiyarta ma shi yake yi mata komai, ina ga kuma yanzu da lalura ta samu, ai sallah ne kawai yake barinta ta yi da kanta, sai kuma shiga toilet, amma harta kaya, shi yake sanya mata bayan ya yi mata wanka, ta dawo jaririyarsa da gaske, dan ma yana da ƙoƙarin yi, baya damuwa, har rama shi ma ya yi saboda wahalar da cikin nan yake basu, da kyar yake iya lallaɓata ta ci abinci, nan ma sai ya nuna mata zai yi kuka, da zarar


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login